Showing 102001 words to 105000 words out of 328222 words

Chapter 35 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

wanda zan fara tunkara da zancen nan saikai
habu don nasan zaka sama min mafita in sha Allah.
Soyayya kuma J kana da mata biyu fa a gida me zaisa ka fada tarkon wani soyayya
kuma a yanzu again ?
Nima abinda nake duba ke nan Habu abin mamaki ban taba tunanen zan fada tarkon
soyayya irin haka ba lokaci guda sai gashi Allah ya jarebeni da hakan .
Lokaci guda habu Allah ya jarabeni da matukar son yarinyar da kowa zaiyi mamakin
hakan a gareni amma ubangiji cikin hikimarsa da buwayansa da masifan sonta haka
lokaci guda.
Guntun tsuki Habu ya saka lokaci guda yana fadin wanan ai baikai na tashin
hankali haka ba ni harka firgitani wallahi .
Aure a yanzu gareka ai wata mafitace ga wanan matan naka da basu san ciwon kansu
ba Allah yasa dai ita wanan din ta kwaraice da zata fiddakai kunyan abokanka.
Kaifa Habu dadina da kai ke nan ba sai kajira kaji ko wacece yarinyar ba a yanzu
kana zaton zan yarda in kara jefa kaina a duhu irin hakane ?
Wa yan nan ka dauka auren kaddara da kurciya nayi dasu yanzu ko aure nake so na
kece raini a kaina wai kasan yadda nake zaman kaddara da kazaman matan nan kuwa ?
Ankai fa nida part dina habu har gudunsa nake wani lokaci ka dai sanni da
kyankyamin tsiya tun farko sai gashi ubangiji yai min wanan jerabawan kazantar
akansu.
Ankai habu ko ruwa na dauka koda a gora ina jin kyankyaminsa haka inda zan kwanta
sain kakabe da kaina in samu in raba in kwanta sabo tarin jakkanci irin nasu.
Ni nakance ashe shiyasa suke abokai tun farko haline yazo daya ashe babu wace
zata gyara wata a cikinsu ranan ina jin kannen Asmau suna mata fada wai har yanzu
ashe tana nan da kazantar ta suna ganin kokarina da nake iya rayuwa cikin wanan
bolar dasu haka ka duba fa Habu yan uwanta ma sun shedeta da kazantan tanan ashe
haka.
Habu yayi kasake yana sauren dan uwan nasa tare da kara tausayawa irin rayuwan
daya tsunci kanshi a ciki da matan nasa don zai iya cewa dan uwan nasa sam bai
morewa aure ba.
Haka kuma wanan zancen da dan uwansa ke son fada mashi a yanzu matsalace babba
don abin bai tsaya akan soyayya kadai ba game da yarinyar da yake son ya aura din .
Yaji J din yayi huci gumi yana dan tartso mashi saman goshinsa tankar wanda yake
cikin mumunan yanayi da sauri ya kara waigo dan uwan nasa yace.
J wai meke farune dakai haka nifa gaba daya ka rudani ma ka wani sauya kamar ba
kai ba wanan wace yarinyace haka wai take son baka wahala ?
Ko kuma ita din ba musulma bace kake tunanen abinda zai biyo bayan zancen ga
iyayyen mu ko kuwa sun hana maka itace an samu matsala daga iyayyen yarinyar ne ?
Murmushin karfin hali J din yayi yace haba Habu ba wata bace fa yarinyar da sonta
ya rikitani min tulin tunane illah Rahama dai kanwar matarka da matana sukai min
zargin kulata wanan abinda sukai min kamar sun ingizanine ko haske min hanya akan
wanan yarinyar Rahama a yanzu.
Saida Habu yaja wani uban burki a saman titi Allah ya taimaka hanya ba wasu
motoci a cikinsa sosai ya juyo yana kallon dan uwan nasa yace.
Rahama dai Ramaah ta wajen maria matana kake nufi J ?
J din ya marairaice murya tamkar zaiyi kuka cikin yanayi na kyarmar murya yace
Habu mafita nake so da zancen nan don har nakai kaina gareta garesu da ita yayan
nasu nacan .
Ban samu matasala ga yar uwar tasu ba saiga Rahama din ita ta nuna kaduwa da jin
zancen saidai nasan yar uwar nata tasa yanzu ta soma saurarena.
Shiru Habu yayi yana wasu tunane da baisan iya adadinsu ba lokaci guda kafin
yaji muryan dan uwan nasa yana fadin .
Habu ina son auren yarinyar nan a yanzu don irin halaiyansu nagari dako wani
namiji ke fatan samun mace ta kasance a hakan.
Bani barci da dadi akan tunanen yarinyar nan a yanzu duk abinda nake wanan abin
ne yanzu a gabana na rasa ta ina zan fara nasan akwai cakwakiya sosai da rigimar
auren nan idan hakan ya tabbata din saidai na matana mai saukine tunda ba waje daya
zan ajiyesu ba don gudun fitina kuma ga yarta a gidan hakan ba zai yuyu garesu ba.
Ina matukar jirkita akan zancen nan Habu rasa Rahama a wajena tankar rasa
rayuwatane habu ban kara furgicewa ba saida naji ita wanan yar uwar tasu tana
fadin.
Koda Rahama zata dawo zaria school ba dai a gidan mu ba saidai ta zauna hostel ko
kuma ta kama mata campus ta zauna ina hakan zai yuyu gamu habu ?
Habu ya nisa yana fadin ni a ganina wanan ba matsala bane babba haka J matsala
dai dayace shine ka samu yardan yarinyar wanda nasan da wuya gaskiya hakan ya faru
a cikin sauki.
Duk da haka idan matanka sunji wanan zancen yaya zasu dauki hasashen su akanka na
baya zaka iya jure kalubalin da zai biyo bayan zancen.
Idan har zaka iya ninasan hanyar da zamu bullowa ita Rahaman da yarta dama wani
da zai iya kawo cikas a cikin zancen mafita dayace shine muje muga hardo bakin mu a
laikum in yaso daga baya sai a baiyana wa kowa yasani.
Amma kuma ni dai shawaran da zan baka shine idan kasan matanka zasu kawowa
yarinyar nan nakasu a rayuwan ku gara tun wuri kayi hakkuri ka cire wanan zancen
Rahaman a cikin zuciyar ka don na fahinci har da gaiya kake son aikata hakan.
A harzuke ya soma fadin wai Habu su suka ajeni koni na ajesu dubaiya nakeyi nake
zaune dasu kasani amma kuma yanzu kana fada min in hakkura da Rahama ?
Kai Habu ya girgiza yana fadin J kayi hakkuri ba wai bani sonka da Rahama bane
nima na dade inawa wani dan uwana samun wanan yarinyar Rahama saboda halaiyanta
dayayi min.
Amma yanzu kai daka bullo da wanan zancen akwai babban aiki nake hango maka
agabanka don fitina kake son janyowa kanka a ganin ka ita Rahama yanzu bata da
wanda take sone ?
Haka kuma matan ka kana ganin zasu kyaleku ku zauna lafiyane wanan abubuwan nake
hango maka J don tasu mama mai saukine matukar muka samu kan kawu ai an gama
zancen.
Wayan J din yayi kara amma ya kasa dagawa har saida Habu din yace dashi wayarkafa
na ringing J ka daga mana.
Sannan yakai hannunshi ya duba Saiba ce ta kirashi bai san lokacin daya saki wani
dogon tsuki ba yana fadin wai meye kike kirana haka ba yanzu na fito gidan ba ?
Ya katse kiran cike da jin haushinta da takaici don yasan sauraren wayan ba zai
haddasa mashi komai ba a karshe sai bacin rai .
Yanzu duk fadin duniya inba Rahamace zata kirashi ba baijin zai iya daukan wayan
wani a lokacin fahintar halin da yake ciki da habu yayi yasa ya dan sasauta murya
ga dan uwan nasa yana fadin.
Kayi hakkuri J ka bani nan zuwa safe zanyi tunanen abinyi amma kabi komai a
sannu kada a gane kana cikin wanan damuwa komai zaizo da sauki in sha Allahu.
Nidai yanzu abinda nake so da kai shine ka kwantar da hankalinka saboda kasan ba
lafiyane dakai ba sosai gaka kuma ka rikitowa kanka wani aure yanzu.
Sai lokacin yayi dan murmushi yacewa kanin nasa ai wanan yasa nake son nuna masu
iyakar kyamata da sukayi akan ciwon nawa don kowan su saita gane kuren yin hakan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,

3️⃣6️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Kwace nake saman gado na rufe jikina lif da bargo don yanayin akwai sanyin safiya
a ranan gashi dai ina ganin kamar banyi barci ba amma kuma a zahirin barcin ne
saidai ba sosai ba ya dibeni.
Har anty Salma ta shigo dakin nawa amma banji shigowan nata ba lokacin zama tayi
a bakin gadon takai hannu tana dafani tare da ambatar sunana lokaci guda.
A hankali na bude idona ina yaye bargon dana rufa dashi nakai kallona da lumsasun
idanuwa dake nuna ina jin barci a lokacin ga anty Salma dake zaune a kusa dani ta
dafani.
Ta bushe da dariya tana fadin lalai Ramaah ta yau don ba fita kika samu sakatan
barci haka tun daga kofa nake ta sallama amma baki jini ba.
Yunkurin dagawa daga kwancen nayi ina fadin kuma fa ban dade da kwanciya ba
barcin ya daukeni haka ashe ina kwana anty ?
Ta saki ajiyan zuciya ta dago idanunta gareni tana amsa gaisuwan kafin tace dani
mijin maria ne mukai waya dashi game dake jiya da dare yau da safe ma ya kira shine
nace barin sameki ?
Ya Habu kuma na fada a sanyayye take yanayina kuma ya sauya lokaci guda nake
fadin wai in koma zaria ko dama nasan idan ya dawo ya samu ban nan sai yayi
barazanan fadan nan nasa yanzu cewa zaiyi an kusa komawa hutu kila ?
Murmushi ta sauke a fuskanta take fadin kusan haka dinne saidai wanan ba wai
zancen school bane Rahama zancen tsakaninki da dan uwansa yake min.
Cikin firgici na sake kallonta nace ya sani ke nan anty ?
Ehh ya fada masa komai har da zuwansa nan Rahama yanzu na yarda guy din nan da
gaskiya yana son ki sosai wallahi kuma tsakani da Allah yake kaunan ki badon
sha,awa ko wani abuba.
Amma ke naga tsoron matansa kada su cinyeki danya yayi tasiri sosai a zuciyanki
sun riga da sun firgitaki da mijin nasu.
Ba haka bane anty ?
To meye idan ba haka ba Rahama kin fada da bakinki guy din nan yana da mutunci
sosai haka kuma yana kaunan ki din me ake nema ga aure.
Kawai ki fita zancen matanshi ki bada kai bori ya hau musha buki mukan muga yadda
zasuyi tunda dai da kurciyanshi har yanzu ba mai cewa ma yayi auren farko balle
mata biyu.
Kawai dai rigimace irin ta mallam bahaushe na atara mata a gida ana tunkaho
shine kawai matsalan shi amma meye a ciki ?
Ni abinda yasa nake maki kwadayinsa yadda naga dan uwansa da mutunci mijin maria
shiyasa nake maki fatan ki sameshi a matsayin miji kema don nasan zasu rikeku bisa
amana.
Mutanen yanzu ba ka shedansu Rahama sam hankalina bai kwata da zancen Adamu ba
shiyasa nanuna mashi bazan bashi ke ba gara tun wuri ya bari.
Akwai da dama suna sonki ta wajena sam hankalina bai kwanta dasu ba ko kadan
donshi nake kore zancesu idan sun nuna hakan.
Daddy ya nuna muna cewa abu na farko da zamu fara yarda dashi ga mutum shine
natsuwa da mutunci mutum a ganin farko da nayiwa bawan Allah nan Jafaru na hango
natsuwa da kamala a tare dashi baizo gurin da wasa ba Rahama.
Da niyar aure ya tunkareki don haka ba wasa a cikin zancen shi gashi yanzu kuma
har ya gabatar da zancen ga dan uwansa alama ya nuna ke nan bai kaunan dogon dadewa
da zai iya kawo maku cikas a zancen.
Sam banji wani faduwan gaba ko darr na shakunsa ba donshi kikaga ina baki kwarim
gwiwa akan zancen dan nasan a gaba hakan zaiwa kowan ku dadi.
Kada ki duba bayan ki duba gaba a rayuwan ki ba lalai bane Allah yaba bawansa
dama irin hakan sau biyu damankine a yanzu yazo maki don haka kada kiyi wasa da
wanan daman a rayuwanki.
Shidai din ba wai tsoho bane ina fada maki akwai sa,anshi da basuyi ko auren fari
ba a wani wajen wanan kawai rigimace irin ta malam ba haushe.
Don haka nidai ba zan maki dole ba Rahama kiyi shawara da zuciyar ki koda ita
maria duk abinda kuka yanke mai kyaune don kece mai zama bani ba .
Kallon da nayi mata take fadin No banson na fada maki ra,ayinane a yanzu daga
baya ki dawo kina fadin nice na sakaki aurensa idan ba haka ba da zance kawai ki
yarda ki amince da bukatan sa don dai zuciyana ya kwanta gaskiya da zancen guy
din .
Na fahinci shi mutumne mai saukin kai yana bukatan macen da zata kwantar mashi
da hankaline yanzu akusa dashi wananne kawai yasakashi kara aure a fahintana.
So ki bashi chances mu gwadashi mu gani don bai kamata ace kin kinki yarda da
tayinsa ba in sha Allah hakan zai zamo alheri a gareku baki daya.
Shiru dakin yayi na dan lokaci kowa da abinda yake tunane a zuciyarsa nikan a
bangarena saina dauka anty salma ashe bata kaunana da zatace in shiga cikin
kwamacalan gidan ya J a buga wasan dani.
Matan da babu zaman lafiya a tsakaninsu suna su biyun suma basu bar kansu ba ni
wani gulma ko kwadayi zai daukeni zuwa jefa kaina irin wanan gidan ?
Idan har naga zata takura min da zance J gaskiya gara na hakkura da zama
wajenta in koma wani wajen da zama nasan dai banda wani matsala ga zamana a gidana
ta banda wanan zancen J daya bullo a yanzu.
Shi din ne kuma zaisa na bar wajenta in koma gidan daddy don ban tashi komawa
zaria a wayanzu saboda har lokacin ina jin zafin cin mutuncu da matan nan sukayi
min duk da bani kadai bane da Nafisace.
Amma ai sun labe ga sabarane suka halbi karsana don ni dai sukafiyiwa mumunan
kazafi da alakantani da mijinsu kan kwadayi.
Idona runtse naji anty Salma na fadin zan tafi in shirya nasan dai mijin maria
din zai kirani yaji ya mukayi dake zan kiraki ki fada mai shawaran da kika yanke
din.
Ta mike ta fice daga dakin na daga kai ina binta da kallon mamaki da zargin yau
inda yar uwarta na jini nake ba zata taba min fatan auren mutum irin yaya Jafar ba
haka kwatsan in fada cikin cakwakiyar gidansa da gangan da gangan haka.
Dolema ace saboda kudine nashiga ba wanda zai kawo cewa wani dalili na daban ne
Allah ya hadani dashi ina kallon irin hassadan da matan sauran yan uwansu suke
nunawa yar uwata dasu kansu matan yaya J din da idona nasan komai don ina gani kuma
ina ji ai.
Shawara nake tayi a raina dashi na wuni ranan shawarana yafi karkata da inbar
gidan anty salma idan zata takura min da zancen J in koma gidan daddy baki alaikum.

ZARIA
To zance dai kawu dauda baiyi wani dogon mamaki ba da zancen da yayan yar uwar nasa
suka zo mashi dashi tunda shina mijine yana hango dacewan hakan.
Saidai shakuwan daya kawo shine anya kuwa Jafar yayi tunane kafin ya yanke
hunkuncin hakan da zuciyarsa aure fa ba abin wasa bane.
Tabbas nayi tunane kawu ko banyi tunanen yin hakan akan yarinyar nan ba kukanku
masu hango hakan a garenine.
Duba ga irin kyautatawan da yarinyar nan ta tsaya tayi a kaina lokacin da nake
bukatan kulawan matana a gareni ba tare data nuna kyama ko gajiyarta ba kawu ?
Tabbas hakane Jafar nasan wanan kwarai kuwa to amma baka duban zargin matanka
akan kana yawan kula yarinyar nan zai zama gaskiya idan hakan ya tabbata.
Kawu nafi tsoron Allah da mutum Allah ne ya halasta min hakan ba wani abin
kaucewa addini zanyi ba a yanzu abune na raya sunnan ma,aikin Allah nake kokarin
gudanarwa.
Jafar na dai fahinci daka riga daka yanke hukuncin hakan a zuciyar ka tun kan
kazo nan din nima kuma ba zan hanaka hakan ba duba da abin da ke hasashe akai.
Amma kai Habu kana ganin ba matsala yun hakan game da naka auren matarka zata
bada goyon bayan yar uwarta ta shigo gidan da take aure da sunan auren ahali daya
kuma ?
Sai lokacin Habu dake zaune yana kallon ikon Allah yadda dan uwan nasa yake abu
kamar ba kai sake ba ya soma gyaran murya da fadin.
Kawu ni ina ganin tunda Allah bai hana abin nan ba kawai ku kyaleshi yayi abinsa
har in yarinyar zata amin ai kamar ba matsala dai.
Kawu din yace ke nan akwai matsala daga bangaren yarinyar ke nan kana dai
nufin bada sanin taba yake shirin hakan kome ?.
Eh to gaskiya ta sani amma kasan halin mata dubaiyan halaka wanan ne suke duba a
yanzu yasa sam bata amince ba duba ga yadda ake da matansa.
Ita me dakinka fa tasan da zancen kawu ya tambaya da sauri Habu din ya girgiza
kansa yana fadin bata sani ba gaskiya ban ma son ta sani ai yanzu gudun kada mu
samu matsala.
Don gaskiya idan har tasan da hakan yana da wuya ta yarda da wanan abin hakan
yasa nake son mu rigata zuwa can garinsu muga shi hardo don yasan ta hanyar da zai
bullo mata kafin ta ruguza abin nasan halin maria da wuya ta amince da hakan
gaskiya.
Hakan baida matsala tunda kana ganin hakan zaifi sauki yanzu yaushe kuke son ayi
tafiyan sai ita nahaifiyar ku kun sanar dasu zancen.
Kawu ni banson wanan zancen ya fita a yanzu sai idan Allah ya tabbatar dashi duk
maiji ma yaji amma yanzu fitar da zancen yana iya kawo matsala a gidan mu.
Kaga ga ita matar hakan ba zai mata dadi ba haka kuma ana iya samun matsala a
bangaren mama ta kawo cikas a cikin zancen


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login