Showing 207001 words to 210000 words out of 328222 words

Chapter 70 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

komai yake ba a wajen Allah.
Iya kar dan adam a lokacin da yake a raye shine yake cikin koshin lafiyansa yake
jin kansa dashi wanine ashe da zaran ka rasa lafiyan ka ka rasa komai ke nan a
rayuwanka.
Yau yayane haka ake dagashi kamar dan jaririn da bai taba sanin duniya ba balle
abinda ke cikinsa shine yau yake lalura a kwance har ake kyamar tabashi haka ?
Komawa nayi still na wanke kayan daya bata din na nado wa yan nan din dana
wanke da farko saidana dawo na zauna mama ke fadin waiko kinci abinci yar nan ?
Maria ta kalleni take fadin bansa taci komai ba mama don tunda safe tazo wajen
nan gara dai kici wani abin a cikinki kada ke ma ki kwanta ciwo .
Shi jinya saika daure kana kula da kanka kaima in ba haka ba sai anyi haihuwar
guzuma da kwance uwa kwance.
Ki duba ko zuwan nan yan uwanki naga sunsha su lemo da kayan sanyi kada ki yarda
ki bari ciwo ya kasheki hakan ba damuwansu bane su .
Kece dai din a tsaya don sauya masa tufafi ita mai fadan gashi ta kasa mashi
komai amma don daurin gindin iskanci nan tazo tana muna sababi dazun .
Yanzun gashi don bata da kunya ta kasa daukan kayan ta wanko ina nan iskancin
nan ba zan lamunceshi ba idan ta samu dubune tana juyata yadda take so niba zata
sameni hakan ba .
Yaya da dai kin saka masu ido don koda kikace su sauya mai kaya ta kuma daina
daga murya bakiga irin kallon da taimaki ba ?
Amina na sani sarai shiyasa nake son nayi maganin rashin kunyar yarinyar nan a
wajen nan tea maria ta hado min mai zafi ta ban nasha don haka mama idonta yana a
kaina.
Su ummah da mijinta da maria ta kira a waya ta sheda masu halin da yaya J din
take ciki suka taso daga kaduna da yaransa maza biyu suka zo ganinsa.
Mun jima dasu a cikin dakin yayin da saiba din tazo ta zauna ta kafemu da idanuwa
saikice taji labarin zamu bashi wani mugun abinne da bata yarda da hakan ba.
Koda suka fito donsu wuce mun jima da ummah tana bab magana banda kuka ba
abinda nakeyi shima mijinta haka ya ban baki danayi hakuri hakan jerabawane a
gareni.
In dage da addua da rokon Allah ina nema mashi saukin hakan a wajen Allah inda
ummah take fadin sunyi magana da Hardo yace akwai abinda zai turo muna zuwa gobe.
Sun tafi ina jin kamar kada su tafi su barni a cikin wanan halin dana tsunci
kaina a cikinsa don gashi ina kallo farin cikina a cikin wanan halin .
Haka anty Barakha ta iso zuwa yamma itama inda tasha kukanta tare da nuna
alhininta ga halinda dan uwan nata keciki nice na debo mata abinci ta samu tayi
sallah ta zauna taci suna zancen da yan uwanta mata su salima da saare.
Gudu kawai ya habu ke shegawa tun suna dan hira a motan tsakanin iya da yayanta
har yakai duk sunyi shiru saboda tafiya da nisan wajen da suka dosa din.
Sai iyace da tayi barci ta tashi take fadin kai Dauda a ina kasan wanan wajen da
har kazo a lokacin ?
Iya me nema ai baya ganin nisan waje idan yana da bukata nima wata yar uwar
Hafsatuce ta nuna min wajen don ita wajen zuwantane a lokacin.
Hafsatu ke mata hiran ita halima shine tace da za aje wajen za a dace don ba
wanda yajen bai dace ba .
Kinji dalilin dayasa na shawarci ita halimatu din da mijinta a lokacin don da a
tare zamuzo dasu sai bai bada goyon bayan hakan ba yasa nazo ni kadai a lokacin.
Saidai bayan nazo dinne na fahinci irin aikin mutanen da garama da banzo dashi
ba ashe don ba zai yarda muyi irin abinda akace ayi ba lokacin.
Kinsan halinsa zaice shirkane ko wani abin kaucewa hakan yasa na karbo mata
baki alaikum nakai mata tayi amfani dashi Allah kuma ya kawo rabon.
Kaiya rabon wahala ko tunda lokaci yayi idan akai hakuri ai samu za ayi tunda
komai dan lokacine Allah ya riga yayi tana da rabo don haka ba mahalukin daya isa
ya hana yaran nan zuwa duniya nan.
Don ni tun a lokacin ban so irin wanan abinba dauda kaida matarka kuka kafe akan
hakan har kukafi yar uwar taku damuwa hakan a lokacin
Yanzu ina dadin hakan don Allah abinda a karshe ake wanan irin wahalan yaron
nan Allah kadai yasan irin halin rayuwan da yake tsintar kansa a cikin sa.
Yau har abin yakaishi ga halin da ba aso yanzu dadin kuke nan anyi ba ayi ba ke
nan wanan abin kana ganin idan yaron nan ya mutu a halin nan zai yafe maku dauda .
Iya kinsan halin hafsatu fa kinsan ta da yarda da irun abin nan balle da taji
ance ba zanyi arziki ba sai yar uwata ta haihu a duniya tun lokacin hafsatu
tasakawa kanta damuwa.
Kaji wani shirme dan Allah diyan dubu diyan kune kai da hafsatu ko diyan Dubu ne
ita da mijinta ko yanzu da sunan ku suke amfani ?
Ni dama nasani nadade da sanin da manufa kuke wasu abubuwa akan yaran nan ka taba
jin inda dan wani ya zamo jinin wani inba shirmen ka ba dauda ?
Yaron nan Jafaru yana da kawaici yasan komai ya dade da sanin komai da kuke
kulawa akansa kaida matar ka amma ya kyale yake binku a hakan .
Yau na tabbarta da ba jafuru bane abin nan ya sauka a kansa haka har ya sani
kana ganin bayanshi akwai wanda zai kyaleku haka a cikinsu ?
Dauda kaji tsoron Allah ka daina wanan rayuwan banzan yau gashi saboda son
kanka dana matarka kun jefa rayuwan mu a cikin wani hali mara dadin fada ?
Yaran nan sun san komai ido kawai suka saka maka dauda saboda kawaicinsu da
uwarsu ita kuma tana shirme kamar tababiya ta kasa kwantar da hankali ta fahinci
hakan a gareka.
Sun sani fa iya kikace kawu din ya juyo yana tambaya tace kwarai ga habu nan
sun jima da sanin komai a kanka har uwar tasu sun dai kyaleku kawai ne .
Zufane ya fara karyowa kawu lokaci guda da har yakai ga cire fulanshi dake
kanshi yana fitara dashi lokaci guda.
Kalloshi Habu yayi yana gyada kai kafin yace kawu abinda nake so dakai yanzu
shine ka fada muna gaskiyan zancen nan tun a nan ba sai munje gaban mutanen nan
ba ?
Menene asalin abinda ya kawo hakan don Allah don a gaskiya ni dai ina yawan
mafarki da wata mace kai bama mafalki ba wallahi matar nan sau biyu ina arba da ita
a zaria .
Na farko a gidanmu nan tudun wada ta shigo da kwalan maciji tana tallah muka bata
sadaka a ranan da zanyi tafiya zuwa kasan su maria a bakinta naji cewa zan hadu da
maria.
Bayan na dawo kuma da kwana biyu na sake haduwa da ita take fada min in fadawa
mama tazo ta ganeta tun kan mai faruwa ya faru damu.
Saina dauka zance ne kawai irin na mutane don haka ban dauki zancen da
muhinmanci ba amma na fada ma mama a lokacin.
Koda ka fada min ai munje bamu sameta ba ta tafi mama da damuwa ya dama ta tsoma
masu baki karo na farko a motan .
To bayab haka ban kara tuna komai ba akan zancen sai lokacin da Jafar ya kwanta
ciwonsa na farko nayi mafalki da wanan matar tana min gargadi sosai kan wanan
maganan .
Kodana dawo kuma saina samu J a cikin wanan halin tun lokacin na san zancen nan
ba karami bane haka kuma yana cikin abinda yasa kukaga J ya auri wanan yarinyar
Rahama.
Don yadda matar ta fada haka ya faru bazan boye maku ba yau don boyo baida amfani
ita Rahama itace tayi amfani da wani magani a lokacin da j ya kwanta wancan karon
itace wace tayi amfani da daman data samu ta dinga mai amfani da wani magani na
gidansu har ya samu sauki.
Rahama mama ta fada yace wallahi ba wanda ya sani sai Nafisa dani a lokacin don
saida ta kafa huja kada a zargeta yadda wallahi nayi mafarki akan gun Rahama za a
samu maganin nan haka abin ya faru shi j ya fada min komai a lokacin.
Shine kukaga yayi hanyar daya aureta ake ta zarginsa dayaci amana ya fifitata
akan matanshi.
Amma ai baku fada muna ba mama ta fada yace ko mungaya maki mama ba yarda zakiyi
ba saima ki juya zancen ta wani tsiga tunda gashi kuna fadan sun mallakemu.
Ni dama nasani wallahi nasan dole akwai jafaru ba zai amfakawa yarinyr nan haka
a banza ba dole akwai abinda kuke boye muna wanan ai taimakon kaine tayi balle ace
za a zargeta akai iya ke fada.
Iya kinsan su wanda suka tashi wajenshi aikinsa ke nan bada magani kaf nahiyarsu
asan dashi zuwan da mukayi nakaisu ganin gida lokacin dansa ya bata maganin akai
dace kuma ta gwadawa jafar din yayi amfani.
Dole taji tsoron fitowa fili ta nuna tana bashi magani irin haka don gudun
zargin matansa shi kuma dayaga ya mike shine ya ban shawaran yana son ya aureta
tunma da ita Saiba tayi masu wanan zargin suna tare saiya kasance kamar ta
zugashine akanta.
Aida kun fada da duk hakan bai taso ba nasan Rahama zata iya komai daka fada habu
don yadda ta nuna damuwata akan shi lokaci ko ciki daya suka fito ya tsaya a hakan
mamake fadi.
Tacigaba da fadin na dauka daga baya tayi hakan ne don kawai ta samo kansa ya
aureta tayi wanan ladabin shegu din a lokacin.
Ko ladabin shegu tayi ai ta cancanci hakan don ni jafaru yayi min daya aureta
kece dubu yakamata ace kin gane hakan tun lokacin.
Yarinyar da bata kyamarsa bata gudun ta dauki ciwon dake tare dashi wanda matansa
na sunna da yan uwansu suna gudunsa don yadda fatan jikinsa kuraje suka feso masa
banda ita da Nafisan a lokacin waya tsaya ya taimaka masa bai kya macesa ba ?
Amma haka kika rufe ido kina nuna baki kaunan yaran nan har jininsu kada kice ko
ba a fahinciki bane har yaron nan dan wajen Habu kirikiri kike nuna laifin
iyayyenshi ya shafeshi kowa kuma yasani.
Yanzu ga komai ya lalace maki magani a gonan ki kin kasa tsayawa ki fahinci
hakan sai bin yarinyar banzan nan da kikeyi tana cusa maki bakin ciki a banza.
Idan har Jafaru ya mutu a halin nan wallahi ki nemi gafaran ubangijiki biyu don
alhakin yaron nan sai ya kamaku dake da dauda bama shi kadai ba tunda alama ya nuna
akan diyan kaf abin yake.
Innalillahi mama din ta ambata tana fadin nifa iya ba wanda ya taba tsayawa yayi
min bayanin wanan abin haka inba yanzu ba.
Ni yaya ake son nayi don Allah shi yaya bai tsaya ya fada min gaskiya akan
maganin ba lokacin daya kawo min balle in dauki abin da muhinmanci a raina ?
Dubu laifin hafsatune wallahi kuma ba komai yasa hakan ba ta hana in fada maki
hakanne don cewan da akayi da arzikin yaran ki zamuyi namu arzikin .
Saita dauka idan har mun fito fili mun nuna maki abinda ke nan keda yaran naki
zaku juya muna baya ko nayi yunkurin fada maku saita kawo min musalai na banza akan
illan dake cikin fadin da zanyi din .
Kuskure kan nasan nayi wallahi saidai kawai ayi ,,,,, kai rufe muna baki shasha
kawai kaji kunuan duniya wallahi sauran ka na lahira ka rasa wace zaka cuta sai yar
uwarka tillo ciki daya dauda akan matar ka ?
Hansatu mutumiyar banzace kasani kuma kake take sanin don son kai meye yaran nan
suka rageka dashi don Allah koma meka boye muna yanzu ai zamuji tunda anzo wajen
insha Allahu.
Don Allah ku gafarceni nasan nayi kuskure kuma nayi nadama ku yarda dani hakan
nima banyin kaina bane laifin hafsatune wallahi.
Wani dogon tsuk iyan taja tana kauda kai yayin da mama keta wani irin gumjin
kuka ta kasa magana sai can tace yaya daka fada min tin farko da banyi amfani da
maganin nan ba tunda baka fada min ka,idanshi ba a lokacin.
Habune ya kallo kawu dake faman zufa rai bace don har lokacin kawu yana hitarane
kanshi yana faman zubar da zufa .
Yace munzo ta wani hanya zamu dauka yace ka dauki hanyar dama shi zai kaimu garin
da zamu dauki hanyar zuwa kauye daga nan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join
my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ
[3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

6️⃣6️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



Kuka kan kallo daya zakiyi min kisan nasha kuka a wanan wunin don yadda idanuwana
sukai hulu hulu saboda kukan da nake kebewa inyi,
Tare da tunanen duniya kala kala dake sauka min a zuciyana game da halin da yaya
Jafar din yake ciki.
Ina zaune nayi shiru a gefe tabarman dasu mama ke zaune sama bayan mun idar da
sallah la,asar nagama maman tudun wada ta miko min kofi cike da fura har da kankara
a sama .
Kaina girgiza alaman a,a don banson komai a lokacin take fadin maza karbi kisha
ina kule dake tun karyawan safe baki kara saka komai a cikinki ba yar nan.
Masu fadin suke dashi don suke da diya dashi aun zage nan suna ciye ciyensu a
gaba kowa balle ke din da sukewa arashun baki aje ko kwai a tare dashi ba balle ki
fisu nuna damuwa sun zage suna kai abu ga bakin salatinsu.
Maza ki karba kisha ki danji nauyi a cikinki kinji Allah ya kareki da takaban
kuriciya da suke maku fata hakan don yafi komai daci da muni ga ya,mace .
Hawayene suka sulalo a idona take fadin ki daure ki daina wanan kukan haka Allah
ya tada kafadan mijinku yasa hakan zakan jikine a garesa.
Karbi maza ki shanye ba a jinya da yunwa don saika fadi mai ciwo yazo ya mike
Allah ya tsare dole na karba nasha din datace min saidai ban iya shanyewa ba na
rike sauran a hannuna take fadin maza na shanye na miko mata kofin .
Dole na kara kurbe sauran ban kaiga idawa ba Asmau ta kwala min kira da nazo
daga kofan dakin hakan yasa na aje kofin da sauri na mike tsaye na nufi dakin .
Don na fito saboda karmu saida hali a waje don yadda take nunawa lokacin dana
shiga dakin ko abu zanyiwa yaya din zata taso da sauri tace dani na bari kawai ai
zasuyi mai ko idan na dauki abu zatace na miko mata abin.
Ganin hakan yasa na fito daga dakin don zuciya bata da kashi zan iya kasa hakkuri
na biye mata muyi abinda ba daidai ba har mutane suji a tafi damu a baki.
Koda na shiga dakin na zata wani abune sai take cemin wai na duba ko ya sake
bata jikinshi wani kallo nayi mata mai nuna baki isa ba.
Kin fimu karfin hali yasa muka kiraki Asmau ke fadin hakan gareni nace na zata
ba saini ba zaku iya hakan ga mijin ku ai.
Ke don mun kiraki kada ki fadawa mutane maganan banza don Allah idan ba zaki iya
ba kice ba zakiyi ba kada ki kawowa mutane wani zancen banza a nan ?
Banda lokacin ki don haka kiyi haushin ki ke kadai dama kin saba ciwon nasa
aida alaman ba damuwanki yayi ba don da baki zauna kina damunsa da waya haka ba
akai.
Ashe kinji zafin wayan da nakeyi din inkin isa kizo ki karbe wayan insan kincika
yar jin haushi kaji min yarinya da zancen banza har wakike inbashi dayaga abin
banza ya nace akanki ba ?
Subbahanallahi dama nayi tunanen hakan ai yasa na biyo ku, yanzu yarinyar nan
har bawan Allah nan yana kwance haka cikin wanan halin ?
Amma baki saduda da wanan halin naki ba sai kin dagawa mutane harshe a nan kuma ?
Muryan mamace data biyoni bayan shigowana take fadan hakan tana tafa hannu don
bata jini ba saiba din ta sama tana fada min maganganu a bakinta lokacin.
Wani daga harshe nayi yanzu kuma mama ita har waye da zata tsaya tana fada min
magana akan abinda zanyi yaushe ta samu wanan power din take ganin takai ?
Amma kin kai sakarai ashe ? har yaushe wanan taga lokacin fadan wani magana
gareki a nan yarinyar dake ta faman darzan kuka tun dazun a waje .
Gadon da yake kwancene ya fara jijiga gaba dayan mu hankalin mu ya koma kanshi
hakoransane ya datse a waje daya yayin da idanuwansa suka firfito waje ma,ana dai
ya kara shiga wani sabon hali lokaci guda kuma.
Ko salatin mama ya isa ya rudamu a lokacin inda Asmau ta fita waje da gudu tana
neman taimako ga mutanen dake zaune waje cikin rudewa da tashin hankali.
Ba maza a kusa iya mu matane da muka cika asibitin a lokacin sai salima data hari
dakin likitocin hankali tashe don kiransu.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login