Showing 189001 words to 192000 words out of 328222 words
Chapter 64 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
irin tasa ai
sai yar uwarta da suke kira da Laraba tace nikan dai haka zance kina nufin in bata
gane komai zata kai hakane a gidan ai da ta bar gidan don cin fuskan yayi yawa ai ?
Gaskiya kowa da irin nasa suna dai rigima sosai amma kuma ba wai yadda ake nufi
suke zaune ba don naga yana kokari da kowansu sai yamma ranan suka bar zaria.
Murmushi nayi don tuna hakan nasan mutane akwai fadin abinda bai shafesu ba
nasan ko yanzu nima da akwai abinda ake fada a kaina zama tare dasu din.
Muna shiga gida iya ke fadin haba dai har ina batun soma cigiyar ku a gari haka
shiru daga fadin bari muje mu dawo yanzu sai kuma shiru ?
Yakai zaune yana fadin iya wanan mai kukan banza dince na fita da ita taga dangi
dangina su ganta kada in barta gida ta cika muna kunnuwa da kuka haka .
Kuka kuma jam da akai mata me yayi dariya yana daukan ruwan da Biba ta aje muna
yana balle gora yace kinsan duk abinda mama suka fada dazun ai tana ji nasan shine
yasata kuka kila ?
Ehh banga laifinta ba don ko nice hakan zanyi tunda nasan banyi komai ba don na
auri danki kawai zaki dauki karan tsana ki saka min ?
Ba laifin kowa bane kaifin Daudane shike zugota anzo nan sai ya noke zai jini ai
don bashi na basu dama so nake mu kebe dasu in masu iyaka da hakan .
Ta bari daga yau idan ka taka kafa wajenta ta fadama duk abinda tayi niyar fada
amma a gaban yarinyar nan haka kiri kiri ?
Tajuyo gareni tana fadin kinga mutumiyata irin hakan ba kuka akeyi ba nasan
akwai cin rai amma ki daure kada ki kara yarda ki nuna abin yanaci maki rai don in
kin yarda tasan hakan ba zata daina ba tunda halintane hakan ai.
Abunda na dauka shine harda son da Dubu keyiwa yaranta shine yake sakata hakan a
yanzu tana ganin auren yaran nan da kukayi yana son yasa kan yayan ta ya juye ta
kasa gane masu.
Wanan shine kawai abinda tunanena yake bani akan halin nan nata don ko zama
kayi da ita a yanzu kace mai yaran nan sukai mata ba zatace ga laifinsu ba amma zan
zauna din inji inda matsalan yake don a gyara.
Iya da kin barta don kada ta dauka kuma anyi wani abune yasa kike tambayanta
idan anyi hakkuri ai abin mai wucewane in sha Allahu.
Matsala dai a yanzu shine na farko kan auren yaran nan Saratu da Salima ya
kamata suyi aure hakana zaman nasu ya fara damuna har ita Nafisa nake son a hadasu
lokaci guda in hakan zai samu.
Wanan shine daidai don matukar wanan saratun na gaban mahaifiyar ku a kullum
zancen bai karewa tunda itace mai kai mata tsegumi akan matanka saidai taki yarda
itace matsalan rayuwan nata.
Nan na mike na barsu suna zancen sun jima don bai fita ba sai kusan magariba
nasan daga masalaci can gidan ya nufa wajen matanshi yakai goma na dare bai dawo
ba.
Koda ya dawo din muna falo zaune ana hira ya shigo da ledoji a hannunsa a gaban
iya ya aje ya mika mata daya yana zama yake fadin na rasa irin sakaci na Asmau
iya ?
Wai ace mace na jego bata iya kula da kanta balle yaron nan koda naje gidan
gashi tace baida lafiya amma ta sake fanka har karshe ko rigan kirki bata sakawa
yaron nan ba iya ?
Asmau ai halinta sai Allah na rasa meye matsalan yarinyar nan ko wanan babban
ai Allah ne ya raya mata ita don komai safiya haka zaka ganta da dan pant a jiki in
anyi magana tace zafi.
Yaja tsuki na kalleshi a gajiye ina fadin abinci fa ya dago yana fadin bar
abincin nan Rahama wanan dai zan danci in kwanta tunda naje muka fita zuwa asibiti
sai bayan isha,i muka dawo.
Yanzu dai likita ya fada mata ai idan kasheshi take sonyi ai sai ta matsa kada
ta kula dashi din na rasa meye matsalan Asmau wallahi ?
Bata da matsalan komai sakacine kawai yake damun ta inka duba kamar ai haka yan
gidansu suke a watse kowa abinda yaga dama yakeyi a gidansu.
Rayuwane na zaman kishin matan yanzu ya haifar masu da hakan tunda kowa dansa ya
sani a gidan ba mai tsayawa yayiwa dan wani fada kan abinda ya dace yayi makyau in
bashi ba ko ita wanan ma,aikaciyar matan mahaifin nasu ai naga zata iya basu
tarbiyan daya dace ai amma ina sun yafawa kansu zama na cin kai a tsakaninsu kowa
na jiran wani sheri ya fito daga dan uwansa.
To irin abinda akewa gudu ke nan ga wanan zaman ko kuna abinku kada ku yarda ku
hada da yaran ku kuyi kishin ku ku kadai su kuma yara ku barsu suyi zumuncin su
tunda Allah ya hada zama a tare.
Na mike a kasalace zuwa kitchen na kwaso plate na kawo masu na iyan na fara
budewa sai kamshi ke tashi na zube mata namane na rago da aka gadashi da zafinsa da
yaji sai abinsha.
Haka sauran ledan kuma suma suke ina kokarin zube masa nasane wayanshi ya dauki
kara ya duba naga ya dauka a yanayin yadda yake magana don jin da nayi yana fadin
ni gani gida ai.
Ba nashiga sallama dake kina ganina kikaki aje wayarki ba na juya nikan wajen
biba ina fadin hjy habiba ko kin koshine sai gobe zakici ?
Da sauri take fadin haba anty saida idan zan aje naci na iya gobe naci nawa na
fita dashi zuwa school ko ?
Kaji yar wayau nice bansan dadi ba miko min nata in karama dashi nan kinji iyan
ke fada muna dariya muryanshi ya katsemu don tsawan da yayi yana fadin.
Wai kina da hankali kuwa Saiba in dawo in maki me tun dazun da nake gidan meyasa
baki fada min ba sai yanzu wai meye matsalanki daine dani haka ?
Look Nusaiba duk abinda kike nema dani fa zaki sameshi ina jin ta kashe
wayartsne shine yasa yaja tsuki yana aje wayan a saman table din gabanshi.
Matarkace ko iya ta fada yaja tsuki yana fadin itace don rainin wayau wai sai in
dawo in sayo masu magani ita da laila yanzu wai ai suma basu da lafiya na kyalesu.
Murmushi iya tayi tana fadin karma ranka ya baci halintane hakan kayi hakkur da
abinka wasu mata basu da hakkurin saka ido akan abinda akaiwa yan uwa sai sun
maganta wanda hakan ke jawo bacin rai a karshe.
To iya haka zan zauna da ita kullum a cikin matsala ban isa inyiwa wata abuba sai
tace don me ni wanan abin ya isheni wallahi kullum ita dai ban mata daidai ba a
rayuwanta.
Shiru falon yayi na dan lokaci ya karaci fadanshi shima yayi shiru din don ba
wanda ya tanka masa kuma dama kuma ai iyance daidai ta tanka ta kuma bashi amsa ai.
A raina nake fadin ke nan har yanzu badani kadai take kishinta ba ashe dukkan mu
ta tasa a gaba tana yaka da kishi tunda naji ya fadi hakan.
Wanan ke nan yasa anty salma fada min cewa zamana kishi irin namu zamane na kowa
tasa ta fusheshi a gurin miji don ba zancen hadin kai a nan don ko an hadadin wata
rana sai anji kanku da wace kuka hada kai din.
Bai jima ba ya mike zuwa daki sai lokacin iya ke fadin ninasan wanan yarinyar ba
zata canza ba ai don kishinta na haukane .
Kinzo kin samu yarinyar nan da mijinta kince ba zaman lafiya ankawo wata daga
baya kuma kince dai ina miji ya fito irinsu saidai a zauna dasu kawai da halinsu.
Aida agida daya kuke zaune na tabbatar da yanzu dole dayanku tabar gidan saboda
fitinan wanan yarinyar da kowa baida daraja a wajenta.
Tsugul naji muryan biba tana fadin iya ai shiyasa maman mu tace mubar zuwa gidan
tunda ko muje bamu samun taron arziki a wajensu.
Tun wani zuwa da mukayi da sallah uncle yace a dibar muna nama muda maman mu a
gabanmu tace an raba nama ya kare har muka fito bata bamu ba .
Habiba daga yau karna kara jin kin tsoma baki cikin irin maganan nan abinda akayi
ya wuce ina ruwanki da kawoshi yanzu ki daina bana so don Allah.
Shiru falon yayi na dan lokaci sai can iyan ke fadin kinji tarbiyan kwarai
haka ake son ya kasance kanayi kana kwabon bakin yaro ko yaushe baka kyale yaro na
tsoma baki a zancen manya ba shine matsalan dake damun uwarku.
Kada ki kara bayan haka duk uwa tace bata kwaba yaro duk abinda ya fada shine
daidai a wajenta to itako da zaman lafiya sunyi ban hannun makafi ke nan.
Ki bari gaskiya ta fada maki ko ita da zancen ya shafa inkin kula bata fadan
kallal kahu a ciki idan anayi don haka kada ki kara kinji.
Iya idan na kyaleta watarana a kaina zatayi kuma ta dauka ai hakan daidaine ban
taba zama dake ba habiba ina maki zancen wata a gidan don haka ki daina don Allah
hakan ba halin kwarai bane kinji.
Bazan karaba anty ko yanzu ma subutan bakine mamanmu ta kwabeni da hakan kullum
naje kuma sai tayi min fadan hakan ta fada a dan maraice.
Saida mukaci muka sha donshi bai tsaya yaci abin kwarai ba na kwashe kayan tare
da biba kafin mu fito iyan ta shiga dakinta na leka ina fadin har zata kwanta ke
nan ?
Tace meya rage min kuma yar nan baku barni da komai ba sai godiya ga Allah Allah
dai ya tashe mu lafiya kuma ya karawa mai nemowa dake mai dafawa lafiya na amsa da
amin na kalli biba ina fadin saura ki kwanta da kayan nan baki sauya ba don har
yanzu kina da matsalan haka biba kije ki watsa ruwa kiji dadin kwanciya don Allah.
Akwance na sameshi yayi shiru jin motsina ya kalloni na karaso ina fadin a
hadoma ruwan shayine naga bakaci komai ba kai ?
Naci abinci da habu a wajenshi ya dawo da yamman nan anfito da abinci ya matsa
sai naci shiyasa banjin yunwa.
Ashe ya dawo ke nan yace ya dawo dazun ashe maria din bata jin dadin jikinta
shine ya dawo da sauri nace bata fada min ba kuma munyi waya da yamman nan tana
fada min zancen haihuwan yar mijin ummah a kaduna.
Ta boye makine gobe sai ki shiga ki dubata idan zaki dawo school amma taji
sauki don naga tana aiki da kanta ai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/C8kkr4INYY7FydHKKKRVhL{2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
6️⃣2️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Rayuwa kenan haka take tafiya da dadi ba dadi ga dan adam amma idan ka saka hakkuri
ka dauki komai a saukake sai Allah ubangiji yasa abubuwa su dinga zuwama a cikin
sauki ta yaddama baka zata ba.
Haka shima rayuwan aure ya kumsa garemu mata idan kina tausan zuciyarki akan
kishi zakiga abubuwan suna zo maki a cikin sauki matuka zaki daure ki ba komai baya
ki dauka a ranki cewa aure bautan ubangijine a gareki.
Hakan ya kasance a rayuwan auren dana tsunci kaina a cikinsa na yaya Jafar auren
da bantaba zato ba ko tsamani nasa akaina.
Haka kuma nake daurewa da duk wani abinda zasuyi min dashi da matanshi ina nuna
ba komai bane hakan a wajena.
Idan yazo wajena mijina idan ya koma gidan matansa kuma mijinsune ban damu da
irin rayuwan da sukeyi a can ba dasu din zan kawar da kaina ba tare da son sanin
yaya yake ciki dasu ba can ?
Duk da yan tsegumin da nakan tsunta nasu abakunan dangin miji cikin zance hakan
ban yarda na sakawa zuciyana damuwa akansu ba.
Bazance bamu haduwa ba mukan hadu can ba a rasa ba don ina zuwa ganin yar uwata
a gidan kuma saiba bata daina kawo muna hari ba da sunan kishi.
Balle yadda na dauki lokaci ban samu ciki ba shima wanan din ya zamo kamar abin
gorine a wajenta don takan sakar min magana a kansa wani lokaci.
Yau,ma daga school nan na nufo don in duba yar uwata dake fama da laulayin ciki
a cikin yan kwanakin wanda hakan ya zamo mata dabi,an da zaran ta samu ciki babu
zaman lafiya a rayuwanta ke nan.
Don ko yanzu likita yace dole sai tayi zaman asibiti irin wancan din da tayi a
baya donshine nazo gidan muyi shawara da ita don ni ta fara nema da zancen hankali
tashe.
Yunwar dake cina yasa ina shiga na fara neman abinda zan aikawa cikina agaji
dashi tace na duba fridge dinsu ko zan samu abinda zanci a ciki .
Yoghout din Rufaida na dauko da cake na dawo saman kujera na zauna na bude ke
nan yaran su saiba din suka shigo part din.
Sun biyo dan wajen Yanda suna wasa ba zance yaran basu sanni ba saidai babu
sabone yanzu sosai tsakanina dasu kamar da amma don sani sun sanni ai.
Haka kuma kowa yasan yaro da daukan ido idan yaga wani abinci a hannun wani
hakan yasa na rasa yadda zanyi saboda idon da suka zuba min din ga Rufaidan dake
hannuna ina sha.
Banda kyakyamin yara donshi nake diba ina basu a baki wanda hakan yayi daidai da
shigowan Saratu part din tazo amsan hairdryer a wajen yar uwata din.
Haka kuma bata sanda na shigo gidan ba sai a lokacin don banshiga wajensu ba
tukunna na nufo wajen yar uwata din.
Har ta karba zata fita sai kuma ta dawo baya tana fadin jimun yan iskan yara da
saka idon tsiya me kuka rasa a wajenku da zaku dawo nan ku rufawa wanan abin ido
haka ?
Tsawa tayiwa yaran suka fice a cikin kuka nace da kin barsu ai munsha tare aini
na basu bata ko tsaya kallona ba ta fita a fusace ta tasa yaran gaba.
Sai bayan sun fita naji maria tana fadin yanzu wanan abin ya isa uwayensu jidali
bansan meyasa saratu take halin nan ba ko shigowa yaran nan sukayi sai tayi masu
jan ido akan su fita zakice ina masu wani mugun abune a nan.
Kyaleta kawai neman maganane irin nata idan da sabo ai yaci ki saba da halinta
bata so a zauna lafiya ita ko kadan dama.
Na mikawa Abbanta roban gaba daya na gyara zama ina fadin yanzu yanda dolene sai
asibiti zaki zauna ?
Ba zaki zauna gida a dauko maki wace zata kula dake ba ninaga kamar hakan zaifi
sauki da zaman asibitin nan tunda kinga dole wancan karon ummah ta zauna dake yanzu
ko ummah tana da aure.
Idan ance tazo ta zauna akwai takura acikin hakan yana da wuya mijin nan nata ya
yarda da hakan gaskiya.
Tace Ramaah abinda nake tunane ke nan mama dai yanzu kinsa ba dadi a tsakanin mu
don tunda ta kula da cikina samu nake wanan wahala naji tana fadin.
Ai hakan ya zama takura ace duk ciki sai an wahala dama abinda akewa yaran nan
gudu kenan kaje ka daukowa kanka wahala yanzu gashi abu ya zamo fitina wa zai iya
wanan wahala ace duk ciki sai mace taje tayi kwance ta mike kafa asibiti.
Dama ai kinsan zata fadi har abinda yafi hakan ai tunda ba yan sonta bane sukayi
hakan kofan da aka turo a fusace yasa duk muka juya lokaci guda.
Ita kanta a yadda ta shigo din ta samemu saida ta raina kanta don jikinta saye
yake da wani dogon riga na atamfa baki daya kode.
Roban youghot din dake hannun Abba yana sha ta kalla ta soma fadin ai dama
nasani akan wanan tarkacen kwadayin zaki mayar muna da yara kamar marasa galihu ?
Haba dai anty Saiba meya kawo wanan maganan kuma anty Maria ta fada cikin tsawa
take fadin don Allah rufa min baki kinji malama.
Shi Rufaida din inba abin yaro ba nawa suka sha da zasuzo nan ana yan masu a
hannu kamar wasu almajirai dasu ?
Ku ya zamawa bakon abu har kuke kwadayinsa koda yake ba abin mamaki bane don ba
asaba ganin hakan ba sai a nan din ake samu kuma dai kudin ubansune dai ake ci ko
saukin abin ke nan dai daga yau bance wata ta kula yata ba balle a bata wani mugun
abinda za a sabauta min ya in rasa gane kanta yadda akaiwa ubansu.
Wanan kuma ke kika sansa ai don bamu gaji mugun abuba balle muyiwa yarki don
baki tsarewa kowa komai ba balle yarki
To mara kunya nasan idan ita bata tanka ba dama ke zaki tanka ai nace kwarai
tunda ba tsoronki nakeji ba kuwa baki da wuta baki da aljannan sakani akan me zanji
tsoronki Saiba ?
Kazan uba nice ma Saiba haka gatsau a bakinki nace kina da wani suna da yafi
hakan ne a bakin mutane Nusaiba.
Na fahinci sanyin da yar uwata keyi masu ya jawo raini a tsakaninsu tun ina
gidan wanan yasa a yanzuma nake son in kakabe hakan