Showing 261001 words to 264000 words out of 328222 words

Chapter 88 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

na fada maki ina son in fara sana,an kayan kitchen ne
irin na Fatiq .
Lokaci guda kawu ya debe hulan kanshi yanawa kansa fitara a hankali ga zufa
daya tartso mashi a goshinsa salima tana kallon ikon Allah don ita kadai ta fahinci
halin da kawu din yake ciki.
Jin yadda Mama din suke fafatawa da saratu yasa ya samu da kyat bakinsa ya budu
yana fadin dubu barinje sai dai kinjini kuma.
To yaya har zaka tafi kyale yaran nan kada ka daga hankalinka ga zancen nan don
Allah rashin hankaline irin tasu kawai sukeyi.
Ya dai samu ya fice daga gidan amma hankalinshi ba a kwance ba don yasan akwai
magana yau ko kaddaran da yake fadan ya saye baisan inda zaikai Yazid din ba.
Hana rantsuwa dai akwai wani fili daya saya amma karamine da niyar ya gina nasa
gidan na kansa su tare ciki da iyalinsa don wanan din da suke ciki ya tsufa sosai
gashi kuma nagadone da yan uwansu dake jahar Naije zaune saukin abin basu taba bin
ta kan gidan ba tun bayan rasuwan tsohonsu da aka dan samu matsala saboda makwabta
sun sheda kudin iya yafi yawa a gidan nasu dasuka gina lokacin.
Hakan yasa suka fitar da ransu ga wanan gidan harma da yan uwan nasu sai Jafarne
ma yake yawan maganan cewa zai kaisu wajen yan uwan nasu shi kuma jiki yaki lafiya
a yanzu.
Su din kuma ba wai damuwa da zuwan sukayi ba don kawu ya tsorata mama din akan
bin yan uwan nasu yace su din matsafane zasu iya tsafesu.
Iya kance komai tsafinsu kawu yafisu tsafi ai don zuciyarshi bata da kai zai
iyayiwa koma waye mugunta akan abin duniya idan ff,za,ff,fafamfaaftana masu
wraffada kalaminta ke nan ga dan nata.
Kwantar da hankalina da nayi yasa nayi fresh dani nayi kyau farina ya fito fili
da kyau idan kika dubeni sai kin koma ina zaune a falon ummah nida saudatu mun
na kallo da rana.
Ummah ta shigo falon ta zauna tana fadin Yanda ta kiraki na dago na dubeta
kafin na bata amsa da a,a take fadin munyi waya dazun take fada min cewa.
Mijikin yanzy ya koma abin tausayi duk ya kara lalacewa ya rame halama kamar
ciwonsa nason ya dawo mashi saboda rashin kullan da bai samu yanzu sosai dama kece
dai karfin jinyan nasa ai ?
Kaina kawar na mayar a tv ba tare danace da ita komai ba a lokacin saidai a
zuciyana na fada nakeyi ina fadin wanan shiya shafa a yanzu don sun fini sonshi ai
idan ya halaka sun huta don kowa saiya kama gabansa.
Haba dau uwata aida kinyi hakkuri kin koma Saudatu ke fadan hakan gareni da
sauri na juyo ina fadin in koma ina saudatu gara dai kowa ya taba yaji a yanzu ai.
Ba komai ya kawo hakan ba don itama maman tudu ta koma gida sati biyu ke nan
yanzu kingako inba iya ba a yanzu ba mai tsayawa ya bashi kulawan daya dace ?
Iyan kuma ba karfine gareta ba sai naji ummah tace mahaifiyarsu saida na juya
idon nake fadin in kawu ya bari ta zauna har ta kulashi ba ?
Ni dai sai ince auren ki da bawan Allah nan uwata auren kaddarane kawai amma ba
wani jin dadi ga hakan sai bakar wahala kana amaryan ka ko haihuwan farko bakayi ba
zaka tsaya jinya irin haka don Allah ?
Haba saudi ai hakan ma bautan aurene tasan irin ladan da zata samu a wajen Allah
jinya takeyi fa kuma na mijin aurenta.
Duk abinda kagani ya faru da bawa da sanin ubangiji Allah kadai ya san dalilin
haka ga bawansa Allah yasa hakan alherine gareta damu baki daya ummah ta katse
maganan da hakan duk muka amsa da amin lokaci guda.
Take fadin ni kingani nan saudi bawan Allah nan tausayi yake ban abu daine na
dan yau wallahi da yarinyar nan da daddy sunbi ta tawa datayi hakkuri ta koma
dakinta hakana .
Duk abinda zasuyi ko suce mata ta sharesu kawai ladanta yana ga Allah haka kuma
wata rana duk sai labari insha Allah don gaskiya mutumin nan yana sonta banga
abinda zata tsaya duban iskancin wasu ba dama su ba son ganin ki sukeyi tare dashi
ba ai.
Hakan da kikayi kuma ya basu daman samun kafan da zasuci gaba da musguna maki ai
mutum in makiyinkane kada ka yarda ya samu kafan galaba a gareka ?
Ina kurum ban tanka mata ba don nasan indon tasuce ita da yar uwata basuki in
shirya kwatsam ince na koma ba a yanzu din ba tare da anyi min gatan da daddy keson
ai min ba.
Ummah kodana koma wanan matar bawai zata canza halinta bane a garemu na sani
amma hakan zaisa na samu dan dama a wajensu ai.
Ita Yanda mijinta yana tsaye garesu shiko wanan fa ummah bai iya katabus ga
iyalinsa sai abinda tace dashi zaiyi haka kanninsa mata.
Saidai hakan amma dai gaskiya ya ban tausayi sosai wallahi zan samu lokaci ai in
kirashi mu gaisa inji yaya karfin jikin nasa.
To hjy idan kinyi hakan ba laifi bane amma ya kamata kowa ya sharesu nan yadda
suma suka share kamar basu damu da itaba yanzu idan kin kira zasuga kamar kina
bikonsune suzo nan.
Shiru nayi don gaskiya saudi ta fada ba karya a zancen ta don ko kowa bai fada
ba mama zata iya fadin hakan kuma naga zancen yayi tasiri ga ummah .
Don tace hakan ne kuma tunda matar ba mutuncine da ita ba ta fahinci hakan tun
haduwanta da Hjy Sa,a data hada ummah din da mijinta na yanzu da take aure.
Don yadda mama taso kushe abin sai Allah ya kawo ciwon Jafar na farko a lokacin
hankalinta ya dauke da jinyarsa har aka samu akai auren don hankalinta daya dauku
wai a cewanta ga kawu nan ya nuna yana son ummah din a lokacin.
Ganin yadda ya rame a kwanakin yasa mama din mayar da hankalinta gareshi saidai
tafi saka rai da fadan cewa saboda nabar gidan yake son ya halaka kanshi ga
banza ?
Har yakai ranan ya bata amsa da fadin mama koda tunanenta nakeyi ai hakan ba
laifi bane ki duba yadda aka barni haka ba gyara ba komai kamar mara gata mama ?
Ace Asmau bata da lokacina saidai kwanciya idan anyi magana tace aiki yayi mata
yawa a hakan kuma take son in barta ita kadai ba tare da wata ba ?
To ai tasan hakan ba zai yiyu ba ita dai waccan mara hankalun idan ta gama
shashancinta ai dole ta dawo a zauna tare ai yanzu tayi hankali hakan ?
Wa kike nufi yarinyar nan Rahama kowa iya ke tambayan mama din tace Rahama kuma
uwar yarsa dai ta dawo ta samawa yarta abokan shawara hakana.
Bako a gidan nan ba mama don na gaji da fitinan Saiba hankali a kwance yake
banson abinda zai raba min hankali biyu yanzu kuma.
Rahama dai nake Habu nake son ya dawo daga legos zuwa jibi inbi bayanta in
dawo da ita bakai kadai zaka tafi ba dole uwarku taje har yaran nan suyo maka bikon
matarka kamar yadda mijin uwarta ya fada.
Iya kikanso kamawa karya yanzu don ance sai naje shine zakice har dani zasu
tafi in yabi ta tawace ai ko zuwanma ba zaiyi ba shi balle aje zancen wai nima in
shirya inje din.
Anya biyu kina kaunar dan nan kuwa duk cikin yayanki na kula Jafarune baki damu
da damuwansa ba dubu ?
Yau da kina da tunane da yarinyar nan batakai wanan lokacin ba a gidansu zaune da
akace kece matsalan dake da yayanki da tuni kin tasa keyan yaran nan kun dawo mashi
da matarshi.
Amma da yake haka rayuwanki take kamar mara kwakwalwa Dubu baki san mutanen nan
tarko suka dana maki ba don su gaskanta abinda yarsu taje ta fada.
Ki barshi ya taka a hakan har kaduna tunda sakariya kike baki da lissafi kiga
abinda zai biyo bayan hakan a karshe.
Don ke da kanki zakiyi dana sanin rashin zuwa din duk ranan da tunane ya kara
turmuze yaron nan har ya kwanta a gidan nan don saura kiris a kai ga hakan yadda
yaron nan ya koma don tunane.
Matukar kika bari har ya taka yaje bikon matarshi aka hana masa ki saurari naki
bakin cikin da zaki tara akan hakan tunda yaran nan suna son junansu.
Har yanzu kina wani zancen wanan mara hankalin ta dawo ta dawo a yanzu tayi mashi
me yarinyar da bata san Annabi ya faku ba har yanzu.
Matukar Rahama taki daaowa gidan nan dubu bake ba harmu ga baki dayan mu sai
abinda zai biyo baya gidan nan ya shafemu kaf a gidan nan .
In kuma kince a,a kada kije tunda kece sauniya mara hankali kawai ina mamaki
matuka sauyawan yanayin ki dubu ?
A yanzu kowa ya zuba maki idone yana kallon wautanki dubu kinsan farin cikin
yaron nan kin kuma san komai game da hakan ?
Ke yanzu ba abin kunya bane a gareki dubu yadda kowa yasan zancen da irin
dawainiyar yarinyar nan a gidan nan kan yaron nan amma ace wai har kin yarda haka
ya kasance da ita akan yayanki.



ZAINAB IDRIS MAKAWA

MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

8️⃣2️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Ya kasance jumma,ace ranan hakan yasa nayi kwaliya na dan gyara fuskana duk da ba
inda zan fita don tun zuwana ban fita ko ina ba.
Duba ga zancen daddy a gareni hakan yass na kara kama kaina ko marmarin fita daga
gidan banyi dama ba gwanar fita irin haka baceni.
Wasu material da ummah ta saya min duk da nace da ita kayana suna nan banyi
amfani dasu bama a lokacin saidai hakan bai hanata ta saya min ba.
Suna dauko na saka ance yaba kyauta tukwici kayan sun karbi jikina sosai zaune
nake muna shan ferfesu kwatsan muryan salima ya daki kunnena.
Wani irin faduwan gaba ya ziyarci zuciyana lokaci guda a daidai lokacin data
tsaya kofan dakin tana kara kwada muna sallama akaro na barkatai ana kuma amsawa
tare da fadin tashigo mana.
Anty salima don har lokacin ina saya sunansu a yadda na saba kiransu dashi da
farko tashigo ta sauke idonta a kaina inda nake zaune kasa saman carpet tare da bin
plate din dake gabana da kallo wanda yake shake da koda zallah da saudatu ta gyara
muna.
A,a kune a tafe salima tace eeh tare muke gaba daya ai harsu yaya da mama jin
hakan yasa naso tashi a inda nake zaunen .
Saidai na makara da hakan don sun riga da sun fara shigowa falon ko da
sallamansu anayi masu sannu da zuwa tare da dan kauce kaucen abubuwan dake gaban mu
duk daba muni a cikinsa.
Saare da tayi zuwan dole tana ta faman mede muna fuska tana wani dube dube a
falon suka zauna kafin ta mayar da hankalinta a kaina.
Kallo daya nayi mata na fahinci ranta a bace yake wai ashe tun shigowansu
kaduna ta soma fadin amma mama yakamata mu leko su mami muga lafiyansu.
Shine ya yazid ya bata amsa da fadin ke saratu nan makirace watau kin kulla
gulma duk wanda kikayi a waya bai isheki ba sai kinyi na face to face a gabanta
toba zamuje ba din din ba shi ya kawomu ba .
Saratu ai zaki iya sauka ki karasa idan kin gama saiki samemu mami kuma idan
suna son mu ganta ai sunsan hanyar gidan mu ko ?
Yatace mami amma bakin jinin dake zuciyana na uwarta ya sa a yanzu har ina
mantawa da ita a yanzu daga inda mama take zaune ta sake wani sallati tana fadin
subbahanallahi kanka daya kuwa Jafar kake fadan haka ga yarka.
Yarkace fa koma me uwarta tayi ma karka manta yarkace ai dinshi nace ina mantawa
dasu a yanzu ya sake fadan hakan.
Ita kuma mama sai cewa tayi lalai kanka ba daya bane Jafar na yarda akwai
abindake damun kwakwalwanka a yanzu to sai ita,,,,
Haba dai dubu don yaron nan ya fadi haka ai kinsan bacin rai yakaishi ga fadin
hakan ku bar wanan zancen tunda ransa har yanzu a bace yake game da yarinyar nan
Nusaiba.
Ai don jan magana munafukar nan ta dauko zamcen Nusaiba din don irin haka tunda
tasan abinda ya kawomu garin nan .
Tasan ba wurin Nusaiba muka zo ba munzo bikon yar mutunci da sanin ya kamatane
wacce tasan metakeyi ba wace son abin duniya ya dama ba Yazid ke fadan hakan.
Wanan abinda yazid din ya fada shine yasa ta shigo gidan tana fushi duk gaisawan
da saudi ke masu fuskanta a daure yake ita.
Kafin komai har saudi din ta cika masu gaba da abincin karyawan mu da akayi
hakan ba karamin daukaka saudi din ta ja min ba duk da sunsan ba gidan ubbana bane
nan din amma ko hakan yayi min dadi har cikin raina.
Mazan suna waje basu shigo ba daddy ya fito suka gaisa dashi shi yayi masu
jagora zuwa cikin gidan nasu inda suka samesu a falo suna karyawa nan yazid ya hau
masu sheri da sunshigo sun buge da cin abinci.
Saudatu ce ta shigo take fada min yaya Jafar dashi akazo yana nan yana baza
ido yaga ta inda zan fito a gidan ai sai ya matsa na fada ina tsuki.
Uwata ba aiwa miji tsuki haka don shiryawa zakiyi da abinki adaiyi hakkuri din
bawan Allah nan yana kaunarki matuka ki duba yadda akazo dashi a daddafe haka
daganinsa har yanzu yana jin jikinsa.
Amma ya taso saboda ke zuwa nan don Allah ki sassauta mashi kinji kada kice ba
zaki bishi a yanzu ki koma dakinki hakana kinji ?
Daidai lokacin ummah ta shigo ta samu tana fadan haka sai cewa ummah tayi gara
dai ki fada mata donni banga laifin wanan mutum ba.
Kada fushin daba nasa ba fushin yan uwasa ya debe maki ladanki ga banza saboda
kawai suga kun samu barka dashi suke fata.
Saudi ta kara fadin shiyasa nake bata shawara ta koma idan an shirya idan anji
abinda ya kawosu sai kiyi hakkuri don Allah ?
Muryan Abba daya dawone yake fadin ina ummah yasa ta fito falon aka zauna naji
falon yayi shiru iya ta soma magana tana fadin to Alh .
Kamar yadda nayima alkawarin dawowa gashi Allah ya dawo damu cikin ikonsa tare
da iyalina da kowa don muzo muyi bikon yar wajenka da fatan an huce zuwa yanzu ?
Don Allah ayi hakkuri wanda yace zomu zauna kamar yace zomu sabane sai an hada
da hakkuri zama ke dadi in sha Allah abinda ya faru da farko ba za a sake
maimaitashi ba in sha Allahu.
To hjy naji aimu ba fushi mukayi ba kun sani illa iyaka so muke a tsawata akan
abubuwan cin fuska da izigilanci da akewa yaran nan yayi yawa.
Ina son ku gane bayin yaran nan bane gaba dayansu kaddaransuce hakan aure a gida
daya hakama yaran ku maza suma hakan tasu kaddarance tazo a hakan.
A zatona yau duk wanda yaso naka haka yagama dakai a rayuwa ba sauran zargi ko
wani hasashe ga wanan bawa ko don alherinshi gareka zaka daga mai kafa ka kawar da
kai ga duk wani abu tunda yaso naka tsakani da Allah.
Ayi hakkuri don Allah a zauna da juna a cikin mutunci sai aji dadin juna a gama
da duniya lafiya ga zuwairatu nan a gidan nan ba haihuwa tayi damu ba amma ta kama
kan diyan nan ta hade min kamar itace ta haifo abinta.
Tsohuwa meyafi wanan farin ciki a wajena yau na samu macen data san darajata
data yayana tasan zafinsu tankar itace ta haifesu yanzu haka saisu shigo gidan nan
suyi shawara da ita ba tare dana sani ba wanan ai kwanciyan hankalina ko bana raye
a duniyan nan haka yan uwana kaf dinsu kowa na zuwa gidan nan yanzu ta dalilin
wanan macen da Allah ya ban.
Don haka ni a ganina wanan abin farin cikine yau a gareku don duniya ta sheda
yarinyar nan bata bar mijinta a wullakace ba daidai lokacin da yake bukatan
soyayyan na tare dashi.
Duk wanan bayanjn da Daddy yakeyi saratu sai wani harare harare takeyi tana
yatsunan fuska tana basarwa tana nuna maganan zucin da takeyi a fili.
Ba daddy din ba duk wanda ke falon ya kalketa yasan abinda take nufi da hakan
mai karatu ba saratu bafa har mama dake zaune irin shigen wanan yanayin take itama
a lokacin.
Yazid ne ya karba da fadin Alh munsan kokarin Rahama a gidan mu duba ga yan
kwanakin nan da bata gidan bashi da yake mijinta take jinya ba kowan mu a yanzu ya
fahinci ranan ta a tare damu.
Kwaraima don wallahi ba sai an fadi ba mutum ko yaya yake ai rana gareshi ba a
sani kuma sai ranan daya bar wajen za a gane hakan.
Balle yar nan data zama tauraruwar gidanmu a yanzu ta share ko ina tas ba
kyashi ba hassada kafin gari ya waye tayiwa mijinta komai saidai a zo a sameshi a
gyarensa duk wake hakan ita ?
Yanzu fa Alh yaron nan sai yabaka tsusayi kamar ka zubar mashi da hawaye don wani
abin yana so ba,,,,,,,,,,,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login