Showing 300001 words to 303000 words out of 328222 words
Chapter 101 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
don haka ko yanzu da tan uwa suka watse
suka barta bataga laifisa ba tunda ya fa mata din abu dayane har lokaci bata
tantance ba cewa da akayi itace ta hudu a gidansa.
Bata gaskanta ba saida yan uwan mijin suka hadusu waje daya ana tsawata masu kan
zamantakewa nan tasha mamaki ganin su hudune dai matanshi kamar yadda mama hafsatu
ta fada data koma daga jere.
Wanan yasa hankalinta tashi sosai har saida ta kasa daure ta kira mama da kuka
tana fada mata itama uwar kasa daurewa tayi nan ta nemo kan iya tana labarta mata a
zatontama Jafar bai gidan saboda rudewa ranan bata tsaya yin lissafin kwanan mu ba
don ga yarta cikin bala,i.
Ke dubu ki natsu dob Allah zama da kishiyoyi haka kan saratu ne farau din haka
keda kika zauna a cikin kishiyoyi meya sameki nace ?
Iya ba daya bsne da nawa don ni a cikin gari nake kuna jin duriyana kuma ina
ganin na gida wanan kuma wani uwar duniya fa take bako kusa da yar uwarta hannatu
ba can fa kauye ya ajeta.
Sai akace kauyen ba a zama ko aure inane bai kai mace wai don Allah ana ce baki
ga zuma kina ina badaci yarinyar nan dai tana son mijinta ko batace dake bata iya
ba dubu ?
Suna zancen jafar da habu suka shigo part din suna gaidasu nan iya ke fadin to
kuyiwa uwarku magana tun bata jawo maku abin kunya ta kashe auren saratu ba ?
Kashewa kuma akan me mama jafar ya fada yana kallon uwar iya ni baki fahinceni
bane abinda nake nufi don me yayi muna karyan mata daya gareshi ?
Haba mama ai hakane daidai da saratu gidan mata da yawa inda zata ji dadin yin
gulman ta da makirci ba ta iya tsegumi ba tun nan tana shiga matan yan uwa tana
hada fada yau gata Allah ya kaita inda zatayi nata.
Habu nagane saboda matarka ka tsani yar uwarka to koma meya samu saratu yar
uwarkace dai mama ta katse ya Habu daya soma magana.
A,a mama ba wai zancen tsana bace kece kika damu akan wanan abin yarinyar nan
itafa ta gabatar da mutumin nan tana son sa banga abinda zaisa ki damu kanki ba
yanzu don Allah ?
Habu yana nufin cewa zata iya zama a duk inda ta tsunci kanta tunda ta koya a gun
matan mu da suke rayuwa tare a gidan nan shi kuma sai bai fada ba kai tsaye.
Iya sai murmushi takeyi tace banda abin dubu saratu mace ce fa yau ko sha biyar
aka wanketa a zamanin nan a kai cikin mata ukku ai tsab zata zauna dasu balle mace
kamar saratu.
Ai maganan habu gaskiyane zata zauna tunda ita ta saka kanta auren nan idan kika
sa damuwa har ta fahinci hakan ta kaso aure tazo ta zauna maki gida shike nan.
Addu,a yakamata kiyi mata mama yadda ko wata uwa kewa yarta in yaso sai a
saurara aji ko zatayi korafi aka zaman nata kinga sai a san matakin dauka a
lokacin.
Wanan magana ta jafar ya kwantar mata da hankali suna cikin zancen saiga Saiba
ta fado masu tana huci take fadin mama naje can ban sameki ba ?
Ashe kina nan dama karan su na kawo maki kowa yasan dai nice zan karbi girki a
jiya amma sai J yasan ban gari ya dawo yaba Asmau girkina.
Wooo,hwahoo ni jikan mutum biyu yar nan kina data ido kuwa Iya ta katseta sa
fadin hakan wani kallo tayiwa iyan kafin tace da hankalina wajen mama nazo.
To meye a cikin hakan kuma Nusaiba akwai mana mama tunda ban karawa Rahama
kwanan ba na dawo nan bata samu yadda take so ta bata min suna da yar mutane ba.
Na dawo na kwana da Asmau ko kike nufi idan na tsaya can kuma ki dorani a ture ki
yawata kina fadin na saci kwanan ki ?
To na kwana din kiyi abinda zakiyi marata ido kawai bansan baki da mutunci ba
ai da bandawo na samu kinwa Asmau duka ba yau.
Tsuki habu yaja ya mike yana fadin ni zan tafi iya yaya karfin jikin naki dama
nazo na dubakine zan tafi ya mike yana fito da kudi cikin aljihunshi ya mika mata.
Da sauri ta mika hannu ta karba tana godiya hakan yabasu dariya aka wasance J ya
mike suka fita da habun sun jima a wajen motar suna magana kafin ya bar gidan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/5, 13:47] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
9️⃣3️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Ina jin irin cakwalin da akeyi cikin dangi game da zancen aure Saratu ban taba
furta komai ba game da zancen shi zance a yanzu tafiya yakeyi.
Bayan haka alhaki kwikwiyone don bin mutum yakeyi koshi yaya shiyasa na katseshi
da irin nuna haushin ta da yakeji yana mata gwai da hakan data fada ciki.
Na nuna mai tankar uba yake a gareta duk abinda ya cika da ita a yanzu ya
sameshi don shine matsayin babba a bangaren mama yanzu.
Ya kance dani haka kike gani Rahama amma su a bangaresu ai yanzu tunda banda
komai ai basu ganin hakan kowansu kar nake kallonshi a yanzu.
Habu ma yafi kowa ban mamaki yasani sarai nina sakashi a wanan harkan asalima
sana,atace ta baya na bar masa amma wai habu nan nace ya cika min kudi nayi wani
bussiness ko Allah zai taimaka un daga yaki ban .
Nayi mamakin wanan zancen da naji duba ga yadda nasan ya taimaka masu sosai a
baya koda yake ba abin mamaki bane idan ance yaya habu yayi irin hakan donshi mutum
ne da bai kwantuwa ko kadan.
Ko iyalinsa gaskiya din tana da hakkurine ba a jin kansu da ita don da watace
yadda yake tauyeta din nan da anjisu tuni wajen irin halin nan.
Mutane sukan manta da arziki na Allah ne duk akace mutum mai arzikine daga Allah
bana haye irin na zamanin nan ba kabar maishi kawai kada ka jefa hassadanka
akanshi.
Ire iren halin rayuwan da bawan Allah nan yake fuskanta suna da yawa gana yan uwa
a gida don wasu har yanzu basu san da baida hali irun na baya ba gani suke shi
maishine akoda yaushe.
Ga fitinan iyali a kullym sai anyi ance ya samu ya shiga wani hali balle yanzu
da abu biyu zuwa ukku sune a gabanshi na farko zancen haihuwana daya nuna damuwa
akai sosai tun anan nasan lalai bada kudi kamar da.
Sai zancen jikin iya da shine tsaye a kai yana bata kulawa sai kuma salima dake
kula da ita din da mama sai kuma zancen jikinshi da halin rayuwan matsi dake
tunkaronshi.
Cikin haka dai ranan na tashi da nakuda gashi ba a gidan mu yake ba gashi
saboda alkunyan mu ta filani na kasa kiranshi in fada mashi duk da jaddada min da
takeyi tunda watana ya kama akan in naji wani abu in buga mashi.
Kasa zama dakina nayi na koma wanan dayan dakin da babu kowa ina sintiri ina
gudun wani yazo ya ganni aga gazawana.
Ya kira waya tun asuba kamar yadda ya saba ban daga ba har rana ya fito gashi
hankalinshi yaki kwanci hakan yasa ya fito zuwa gidan namu.
Kofa na rufe har lokacin ban bude ba yayi ta nocking saida kyat na iya zuwa na
bude kofan kafin ma ya shigo na duka a inda nake don taso min da abin yayi a
lokacin sanadin dan tafiyan da nayi din.
Salati ya sake yana tambayan meya faru meyasa ban kirashi ba shi haka kawai
jikinsa ya bashi akwai abinda ke faruwa dani tun dare.
Tashi maza muje asibiti ya fada a gigice na dago ido da kyat na dubeshi ina zufa
nake fasin zan iya ai ?
Zaki iya me kin taba sanin haihuwane common tashi don Allah muje asibiti jin
hayaniyarsa yasa Biba dake ta sharan barci fitowa daga daki.
Turus taja ta tsaya tana kare muna kallo tace baki da lafiyane anty ya juya
wajenta yana fadin ke dauko mata wani zani daki da sauri ko kuma tsaya in kira mama
dai tazo.
Maman tudu ya kira ya sheda mata ta shirya gamu nan zuwa a dauketa zamu asibiti
take fadin a,a yau abin yazo ke nan ubangiji Allah ya raba lafiya ya amsa da amin
take fadin ai a shirye take.
Saidai ka dauko zannuwa kamar uku da kayan jariri a je dashi ya amsa tare da
kashe wayan a cikin sauri yama rude ya dannawa yaya Ai kira kuma.
Yake tambayana ina zanga zani din da kayan baby akwaisu kaina na dago da kyar na
dubeshi ina gyada masa kai alaman akwai.
Ina zamu dauko zanin suna a cikin kasan closter dina don yakai sati dana hada
komai don gudun irin girshi haka nayi wanan dabaran gashi yayi amfani yanzu.
Da kyat muka kai wajen motanshi a nasa yaso ya daukeni naki hakan dole ya barni
na taka zuwa bakin motan muka shiga yake fadawa biba ta kula da gida da kanta.
A hanya muka saida ya tsaya saboda wani yunkuri da nayi kamar zan rike mai
hannunsa da yake jan motan ban tsanmanin ya taba ganin matarsa tana nakuda urin
hakan yasa ya gigice sosai a lokacin duk da dauriyan da nakeyi kuwa.
Saidai tunda mama ta shiga motan dole na daure ga duk abinda nake jin din
saboda alknyan mu ta fulani ban yarda nayi koda dogon motsi ba sai shine ke dan
juyowa yana fadin sannu ya lafa ko saidai in gurgiza mashi kai kawai ban iya magana
a lokacin don mama kada taga raunina a cewan mu.
Sun karbeni sun duba kiran da likita yayi mai ya kara daga mashi hankalinsa inda
likita ke fada dashi kan cewa yasan matanshi nada matsala meyasa basu zuwa awo ?
Tana zuwa awo saidai asibitin can na mata take zuwa a dubata likita yace to
yallabai gaskiya matarka ba zata iya haihuwa da kanta ba saboda yaro nason fitowa
amma ba hanya.
Anyi arziki ma da yaron yake da rai har yanzu bai mutu ba don haka dole sai munyi
mata aiki an cire abin dake cikin nata.
Zufane ya karyo mashi son haka yanzu idan ka shirya sai ka saka hannu ga
takardan nan a nemo muna jini da wanan maganin muyi shirin aikin yanzu dole sai
aiki za ayi mata a cetosu ita da dan nata.
Zufane ya karyowa yaya din lokaci guda yacewa likitan go ahead ya mika hannu aka
miko mashi takardan aikin yasa hannu sai kudin magani da sauran abubuwan da zai
sayo din na aikin.
Lokacin daya kira gida yana sheda masu mama na zaune dasu iya tana jin ance
aiki tace jam kukan yaran nan kun daukowa kanku jamgwangwan ace mace bata iya
haihuwa sai anyi aiki wanan wani irin masifa suka jajibo haka wai ?
Assha dubu asha abin naki har yakaiki ga rashin tausayi akwai macen da son kai
zai kaita ga askan likita inba dole ba wata mace ke fatan a fede ta don Allah ?
Kema fa uwace dubu kin haifa kuma za a haifar maki ki tuna kina da yayan nan
gasu nan maki har yanzu a gaban ki kike irin wanan magana.
Keda ya kamata aji furcin alheri na Allah ya tashesu lafiya kike wanan maganan
haka nasan ko agaban yaran nan zaki iya fadan hakan cikin rashin damuwa da abinda
kika fada.
Haba iya ace ga yadda yarta take ita kuma yanzu ace sai anyi aiki wanan idan an
samu mai karamin karfi don Allah yaya ke nan za ayi kullum kashin kudi kan mace ?
Rufa min baki don Allah mara imani da tausayi kawai Allah yana nuna maki abinki
hakan baisa kin saduda kin koma gareshi ba har yanzu ?
Da kike aibanrta yaran nan haka yasa mazajen nasu sun tsanesu ko sun rage son da
suke masu din ke dai ki kama girman ki tun bai bare ba kin kasa kwasa.
Balle yanzu ai mama wayewane ga mata mace taje asibiti ko tana iya haihuwa a
fedeta don kada tayi saurin tsufa a idon mijinta balle wanan da nasu yake da
dalili salima ta fada.
To iya kinji ko nikan nace haba gaskiya dai a yanzu yawan aikin ga mata ya
yawanta wanan wani irin zamanine muke cikinsa wai tsufan banza da komai wayau ki
sai kinyishi.
Ki daiji dashi idan kayane kada ki bari don Allah ki matsa kinji har su gane
kina kishi dasu irin haka raini ya shiga.
Kishi kuma Iyaa su zan tsaya kishi akan me zan tsaya kishi dasu suna yayana da
sauri iyan tace, a,a dubu kowa yasan kina kishi da yaran nan akan yayanki maza waye
gwanarki cikin sarankanki kaf ?
Babu gaba dayansu kishi kikeyi dasu kowa yasani ko don ba,a iya fada maki a
gabanki ?
Ta mike tsaye da kyat tana fadin salima tashi ki kaini asibitin don Allah kada
mu barsu su kadai a can gashi ance aiki za ayi.
Ke iya ina kuma zaki keda ke fama da kanki tashi nace ki kaini ta fada da tsawa
bata tsaya kallon mama da mamakin furcinta ya kashe a zaune.
Duba min Yazidu idan yana nan ya kaimu in kuma bai nan mu samu motar haya mu
tafi salima dai ta mike tasan mai iya hana Iya tafiya asibitin wanan lokacin sai
Allah.
Dole salima ta mike ta shirya suka fito duk da safiyane matan yaya na waje da
yaransu suma kansu don tsamin shiyan basu faye son zama a cikin part din nasu ba
wani lokacin.
Yanzun ma ruwan wake da Saiba tayi alale shine bata zubar ba part din ya dauki
wari su kuma basu gane kome ke wanan wari ba saboda kazanta suka fito daga waje
suka zauna.
Ganin su iya sun fito yasa Asmau tambayan yau iya fita za ayi ke nan tunda safen
nan ta juyo tana fadin asibiti zamu abokiyar zamanki aka kai asibiti haihuwa za ayi
mata aiki.
Aiki kuma har abin yakai can ne shi sani gaibu aisai Allah yanzu Jafaru ya bugo
waya yana sanar damu hakan suna can aaibitin dai tun dazun.
Allah ya raba lafiya ya kawo rayayye Asmau ta fada samun waje itama bata iya
haihuwan ke nan da kanta ko irin na yar uwarta ?
Aikan tunda akace aiki za ayi kema kinsan hakane to shine don munafunci ya fita
bai fadawa kowa ko yana tsamanin wani abune ?
Wa zai tsaya yin wani sheri a kanta ko yar da zata haifa Nusaiba ke fadan hakan
cikin hasala tana fadin shiyasa ake jin mu ni banson harka da munafunci wallahi ?
Kila shima baisan aiki za ayi mata ba Asmau ta fada ta juyo tana fadin kamar ya
baisan aiki za ayi ba tunda haka ta zaba wai ita wayewa oho dai su suka sani ta
fada cikin bacin rai.
Allah akbar kishin ke nan fa mata kishiya idan ba ta daina ganin numfashin
kishiya ba ko taji an fasa ihu shine kawai zata numfasa amma wani ciwo ko wani
kakanakayi bai hana kishi ga wasu.
Asibitin kuma habu ya fara kira yake cewa dashi muna asibiti da Rahama idan
akwai kudi a wajenka don Allah turo min an rubuta min magani.
Yana hamma don barci yakeyi yace kudi gaskiya ba wasu kudi a hannuna sosai
yanzu amma bari in duba yace ba matsala.
Shiru yayi bayan sun gama wayan ranshi a bace ya kira abokinsa na nan dake juya
mai kudin Salima yace dubu dari biyu yake so don Allah ina asibiti da matana aiki
za ayi mata yanzu.
Subbahanallahi aiki kuma gani nan zuwa amma ai sha,anin asibiti dari biyu baiyi
gaskiya bari dai in karaso yanzun nan zan watsa ruwa in sameka kuna wani asibitin
ne a ciki ?
Ya fada mai yace gashi tafe har yazo aka shiga aikin bayan ya kawo mai dari hudu
duk wani zirga zirgan asibitin akayi dashi saida aka fito mai da jariri ya tambaya
akace za a fito dani yanzu yayi godiya ga Allah.
Mama da Salimace suka tafi gida da yaron don ai mashi wanka suka bar iya da inna
data biyo mu daga baya ita da Nafisa.
Duk abinda yakeyi hankalinsa yana ga dan uwansa yana mamaki furucin yaya habu
din don mamaki shi kwarai yake a zuciyarshi.
Yana aiyana lalai kudi sune rufin asirin bawa yau shine dan uwansa na jini
yayiwa hakan gara yazid ya san baida kudin amma ya turo mashi da abinda ke akwai a
lokacin.
Haka yayi ta sintiri da yunwa a cikinsa sai karfe biyu ya koma gida don ya watsa
ruwa ya samu abinda yaci lokacin abokin nasa shima zai tafi yace dashi zaka jini
insha Allahu sulaiman nagode kwarai da taimakonka.
Haba dai dole muyi maka ai J waye silan zaman mu hakan a yau i bamuyi ma ai
Allah zai tambaye mu ni wallahi ba wancan kudin bane kyauta na baka wa yan nan din.
Abinda bai tsamata ba hakan ya sama don koda ya shigo gidan da saiba ya fara cin
karo tana shayi a wajen haraban gidan har ya aje mota ya fito ko kallo bai isheta
ba.
Saida ya shiga ciki ga wari ga komai ya fara kwalawa Asmau kira da