Showing 216001 words to 219000 words out of 328222 words

Chapter 73 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

suna gidajensu amma basu barin asibitin sai wajajen karfe
daya da wani abu na dare koshi sai iya ta matsa masu akan su tafi zasu wuce din.
Iya na daga waje tana sallah bata shigo dakin ba tukun na na dubi mama a cikin
karfin hali nace mama naso nayiwa yaya wankan magani a gwada a gani amma ina
shakkun hakan da zanyi din.
Kwana uku zanyi mai hakan amma sai abinda kikace shiyasa ban fada ba a gaban
mutane ta yunkura ta mike zaune tana fadin idan zaki iya ki gwada a gani mana yar
nan ai sauki ake nema ba wani abu ba dama kuma zaman hakan muke a nan din.
Tana zaune tana kallona na hada komai sai naji ta mike tana fadin bari naje
daga waje in tare tsohuwar nan kada ta shigo.
Ta fice ta barni dashi a cikin karfin hali hakan kuwa na cude mai jiki da ruwan
hadin maganin na kuma bashi ya sha sosai na mayar dashi ya kwanta a nan na kife a
jikinsa ina kuka.
Sai da mama taji shirun yai yawa ta leko tana fadin yayane har yanzu cikin
karfin hali na dago ina fada mata angama.
Sun shigo sun tsaya akanshi suna kare mashi kallo tare da fatan alheri a gareshi
kafin suka juya suka samu wajen kwanciya don ni ban faye kwanciya ba ina zama a
kujeran dake gefen gadon nasa koda yaushe.
Tsawon kwana ukku muke a hakan dashi kullum da safe kafin su shigo zan shafa
mai na bashi yasha bayan na gama mulke masa jiki ko ina da wann ruwan da doki yasha
ya raga don ba karamin magani da alfanu yakewa mutum a jikinsa ba.
Kamar yadda dage ya tabbatar min ni kuma na fadawasu mama da iya ance ka,idan
maganin har in akwai alaman sauki kwana ukune kacal za ayi amfani dashi ga mutum
aga alfanun maganin.
Don mutum zai fara nuna wasu alamomi na jin sauki ko wani sauyi nadaga ciwon
halin da kake ciki din Allah da ikonsa kuwa ranan na gama mashi amfani dashi na
bashi yasha na zauna ina rufe goran nakai idona akanshi sai na ganshi ya kura min
ido kuri yana kallona.
Da sauri na cusa magani a cikin jakata na karasa wajensa ina kiran sunansa
saidai bai amsa ba illa idon daya kafa min din baya kyaftawa hakan yaban tsoro na
nufi su mama ina kiransu hankali tashe.
Suka shigo dakin gurinsa suka nufo cikin kidimewa suna mai sallati da kabbaran
iya ta karasa tana fadin Jafaru idon kane nan ?
Sai ya dan lumshe idanuwan nasa kamar ya sauke ajiyan zuciya ya mayar ya rufe
can kuma ya kara budewa yana kallon mama dake mashi sannu a lokacin.
Ya Allah yadda ka nuna muna hakan ka tayar muna da kafadan yaron nan a cikin mu
cikin salama da kudirinka ya dawo muna a hayacinsa ya koma walwala kamar kowa.
Hawaye kawai ke fita min daga idanuwana na kurasa masa ido a cikin tausayi ni
kaina a lokacin abin tausayi nake na sani amma duk bacin ran da bawa zai shiga
matukar yana lafiya ya godewa Allah don na kwance ya fishi shiga tashin hankali.
Ganin yadda ya kura min idanuwanshi din yasa iya min magana tana fadin ki daina
wanan kukan ki karasa kusa dashi kiji ko wani abin yake so don ke yake kallo a
yanzu din.
Hakan na dan karasa gabanshi na dan rankwafa ina fadin yaya kana son wani abune
da idon daya kifta min na gane yana nufin a,a sai ya maida idonsa ya rufe a
hankali.
Ya Allah kasa hakan saukine a gareka jafar Allah ya kaddara tashin ka a cikin
yanayin nan ya baka ikon cin jarabawan nan da Allah ya aiko maka muka amsawa mama
dake fadan hakan da amin.
Munyi tsaye cirko cirko a kansa sai iyace take fadin ko abinci yake bukatane ni
dai banyi magana ba don nasan yana da wuya idan hakanne.
Saidai na karasa gaf da fuskanshi ina fadin a hado maka ruwan shayine zaka sha
yaya sai naji iya tace keko dai ai basai kin tambayesa ba a dai hada mashi din a ga
ko zai sha din.
Shayi mai kauri na hada mashi don ya kama mashi cikin nasa na mikawa mama na
kamoshi tare da ita muka bashi shayin.
Alhamdullahi don yasha sosai ya maida idon sa ya rufe kuma alaman ya isheshi ba
zai kara ba a haka mazan suka shigo suka same mu dashi ina zaune rike dashi na dan
dagashi ya fada mai.
Sunyi farin ciki da halin da suka sameshi sai mama ke fadin dama yar nan tace
insha Allah maganin nan datake mashi kwanan nan ance da yardan Allah a cikin
kwanaki uku za aga fa,idanshi gashi ko mun gani.
Alama ya nuna wanan matsalan bata asibiti bace ke nan don haka gara in an kara
ganin hasken hakan a mayar da yaron nan gida aje acigaba da neman na gargajiya a
gani.
Ya Auwal yace haka kowa ke fada shima Habu jiyan nan yake fadin ance wani zubin
idan an rasa gane kan ciwo kawai mafita abar asibitin da mutum don shedanu da
miyagu masu sihiri suna son hakan.
A asibiti suke samun galaba don sunsan babu wani maganin tsari ko riga kafin da
zai taresu a nan din sun daita maganganu a tsakaninsu har yan uwa suka taru
asibitin kowa na murnan cigaban da aka fara gani akansa din.
Lokacin tafiyana gida yayi don ganin matansa sun iso don ina kaucewa duk wani
abinda zai iya kawo muna fitina a tsakanin mu a lokacin tun bayan rabon duty da
mama tayi muna a kansa din.
A haka kuma na kan dan samu daman leka school cikin damuwa da farga ban dai
fahintar komai a hakan bayan attendees din da nake dauka kada karatun nawa ya samu
cikasa da yawa a lokacin gashi zamu fara final exam din mu next week.
Abu ya taru yai min yawa a kai ga zuwa asibiti ga karatu duk nabi na fige
hankalina ba a kwance ba umma tazo kusan sau uku tana dubashi.
Hakama mutanen abuja sunzo dubashi din don a gaskiya zance a yanzu akwai sauki
sosai saidai na fahinci kamar hankalinsa ya dan gushe masa kuma bai magana bayan
bude idon da yakeyi din .
Gashi kusan satinsa hudu ke nan asibiti har wasu kwararun likito suka
consultants aka dauko don shi suyi duba iya abinda zasu duba a kansa din magana
dayace sun kasa gane ainihin abinda ke damunsa din.
Exam din dana soma yasa sam banda lokaci ga yaya habu dasu mama sunyi min fada
cewa na maida hankalina wajen exam din tunda akwai mutane a tare dashi.
Amma matsala daya shine tunda ya fara dan budan idonsa din nan a ni kadai ake
gane wani abin da yake bukata wani lokacin ko ban kusa zasu kirani in zo in duba
masu shi din.
A cikin hakan har exam dina yayi nisa sosai ga jinya ga kuma karatu wata rana
ina zuwa mama ke sheda min cewa tana ganin za a bar asibitin nan don tayi masu
bayanin cewa su gwada dagashi daga asibitin a gani kuma.
Munyi hakan da ita kamar kwana biyu na dawo ina hanya maria take fada min cewa an
bar asibitin da yaya an mayar dashi gida.
Jin abin nayi wani iri sai kuma na barwa zuciyana komai nake tambayan yanzu yana
ina ke nan tace yana gidanshi wajen matansa.
Saidai ance a tsohon part dinsu da suka tashi aka ajeshi ba a kaishi ainihin part
dinsa ba don kada a dameshi a nan din .
Ajiyan zuciya na sauke ina fadin to yanzu yaya zanyi Yanda tace dani ya habu yace
dole can zan koma nima mu kula dashi tare dasu saidai na dinga yi ina zagayen
gidana.
Sam banji dadin hakan ba a raina amma na bar zancen kamar yadda tace nayi sai
idan sun nemini da maganan hakan na karaso gida a cikin bacin rai.
Don kuka dai nayisa a yanzu har na daina saidai tunanen zuci kuma dana koma yi
wanda yafi kuka wahala donshi yana cin jiki.
Nashigo nayi wanka tare da alwala nafito ina kimtsawa yaya Habu yayi salma a
gidan hakan yasa na fito daga dakina don ni kadaice yanzu a gidan Biba ta koma
wajen uwarta tun faruwan al,amarin nan a can take yanzu saidai tana zuwa kwana
bibiyu da yan uwanta su gyara muna gida suyi min wanki da sauran wasu aiyukan.
Na fito muka gaisa na samu wuri na zauna yake fadin bayan ki dazun mun bar
asibiti da jafar yana gida yanzu haka.
Na dago kai na kalleshi yace ehh saboda mun yanke shawaran a mayar dashi gida
acigaba da wanan na gargajiyan tunda duk munsan ciwonsa dai bana asibiti bane.
Don haka zaman nasa a asibitin baida amfani banda zaman kashin kudin da akeyi
kawai naso a kawo shi nan don zaifi jin dadi a nan din sai kuma nayi tunanen cewa
mutane ba zasu gane hakan ba zasu dauka da wata manufa muka kawo shi nan din.
So shiya dai na kaishi can aka bude masa part din mu a nan yake yanzu don haka
nazo in fada maki dole kema din zaki koma can din a yanzu har muga abinda hali
zaiyi.
Idan ya kama din mu fita dashi wajene sai mu fita dashi din aje can a gwada sa,a
kuma yanzu dai zuwa nayi na fada maki zuwa dare sai ki shirya zan dawo in daukeki
nida maria mu kaiki can din .
Hawaye na soma sakewa yake fadin kiyi hakkuri hakan jerabawan mune mu daku
saidai shi dake kwance ya fimu shiga wani rayuwa.
Don haka ki natsu banson kije ki biyewa Nusaiba kuna saida hali har mutane suyi
Allah waddai da halin ku ki natsu kisa ido ga jinyar mijinki shine abinda zai kaiki
gidan.
Ya barni da zulumi ya tafi na rasa abin yi dole maria din na kira ta ban shawara
na dauki dan abinda zanyi amfani dashi a can din tunda ba zaman dindindin zan tafi
yi ba gidan.
Hakan ya faru sunzo bayan sallah isha,i suka daukeni bayan yaya yayi gargadi ga
maigadin mu na nan gidan sosai akan ya kula da gida kada ya bari kowa yazo gidan ya
shiga idan bani bace na turoshi.
Mun isa mun samu motoci biyu a gidan hakan na nufin akwai baki a ciki lokacin
haka muka karasa ciki da sallama abokanshine suka zo daga abuja dubansa suka samu
an sallamishi suka zo gidan.
Suna zaune a falo dasu mama sai yaya ibrahim da zai zauna a na shima tare damu
din suna bayani saiga ya habu don shine a gaba aka gaisa ya kara masu bayani halin
da ake ciki nan suke fadin har idan za a fita dashi waje din ne don Allah su sani.
Da zasu tafi suka kawo kudi mai yawa suka bayar Asmau suka mikawa akai masu
godiya suka tafi.
Sai bayan fitansune maman tudun wada ta juyo tana fadin kin iso yar nan sai
kikaji shawara ya canza mun bar asibitin ?
Ai nace habu ya kiraki ya sanar maki tun dazun din yace kina makaranta a lokacin
idan kin dawo dai zai sameki.
Ya habune ya shigo da kayana dan troler ne dana saka kayana a ciki sai sallaya da
al,qura,n dina dana dauko yana shigowa ya nufi ainihin dakin da suka zauna da maria
don gadon dakin da komai yana nan a dakin yadda suka barshi.
Ya fito yake fadin dakin nan zaki zauna ke Rahama mama dubune tace a nan zata
zauna ke nan kuma ?
To me zata tsaya yi can mama tunda yana nan sai mama tudun wada ta karbe da
fadin inba ita ba waya san yadda zaibi dashi haka yadda takeyi ai itace dai karfin
jinyar nasa ko .
Asmau ta miko kudin tana fadin habu ga kudin nan dasu Mansur suka bada ki bawa
mama koda wani abinda za ayi nan koda yske mu gani nawane ya mika hannu ya karba
daga hannunta.
Dubu dari biyune yace ya juyo yana fadin ga dari da ashirin ku raba ku ukku sai
wanan su mama kuma su raba ya mika mata sauran.
Ina waje daya nida yar uwata a takure yake fadin tundazun barcin yakeyi ke nan
mama tace ya bude idanunsa dazun kafin magariba nan dai ya zauna suna hira dasu
mama din da iya data shigo .
Saiba ce ta fara mikewa bayan ta sauke ajiyan zuciya tana fadin aina zata ko mu
nan zamu iya jinyarsa ba sai wata tazo ba don me za a kawo Ramaah ace itace zatayi
jinyarsa.
Keko kikan fara abinki ke nan mama dubu ta fada tace a,a mama abinda ake muna a
gidan nan yayi yawa ke nan dai mu bamu da amfani garshi yanzu sai Rahama ko ?
Yanzu meye abin fada cikin zancen nan wanda ke fama da kansa a yanzu har kun ga
wajen wani fitina a nan kuma ?
Ba fitina bane mama akan so a raina muna wayaune wani lokaci aiba a gidan nan
take dashi ba saita zauna gidanta tunda ba nan take ba.
Don me za a mayar damu yan kallo ace wai itace tasan kan jinyar sa to ai sai mu
barta dashi tundaan kawotane ita data iya ta kuka dashi.
Umm,uhmm duk abinda zakuce saidai kuce amma ba inda yarinyar nan zata a yanzu
tunda itama mijintane don haka wace bata hakkuri ga hanya nan mama ta fada.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join
my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ
[3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

6️⃣9️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Kasamcewar manya a wurin hakan yasa na rakube gefe daya kokai ban dago na kalleta
ba mama ke fada da ita sosai hakan yakai ga tace da iya .
Lamarin yarinyar nan dole in kasance a gidan nan tare dasu don abin nata ba
hankali sam a cikinsa .
Ga yaron nan kwance amma yarinyar nan bata saduda ba sai banzan haukan kishi da
take kokarin nunawa mutane ina ita din dai matarshice ko ?
Ko har da hakan baki yarda dashi ba na taba ganin wanan rashin hankali wanan ba
kishi bane haukane ai har yaushe mijiki yana kwance haka sharkaf a hannun Allah
kika samu bakin kishi ?
Koda yake bata da laifi laifin Dubuce dake kama mata duk abinda tayi yarinyar
ko yar gidan uban waye aini bata kai min hakan ba na rasa meke damun Dubu akan
wanan yar ?
Irin haka ai dole ta dauka kowa baida daraja a nan tayaya zan zauna matan dana
tana wanan iskancin a gabana ban dauki mataki ba ?
Har idan an barki dashi din uwar me zaki tsinana masa a nan din banda fitinan
da kika saba don kinga Dubu tana kama maki kafan iskanci.
Mama ba sai kin tanka mata ba ai ku barta muga abinda zatayi din a nan Rahama
zata zauna har zuwa lokacin da Allah zai bashi lafiya to ai shike nan mama ta kara
fada.
Da farko banyi niyar zuwa dakin da kayana suke ba don wata zuciya dake dibaba
akan na koma gidana kawai in zauna yafi min sauki da zama nan tare dasu din da
zanyi.
Sai kuma nayi tunanen idan nayi hakan ban kyautawa yaya habu dasu mama din ba
wanan yasa naja bakina nayi shiru saida aka rage a falon na shiga dakin komai a
gyare yake tsab a dakin.
Sai yar jakata dake saman gado aje na dauka na bude wardrobe na saka a ciki na
shiga bandakin nayi akwala na fito sallah nafila nayi na roki Allah ubangiji ya
tsare ya kareni daga duk wani fitina daka iya tasowa a gidan.
Muryan mama dake kirana a falon yasa na fito take fadin zoki gyara muna wajen
kwanciya ita wanan mai sababin da a haka zata barmu mu kwana a zaune ke nan ?
Na gyara masu shimfida don a kasa sukace zasu kwana ni kuma na zauna a saman
dogon kujeran da aka bari a falon don zama don an kwashe sauran kujerun falon ankai
ta bayan ginan .
Asmau ce ta fara shigowa da yaran ta ta zauna an dan jima kuma saiga saiba din
ba wanda yayi magana don kowa ya gane manufarsu a nan zamu kwana dukkan mu dasu ke
nan abindai ba tsari gaskiya.
Ni dama ace rabawa akayi akan duk ranan da girki ya dawo kaina sai inzo nayi
aikin da zanyi in koma amma ba ace in dawo nan din in zauna haka a tsakaninsu ba.
Na dan jima a zaune na mike zuwa dakin bancewa kowa komai ba na kwanta don duk a
gajiye nake addua nayi na lumshe idona ina tunanen duniya.
A hakan barci ya daukeni ban sani ba barci ko sosai nayi don ban falka ba sai
tsakiyan dare sosai da fitsari ya tayar dani dana kewaya na dauro alwala na fito.
Ina sallah nake jin muryansu a falon sama sama hakan baisa na fito ba don ina
son kama kaina don gudun zargin kishi .
Har yakai ina jin muryoyin nasu sosai hakan yasa na daure nafito don na fahinci
akwai matsala a lokacin shina sama yanata kwara amai daga kwancen da yaken wani
irin bakin amai kamar an wanke bayan tukunya ga yawan yunkurin da yakeyi din sai ya
baki tausayi don


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login