Showing 246001 words to 249000 words out of 328222 words

Chapter 83 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

kwance maki mijin ki duk
ranan da Allah ya bashi lafiya in zai iya zuwa gidana yazo idan ba zai iya ba kuma
yasha zamanshi nima nagaji da wanan wahala haka .
Na juya zuwa ciki na kwaso kaya ban ko kalli inda yake ba balle su mama get din
gidan na nufa na fice ban sake juyowa na kallesu ba .
Yau nasan yarinyar nan tsatsan bafulatanace ashe haka ai basu iya fada ba ransu
bai iya baci ga abu ba to yanzu dai ankai ga yadda ake so ai ina kula yarinyar nan
ko zuwa tayi gidan nan an kama sakin magana ke nan ana mata haibaici tana sharewa
tun farkon lamarin nan .
Shin garekune farau zama da matan yayyu koko kun zama yan idone da ba a kwaba
muku ku auren dai ai kowa zaije yayi yaji abinda ke cikinsa.
Ba yarinyar nan ba koni yau zan bar gidan nan tunda Jafaru ya fara samun lafiya
nake ganin abubuwa daban daban daga gidan nan hadewa kawai nakeyi .
To Alhamdullahi tunda Allah ya bashi lafiya a yanzu Allah ya kara mikar muna
dashi lafiya amin daga kofa ya dogaro yana fadin ta wuce ko ?
Maman tudu tace dole aita wuce tunda sherin har yakai na sheganta mata abin
cikin cikinta a gabata kuma ba a dauki wani mataki ba ko nice ai zanwa kaina gata.
Saidai ku sani yau abinda baku sani ban kan yarinyar nan tayi abinda duk cikin
mu nan kaf babu mai iya yinsa ga yaron nan.
Itace zata hana kanta barci ta kwana tana masa karatun kur,ani tana sallolinta
tana bashi magani tana tofeshi ko yaushe ka falko kana iskata a kan shi tana mashi
addu,a.
Tau ku sani idan jinyar yaron nan ya koma kasa kada kuyi kuka da kowa kuyi kuka
da kanku wallahi don daku aka hada kai aka koreta a gidan nan yau.
Dama makiran kishiya tafi mai fitina hatsari don gara mai fitina tana fitowa
fili ka fahinceta amma wace ke sari ka noke itace guba mai cutarwa farat daya.
To yanzu fissabillahi yaya daga dan maganan fatar baki saita kwasa tayi fushi
tana fadin magana haka dama dai ai sallon ta samu hanyar kubucewace tayi don ta
nuna ta gaji hakana ?
Yanzu idan bata zo ba sin yadda tace ai zai nade ya bita can din inda ta saba cin
karanta babu babbaka ana kallonta can ko sai abinda taga dama tayi.
Itama yar kauye tasan tayi wanan shirin ga mutane balle muna da aka haifa a cikin
gari taje wa zuwanta ya dama a gidan nan koda ita ko ba ita in Allah ya bashi
lafiya sai ya mike da yardan Allah.
Kaico iya dake tafe tana gyara daurin dan kwalinta take fadin haka badai da
abokiyar zaman naki ba kuma kike wanan abin kunyan haka ?
Aa,ha iya badani bace da dai sarakuwartace da yaranta tunda su ba ai masu fada
nikan ai kafin nima su koreni din yau zan koma dakina insha Allahu kar abin ya juyo
kaina yanzu kuma ?
Yaya sai kinso saka kanki cikin zancen nan gaskiya don wallahi dai bada ke akeyi
ba kin sani yaran nan kuma kin dai san dan yau banice zan turasu sunawa matan dan
uwansu haka ba ?
Wai sai meyasa matan jafar ne ko kafin yarinyar nan ta auri Jafar ai yar uwarta
habu ya fara aurowa gidan nan da zaku dauki karan tsana ku sakawa yarinya guda duk
kokarinta ga dan uwanku.
Aike Amina baki sani bane dan uwanne nasu basa so shiya kawo haka kiyayyan jafar
dasune ya shafi amaryansa .
Haba iya in antashi magana kiyi ta hadawa dani don Allah ni yanzu mena cewa
Rahama anan daga muna maida maganan zagin da Nusaiba tayiwa Asmau shike nan fa tayi
fushi inma maganane ai ita Asmau itace ke fadin magana da har ya shafeta ni meye
nawa a cikin zancensu.
Tun bayan fitana daga gida kuka baizo min ba asalima taxi na tare zuwa gidan
saidai inata faman sakawa da kwancewa a kasan raina.
Ina shawaran barin garin a ranan in nufi abuja ko adamawan cameroom gun yan uwan
mu zaifi min sauki a rayuwata sam ban taba nasa cewa zanwa wani shige shige a wajen
boka ko malami da sunan in kuntatawa wani.
Amma sai gashi ban tsira wajen sherin abokan zama ba kullum duba sukeyi ina da
asirin da nakewa mijin namu yasa bai yarda yaga laifina.
Duk magana idan zai taso nice wai za a bawa gaskiya na sani ai na kuma san irin
azaban da Allah zaiwa mutum.
Nagama komai na shiri kwance na dawo falo don in danci wani abu duk da bakin
nawa ba dadi a lokacin amma haka nake daurewa kamar yadda manyana suka fada min.
Ance in daure ko bakina ba dadi in dinga cin abincin ya kasance ina da kuzarina
dan kada na lalace abin cikin cikina kuma zai wahala .
Fruits din dana sayo a hanya da zan dawo na yanka nake sha naji bugun kofa don
munyi da Biba saida safe zata dawo ranan don haka ni kadai ke nan zan kwana a ranan
sai megadin gidan dake waje.
Daga ciki nake tambayan ko waye muryan ya Yazid naji yana fadin bude mune da
iya hakan yasa na dauki gyalena dake gefe na yafa akaina na bude kofan.
Shida iyace sai matarshi da yaransu sukazo na danyi murmushin dole a fuskana ina
fadin kune a gidan yau ?
Ba doleba ance amarya mu tayi fushi harda rantsuwa ba zata sake taka gidan muba
murmushi yake na komayi ban daiyi magana har lokacin.
Muka samu waje muka zauna dukkan mu a falo na mike na dauki sauran fruit din a
cikin fridge din na kawo masu sai bin ko ina na fidan sukeyi da kallo.
Iya ke fadin kagani ko na fadama ko acan din tauye take don laluran nan ne kawai
yake kaita amma yaran nan yau saida suka kure hakkurin yatinyar nan.
Ai tunda nadon su takeyi ba iya ba zatabi ta nasu ba tace bata kara zuwa ganinsa
yanzu gashi can kun barshi ya rikice bayan tafiyan ku ita mama tayi fushi ta wuce
gida ke kuma kin dawo nan ke kadai ina yarinyar da kuke zama da ita din ?
Saidana hade wani malolon bakin ciki nake fadin tana gida yau yar uwarta ta haihu
suna suna sam banyi tunanen zaki bari suci galaba akanki ba ai tunda kinsan da
gaiya suke abinsu.
Kowa yasan meyasa Saratu take hakan ni dai na dauka ba banza take hakan ba don
ban taga ganin inda mutum yaki dan uwasa ba haka ?
Amina tun bata kai gida ba nasa aka dawo da ita kema munzone da safe idan Allah
ya kaimu ki shirya yadda kika saba kizo ki duba mijinki kinji na amsa masu tare da
godiya.
Sun dan jima a zaune iya ta matsa akan su tafi dare yayi don sam ita bata fitan
dare wanan fitowan ma ya kanane haka.
Nayi masu rakiya akan washegarin zan shigo suka tafi matarshi sai bina da kallo
takeyi kawai don hausan a lokacin take koyonsa.
Bayan sun wuce ina shiga daki na jawo dan jakkata na hada kayan bukatana a
cikinsa nayi ready komai na saka a jakar safiya kawai nake jira a lokacin.
Barci sama sama nayishi a ranan don abinda na yanke a raina gidan ga baki daya ya
fice min a rai abin cikin cikina kuma yana ban tausayi.
Don nasan haka zai taso da kalubali idan ban dauki matakin hakan ba tun yanzu don
haka dole in kauce in samu a daukar min mataki akan saratun nan da kowa ma don har
mama gaskiya.
Washegari sallah kawai nayi na zauna addua na jira gari ya dan haska na fito
inacewa maigadi zani can gidan kila in kwana biyu a can din waman zuwan.
Yana ta min adawo lafiya yana gaida maigida shiya tare min keke na hau ina sauke
ajiyan zuwa dana bar wajen muna fita titi nacewa mai keken kaini tasha in shiga
motan kaduna.
Ya dauki hanya sai tasha din muna zuwa ga mota saura mutum biyu zuwa kaduna na
sallameshi na biya kudin mota na fada.
Saiga cikon na karshen yazo muka daga na sauke ajiyan zuciya ina jan hijjab
dina zuwa hancina saida muka bar zaria na sake gyara zama ina lumshe idona.
Mai karatu abinda yasa banje abuja ba son zuwan dasu daddy sukayi na nuna masu
zan daure da duk wani abinda zan gani amma yanzu na kasa hakan .
Gara inje wurin ummah zaifi min duk da banson zuwa gidan nasu don yadda mijin
nata yake like da ita kamar wasu yara hakan kan ban haushi idan na tuna da mahaifin
mu da basuyi irin wanan rayuwan barikin dashi ba haka har ya tafi kullum shi yana
kofan gida yana tsaro wajen aikinshi ko in daddy yana gari su fita tare dashi din.
Amma shi wanan ya samu wanan daman da mahaifin mu bai samu ba Allah ya gani ina
taya mahaifin mu kishi a kansa gaskiya.
Ashe yazid ya biyoni zuwa gidan ya daukeni ya samu ban gidan maigadi ke fada
mashi ai tun safe na fita da jakata nace can gidan zani a lokacin.
Gidan mu tace dakai zata ni yanzu daga gidan nake ai fitowana ke nan nazo nan
don jikin mijin nata ya dan tashi subbahanallahi maigadi ya fada ya dora da fadin
har da jakar kaya ta fita ai nina saka mata a mota don tace wanan karon zata kwana
biyu a can din.
Waya ya daga ya kira yana tambaya ake ce mai to ban iso ba ya juya ya fita sun
kira wayana a kashe yasa suka kira Maria ta dauka cikin sanyin muryan nan nata suka
gaisa bai tsaya ba yace ko amaryan J tana wajenkine sister ki ?
Rahama ta fada cikin mamaki ta dora da fadin wallahi bata zo nan ba ai mun kwana
biyu gaskiya yake fadin habu bai dawo bane ?
Ta amsa maida yace sai jibi zai dawo bai tsaya ba ya kashe wayan ya karasa gida
sun ta maganan maman tudu ke dadin dama nasan zatayi gaba tamayi kokari tunda har
takai war hakan.
Bafulacene zai tsaya ana gardaman abinda yake da gaskiya a kansa tayi kokari dama
ta zauna ai tunda tana son mijinta yanzu dai kubar zancen nan kada yaji don Allah
mama ta fada.
Basu sameni ba sai zuwa yamma nayi barci na tashine suka sameni kira ukku na
dauka da sallama muryan yazid ne yake fadin Amaryan J kina ina don Allah ?
Hanyar garin mu na bashi amsa na kashe wayan ban tsaya saurara mashi ba don ban
son yawan magana tunda mun kwasa da ummah tun isowana.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:44] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

7️⃣7️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Ban san ya akayi ba ummah ta kira Maria ta sheda mata ina kuduna wurinsu nace daga
nan kasan mu zan tafi amma sun hanani tafiya gida.
Hakan yasa hankali a tashe maria din ta dinga lalubar wayana ina ganin kiranta na
shigo min naki dauka a karshema na kashe wayan nawa gaba daya.
Ina nan dakin ummah kwance sai gata da waya tana fada min in karba yar uwatace
a layin, fuska na bata ina fadin banyin magana da ita a yanzu ummah.
Kina da kafuwa Annini ita meye hadinta dasu da zaki ki fada mata damuwanki kuma
ko baki fada ba ki karba ku gaisa mana da ita.
Dole na mika hannu na karba ummah ta juya ta fita daga dakin ta batmu muna waya
ina dauka a dakile nace hello naji tana fadin Ramaah baki kyauta min ba yaya zakisa
kafa ki fito gidan mijinki bayan kinsan yana kwance ba lafiya.
Kin kuma san yadda ya samu dake a zuciyarsa dole in kikai hakan ya shiga damu
gashi ko ya shiga damuwa din don ana kokarin boye masa tafiyan ki har yanzu ya gane
abinda ke _fa_ ruwa.
To ya gane mana Maria ke kika damu da hakan ni yanzu ta kaina nakeyi bata shi ba
don gara dashi yana gaban kowa nasa a gabanshi kuma akeyi min abinda akaga dama bai
dauki mataki ba kin kuma sani.
Haba Rahama wani mataki kike son ya dauka shida yake kwance bayan haka kinfi
kowa sanin yadda suke tsoron mahaifiyarsu ai dukkansu mazan matan ne dai basu faye
tsoronta bama nake gani.
To suje can suyi ta jin tsoron ta ni ban sake komawa gidan nan wallahi da sauri
naji tace ki daina rantsuwa don Allah haka Rahama idan baki koma ba yaya zakiyi da
cikin jikinki ke nan kuma ?
Nace ciki ciki ai zubarda shi zanyi don ba zan yarda in haifi cikin da zaizo
duniya yan uwan ubansa na kirasa da shege ba .
Ke Rahama wanan magana ina ya fito kuma nace a bakin Saratu don tace ba a shege
waje sai a gidan miji macen data hada kwanan yan uwanta tayi ciki wanan dan ake
kira da shege.
Innalillahi ta fara ambata tana fadin ita Saare din ta fadi hakan gareki lalai
kuwa inta fada akwai magana ke nan gaskiya amma don Allah ina rokonki da kada ki
taba cikin nan don Allah saina kashe wayan don takaici daya rufe min zuciya.
Sam ya J da kowa nasa har maria dake tare dasu a yanzu sai naji gaba daya sun
fice min rai lokaci guda ina dana sanin saninsu ma baki daya don yadda nake ji din.
Zuciyana ya dake sosai ba wani zancen kuka a gareni yanzu kawai solution nake
nemawa kaina a yanzu wanda kuma zuciyana yafi yarda da in zubar da wanan cikin
kaddaran dake jikina lokacin.
Kwanciya nayi na lafe muryan ummah yasani dagowa don tashigo tana fadin ki
tashi ki saka wani abu a cikinki tun dazun kina daki dunkule.
Wayarta na miko mata na dago daga kwancen da nake ina jingina da gado ga abincin
nan falo ki fito kici ki watsa ruwa ta fada a cikin tsigar umurni a gareni.
Bin bayan ummah din nayi da kallo ina son in fahinci fushi takeyi ko goyon
bayana don tunda nazo bata furta min komai ba.
Kuma tana falon nayiwa mijinta bayanin zuwana din mikewa nayi zuwa falon inda na
hango abinci a kuloli tsakiyan falonta waya takeyi daga kofan dakin ta juyo tana
kallona kafin ta karasa fita daga falon gabaki daya.
Abincin na bude inda naga shimkafane da miya sai ganyen salad amma miyar na
kifine ko ta manta cewa ni bafulatanan asalice ban damu da kifi ba oho ?
Su sun iya ci a gidan daddy Abuja tun wani ciki da tayi a yadda take fada muna a
baya saini da Abban mune bama son kifi dan gara danima nakanci miyar kifi din wani
lokaci ba tare da nayi amanshi ba .
Shiko mahaifin mu har ya rasu sam baya cin kifi a rayuwansa na gwada ci din duk
da budewana naji yana hawa min kai amma haka na daure na kai a bakina.
Kamar kada ya sauka a cikina da sauri na mike zuwa waje dakin inda keda kasa da
fulawowi na duka na fara shega amai na fitan hayaci.
Sai mai aikinsu ummah dince tazo tana faman yi min sannu daga inda ummah din
take taji kakarin aman nawa ta fito da sauri tana tambayan yaya haka kuma ?
Na kasa bata amsa a lokacin don yanayin aman da nakeyi din saida ya dan sarara
min suna tsaye kaina don har mijin nata ya fito yana tambayan ba,asin aman ?
Na lalaba na koma zuwa daki na zauna a falo ina maida numfashi ummah ta shigo ta
zauna takara min sannu kafin ta dora da fadin kardai wani abu kika sha don sakarcin
da kikeson yiwa kanki ?
Idona na kasa ina karewa jan lalen hausa dake kafanta yayi kyau ya karbi kafan
nata da kyau na dago a cikin mamaki ina binta da kallo.
Sake maimaita tambayan tayi daidai mijin nata yana shigowa dakin ga yar aikinsu a
bayanshi dauke da ruwan sanyi ta kawo min shiya cabe tambayan da bata amsa .
Yana fadin haba dai har me zata iya yi yanzu kinsan mai karamin ciki da jin
tashin zuciya ai na sauke kaina kasa a ciki kunya na nuna mata abincin dake cikin
plate din tabi da kallo.
Kafin tace abincin bai maki bane in badon ummah bace sai ince tayi min ba daidai
ba wallahi wanan tambayan don tafi kowa sanin bancin kifi tun fil azal a rayuwata
tundai wanan na tekun mai bakin karnin nan haka ?
Bai mata bane nasan tsohon ya fada yanawa kansa matsuguni a daya daga cikin
kujerun falon a kasalance na basu amsa da KIFI ?
Kifi ta fada a cikin mamaki tana bina da kallo muryan na gwada mamakin hakan
tace dama har yanzu ke baki cin kifine Rahama ?
Kaina gyada mata tace sam na manta wallahi na zata ai ta daina wanan matsalan na
rashin cin kifi a yanzu tunda naga an dade ai ashe matsalanta guda da mahaifinta.
Ai dama na fada maki akwai dai wasu sam basa son kifi a rayuwan yanzu me zataci
ke nan ko akwai abincin da ba kifi a bata taci ?
Yanzu aka dora abincin dare ummah ta fada sai tsohon ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login