Showing 285001 words to 288000 words out of 328222 words
Chapter 96 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
Bata tanka min ba take fadin bari ta kawo muna ruwa ki barshi saidai su nikan a
koshe nake ta dai mike zuwa kitchen dinta wajen fridge dinta sai gata da gora biyu
na ruwa ta aje muna .
Nan suka fara gaisawa da yaran kamar mintuna goma na mike da gaiya ina fadin
zamu tafi dama munzo kawai mu duba sune.
Haba Rahama tun yanzu ko zama bakuyi ba ina ce a nan zaku wuni ai a,a nazo duba
yaran nan ne kwana biyu bangansu ba.
Suma suna kewanki baba yace in ya dawo zai kaisu which means bada ita ba take
fada min hakan kai tsaye to ni zan tafi zamu biya gidan yaya Ai mu gaida ita.
Sai lokacin take tambayana waya kawoni nace Nape muka hau take fadin kuma yaya ya
yarda to yaya zaiyi tunda ba zai hanani zuwa in dubaki ba matukar ina da lafiya ?
Idan kinga ya hanani fitowa ya fahinci banjin dadin jikina shi kadai zaisa ya
hani zuwa gidanki ko kuma yana jin jalin maza a lokacin.
Dan kame kame ta farayi don itace ko yaushe take fadin mijintane yake hanata
zuwa dubana ko tayi mashi magana.
Daga gidanta gidan yaya Ai muka tafi saida mukai azahar muka fito zuwa family
house dinsu mugaidasu maman tudu.
Takuwa ji dadin zuwan mu din sosai don sabo a yanzu ya shiga tsakanina da ita
duk da munci wani abu gidan yaya Ai amma saida mama tasa mukaci dambun shimkafa a
wajenta.
Ta sayo muna sobo mai sanyi mu kora sai hira take jana dashi bandai yarda na fadi
wani abu mai muni game da mijina ba ko mahaifiyarsa.
Mun jima na bata alherin dana rilko mata koda muka dawo gida mun samu ya rigamu
dawowa halin mazane don ko yayi fadan dadewan mu sosai.
Har in kaga yayi fada akan abu ransa ya baci da abin donshi nayi shiru na shige
daki na sauya kayana zuwa kitchen don yamma da yayi muna lokacin.
Har dare bai sauka ba yana fushi dani nidai ya dawo daga sallah na hada mai
abincinsa na aje mai daki na koma nayi sallah dana idar kuma na kwanta abina.
Daga falo ya kwala min kira nasan abinci zan zuba mai lokacin na fito na
sameshi nima fuska a dare nazo gareshi ya dago ya dubi fuskan nawa yana fadin
abinci zaki zuba min ?
Nan ma banyi magana ba na duka na soma zuba mai abincin har lokacin ban cikin
sakewa sai naji yana fadin kin san bake kadai bane zaki fita tun safe har yamma
haka ?
Idan jigila yaja maki wani matsala fa tunda jikinki ba karfine dashi ba har
yanzu gashi ance ba,a son mai ciki fitan yamma ?
Gidansu mama muka fito fa mun jima a gidan yaya Ai har kusan la,asar muna can
gidan ta ya tare da fadin bandai sin hakan na fada maki nayi shiru.
Munyi hakan da kamar kwana biyu ya sameni da zancen a gobe in sha Allah yake son
ya koma can gidan ban nuna komai ba duk da naji abin a bazata.
Kinsan mu mata ko yayane sai mun dan nuna halin kishin nan gashi kuma sati biyar
cur yayi a gida dole ko kome naji in taushe a lokacin don yayi min ba zance ga kara
ga ittace ba irin namu na mata.
Donshi nace Allah ya kaimu gobe lafiya shiko gogan ya tsureni da idanunsa yana
kallona ko zai fahinci wani abin daga gareni.
Yaron nan iyayyensa basu ce komai akansa ba har yanzu donshi nake son a nema
mashi makaranta ya fara zuwa a nan in kuma uban bai yarda ba ya koma gida gabansu.
Me zai hana ya yarda tunda yaran ba damuwansa sukayi ba yanzu inda ya damu aida
ya bugo waya yaji ya fada nayi magana a sama mashi gurbi a nan saiki fada mai ya
aika su turo mai da takardunshi daga can gida.
Naga ke kina son zaman yaron a nan iba haka ba niba zan barshi nan wajena ba
saidai ya koma can gida wajen mama su zauna abinci daine Allah ya hore min in basu.
Ai yiwa kaine dan yar uwarka ai dankane ba a san moriyan da za a samu ga hakan
ba yace badai a wajen barakha ba kuwa a daiyi din kawai don zumunci Allah yace
wanda ya yanke zumunci zai azabatar dashi .
Donshi nake duba ina dan rage wani abu amma su suna ganin hadani da boka da malam
din da sukeyine yake tasiri a kaina.
Ita saratu yanzu naji ance ta turawasu yaya mai nemanta wani mutumin sokoto ta
samu yana aikin banki a nan garin .
Masha Allah nace ashe aure yazo ke nan tunda har yaje gida sai naji yace ita
dai ta sani niba ruwana da zancen yar iska yanzu tunda bata son farin cikina.
Bance ban mata komai ba amma ba dai irin na salima ba kan da sauri nace hakama
ba zai yuyu ba tunda su biyune kadaiyi din a fitar da hakkinsu akanka.
Wani haki take dashi a wajena yarinyar data hada min banga a tona min asiri ai
duk naji komai shiyasa kikaga ban saka kaina a rikin kawu da yazid ba dukko yadda
mama taso naki hakan dole sun kyaleni yanzu.
Shi kawune bai kyauta ba ai tunda yasan amana aka bashi don me zaisa kudinsu
gaba ya cinye har da aure da dukiyan marayu don Allah ?
Murmushi yayi ya mike tsaye yana fadin ke aurema da yayi shiya dameki ai auren
amman da matarshi tacine ya fita mata tanan .
Da kinji abunda yayi da gudin aida baki kara kallonshi da daraja nace to Allah
ya sauwaka ya fita yana fadin zaije family house dinsu a can zaiyi magariba.
Nayi mashi Allah ya tsare ya dawo lafiya da haka ya mantar dani takaicin kishin
daya fara min tukuburin a zuciyana .
Don kodaya fita ban koma takan maganan tafiyansa ba sai zancen kawu da yayi min
ne ya tsaya min a zuciyana.
Ni dama mutumin yana da zubin munafukai inkin gashi haka kuma tunda ya fara sukan
Yanda akan kwanciya asibitin ta na farko yasa na fara kinsa a raina.
Lamarin yaya kuma nasan dole dai ya koma wajen matarshi dama tunda yanzu alama
ya nuna ya samu lafiya sosai tunda na dukufa da mashi addu,oi da bashi makarun dana
amsa a gida tun wancan lokacin da gardama yayi yawa na kwashe abina na boye sai
yanzu nayi mai amfani dasu yadda akace.
Don kiri kiri mama ta nuna a daina mashi amfani dasu tafi amincewa da wanda suke
karbowa da kawu ko kawu din ya kawo shi kadai ayi amfani dashi.
Kamar yadda yace din kuwa washe gari karfe biyar yayi muna sallama ya nufi can
sai naji gidan ya koma min shiru a lokacin.
Na dawo falo na zauna har akai magariba kafin na shiga dakina nacewa Biba idan
ta idar ta sameni daki sallah magariba nayi na jira isha nayi kafin na shiga wanka
na fito na gyara jiki ranan banjin cin abinci bread da gesha gwagwani nake so shi
muka zuba a plate na dan kara garin yaji mukaci.
Saidai su sun kara da abincin ranan dana aje masu don Aminu bai wasa da cikinsa
abinci yake kwasa sosai abinshi.
Tunda na gane haka kuma nake shake mashi abinci a kulansa sai yaci ya koshi tas
yake share abincin sai kula.
Ashe dayaje can gidan ya shiga gaida mama take fadin yau ko ya bace hanyane
yazo da yamma gidasu tunda matarshi ta hanashi kula kowa nasa yanzu sai ita kadai
da yan uwanta ?
Yan uwanta kuma wasu yan uwansu ke zuwa wajensu kuma mama tace nasani malam
kaban mamaki kwarai wallahi da wanan yarinyar har zaka iya zama ta juya ka ?
Nasan zaka dawo ai tunda nima ban zauna ba don ba zan saka ido ina kallo na
haifawa yan daji kai ba su suka iya balleni ?
Iyawan me kuma mama dama kwanakin dana diba ke nan zanyi a wajenta don irin
hakkurin da tayi dani da banda lafiya na kuma ba Asmau hakkurin hakan kafin naje
kuma ta yarda da hakan itama.
Inma kinje wani wajene akan hakan mama sunci kudinki a banza wallahi kafin
yacigaba ta katseshi da fadin .
As,maun me can don Allah ana batun mutanen arziki Asmau wayau da ita ko wauta
koma meye saina nunaqa yarinyar nan tayi kadan wallahi.
Dama tafi yar uwarta rawan kai ko a yanayinsu ba daya bane da yar uwarta don yar
uwarta na boye halinta zaki dai bata kudinki ga banza mama.
Kawu dai ya sauya maki halin ki a yanzu da karfi da yaji wallahi irin abin nan
baida kyau mama komai mutum yace bai barwa Allah sai wanin Allah yafi masa wanan
hanyar halakace babba wallahi.
Au ashe kai malaminefa mai da,awa ai ban sani ba saika kafa munbari kofan gidan
nan kace ina wanan aikin mama ai gaskiya yaya fada salima dake zaube ta fada.
Ta mika mata hannu tana mata dakuwa tace Allah mama har an soma gulman ki yanzu a
gida kan hakan don Allah mama ki bari hakan baida kyau.
Gashi yace Asmau tasan zaiyi hakan ashe kullum mama ke kika tashi shine anci
amanan Asmau da yake munafukace ba ?
Waya sani ko sayar mashi da kwanan tayi don jakkanci haka kawai zan sake namiji
zuwa gidan kishiya tsawon wata da dan kai doluwa kawai na banza.
Yarinyar nan badon mutuncin iyayyenta ba da tuni nayi gaba da wagarar banza kawai
mara aji mace chusu kamar an shuka dusa tunma data kara kiban nan sai duk ta koma
wani iri da ita wallahi.
Haka kuma danki ke son taba saratu ta fito tana fada jin ya dade da fita dakin
tunda salima ta soma magana ya fice abinshi.
Ni banga abinda yaya ya gani gun Asmau ba tun tana da kurciyarta ita ba kyau ba
ba tsarin macen shiga gaban mota ba ita dai gata nan wace iri da ita ba kuma gyara.
Ummh mai kyau da gyaran kuma ance karuwa yar kauye kowa dai yaji da nasa ku
barshi da matansa son Allah salima ta fada tana mikewa tsaye.
Ni mama salima tana ban mamaki wai sai taita nunawa kamar tafi kowa son yaya j a
gidan ni abin yana ban mamaki wallahi.
Salima din dai bata juyo ba ta shige daki sai saratun ke fadin wai ya dawo nan
ke nan kome naji yana fadin wai sun shirya hakan da Asmau ne dama ?
Munafuka amma bata fadi ba idan taji kina fada sai dai tace ba komai ai mama
ashe da saninta yake can duk dadewan nan ?
Allah ba din mugun fata baida kyau ba danace yadda tayi makircin Saiba ta fita
itama Allah yasa wacan bafulatanan banza ta futar da ita gidan nan don bata da
amfani sai zuba wasu yaya masu gajerta dasu.
Iya ruwa dai fidda kai abinda ke hada ki da yan uwanki kenan kuke fada zaki soma
kuma aibanta mashi yayanshi ke meyasa kike hakane wai ?
Shiru tayi don tasan tunda mama ta kwabeta zancen yaci mata rai da gaskene da
ake cewa mama din tana da son jinin ta ita tasan hakan ba karya bane da ake fadi.
Don indai yaro dantane ko jikinta tana son abinta ta gano hakane tun akan diyan
habu duk yadda taki maria tana son yayanta data haifa da danta wanan yasa ta kame
bakinta tayi shiru.
Tun a lokacin ba wanda ya kara wani zance a kai game da daaowanshi gida din
kamar yadda suka dauko zancen da farko da ace mama ta kama zancen saratu ta fitone
tayi maganan aminiyarta lokacin.
Sai gashi uwar ta katseta da zancen yasa tayi shiru can kuma bangaren itama
Asmau daya shiga wajensu ta nuna bacin ranta a irin sallon nata kishin don cewa
tayi dashi aida ya zauna can din ya kara kwanaki.
Ba abinda ya dameta sai takura masu da zaiyi a yanzu da gyara wancan kinyi kaza
kinyi ba daidai ba ke kazamace hakan kuma baisa ta gyara halinta.
Aiko yana shiga daki ya fito ya fara fada yana fadin tunda ya kwanta jinya
baijin an taba share mashi dakin nan ma ?
Ta yaya mace zata zauna bata da aiki sai kazanta da lalaci ya nufi tsintsiya ya
dauko ba abinda yafi bashi haushi kamar bandakin dayaje alwala har wani renewa yayi
saboda kazanta.
Ganin hakan yasa ta karbi tsintsiyan a hannusa yasan ba gyaran kwarai zatayi ba
amma ta fara kore wanan kazantan dake daga mashi hankalinsa.
Koda ya dawo bayan sallah isha,i ya samu tana girki wai dama basu da niyar dafa
abincin dare sai kuma gashi shine ta dora girkin dafa dukan shimkafa tayi.
Ya shiga daki tagama ta kirashi take fadin ga abinci nan an gama ya dan jima ya
fito ya dubi yaran dake kwance har sunyi barci cikin tausayi yasan basuci abinci ba
sukai barci.
Yake fadin sunci abincu tace kafin tagama sunyi barci nan ya soma fada da ita
waike Asmau wata irin mace ce ke don Allah ?
Wanan hali naki dole mutum yayi aure ko bai shirya hakan a rayuwansa ba ai ki
duba yaran nan kefa kika haifesu Rahama dana fito gidanta yaran dake tare da ita
irin dadin da sukeji a wajenta.
Ke yaushe zaki hankaline wai Asmau kefa kika haifi yaran nan zaki barsu su kwana
da yunwa shiyasa a kullum suke fige kamar kar Saiba tabar gidan nan komai naki a
yanzu ya kara tabarbarewa ga baki daya wallahi.
Dama ai ka saba fadan tafini don kafadi haka matanka sunfini aiba yau ka saba
fada min hakan ba ?
Ni wanan bai taba damuna tunda nasan ina kokarina kaine baka ganin hakan yaja
tsuki ya bude plate din abincin data kifa wani saman wani da niyar yaci.
Abinda ya gani shiya tunzurashi ya mike kawai yabar falon zuwa dakinshi dama
tsamin falon ya isheshi a cikin daurewa yake karfin hali.
Haka a yadda yaken ya dan kara gyara dakin ya feshe da kamshi har zuwa ban
daki ya samu waje yana maida numfashi.
Haka ya kwana da yunwarsa cikin dare kodaya falko ya ganta a bayansa tana nasari
da safe ya fice sallah daya dawo wajen iya ya nufa.
Ya kai karan Asmau din iya dai hakkuri ta bashi tace idan ya matsa ni zai shafawa
laifin yanzu don kowa zaice ban barshi a banza tunda ance so nake in kore su in
mamaye gida ni kadai yadda yar uwana take zaune ita kadai.
Iya din dai ta kira Asmaun tayi mata fada sosai ta kuma gaya mata ta kama kanta
in har ta bari ta tunzurashi ya kara aure ita tasani.
In kuma so takeyi Saiba ta dawo ta hanata kwaciyan hankali to ta matsa tasan
komai yana iya faruwa don da ya auro wata gara ya dawo da saiba din dakinta.
Wanan zance shiya daga mata hankali sosai in akwai abinda ta tsana taji anyi
zancen dawowan saiba gidan gashi iya ta fara fadin hakan kuma .
Taji fadam iyam don kuwa a ranan ta wuni gyaran gidane tun safe ga girki data
daukeshi wani jar duniya a wajenta runda yace bata iya girka abin kwarai ba shine
ta zage tayi masu tuwo da miyan shuwaka.
Yazo gidan mu ya dubmu lokacin sha dayan rana har ta gwauta koda ya shigo ina
daki ina barci naji ana ja min kafa hakan yasa na falka.
Yana tsaye cikin fararen kayan daya saka a jikinshi annurunsa daya fara dawowa
lokacin sai naga ya dan gushe min ga gani.
Kun tashi lafiya ya fada na tareshi da fasin ina kwana ya amsa min yana fadin kun
bar gida bude kun shige daki kowa na barci.
Nayi mika ina fadin mun karyane naji kasala ya kamani nazo na kwanta bansan nayi
barcin bama wallahi na fada ina kokarin tashi zaune.
Falin muka fito tare mun dan taba hira ga kuma girkin dana dora muna na rana
yana gidan saida akai sallah azahar ya fita.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/29, 07:53] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
8️⃣9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Zan iya cewa cikina a yanzu yakai wata takwas a jikina a lokacin kuma zancen
services din mu ya fito haka na shiga na fita na samu result dina yayi kyau.
Wanan daman na ciki akai amfani dashi banje ko ina ba ga sha,anin bukin saratu
wanda ya taso a yanzu don mijin data samu kamar a shirye yake da zancen auren .
Don bai tsaya jan wani lokaci ba duk abinda ya dace ayi na al,adan aure yana
gabatarwa ba bata lokaci wanan yasa hjyn rawan kai don ganin tayi sa,sn mijin aure.
Don ita salima mijin bai karasa ginan shi ba don shine ba za a hada bukinsu ba a
cewan mama wanda ya shirya ayi kawai kowa da sa,anshi yake zuwa duniya dama.
Wanan yasa suka tsayar da ranan aurenta ita kadai ba tare da yar uwarta salima
ba tunda mijinta bai shirya mai karatu dama na fada maki yarone kusan sa,an juna
suke dashi a cewarsu alhalin kuma ya girmeta da shekara biyar shi din.
Don dai basu sone suke fadin hakan