Showing 288001 words to 291000 words out of 328222 words

Chapter 97 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

akanshi wai yan sa,a guda suke da saurayin
nata ai bata damu ba tunda tana son abinta har ankai ga zancen aure yanzu
tsakaninsu.
Ni fargaban haihuwa da yadda nake jin labarinsa ya dameni a yanzu ba wani zancen
auren saratu ba can donko na sa kaina ba ama yi dani din don me zan matsa kaina da
zancen abinda bai shafeni ba.
Saidai duk da hakan ban tsira ba a wajen matar yazid nake ji wai nice ke zuga
yaya kada yayi mata abin arziki na hanashi kashe kudi ga yar uwarshi kiji alhaki fa
don Allah yar uwa ?
Ni dako zancen bamu tabayi da yaya ba wai amma mama ta dauki laifin komai ta
dora akaina kuma yanzu koda naji zancen ban damu ba saboda nasan karan tsanar da
mama ta dora min a kai tun shigowana a cikinsu.
Yanzu nagane taso tayi amfani dani kawai inyi ta bautawa rayuwansune kawai a baya
bata so zancen aure ya shiga tsakanin muba da danta shi kuma sai ya shamci kowa
yayi abin ta baibai ba tare da sanin kowa ba.
Zancen kayan electronic sukazo nai dashi yake fada masu har kudinsu ya bada don
haka shi ba zai kara komai ba su barshi da abindake gabanshi na haihuwan matanshi
kuma.
Daga wanan zancen ina ruwan zafi su sakani daga uwar har yar nasha zagi a bakin
su ko ina sai batani sukeyi wai na hana yayiwa yar uwarshi komai a yanzu.
Wai kuma ashe ya bada kudin saitace gadon da za a sai mata bai mata ba shine
mama ta biye mata suka sai gadon da takeso kudin ya kare gaba daya yanzu suka koma
suna kame kame .
An lalubo Habu yabada dubu dari uku sukara shi kuma yazid yace ai sun san baida
kudi tunda da mama aka hada kai kawu ya cinye mashi kudi ta kuma hana yayi magana.
Haushin hakan yasa suka shiga wani rayuwa na tashin hankali a lokacin su a
zatonsu komai yaya J zai mata sai gashi ya make hannu yace iya abinda zai bayar ke
nan ya kuma basu don yanzu ta kanshi yakeyi shi.
Ga buki sai karatowa yakeyi kamar yadda ko wani aure kan kankama har dangin ango
sunzo sun kawo lefe a family house dinsu wanda mama ta koma can a lokacin aka tari
lefen da ita .
Tun wajen kawo lefen tsegumi ya fara ana fadin da gani yan kauyene don ba wata
wayayya a cikin matan da sukazo din .
Mijin kan na nunawa a cikin tsara saidai haline ba mai cewa ga halinsa tunda
ganinsa akayi garin yanzo aiki kuma baifi shekara a garin ba suka hadu.
A cewarshi itace ta biyu don haka ake fadawa kowa a ta biyu zata shiga gidanshi
din ni dai ina gefe ban sa kaina ba kamar yadda ba a sani ba.
Na dai sayi zanin gado masu kyau manya guda biyu a wajen anty salma wanda zan
bada gudun mawana ga bukin har kuma sun iso a hannuna na aje.
A wajen mama nake jin wai yaya j yaje kaduna don yar wajen Saiba da bata da
lafiya yarinyar ta koma kamar sikila yanzu .
Shine mama tace wai ya dawo da uwarta su dubata a gabanshi maman tudu ta dora da
cewa kinga ke nan tana son ayi bukin yarta tana gidan ke nan ?
Duk da naji wani iri a raina ban yarda na bar abin a zuciyana yadda zai dameni
ba yima nayi kamar ban san wanan shirin da akeyi ba na sharesu muna dai zaune kamar
yadda muke dasu duka har shi.
Asmau cema suka kwasa dashi sosai da zancen ya fito cewa Saiba zata dawo gidan
har sukai fada yace idan yayi niya ita bata isa ta hanashi ba .
Wanan zancen kuma yazo min shima na nuna kamar banji ba saidai a wanan karon na
kasa daure hakan tunda nima mutym ce mai jini a jika ai.
Na danyi fushin hakan kuma ya fahinceni saidai tunda banyi mai magana ba shima
ya shareni akan zancen ya nuna ba komai.
Ranan daya dawo gidan muma ban bashi wani kulawa sosai ba kamar yadda na saba
bashi abinci kafin ya dawo daga sallah na aje mai komai na koma dakina na kwanta.
Ina jin motsinshi daya dawo ya zauna falo yana waya amma ban fito falon ba
yanayi yana kallon kofana har ya gama yake tambayan Biba ke ina antyn ki take ?
Tana daki uncle naji muryanta tana bashi amsa lafiya take kuwa ya tambaya yana
mikewa naji tace in dai ba yanzu ba lafiya kalau take.
Mikewa yayi ya shigo dakin ina kwance kasa da tasbaha a hannuna da nake ja ya
tsaya daga kofa yana fadin yaya dai lafiya kike kuwa ?
Na dago na bashi amsa a takaice kamar yadda Biba ta fada mai don ba halin karya
gareni yanzu nace lafiya sai yabini da wani irin kallo na shareshi tunda na bashi
amsan.
To yaya abinci fa ya fada a inda yake din nace yana falo na aje ma yayi shiru
kafin yace ba za a bani ba yau ke nan ko ?
Nayi shiru can naji yace bakiji me nace bane kin kyaleni yana falo na ajema ai
na fada kamar a hasale hakan yasa ya karaso yana fadin wai lafiya kike kuwa
Rahama ?
Lafiyata kalau nace maka ban dai jin tashine yau Allah ko yau ban samun gata ke
nan nan ma ban bashi amsa ba na kyaleshi.
Ya dan jima tsaye a kaina yana kare min kallo kafin ya gama nazarina ya
tabbatar da lafiya din nake sai naji ya juya yana murmushi ya fita.
Har yakai kofa yake fadin idan kin gama saiki taso ki ban abincin ban amsa mashi
ba ya fice ina jinshi ya jima a wajen zaune naki tasowa in sameshi din.
Saida na tabbatar daya gama ya shige na fito don kawar da kayan na kwashe zuwa
kitchen a lokacin na farga da kamar bai taba kayan abincin ba kenan haka na nufin
baici ba ko ?
Na bude warmer din abincin naga bai taba ba nima na shareshi shiya sani tunda duk
kyautatawan da nake mai bai gani yafi bukatan ya dawo da yar cin mutuncin matarshi
azo a dora inda aka tsaya tunda ba barin halinta zatayi ba.
Na juye abincin nasa a fridge don kada ya lalace na koma dakina na kwanta ban
ko tayar da Biba tazo dakina mu kwanta ba yadda muka saba da ita idan baya gidan.
Barci ko a ranan rabi da rabi nayisa don haka bai taba faruwa a tsakanin mu ba
inba lokacin da baida lafiya din nan ba sai wanan karon.
Washegarima ban lekashi ba bai fito ba har na kare abin karyawa na aje mai na
koma daki nayi wanka na gyara jikina na kwanta ina jin biba ta gama gyaran gida har
ta saka kamshi yana tashi na lumshe idona tagama shirinta zuwa school lokacin ta
shigo dakina tana fadin anty nagama zan tafi.
Hakan yasa na bude idona da sukai ja a lokacin don bacin rai dana sakawa kaina
ina fadin ga kudin motarki nan dana kashi saman mirrow ta nufi wajen ta dauka.
Da yake tayi wayau a yanzu harta dan juya zata fita sai kuma ta tsaya tana fadin
anty lafiya kike kuwa ko jiya uncle yana tambayana da bai ganki ba nace ban jin
dadin jikinane Biba tayi min sannu ta fita.
Ina jinshi ya shirya ya fito ya leko dakina ina kwace saman lafiyayyen gadona
daya sha gyara na harde kafa nayi makari da hannuna na rufe fuskana.
Ya dan juma a tsaye kafin ya juya ya fita can naji karan motarshi ya tayar ya bar
gidan na sauke ajiyan zuciya ina jan tsuki.
A lokacin yadda nake jin haushinsa a zuciyana komai zai faru ya faru din tsakanun
mu tunda ba kwanciyan hankali yake kauna bashi.
In mama bata damu da kwanciyan hankalinshi ba aishi yasan abinda ke nan da zai
biye mata don kawai taga farin cikin mu ya ragu a gidan.
Tunda yanzu tana zaton rashin Saibane duk ya jawo mata wani matsalan da take ciki
na rashin samun hankalin danta yadda take son ta mulkeshi.
Sunce da Saiba tana nan wani abin dole yayi don dole ko yaushe yana gidan ai
amma ita Asmau da ita da babu duk dayane a wajenshi tunda bata maida kanta abun
kwarai ba a wajen kowa.
Shigowan Aminu da yayine yazo ya tsaya daga kofa yana fadin mummy ina kwana
yasa na fito falon na zauna a tare dashi yana karyawa yana ban labarin zirga zirgan
da yakeyi don cika takardunshi a school din .
Bayan Aminu ya gamane nan ma ban shiga daki ba nayi zaune a falon lokacin ya
shigo Aminu ya gaidashi ya mike ya fita ni kuma nayi zaune ban dago kaina bama
balle in gaida shi.
Abinda yasa nake baki wanan labarin shine wani lokacin mu mata idan haka ya
faru bamu tsayawa mu duba mu,amulan mu da namiji akan ai zancen bai shafemu ba
shiya shafa makin mu kara kyautata hakan sai mu barar da daman mu daga wajen jan
ajin da muke nema wajen miji din.
Dakinsa ya shiga ya fito ina kallo bai taba abin karyawan dana aje mashi ba
alama ya nuna shima ya hau dani lokacin ban kumayi dabaran yi mashi magana daya
karya ba .
Har ya fito saida yakai kofa ya juyo yana fadin shi zai shiga kaduna wani abu
wani zafinsa na kara ji a zuciyana a yan kwanakin nan ya matsawa kaduna din nan
sosai yana shiga lokaci lokaci ashe bikon matarshi yake zuwa yi na raya hakan a
zuciyana bance dashi komai ba dai har ya fita.
Ashe hakan yaci masa rai bai bar zaria ba saida yakai karana wajen maman tudu
akan tayi min fada kan halin dana dauko mashi tunda abin bai shafeni ba a cewarshi.
Matsalansuce shi da matanshi baiga abin da ya shafoni ciki ba tun nan mama tace
dashi ya shafota takan malami tunda in haukan Nusaiba ya tashi kowa hadewa takeyi
tayi dashi.
Ita dai ta bari tunda bata da matsala da haka sin tana gidanta daban meye nata a
ciki sun jima da mama kafin ya fito ya bar gidan zuwa inda zashin .
Da rana tsaka saiga mama a gidan nayi mamakin zuwanta don in zasuzo aida safe
suke zuwa yaya Auwal daya kawota tace dashi ya tafi idan ta gama zata hawo motan
kasuwa ta dawo gida.
Tun nan na gane akwai magana kuma gashi ita kadai tazo ba Nafisa dake rakota idan
zatazo din na dai tareta yadda na saba na aje mata komai na koma kasa gefe muna
gaisawa.
A lokacin ta fara yi min maganan daya kawo ta din wajena wai yace baiso ya
fadawa iyayyena tunda haka bai taba shiga tsakanin mu ba dashi.
Mama ya fada mana sai me ko cikin nan da nake jira in haife yace ba zan haifa a
gidan nan ba ina da wajen haihuwanshi ai.
Ni dai ba zan shaganta abina ba tunda Allah ya sheda shi yayi min cikin wallahi
ban taba zina ba balle kishiya ta kira min zina da aurena.
Shiyasan abunda yake tsunta a wajenta har yake ganin a yanzu ya dace ya dawo da
ita dakinta tazo taci gaba da aibanta min abinda zan haifa a gidan.
Kukane yazo min da nake fadan hakan a lokacin da sauri mama tace tana farashi
yadda ta kodu din nan bata farawa ai inane bataje kamun kafa ba don ya maidota
dakinta.
Anyi na malamai da bokaye baici ba yanzu ta koma na lalama ga yan uwa da abokan
arziki har sukaciwo karfinsa ta yarinya yanzu ya yarda.
Mama shi ya shafa cikin nan kawai ya tsayar dani gidan nan wallahi da ba zata
sameni a gidan nan bama to a nan na sameshi nan zan haifeshi in wuce.
Ke yar nan kada ki soma wanan gangancin da kike kokarinyi a yanzu don Allah ki
wuce ki bar dan ko yar dawa hannunta ta kama maki ko me ita bagata ta dawo don
yarta ba ?
Sai kece da baki da mafadi zaki bar naki ki tafi a yadda na amsa kuma nakeyi
tasan zan aika don sanin halin mu fulani da karfin hali da tayi.
A,a Rahamatu kada ki hakan don Allah kina aon mijin ki yana sonki kada ki yarda
fushin zuciya ya rudeki ga banza kan wata can da bata shiryawa aure ba.
Sau nawa zan fada maki hakan ne ita fa abinda take nema taga ya samune a
tsakanin yau ko wani shirin tayo a kanku nuna mata kinfi karfinta ke.
Sai Allah ba boka ba malam kike lamarinki barsu badai dubu ta kafe sai ya dawo
da ita a yanzu sukace ba to zai fita a tsakaninsu.
Kusa ido kuyi kallo kawai indai dubu ce ita kuma itace kwana nawane za a fara
jin tsakaninsu ?
Nayi kuka sosai haka na nunawa mama din na hakkura amma itama ta fahinci da
sauran zance a zuciyana saida tayi sallah la,asar na rakota zuwa titi nidasu Aminu
muka daukar mata drop har gida na biya .
Koda ya dawo gidanta ya fara zuwa take mayar mashi da yadda mukayi tace kasan
halin fulani malam to kada kace zakaja zancen nan a bangareka don Allah ?
Don yarinyar nan ta nuna min cewa haihuwan cikin nan na jikinta ya tsayar da ita
tafiyanta zatayi ta barku .
Har ya soma fadin ta tafi mana mama halan tare aka haifemu da ba zan iya rabuwa da
ita ba ko an fada mata idan ta tafi rayuwana zai bar,,,,,,,
Karka soma wallahi don ka yarda yarinyar nan ta subuce maka malam saika dawo ka
raina kanka wallahi ana zama da mace don wasu abubuwa nata daga ciki da zan iya
fada na farko ga yarinyar nan shine hakarci ko iya wanan kadai ya isheka shiga wani
hali idan ta barka a yau din nan.
To mama me nayiwa Rahama da zata dauki fushi dani haka in ma fadana da Asmaune
takewa ai,bada ita nayi ba don me zata saka kanta a zancen mu ita.
Yanzu dai na fadama yarinyar nan kasansu fulani da riko don haka kabi sannu idan
ka yarda ta subucema kuma sai kayi nadama wallahi.
Duk mutumin da zai zauna dakai tsakani da Allah shine abokin zama ba mutumin dake
son ka a fatar baki ba kaidai kasan wanan yarinyar kaduna din komewa halinku zakuyi
da ita ko yanzu.
Ya dago ya dube mama din tace kwarai kaika yarda da tuban mazurun da tayine a
yanzu ai hali zanen dutsene amma mama tayi alkawarin daina duk wani hali nata na
baya za a zauna lafiya sosai da ita yanzu .
Aifa ni yanzu bance kada ka dawo da matarka ba malam amma kada kayi saki reshe
kama ganye a gidan ka tunda uwarka tace ka mayar da ita meye nawa yanzu a cikin
hana hakan da zanyi.
Da tun farkone wallahi malam zan hanaka ka dawo da yarinyar nan gidanka duk da
nasan harkan aurene idan bai mutu ba ba mahalukin daya isa ya raba tsakanin ku
yanzu ko mahaufiyarku ta riga da ta ciwo kanka ka yarda da hakan kaga idan na hana
a yanzu Allah ba zai barni ba nima tunda uwa nake nima ga wasu yayan.
Wa yan nan maganganu na mama tudu sun tsaya mai a zuciya don har sun sakashi
wasi wasin a lokacin.
Nayi abincin kamar yadda na saba amma a ranan ban aje a falo ba kamar kullum
kitchen na barshi na koma daki na kwanta bai shigo gida ba sai bayan isha,i ya biya
can gidan yayi masu saida safe.
Ina jin shigowanshi amma ban fito ba har ya shiga daki ya dan jima a ciki ya
watsa ruwa kafin ya fito ba zance maki yaya ya warke garau ba a yanzu.
Har yanzu akwai sauran jin jiki a tare dashi idan ka sanshi a baya ka kalleshi
yanzu kasan da sauran ciwo a jikinshi karfin hali yakeyi irin na dan adam mai
tafiya da buri a tare dashi.
Dakina ya nufo direct ya shigo sai kamshi yakeyi cikin dakewa da sanyin jiki
yake fadin kwance ake ne kingani sai yanzu na dawo na biya can gidan nayi masu
saida safene.
A raina nace ai dole ka kai dare a can tunda an mannaka da bokaya ance mai
kishiya bata mutuwar Allah haka zancen gizo bai wuce na koki ba ai.
Jin bance komai ba yasa shi fadin banga abincina a falo ba mana ko yau baki iya
girkawa bane kuma sai lokacin nayi magana nace.
Naga ka daina cine yasa ban aje falo ba amma nayi girki tun dazun ai dan
murmushi yayi cikin tsigan neman shiri a tsakanin mu yace kai Rahama kina dai son
zance ni banga abin fushi a cikin zancen nan ba ?
Nusaiba ce fa ba wata mace zan dauko wace baki sani ba kin riga da kinsan halinta
saidai ban san abinda dan gulman naki yazo ya fada maki ba kika hau fushi haka.
Wani dan gulma aini ba wawiya bace da wani zaizo ya zugani ni mutuncina da
darajan abinda zan haifa na jawa tunda ita dabbama ya fita hankali.
Taso kiban abinci don Allah tun safe dana fita ban karya ba har yanzu har ji nake
kamar banda lafiya yau a jikina tunda an saba cika min ciki kwana biyu kuma anki
kulani ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA


[5/31, 05:44] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

9️⃣0️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login