Showing 312001 words to 315000 words out of 328222 words
Chapter 105 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
gidan nan ai
kila mama sai ta kusa bugawa.
Kinsan me Rahama nace a,a anty wallahi ni abin mama yana ban mamaki yau idan
ance meye laifin ku dasu yaya ba zatace ga aunihin abinda akai mata.
Shiyasa nake ganin laifin saratu don harda saratu cikin mayar da mama hakan itace
mai zuwa ta fada mata karya da gaskiya kan mutum yanzu ai gata can tana girban
abinda tayi amma mama bata son a fadi hakan.
A nan na fahinci saratu tana cikin wani hali a gidan aurenta haka kuma mama na
kokrin boye hakan saidai salima din ban sani ba koni kadai take fadawa zancen oho ?
A nan takai magariba bayan munyi sallah ta nufi gida mama tana ta fada da ita
akan tayi dare haka da subar barin dare nayi masu a waje.
Nayi mamakin rashin shigowanshi ranan har goma na dare wai gashi tun safe daya
shigo bai dawo ba hakan ba dabu,ansa bane sau ukku yake ziyartan mu a rana idan
yana gari.
Ashe a ranan suka kwashe ana can ana rikici a gidan don yana komawa yaje da mota
yacewa Asmau ta fitar da duk a binda zata dauka a gidan.
Ya wuce wurin mama ya sameta tare da iya suna magana kan saratu nan ya shigo ya
gaidasu yake fadin to mama yau nake son Asmau ta koma wancan gidam dana gina guda.
Cikin mamaki mama din ta dago tana fadin gida wani gida yace aina jima ina gina
sa an gama komai dama can kusa da habune da yazid wajen kamar unguwa dayane dai
zance.
Jafar ni kake fadawa ka gina gida zaka dauki matarka daga gudan nan zuwa can kan
dan zancen da akayi ya wuce kai yana a ranka ashe har yanzu ?
Wani zance kuma ni ai nagama wanan maganan a bamgarena dama ina da niyar hakan
kudine da bandashi lokacin ban gama saka wasu abubuwa ba yanzu kuma na saka shine
zasu tare a ciki.
To ban yarda ba ba inda zaku idan kaga Habu yayi na kyaleshi kai ba zan kyaleka
ba Jafar don baku isa kuce zaku raba gida dani ba matukar ina raye.
Kamar ya mama nan din fa karki manta gidan gadon mune namu dukka da yan uwana
can ko nawane dana ginasa da kudina don iyalina .
Kwarai kuwa shi muke fata hakan Allah ya kara arziki da rayuwa mai amfani yasa
afi hakan kowa na fatan hakan a rayuwansa da zuri,ansa baki da hujan cewa ba zai
daga daga nan ba yanzu dubu.
Duk yadda akeson biyayya dan nan jafaru yayi maki shi a rayuwansa don haka ban
son in ji ko in gani cewa kin kara tofa mashi kalman baki yarda ba.
Da bakin ki nan gaban mutane gaban kowa kikace saidai ya bar gidashi amma ba
sarakuwarki ba yar so a gareki yace ya yarda yanzu zakice kuma bai isa ba ?
To iya ana son a nuna min iyakata ke nan da ban isa dasu ba yanzu tunda sun
girma suna ganin sun kai iyan tace na dai fada maki kar inji kar in gani duk kika
tofa wani kalma akan zance irinsa zai biyo bayan ki dubu.
Tabbas idan naji kona gani kinsan zancen kema don haihuwa baifi haihuwa ba dubu
kin tauye yaran nan dayawa dubu tun suna maki biyayya yadda akeso har yanzu yakai
sun daina suna ra,ayin kansu tunda sunkai mutane suma ?
Kuka sosai mama keyi saida iya tace tashi kaje Allah yasa ku shiga a sa,a nina
taba ganin haka danka ya samu karuwa irin haka ke mahaifiya kice ba a isa ba ?
Yau ko kango mutum yana son ace ga nasa balle ke da Allah ubangiji ya yayi maki
Rahama ya fida diyan ki cikin yan uba kece kuma da kanki kike son ki bata abinki
yanzu da hannun ki ?
Iya ba hakana bane koda nace su zauna nan don hadin kansune ba don komai ba amma
tunda hakane ai shike nan suje Allah ya bada sa,a .
Ya daga yana fadin mama kiyi hakkuri ni dama ina da niyar hakan wallahi ba don
zancen nan nayi haka ba tsawa iya tayi mai tana fadin jeka nace ubangiji Allah ya
tsare mun koma godewa Allah daya nuna muna hakan gareku tun muna raye.
Yau idan mahaifinku yana rayene akwai wanda ya isa yayi maku wanan rayuwan
tauyewan da ake maku yanzu komai yaro zaiyi naci gaba sai a hanasu ?
Haka ya mike yabar part din ya samu samari nata daukan kaya suna fita dashi yace
ke banda tarkace ba zan yarda yadda kuka bata nan ku bata can ba yanzu iya kayan
amfaninki dana yara kadai zaku dauka wanan tarkacen duk ku barsu nan.
Yayi mamakin rashin ganin Saiba da baiyi ba ashe ta fita zuwa unguwa har aka
gama bata dawo ba sai bayan tafiyansu kadan ta shigo gidan tun a waje take ganin
tarkace hakan ya bata mamaki ta karasa ciki da mamaki a fuskanta zuwa cikin gidan.
Ba kowa a waje nan ma tayi mamakin ganin falin a hargitse haka tadai shiga ta aje
kayanta ta fito tana kiran Asmau shiru da taji ta koma kiran yara shima shiru
hannun yarta ta kama zuwa part din mama.
Mace kadai a lokacin gidan Salima tana gidan mu iya kuma tana nata wajen taki
fitowa tunda ta gama magananta a lokacin.
Mama lafiya ina Asmau na dawo na samu waje a hargitse haka wani abu akayine
bayana kuma ban sani ba ?
Da kyat mama ta iya bude baki tace Nisaiba ni Jafar zai nunawa iyakata da nace
ya bar gidan ba zaki bari ba shine yau ya dauki Asmau wai ashe ya gina gida tun
tuni ban sani ba ?
Kam uban nan ya dauke tafa mama wallahi sunyi kadan dagashi har ita sunyi kadan
wallahi duk inda suka koma nima zan samesu yau din nan me jafar yake nufi dani .
Harta juya zata tafi sai kuma ta juyo tana fadin koma meye mama laifinkine na
nuna maku so da kauna an hada kai dake an cuce yan uwana basu fadi karya ba kece ke
amfani dani bani ba ?
Nisaiba kanki daya kuwa tace kwarai kuwa nagane kinyi amfani danine don wata
manufa taki ta daban mudfin aure na ya mutu mu zuba auren kowa ma zai mutu wallahi.
Ta juya zata fita suka hade da kawu kamar zata bangajeshi ya kauce gefe daya ya
bata waje ta shige shi ya bita da kallo yana mamakinta.
Kawu ya karasa falon yana fadin wai gidan nan lafiya meke faruwa naga duk gidan
a hargitse yaya iso dolene kaga gidan haka hargitse yaran nan sun gama dani kuma
iya ta hanani daukan mataki ?
Meya faru ni baki fada min kina kawo min zancen iya to zance iya mana wai
Jafarne ya dauki matarsa uwargidan suka bargidan nan kamar yadda habu yayi a baya ?
Suka bargida ya koma ina gidan haya ko can inda ya aje wanan yarinyar ya kaisu
aida canne ban mamaki haka yaya ?
Gidafa jafar ya gina ban sani ba kamar yadda Habu yayi min sai daukan matarshi
su tare kawai naji zanyi magana iya tace ban isa ba ina na fito yanzu yaya abinda
iya keyi min kan yaran nan yayi daidai ke nan don Allah ?
Zaudowa yayi zuwa bakin kujera ya dubi yar uwar tashi yace yanzu shi jafar yana
da kudin gina gida shine ya bari dan uwansa mara mutunci na kokarin daureni gidan
yari !
Haba yaya kasan bakinsu daya na yarda bakin su daya shike nan ni Dauda yaran nab
duk sun bata min shiri kaiya bukata bai biya tako ina je nan ?
Bukatan me kuma yaya kedai bari Dubu bar zancen kawai shike nan ai komai ya
tafi yanzu bar wanan zancen kuma yanzu ina jafar yake ?
Sun kwashe ta fada a sayayye cikin bacin rai sun kwashe fa to ita wanan data
fita yanzu kamar zata bangajeni fa ?
Ai kasan ya furta saki a tsakaninsu nace ta zauna shine yabar min ita nan baije
da ita ba yanzu ta dawo take masifa kasan bata da kwanciyar hankalin fahinta.
Naso ince ki rabu da ita ki kama wacan yar fulanin muyi makami da ita a gareshi
yanzu tunda wanan din ta koma bata da fada wajenshi a yanzu bata da sauran amfani a
garemu.
Muryan wa nakeji kamar na dauda muryan iya ya katse masu magana iya nine
shigowana ke nan yanzu nake zance naje na gaida ke ai.
A,a ina zaka gaidani kana nan kuna kulla shu,umancin naku da bansan sai yaushe
zakuyi hankali ku daina bibiyan yaran nan ba tunda ita uwarsu ka gama da ita dakai
da matarka.
Iya mungama da ita kwarai kuwa ko kana zaton ban sani ba ita din yar uwarkace
dauda duk surukullen da kaiwa dubu ya hau kanta yar uwarkace dai kanka kayiwa.
Godiyana ga Allah dana yaran nan baiyi tasiri ba kun halakata kun koma kuna neman
halaka mata diya koka dauka duk dadewan nan ban sani bane ?
Nasan komai dauda ina kuma kai kukana ga Allah ganin na yaran baiyi tasiri ba
yasa kaga na sakama ido kuna ta bace nasan mai hansatu takewa kuka lokacin daka
kara mata kishiya ai ?
Shiru yayi iya ta zuba ta zuba yana zaune baice komai ta kare da fadin dauda na
dade da kumsan bakin cikin ka a zuciyana sai ince ni banga amfanin haihuwan da
namiji a rayuwata ba don hansatu ta shiga ta fita ta rabaka da kowa naka a duniyan
nan.
Ni kuma na dade ina kai kukana ga ubangiji Allah ina fada mashi damuwata akanku
har gashi yau kana fada da bakinka komai yana da iyaka banda ikon Allah da
manzonsa.
Tana fadan hakan ta juya ta fice takai kofa take fadin Allah yasa yaron nan
yazidu ya daureka a kotun nan dan makulin ya bace ka mutu can dan banza mara imani
ka halaka kanka ka halaka yar uwarka saboda macen macen ma figgaga kamar hansatu
wai daba gaba ba baya.
Kun gani ai dakai da ita kaso diyan yar uwarka su tabade kamarka da Allah yafiku
sai yabaku tambadadun diyan ku ya shirya mata nata.
Tasa kai ta fita ta barshi yana hawaye sai mace da bata san kaiba take fadin ni
iya fadan ta yakan ban mamaki wani lokaci bata barin mutane suji da abindake
damunsu a rayuwa.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/11, 06:34] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
9️⃣7️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Tana kwance aka fara dukan kofan da karfi taki budewa sai maishi ya wuce taja
tsuki tana gyara kwanciya.
Ba,afi mintuna biyu ba taji bugun kofan dayafi na farko karfin kara a kunnenta
hakan yasata magana tana fadin wai waye don Allah zai fasa min kunne ?
Ke ki bude da wullakancin banza ke shige daki kin kyale mutane ana buga kofa
konki ki bude jin muryan minjinsu yasa ta mike da kyar ta bude kofan dakin.
Ya fado ciki kamar an turoshi daga waje yana fadin wane irin iskancina yasa
kinka hitowa a dora girkin abin kari dake ?
Ke shige daki keyi kwanciyanki kin mike kafa wa kika son ya dafa ya baki kici da
kinkaki hitowa a dora girki ko wa at bawanki gidan ga ?
Nagajine Habibi nagaji wallahi ke dakata min don Allah ke gaji ba aure kin kazo
yi ba ke nan koso kike ki kwanta daki ki mike kafa a girka maki keko ki kwashi gara
daga kwance ?
Habibi nifa ban saba da irin haka ba a gidan mu wallahi ban girki sai naga dama
kuma baifi gwango biyu muke girkawa ba sai taliya da indomei ko macaroni.
Kina mace kika rakin girki ashe saratu baki shiryawa aure ba kin kayi an fada
maki zuwa dai akai aita harkan gado baci waka baki abinci kina kwance ?
Nifa habibi gaskiya ba zan iya ba don wallahi,,,, dakata min don Allah ba
habibiba wallah habibu in kina hitowa kitai girki yara suna jin yunwa ki hito ?
Wallahi ban iyawa ta kara fada tana juyawa yace haka kinkace baki iya girkin
tace gaskiya indai wanan girkin gandune ba zan iya ba ?
Wai baku hitowana kaje ka zauna kana rarashinta a daki kunyi bukui cikin daki
wa zaku kawowa bulunkoto a nan ka shiga kana rarashinta akan ta hito wa kunka aje
bawanku halan ?
Duk yadda ya raya saratu taki fitowa dakin jin muryan uwargidansu da tayi a
kofan ya kara bata haushi mata yar tsurut da shegen doka ga iya kissa da kisisina
irin na mutanen hausa.
In an barta sai tace itace uwar yan daudun duniyan nan kaf saboda marmadin ido
da iya tafa hannu idan tana magana baki magana hannci magana ido magana.
Bayan fitan mijin taji muryan uwargidan tasu da ake kira da nunu tana fadi a
cikin fada taki hitowa ko to walle mu zuba da ita a gidan nan wa taka son ya girka
mata taci ?
Ko wa a bawanta gidan ga ta iya shigewa daki ta kwana da miji a girka mata yanzu
aiki yazo kanta tace batayi asheko zakiga iskanci a gidan ga walle ?
Ta mede baki tana zama bakin gadonta cikin takaici da dana sanin auren mansur da
tayi inba don sulaiman daya taudareta yayi ta amfani da zuciyarta yaki aurenta ba a
karshe da ina mansur zai ganta har ya kwasota zuwa nan ?
Dama ance rabu da bakauye iskanci da duniyanci yana wurin bakauye tundai in
yana ganin ya fara wayewa sai abin ya hade mashi da wawanci yayi ta abu ba fasali.
Bata fito ba tana jin hayaniyan yan gidan har barci ya dauketa sai wajajen sha
biyun rana da yunwa yacita ta fito don ta samu abinda zataci.
Saidai ta kula duk dan data kira donta aikeshi sai yaro yaki zuwa don uwayensu
sun gargadesu akan hakan sai wani saurayi ta samu maraji yaje ya kwaso mata indomei
tazo ta sullala saman gas a kuryan daki taci.
Jin kamshin indomei din da matan sukayi kuma yasa yan gulma samun uwargidansu
suka fada mata ita kuma ta samu mijin da sababi duk ya rude irin matan nan ne dake
kammala mazajensu sai abinda sukace gata dai bakauyace amma miji idan tana magana
har rawa jikinsa keyi wajen bin umurninta.
Shi kuma ya taso ya samu saratu din a daki da fada kan don me zata dora girkinta
daban suba haka sukeyi a gidansu ba ta fito ayi aiki da ita yadda kowa ya fito a
girka a zauna aci a cikin taro.
Wanan halin yasa bata ko iya loma ukku da anfara zata mike tace ta koshi ita dan
dama ranan da miji ke dakinta inyaci ya rage takan samu taci itama a lokacin.
Ga wata rayuwa ta daban da sukeyi keda miji ke wajenki ba zakiyi girkiba a ranan
sai wace miji bai dakinta itace zata girka abinci ta ciyar daku.
Gashi kuma mata sunkai goma sha tara duk girkinsu a hafe yake mutum ukku ulku ke
girki a rana su ciyar da gidan yadda suka tsara kuma komai da za ayi wajen uwargida
ake karban komai itama hannun uwar miji zata karboshi.
Irin wanan rayuwan na daban yasa zaman gidan ya karawa saratu kunci tayi tayi ta
daure ta kasa hakan wata rana da dare bayan isha,i ta hada kayanta a dan karamin
bag dinta makwabtansu takai ajiya.
Washe gari ana fitowa sallah tayi kamar zata kewaya ban daki ta aje buta ta fice
sai wanan gidan ta ari nikaf ta rufe fuska tana zuwa bakin titi ta samu mai acaba
ya kaita tasha zuwa garin sokoto tashiga mota ta nufo sokoto inda zata samu motar
zaria.
Don tayi kiran mama don su kawo mata agaji ba abinda sukayi kullum magana dayace
mama tace mata tayi hakkuri tana tafe an amma shiru.
Allah ya gani tana son habibi shima haka amma yan uwansa da matansa sun bata
masu shiri don a gaskiya idan tace zata daure tasan karshe zata halaka a wanan
gidan.
Don aiki kawai zai kasheta gashi bata saba hakan a gida mama tudu in tazo ko
sukaje family house daniyar kwana biyu tankayi fada da mama tace ba aiwa diya mace
wanan sakacin don ba,asan inda aure zaikai mace ba gashi ko bakinta ya kamata don
ga inda aure ya kawota yanzu.
Salima da tayi mutuwan tsaye don mamakin kalaman da take ji bakin kawu yasa ta
koma da baya zuwa part din iya.
Ta kwashe ta fadawa iya shine mafarin tasowan iya tazo ta samu kawu tayi mashi
tas barci ta kasa kwanan ba haukan Nusaiba ya hanata barci a lokacin.
Sai zancen da take ji yana fita bakin kawu din wanda da alama kuma uwarsu bata
damu da hakan ba kamar ma bata gane manufarsa ba take gani.
Allah Allah take gari ya waye taje ta samu yan uwanta ta labarta masu komai sai
da tagama komai ta shirya batacewa kowa komai ba ta fita daga gidan .
A waje ta ciro wayanta cikin jakka ta kira lanban yayanta tayi sa,a ya dauka yana
fasin Salima yaya akayi ?
Kana ina yaya gani nan zuwa wajen ka ya amsa da gani nan zanje gidan Rahama in
dubasu lafiya dai ko ya tambaya ta amsa da yaya bari dai inzo akwai magana