Showing 120001 words to 123000 words out of 328222 words

Chapter 41 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

tsoro Rahama aita magana kina zaune baki furta komai
wanan wace irin amaryace wai ?
To na dai bada dinkunan ki da zakiyi amfani dasu idan kinje kada ki fara idan
kinje kice zakiyi amfani dako daya daga cikin tsofin kayan ki da aka sanki dashi
gidan nan.
Haka kuma kada ki yarda ki zauna gida ba kamshi ko jikin ki kwaliya ko baya
gari ki kasance mai gyara Rahama don yana daga cikin abinda mazan yanzu ke so
gyaran jiki.
Abinci kuma nau,in daban daban zaki dinga dafawa kada kiyi rowa Rahama don haka
duk wanda zaizo gidan ki ya kasance kin dan bashi wani abin sakawa a baki don
Allah.
Ban son ki da dogon hurda da kowansu a yanzu don kada ki yarda dayansu tace zata
shige maki ki yarda sam irin hakan yana kawo matsala daga baya don haka ki kama
kanki da kowa don Allah.
Gidan ki babbane amma akwai maigadi kina kuma da makwabta makwabci ba kowane kake
saurin yarda dashi ba balle nasan baki da matsala a wanan wajen don ke din kurace
dama baki da saurin yarda da mutane.
Rahama don Allah ki sauke komai a zuciyar ki kiba mutumin nan sallama abinda ya
kawoshi gareki ke nan neman rayuwan inganci kada ki yarda a samu matsala a wajen ki
Rahama.
Kin daiji abinda mama ke fada muna kullum kada mu yarda mazajen mu su kuka damu
a zuciyarsu idan muna son riban aure.
Maza tankar magene sunfi taushi a inda aka san darajansu ko mutuntasu bawai
ladabi da biyayya kawai ke kai mace da zama mowa ba sai mace ta iya kissa da na
kwatar miji maza suna son haka kin dai gani da Alan,guguro yadda sai nayi dakyat
yake barin gidan nan mu din kada ki manta da rainon mamace fa.
Ya kama ace tun akan mama mun koyi rayuwa basai wani ya tsaya yi muna nasiha
irin haka ba don mama a gaban mu kike ganin yadda takeyi da daddy bata hada komai
da daddy ba a duniyan nan.
Shiru nayi har ta gama ina saurarenta ni ina zan iya wanan abubuwan ga Jafar
mutumin da ban wani saba dashi ina ma nasan abinda yake so da wanda baiso ?.
Nikan dai ganinan zaki iya kirana da amaryan danko amaryan da aure yanzo mata
kwatsam ba shiri shine wai ake so kuma naje na ririta mijin a hakan ?
Kumshi ni kaina naji mamakin yadda kayan hadinshi ke kamshi kai mutanen
maiduguri Allah ya hore masu sanin sirin kamshi a rayuwansu.
Wallahi tun kamshi na damuna har nazo na saba don dole na wanka daban dana fito
ga na tsuguni yana jirana haka za a yafa min wani bakin zani na zauna sai na bushe
a hakan.
Ina mikewa zata ban wanda zan fara murzawa a matse matse da kataruna hardasu
hammata ni kaina saida na koma kamar zanyi kuka wani lokaci har kai akwai wanda
tsohuwar zata rufe iya kaina da kasko tana turaramin kai in gajarce maki jin kaina
nake kamar bani bace tundai da akai min gyaran kai din.
Inda sumana na fulan ya samu gyara yayi baki wulk dashi sai kamshi ke tashi ga
wani kasala dana zauna naji sanyi yanzune zan fara gyangyadi a wajen.
Zan iya cewa Alhamdullahi Alhamdullah gaskiya dan irin ni,iman da Allah yai min
lokaci guda na fahinci gaskiyan maganan da hausawa keyi na dare daya Allah kanyi
bature wanan gaskiyane hakan.
Cikin dan taki ubangiji yai min wani irin baiwa da ban taba sanin ina dashi ba
sai a wanan lokacin gidan daddy na kwana ana gobe zamu tafi nan mukayi wani ganawan
siri da mama da anty Salma mu biyu irin abinda da suka fada min a ranan yasa na
kwana gabana yana faduwa.
Washe gari da wuri muka dauki hanyan kaduna cikin tsalalun motocin gidan daddy
dana mijin anty Salma mota hudu mukai tafiya dasu zuwa gidan mahaifiyata kaduna.
Bisa rakiyan mama da yan uwa da abokan arziki data fadawa ni din yar dan uwansune
daya rasu yabarmu .
Manyan mata kanuri mazauna Abuja su shidda sai kawayen anty salma da ita kanta
sune sukayi min rakiya mun sauka a gidan ummah anyi walima .
Ni saida naji mamakin ummah ta waye ta zama yar kaduna a haraban gidansu akai
walima ana gab da tashi saiga dagin ango sun iso suna bada hakkurin makaran da
sukayi din.
Wai ashe sai a na gobe yaya habu ya fada masu zancen tarewan wasu ma a ranan
sukaji amma sunyi kokarin zuwa din duk da saida akai dan rigima don mama ta hau
kawu ya samu ya lalabata tabada bakin azo din daga nan a dauki amarya.
Nafisa tace yanzu mama tana can ta hake sosai taga inda za a ajekine Rahama don
basu san da zancen gidan ki ba sai idan mun koma ko innata ban fadawa ba kinsan
inna da surutu.
Nayi murmushin yake zakice ba wani abu mai muhinmanci muke tataunawa ba da ita a
lokacin don ko motsi banyi ba ina kallon yadda suka zuba min ido suna kallon
sauyawata lokaci guda haka.
Anzo da Salima da Saratu da sauran yan uwansu da suke uba guda karfe hudu bayan
anci ansha aka dunguma zuwa zaria wajen kai amarya .
Koda muka isa direct family house dinsu muka nufa saisu mama muka sama a gidan
duk da gwargwado dangi sun dan taru lokacin.
Wai mama tana can gidan Iya ita da wasu na kusa da ita nayi mamakin ganin harda
anty Barakan zamfara ta samu zuwa bukin donni ban zata zasu yi hakan bama sai ina
ganin komai makare akeyinsa ai.
Hjy Yabi yar uwa kuma kawa ga mama tace akwasa a sameta can gidan daga nan a ba
uwargidayena girman su kusan magariba muka kwasa zuwa gidan .
A falon iya aka taru aka shiga gaisawa mama tana kallon bazata ko hajiyoyin ai
abin kallone da kawayen salma.
Taji mamakin ganin Salma nayi min yare ina dan amsawa a cikin kanuri iya sai
haba haba takeyi damu tana kokarin ganin fuskana na boye.
Tace yar fillo wayau kikai min haka kika kwace min angona ko da ina da ja amma
yanzu na sake ance mai waje yazo mai aro ya tashi don haka nasake na barki da Jafar
na kara noke kaina kasa cikin kunya.
Hjy Yabi take tambaya ina kishiyoyin nata suke sai matar kawu ke fadin suna
bangarensu ya fada maku inda za a sauke amaryan ?
Basu fahinci me take nufi da zancenta ba hakan yasa sukace a gidanta mana ko ko
a wani wajen ake fara sauka don su basu sani ba ko ana wani al,adane a nan ?
Au ashe ya fada maku inda zaku ajeta din ai shike nan idan mun tashi daga nan
gidanta zamu wuce da ita ai dama mama muka biyo nan din mu kawo mata amarya anty
Salma ta fada.
Basu wani tsaya ba suka mike duk da lokacin sallah yayi muka kwasa zuwa part din
uwayen gidan nawa matan yaya jafar.
Da irin kudansu na kanuri mai kada zuciya ya yamutsa hankalin wanda akaiwa
girshi muka nufi part din matan yaya jafar din.
Zakice basu san da zancen ba suna falo dukkansu muka shigo ita Asmau wani rigar
abayane a jikinta sai ita saiba data saka wasu lace haka baki da adon golden
jikinshi.
Asmau kan tayi muna sannu da zuwa amma ita saiba ko kallo bamu isheta ba ba wani
dogon gaisuwa hjy yabi ta fara fadin amaryace muka kawo kamar yadda al,ada yake .
Da fatan samun zaman lafiya a tsakanin ku kuyi hakkuri da junan ku a zauna
lafiya kwarai kuwa inji matar kawu ta dora da fadin amarya aiba bakuwarsu bace sun
santa ta sansu.
Matar kawu karma tazo da zaman lafiya mana mune dai ba wasu ba ai ta san mu mun
kuma santa sai a dora inda aka tsaya.
Mikewa anty salma tayi tana fadin su tashi zuje kada dare yayi muna aka barta
nan tare da wasu yan gulma tana fada kamar karya.
Bamu koma dakin iya ba muka nufi wajen motocinsu muka shiga ni dai kaina na rufe
gwaggo Yatu najana duk abinda akeyi dai ina jinsune.
Muna zama motan naji an soma fadin wai dama basu sanda zancen gidan bane anty
salma na fadin bar yan iska idan basuyi hankali ba mace gidansu zata kwana ai
wallahi.
Sai gudan su hjy yabi ke tashi da karan motoci muka bar gidan na sauke ajiyan
zuciya ina dan bude fuskana anty salma na fadin akara fesa turare wai zarni falon
su Asmau keyi yasin da kyat idan batayi amai ba lokacin.
Tare da matar kawu aka zo kawoni gidan dasu inna da anty Baraka basu jima ba
suka tafi nan muka samu su Salima da Nafisa da maria an kawo abinci da abinsha kala
kala gidan don taron baki wanda salima da Nafisa suka kai kwangilan dahuwan don
fita kunya.
Hjy Dubu yaron yau kaji tsoronsa kinga gida hjy dubu gida ai iyakar Aljannan
duniya ke nan wannan gida ke kinga gida kuwa ?
Kai lalai dan yau ka barshi inda ka ganshi ni sai ince wanan abu an dade ana
shiryashi mune dai aka rufewa hakan.
Kya fada kema hafsatu aisu salima na can ana sakin hanci kiji wai kamshin yar
nan har yanzu dakin nan keyi don Allah kamar tana zaune wajen nan.
Ga dai magana nan yana fitowa fili shine za ace wai a kyaleshi kada ai magana
kada zumunci ya lalace zumunci ya dade bai lalace ba ya fito muna da hakkin mu ya
bamu abin mu.
In ma ya kama a saida wanan kayan karyan da yayine a sayar abawa kowa hakkinsa mu
rike abin mu ai abin yayi yawa wallahi.
Barshi kawai dai Allah ya kawoshi lafiya ai yazo yai bayani zamuji mai zai fada
iya dake addua ta shafa ta juyo tana fadin.
Kaiya Hafsatu shi babba gyara aka sanshi dashi ba barna ba kina fadin zancen nan
kawai don ki tunzara yar uwar mijinki ta saba da danta.
Baki tunanen kema kin haifa ai hafasatu na rasa dalilin da yasa kuke son a
tozarta yaron nan yau ko ace yaron nan da dukiyan nan yayi auren nan aiba zakuyi
masa haka a bainan jama,a ba dai.
Jidalin nan tun daren jiya kuna abu daya a kansa har mutanen nan sunzo sun tafi
yanzu ko hakan da kuka gani baku tunanen wani abu akan yaron nan Jafaru.
Kuna nan kun kasa kun tsare kuba zai zauna wa dan uwasa wajeba tunda kusan babu
waje a sashenshi ?
Amma ya gwatsale ku ya nuna maku shi dan yaune ya riga ya tanadi inda zaisa
matarshi ko ya barku nan zube da takaici.
Naso ace yadda kuka shirya mashi ya faru da sai ince ke hafsatu da mijin ki ku
fita min a gidana shi jafar ya gyara gidan su zauna sai Allah ya gyara hakan.
Iya saboda jafar sai ki kori su yaya gida iya waya saka yaje yai auren da
zakice su tashi su bashi waje Allah dai ya gyara nace dake iya ta sake fada.
Matar kawu bata sake magana ba tayi shiru don dama itace mai dumi a falon kana
jin muryanta yana tashi tana bada labari.
Anty Asmau kikace yarinyar nan ce ya aura ni sai naga kamar ba ita bace wallahi
wanan fa kanwar matar Habun gidan nan dai yar doguwar nan ?
Ummm,humm bari ke dai safena wallahi itace ya narka kudi ta gyaru mana tunda ba
abin kai sake bane abin daga can sukaji muryan Saiba cikin tashin hankali tana
fadin.
Wallahi bai isa ba yaya dama na fada maki akwai yaudara cikin zancen nan wai ki
duba imaging gidane fa ita kadai a ciki ya kama mata sannan ace wai mutum yayi
hakkuri ?
Asmau ta dan dubi yar uwarta dake kusa da ita tana dan sakin murmushi don duk
da zafin hakan da takeji tafi jin zafin saiba a zuciyar ta don da alama ta manta
duk itace sillan hakan a rayuwansu.
Abinda tayiwa rayuwansu na shigowa rayuwansu ta bata masu zama ita da mijinta da
tun suna kanana suke soyayya sai gata kwatsam ta rusa masu duk wani mafalki nata
lokaci guda.
Wanan yasa bata kai Saiban jin zafin zancen auren ba da farko yadda Saiba ke
cika baki yasa tana dan shan jinita ga zancen amma yanzu da tayi arba da yadda
yarinyar nan Rahama tashigo a tsatsaye yasa ta ji wani dadi yana kume mata
zuciyanta na muguntan kishi.
Don haka zata koma gefe daya tasha kallo duk da ba zata yarda a mayar da ita
tatakan gida ba zata dan turza itama ganin ba aimai da ita baya ba a gidan.
Wanan abin yaiwa Asmau dadi a zuciyata duk da dai kishin kowa nadashi amma ko
hakan da Jafar yayi ya nuna ita din ba kowa bace a yanzu kamar yadda yayi mata a
baya yayi matukar mata dadi a zuciyarta.
Ganin saiba data fito daki fuuu ta nufi hanyar fita tasan part din mama zata
nufa aiko basu rufe baki ba wajen tafawa sukaji hayaniya ya kaure a gidan.
Mikewa tayi da kyat saboda tsohon cikin dake jikinta ta marawa part din iya
baya Nusaiba ta samu zaune gaban mama tana kwasan kuka tana fadin wallahi mama ba
zan yarda ba.
Tunda duk kan mu a nan gidan ya ajemu da kowa don me zai dauki yarinyar nan ya
kaita wani gida wallahi Allah mama ban yarda saidai ya sakeni idan baisona ne ?
Shigowan Asmau da yar uwata yasa ta sasauta zancen tana fadin don ya nuna muna
iyakar mu muba kowa bane a yanzu zai muna haka ?
Ikon Allah iya data dauro alwala zatayi sallah take fadin hakan yanzu ke Nusaiba
namijine don yayi abinda yake gani daidai a gareshi zaki tsaya kina wanan bori haka
?
Iya don Allah kiyi sallah abinki an tabasune dole suyi magana iya tace ina
tabawa wajen nan ina nan kuke da safe kuna mashi dariya don uwarsa tace ba zata
bashi wajen zama da yarinyar nan ba ?
Jin dirin motansu matar kawu yasa iya tayar da sallah don kada su shigo su bata
mata lokaci bayan wanda ta bata din a baya.
Sai gasu sun shigo da sabon labarin da suke bayarwa wanda ya tayar da hankalin
duk wanda ke wajen don Jafar yai masu bazata yau.
Asmau da taji zancen yana batun hautsana mata rayuwa tacewa yar uwarta suje don
a gabansu komai ya wakana.
Saiba sai sabon kuka data saka lokaci guda cikin tashin hankali ba wanda ya
farga da fitanta don kowa da abinda zuciyarshi keyi a lokacin .
Matar kawu dai iya ta rufe mata baki haka mama tana ji a ranan in Jafar baiyi
hankali ba zata iya mashi baki don saura kiris akai wajen yadda take jin yaudaran
da yayi mata da yayanta yana ci mata zuciya lokacin.
Wai ace yau Jafar ne yayi mata wanan tozarcin da bata taba tsamanin hakan
gareshi ba duk cikinsu Yazid ne mai rawan kai da kuma tauri amma Jafar shine
salihin su.
Don haka wanan karyan da akace ance ya shimfida a gidan wanan yarinyar dole ya
sayar da komai nasa a yanzu yaba yan uwansa hakkinsu.
Kwandala ba zata daga mashi kafa daga ciki ko kudin bai kai miliyan goma ba zai
san inda ya nemo aka basu hakkinsu inyaso shi ya zauna haka din tunda shiya jawa
kansa hakan .
Kamar Jafar ace mata ukku ina zai kai mata ukku da shekarun nan nasa sai taji
duka matan nasa tana jin haushin su a lokacin.
Ita saiba da tazo tana wani babatu ba zata yarda ba ta bari ta gani idan yaci
dadin amarcib da yarinyar tunda harsu abin zai shafa yanzu taga karyan iskancin
kowa a gidan yanzu.
Itako maria tasan hanyar da zata fito mata ba tace ta iya kisisina ba daga ita
har uwarsu suna ganin sun kitsa yar uwarsu tazo aci arzikin su dasu to za a ci din
ta gani .
Tasan dai gudu ya kare mai a yanzu tunda yarinyar nan ta tare gidanshi dole ya
dawo garin yanzu taga ta iyakar gudun da yakeyi din nasu yanzu.
Muryan matar kawuce dake fadin hjy Dubu ni zanje gida nabar kawun yara da tsaron
gida tun dazun yana gidan shi muka bari da zamu fito.
Mama dubun ta dago tana fadin hafsatu zaki komai in kinje kyaba yana labarin
abinda ya faru ko sai ki sanar dashi da safe ya sameni nan ina wajen iya.
Wai ina salima ta dauko maku ajiyan abin shan dana bata dazun ?
Wai Salima ai tunda muka dawo kaduna suna wancan gidan da aka kai amarya gaba
dayansu basu dawo nan ba anty Baraka ta fada .
Kaji wata ja,iran watau tasan komai tun safe kallon mu takeyi shine ta kyale mu ta
kara jin abinda ake fada to za a fasa fadane tunda ya kwamshe kudi shi kadai yana
faca ka ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

4️⃣2️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Anan muka kwana dasu salima dake tayi min sheri wai itace ango din zata wakilci
yayanta ita da Nafisa ko a cikin dare muna shirin kwanciya saida aka kara kawo
naman gashi mai, mai da tsoka anyi mashi irin gashin nan mai ruwa ruwa ga yaji da
su kabeji da albasa an cakudashi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login