Showing 156001 words to 159000 words out of 328222 words
Chapter 53 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
kada
shedan ya ribance mu a lokacin.
Anty Salma ta fada min duk abinda zanyi ko ma meye kada in yarda in shaga hakkin
abokan zamana don alhaki yana waiwayan mutum watarana don haka nake kiyayye wanan
huduban nata.
Ruwa da cup na shirya a ture nakai mashi dakin inda na samu har lokacin yana
kwance a yadda na barshi bai min magana ba kuma har na zuba na fita daga dakin.
Duk da banji dadin hakan ba amma ya zama dole in kiyayye hakan kada mu fada ga
halaka dama ta fada min su maza babu ruwansu da hakan wani lokaci matukar zasu samu
biyan bukatansu.
Dakina na koma inda a nan na zauna don kunyan su Nafisa da nake ji lokacin ban
fito ba har akai sallah magariba ina dakin isha,i tayi nagabatar still bai shigo
dakin nawa ba har lokacin.
Wanka nashiga har na fito na shirya cikin wani dogon riga ina sai lokacinne ya
shigo yana fadin ba zan samu abinci ba ke nan ma ?
Cikin mamaki na dago kaina ina fadin abinci kuma yaya naga ba gidan nan kake ba
shiyasa ban hada ba ?
Baiyi magana ba ya juya ya fita yana fadin ina falo ina jira hakan yasa na mike
na fito falon na sameshi zaune yana waya na shige kitchen din tare da tunane idan
na fito zan kara fada mai bafa gidana yake idan ya mantane.
Saida na aje komai dana san zai bukata inda naji yana waya yana sanar da yaya
habu saidai da safe idan ya shigo yasa na koma gefe na zauna ya gama wayan na dan
marairaice ina fadin.
Yaya ya dago kai yana gyara kansa lokacin zai soma cin abinci nake fadin ba
gidan nan yakamata ka sauka ba .
Gidanwa zan sauka ya fada yana yanko loman abincin dake gabanshi yadda ya
kalloni yai maganan yasa nayi kasa da kaina na kasa bashi amsa a lokacin don haka
naja bakina nayi shiru.
Haka falon yayi tsit lokaci guda har ya gama bai kara magana ba ya wanke hannu
na mike na kwashe kaya zuwa kitchen.
Saida na daurayesu na fito ban tsaya falon ba nashiga dakin su Salima ko wacensu
na kwance da waya a hannunta salimane ta dago kai ta kalleni tana fadin.
Da har zan maki tsiya ai ince don mijinki ya dawo kin manta damu yau nace haba
dai anty Salima shida zai wuce can ya barmu nan tare daku yaya za ayi in manta daku
kuma ?
Ok a can zai kwana ke nan nace haka ya dace anty tunda da zai tafi daga gidan nan
yai tafiya ranan wai wanan dogon lissfin sai ku masu kishiyoyi.
Wanan yasa ban ra,ayin auren mai mata wallahi kinga kosu a can haka wata rana
sukanyi ta fada akan kwanan nan ko dan zaman nan da yayi a nan da a can kike sai
anyi fada a kansa yau .
Tundai ace maki wanan Nusaiba da bata aje komai ba sai bakin kishin tsiya don
jaraba kullum fadansu dai in yaya ya dawo akan kwanane sai iya ta raba masu
gardama.
To yaya mutum zaiyi salima in Allah ya kaddara mashi auren mai mata kamar dai
irin na Rahama din nan ai kinga kawai za ace mukkadarine auresu da yaya nafisa ta
fada.
Hakane fa amma dai nikan gaskiya ban iya hakan baki ganin maria ita Allah ya
rabata da wanan wahalan daga ita sai mijinta da dansu baki alaikum.
Karan rufe kofan da yakeyine ya sa sukai shiru suka dubi junansu cikin mamaki
Nafisa tace ina ganin fa a nan yaya zai kwana ?.
Nace nan kuma tace to ba gashi ya rufe gida ba alaman ba can zai kwana ba ke nan
tunda kinga hakan ?
Na danyi shiru kafin in mike na samu yabar falon a lokacin dakina na nufa cikin
mutuwan jiki tunda nasan hakan zai jawo min magana sosai a wajen matansa.
Bandaki na shiga don na rasa me zanyi lokacin saboda jikina da yayi sanyi da
hakan ruwan dumi na surka nayi tsarki dashi sosai na danyi shafe shafena na mata
dana dan sani na fito na zauna na kara mulke jikina da kamshi na daban wanda sai
nasan miji na tare dani dole zan shafa don ban ma taba amfani da humra din ba bakar
humra ce dake da hadi a cikinsa don zaki iya ganin sassaken da aka hada da humran
kasan kwalban.
Ina bakin wardrobe dinane ina daukan rigan barcina ya kasa hakkuri ya biyoni
dakin ban san da shigowansa dakin ba lokacin saida ya tabanine na dan razana ina
dagowa.
Yana tsaye ya saka hannu ga aljihun rigansa na dago ina fadin na dauka ka tafine
ai ba tare dayayi magana ba sai jin nayi ya daukeni cak zuwa gado.
ZAMFARA STATE
zaune take saman kujera abakin murhu tana tsigan alaihu yarta karima tashigo da
kayan islamiyansu a jikinta.
Sallaman yarinyar ta amsa ta dago tana fadin har kun dawo ke nan amma yau kun
taso da wuri karima ?
Ba a tashi ba mama na dawone ta shige daki uwar ta bita da kallo ta juya taci
gaba da aikin ta yar tana daki bata fito ba can tasa mata kira ta amsa ta fito tana
fadin gani mama ?
Kallo yar dake fitowa daga daki tayi ta juya taci gaba da yanka alaihun data
tara a hannunta tana fadin ki wanke kwanukan can da aka tara.
Ta amsa a cikin sanyin jiki ta sake juyawa zuwa dakin nan ta dakatar da yar
nata tana fadin kin shigo sai tukuburi kikewa mutane kamar an maki wani abu ?
In baki da lafiyane ai sai ki fada amma kya kamawa mutane hade rai a cikin gida
haka mama ni lafiyata kalau karima din ta fada tana shiga daki.
Ta fara wanke kwanukan ke nan yan uwanta suka shigo suna hayani suna fadin muna
ta nemanki ashe kin dawo gidane ke muga suwaiba tace taga kin nufo gida kina kuka.
Tashigo gida tana cicika na tambayeta tace ba komai ita ta sani tunda zurfin
cikin tsiya yayi mata yawa ita.
Kodai zancen baba kikewa kuka anty Karima kanwarta mai,gado ta fada tana kwabe
hijab din ta nan uwar ta juyo tana fadin zancen baba da yai me kuma ?
Kallon kanwar nata maigado tayi tana mata alaman kada ta fada amma ina bai
mai,gadon taba da amsa ba Zarah ke fadin wai don ance baban mu zaiyi aure ?
Wani baban naku baraka ta fada tana sake yukan dake hannunta baban na nan gidan
mana mama su Rabi,a ke fada muna dazun da zamu islamiya.
Wai har ya biya sadaki satin sama za a daura aure shida anty Safiyan gidan aska
.
Kirji ta buga take fadin babanku fa tace haka sukace shima baba wallahi ya rasa
wace zai aura sai wanan mai zubin yan erea din don Allah ?
Mikewa tsaye uwar tayi tana fadin a ina kukaji labarin nan wajen su Rabi,a mama
ta nufi daki lokacin ita karima ta mike tsaye tana fadin a,a mama don Allah ina
zaki ?
Kada kije gidan su Rabi,a tunda a sace ta fada muna tace wai
ba,a son gidanmu a san da zancen saidai muji an daura aure kawai wai inkiji ba
zaki bari ba.
Ni wallahi mama yadda baba yaje yana bataki wajensu shine yayi min zafi.
Bata jin me yaran ke fada a lokacin ganin ta fito da hijjab dinta yasa yaran
tareta suna hanata fita tare da rokonta da kartaje don Allah dariya za ai mata
tunda duk unguwa sun sani ashe .
Ke ban hanya gidan uwani zan tafi ta inji kome ke faruwa uwani tasani wata
uwani kuma mama uwanin da kullum a nan gidan nata anty Safiya ke tsayi da maza.
Da kyar yaran suka hanata fita ta koma ta zauna tayi tagumi tana jin wani irin
abu yana rufe mata zuciya lokaci guda.
Lalai in wanan zance gaskiyane malam ya cuce ta kuwa da kudin gadonta yake nufi
zai auro mata kishiya ?
Kishiyar ma Safiya da suka sha artabu da ita kafin ta samu tabar mata miji taje
kauye tayi aure ashe data fito din nan ma suna tare bata rabuba dama lafewa yayi
don ba ko sisi a hannunsa.
Sai yaran suka karasa girkin ranan gashi maigidan yaje kauye cin kasuwa bai
dawo ba ko zai dawo sai cikon dare sosai sunkan iso saboda nisan garin da suke zuwa
din dauko hatsin.
Zancen yaranta gaskiyane Safiya bata wanka ta bushe tana gidan uwani ko yaushe
wanan yasa halakansu da uwani din a yanzu yayi sanyi sosai tunda ta fahinci hakan.
Abincin da bataci ba ke nan ranan don yadda take jin kanta tana ji a ranta har
in zancen nan gaskiyane hakan zai kawo masu matsala da mijin nata kuwa.
Bata yarda ta kwanta ba tana dakon jiransa ga wayanta ba caji balle ta kirashi
taji yana ina don ta fara tabbatarwa tun a wayan.
Shiko a daidai lokacin suna cikin daji motarsu ta lakace masu a daji har barci
barawo ya saceta bata san lokacin daya dawo ba sai asuba da yake tayar dasune ta
gane ya dawo gidan ashe ?
Ta daurene don kada su raba gari da asuba mutane suji hayaniyarsu har yaje sallah
bai dawo ba kuma saida gari ya waye tangararan ya nufo gida da ledan kosanshi daya
sayo ya hada da kunu.
Tana jin dawowan shi din batayi magana ba saida ya samu waje ya zauna yana
kiran zarah ta dauko mashi kununsa ga kosanshi ya aje tare da kullin sugar dari
aganshi.
Baba ba a dama kunu ba yau yarinyar ta fada cikin mamaki yake fadin ba dama ba
saboda me ?
Lokacin baraka ta fito daga daki tana fadin bandama ba don banjin hakan kana iya
zuwa wajen karuwan ka ta dama maka ai ?
Karuwa kuma Baraka a ina na sameta kuma ya fada yana mata kallon mamaki tace eeh
karuwan unguwa da kuka saba sheke ayan ku da ita mana.
Kaje ta dama maka dama ai kun saba da hakan dama malam cutata kaso kayi ka
yaudareni kayi aure ban sani ba ?
Aff zancen banza ke nan to tunda kinji baraka meye na yaudara a ciki aurene fa
sunnan ma,aikin Allah zan raya kike kira da zina ?
Lalai malam ashe kuwa zancen nan da gaskene auren kuwa zaka kara wallahi baka
isa ba kaban kudina dake hannunka in yaso kaje kayi ta auren ka bai dameni ba ?
Kai mata hooo yanzu ke wanan abin yar yakai kiyi min gori a kansa don kawai zan
kara aure baraka ?
Ai kaji abinda nace ba zancen gori a cikin zancen nan ka bani kudina kawai shine
magana tunda da bakai zancen aure ba sai yanzu dana dankama gadona a hannun ka ?
Gadon mu dai tunda ko mutuwa kikayi yanzu nida yaran nan muke da gadonki baraka
kuma aure ba karya aka fada maki ba aure zan kara kiyi abinda zakiyi .
Kudi kuma banda su yanzu a hannuna kin dai gani kema da idon ki sai ranan da
kayan nan suka zama kudi na sayar in baki kudin ki.
Aina dauka zaki min adalci shekara nawa ina zaman hakkuri dake a gidan nan ban
kara maki kishiya ba ashe ban sani ba son kanki yayi yawa har haka baraka.
Meye amfanin namiji kama ya zauna kullum da mace daya kamar laya a wuya ba kari
kullum kana fama da abu daya kiyi min adalci ma ?
Kuka tasaka sosai lokaci guda tana fadin malam ka cuceni ashe duk dadin bakin da
kake min don ka karbe kudin nan ne kayi aure ?
Kudi ban je gidanku na karba ba ke kika kawo min su nan da hannun ki ko kinga
naje gidanku na rokesu subani kudin ki ?
In zaki zauna kiyi hakkuri ki dubi diyan ki ki zauna in kuma baki hakkuri
Baraka hanya a bude take kya iya tafiya nikan aure ba fashi jumma,a mai zuwa insha
Allah.
Shi munafukin dan naki daya fada maki bai maki karya ba na biya sadaki da ko mai
Safiya tana matsayin matana a yanzu kije duk wanda zaki fadawa na karbi dukiyan ki
a garin nan ki fadi bandai je gidan ku na tasa yan gidan ku gaba suban kudinki ba.
Don haka ba a hanani ra,ayina a yanzu aurene ba fashi na fada maki na biya kudin
komai na al,adan aure.
Ya mike yasa kai ya fice daga gidan ya barta nan tana ihu hannu a kai wanan
yasa Aliyu dake dakinsa na soro ya fito yana tambayan abinda ke faruwa ?
Sai maigadone ke fada masa wai baba aure zai kara kuma da kudin mama fa ta fada
cikin wani yanayin damuwa a fuskanta zuciya da rauni.
Kasan me kuma yaya wai wanan matarfa yar bala,in shiya baba zai aura na sani ai
bashi nake son fadawa mama ba lokacin taki saurarena.
Don da bata nan wallahi kullum sai kowa ya rufe gida suna waje suna hira har ana
gulmansu a shiya sau nawa ina haduwa da baba wajen mai nama yaje a yanka masa wajen
hiran mu ?
Cikin kuka Baraka tace shine baka fada min tun lokacin in sani ba sai yanzu da
yaran nan suka jiyo sukazo min da labarin ?
A,a mama nayi niyar fada maki a lokacin kikaga kamar kudin ki nake so a lokacin
kika zageni ni kuma nayi shiru.
Shima baba ya dauka zan fada maki tunda duk muka hadu sai yayi min kashedi duk
yaji zancen nan a bakin ki sai ya saba min rai ni kuma na share nabar zancen tunda
kin yarda dashi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
5️⃣3️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Kawu daudane zaune a gaban iya data kura mai ido cikin mamaki don jin zancen dayake
koro mata a lokacin na karin aurensa dayayi.
Saida ta nisa ta sake fadin dauda kace ka kara aure ma,ana har kayi auren ke nan
ma ?
Wallahi an daura auren yau kimanin sati biyu ke nan don dana tura su baffa
neman aure shine iyayyenta sukai karamci tunda ba budurwa bace a daura auren
gabadaya lokaci guda.
Kwarai kuwa to me za a tsaya jira kace ka fasa hakan ai yayi sosai gara da aka
daura din ma yafi sauki yana washe baki yace wallahi iya nima haka nagani.
Ehh lalai abu yayi kyau tunda duniya sabuwa fil a yanzu gidan ka dauda ni ba
zance kada kayi aure ba don Allah ubangiji ya yardan maka da hakan kaga kuwa ban
isa ince don me ba dauda to amma ina fatan ba dukiyan yaran nan kake facaka dashi
ba dauda ?
Assha iya assha haba ina sane budi daine ubangiji yayi min a yanzu amma dama ina
da niyar hakan a raina sai yanzu Allah ya nufa ayi.
Wananfa shine damuwata da auren ka a yanzu karka samu dukiyan mutane kana facaka
a cikinsa don amana da cancantan hakan yasa suka mika maka.
Kaga ko amanace mai nauyi ya hau kanka dauda amana ko wuyan sha,ani ke garesa
musan irin wanan amanan dukiyan marayu ba kowane ke yarda ya rika ba.
Ina zan yarda iya asalima dukiyan nan basu hannu don ban yarda na ajesu a wajena
ba don haka karki ko kawo wanan tunanen a zuciyarki iya.
Ai Dubu mutumce samun mai irin halin dubu akan zumunci sai antona gaskiya
donshine nake taka tsantsan da komai nasu dake hannuna.
Ni dai Ka daiji abinda na fada kayi hankali a samu a rabu lafiya ni tun farko da
kunji maganata da ba,a karbi kudin nan hannun yaron nan ba da an barshi dasu ya
dinga juyawa a wajensa yafi kwanciyan hankali amma kunce a,a kai da yar uwarka
Allah ya sauwaka ya amsa da amin.
Sun gama hira zai tafi ya fito da goro manya farare ya aje mata a gabanta yana
fadin iya ga wanan na biya na sayo maki da zanzo.
Tayi godiya tare da fadin to a dai kula don Allah kuma a hada da hakkuri da iyali
baki daya hafsatu dai kasan irin hakkurin da tayi dakai na tsawon shekaru a gidan
ka don haka ayi adalci don Allah.
Kitchen nake ina hada breakfast don ina son shiga school muna da test amma sai
zuwa rana don haka na tashi da wuri ina yan aiyukan gida.
Anty Nafisa ta fito ta sameni muka gaisa take fadin ashe har kin fito yanzu nace
bari na fito na dora abin karyawa duk da bansan abinda zaki dafawa yaya din ba yau.
Murmushi nayi ina fadin ai har na hada anty nagode yanzu ma miya nake son
hadawa anjima dana dawo abinci kawai zan dafa.
Banjin zankai rana a gidan nan da nace ki barshi amma da wuri nake son zuwa na
gyaro dakin mama dan kila yau din nan zasu dawo.
Allah ya dawo dasu lafiya na fada ta amsa da amin tace sai kuma