Showing 237001 words to 240000 words out of 328222 words
Chapter 80 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
shiga wajen dan uwansa.
Ya jima a ciki ya fito yana fadin amma mama abinda yarinyar nan takeyi a gidan
nan yai yawa Yazid shima ya shigo ya sameshi suka hade nan wajen iya da mama din
suna fada muna daki da Yanda alokacin tana faman ban hakkuri.
Habu sai fadi yake ban taba gani kojin irin wanan abin ba su lokaci da sukai
cikin su wayayi kokarin sheganta masu cikin su duk da kowa yasan abunda take zuwa
yi kaduna lokacin.
Haba haba kada ka biye masu a zama daya mana kome mutum yayi don kansa ai ba za
a biye mata a zama daya ba .
To tabari yarinyar nan dai bata shiga zancen ta don haka itama ina son tafita
zancen ta tun muna sheda juna tsakanina dasu a gidan nan .
Ranan naga haukan kannan miji a gaban kowa akai tujara har saiba na fadin ashe
su ake cuta da aka hansu kwana daki dashi ansan abinda aka kulla ayi yasa aka
kakabesu da karfi da yaji karshe dai yazid yai tsaye yace.
Wallahi bata kwana gidan idan kuma mama tace sai takwana sai ya kusa kasheta a
ranan hakan da tajine yasa ta fice daga part din.
Don daga inda yaya yake kwance shima bakinsa bai mutu ba a ranan fadi yake
matatace nayi abinda nake gani daidaine a gareni anyi din kije kiyi duk abinda
zakiyi.
Yana magana kamar zai daga daga inda yake kwancen ya karaso gareta ganin da mama
tayi auren saiba zai iya mutuwa yasa ta izata zuwa wajen.
Nan Yazid ya dage kan lalai sai tabar gidan a ranan inba haka ba sai ya halaka ta
dole da yamman nan ta nade tabar gidan don tdoron yadda taga yana kokarin cin mata
a lokacin.
Bani ba har yar uwata tayi koka sosai da tsohon cikinta don a yanzu tana cikin
watan haihuwantane ummah muka iya kira muka sanar da ita abinda ake ciki tace tana
zuwa.
Ashe daddy ta kira abuja ta fada masu saiga kiran mummy tana fadin mu shirya gobe
zasu zo su tafi damu duka idan basu son mune suda suka haifemu sun san darajan mu
ai.
Hakan ne ya faru don kamar hadin baki saiga iyayyeb Saiba sun dawo da ita suna
bada hakkuri ana cikin wanan zaman su daddy da mummy suka iso tare da anty Salma.
Sai ummah da mijinta da suka shigo suma a tasu motar suka hade duka a gidan gaba
daya iya tace yau dubu kinkai ga yadda kike so ke nan
Don ba sassauci a wajensu daddy yace dagani har Yanda tafiya zasuyi damu tunda
uwar mazanmu ta nuna bata kaunarmu to abashi diyanshi ba zai barsu inda ba a
kaunarsu ba.
Nan mama ta fara kame kame tana salati tana fadin ita itace za ace tana nuna
halin kyara da hattara a garemu don bata kaunar mu ita saidai a dauki alhakinta ga
hakan.
Daddy da mummy sun kafe akan sufa tafiya zasuyi damu don amana muke a wajensu
don haka ba zasu saka ido ana tozarta nu suna kallo ba gara kowa ya kama gabanshi.
Banda kuka ba abinda nakeyi a lokacin dole aka shiga ban hakkuri ana tausan su
daddy din da suka hakikance lalai tafiya zasuyi damu.
Iya ta soma magana da fadin to dubu yaukan sunanki ya cika dubu don dubu ya cika
dake saidai ki sani yau ana daukan yaran nan su koma hannun iyayyen su ke kuma zaki
rasa dan ki guda tunda baki yarda da kaddara ba a zuciyar ki.
Dama irin ranan nan nake maki gudu ranan da hakkurin yaran nan da iyayyensu zai
kare a kanki ranan da zasu fito fili haka su nuna maki sun fahinci me kike nufi
dasu.
Ace ka zauna baka da tunane kai maganan yara kake amfani dashi duk abinda yaran
nan suka fada akan abokan zamansu ya zaunu a wajen ji dubu baki bincike sai dai ki
goyi bayansu.
Narasa me yaran nan suka tare maki haka dubu duk wani kyautatawa da akw bukata a
wajen yaro yaran nan suna maki shi a gidan nan amma baki ganin hakan ke abinda nake
maki gudu ke nan a kullum dubu ?
Yanzu dai Alh kuyi hakkuri kubar yaran nan a daku nan su don Allah tunda kowa ya
gane kuskurenshi cikin zancen nan a taru ayi hakkuri don Allah dama haka zama ya
gada wani lokaci.
Daddy yace ai yayi hakkuri amma tafiya damu ya zama wajibi a garesa tunda har
aka nunawa yarsa haka shiba zai lamunci hakan ba gara dai ya dauke diyansa ya tafi
dasu.
Mijin ummah na fadin kwarai tunda abu yakai har ana kokarin shegantawa yarinya
cikin jikinta ai gara kawai ayi hakkuri aje a zubar da cikin kowa ya kama gabansa.
Jam jam Alh kana dattijo bai kamata ka fadi hakan a bakinka ba ai kai mai bada
hakkurine cikin nan kasai ya ishi mu nan ishara don wani hikimace ta ubangiji ga
hakan.
Ace cikin nan bai samu ba saida yaron nan ya shiga irin halin nan haka kadai ya
ishi bawa ya kara yarda da lamarin ubangiji ai don Allah Alh kuyi hakkuri da zancen
tafiyan nan ku bar yaran nan a daku nan su zaifi.
Yunkurin da yaya Jafar yayi don ya sauko zuwa wajen daddy ya bashi hakkuri sai
akai rashin sa,a ya fado saman gadon saida yan uwansa suka tare shi hakan yasa
hankalin kowa a falon ya koma kansu kuma .
Ihu mama tasa tana fadin a ceceta don Allah kada ta rasa jafar don suman da yayi
a lokacin mahaifin Saiba yace to Nusaiba kin gani kinga inda fitinan kishi ya kaiki
yau ?
Rashin hakkurin ki ya jawo mijin ju zai rasa ransa saboda bakin ciki ke yanzu
wani dadi kikaji ga hakan don Allah ?
Ki tunafa mutumin nan Allah ke talkafe damu shine tallafe damu ta sanadinsa muke
a cikin gidan da muke a yanzu shine cin mu da shan mu amma sha shancun ki ya hana
ki natsu ki kwantar mashi da hankalin gidansa.
Komai ace nusaiba ce silla ke wani riba kika samu ga hakan wai haba dai baba ai
wanan kyautatawan tsakanin miji da matanw ba kuma sai ka fada a nan ba tunda
kowansu yanayiwa ai ?
Wallahi a,a don ni baiyiwa iyayyena hakan ba Asmau take fadan hakan cikin jin
haushin abinda taji din a lokacin don ranta ya baci matuka.
Ke yi shiru nan sulhu akeyi mama tudu ta fadawa Asmau din daddy yace tana da
right din da zatayi maganan ta yadda bai maki ba haka muma sai bai muna ba a
bangaren yata kinga ashe yarsu itace da riban shiya take fadan wani yazo ya rabeshi
shima yaci arzikin nasa ..
Habu da yazid suka fito daga dakin suke fasin ya samu barci don Allah daddy kuyi
hakkuri yanzu dai ai taji abinda take son ji haka kuma kowa yasan cikin nan da
ubansa tunda ga matakin da maicikin akaga ya sauka wajen sheganta masa cikin sa
din.
Magana ta gaskiya duk ranan data kara wani magana akan acikin jikin yarinyar
nan ta kwana da sanin zamata a gidan nan yazo karshe.
Nan dai aka samu aka lakashi daddu yayi hakkuri bayan ya kafa hujja akan duk
ranan da wani dan uwansu ko wata mace ta fadi wani maganan daba daidai ba kotuce
zata rabshi da maishi a rayuwansa
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
7️⃣4️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Nayi kuka har nagodewa Allah a wanan ranan daya zamo min kamar na tonon asiri a
wajena ranan da nake jin kamar kasa ya bude inshiga saboda kunya daya lulubeni a
lokacin don hakan ya zamo kamar wani bakon lamari a society ake gani.
Yayin da miji yake kwance a lokacin ni kuma Allah ya nufeni da samun karuwa dashi
karuwan da nake jin tankar i hadiye raina a lokacin .
Wanda bake jin tsanar mijin fiye da kowa don ina ganin shine ya kaini ga wanan
abin kunyan a yanzu wanda a sanadin haka har ya barni da nauyi da kunyar iyayyena.
Wanda ko kafin su daddy su wuce a ranan saida su kai ta zolayata a bakin mota
ina hawaye badai kamar anty Salma dole ganin yadda nake kuka yasa takai ga rikeni a
lokacin.
Haka suka tafi suka barmu a cikin tausayin mu don sun fahinci muna zaman hakkuri
a wanan gidan gidane da baida alkibla baida tsayayyen babba da zai tsawata akai
yaran maza sune tsaye da gidan kuma su din dai tunda akwai uwa da kaka dole komai
zasuyi akwai taka burki da tauyewa ga irin zaman nan.
Zamane da wasu iyayye ke zabawa iyalinsu don gashin kan zuciyarsu su wanda
akasari ya sabawa al,ada da shari,an mallam bahaushe.
Zakiga iyayye masu irin halin nan suna nisanta iyalen su da yan uwa suna kamesu
daga shiga dangi ko wani harka na zununci wanda uwace zata zauna ta dinga shimfida
doka iya son ranta ga zurianta.
Irin wanan rayuwa muka tsunci kan mu a cikin gidan nan matukar ba naku yazo daya
ba da irin matan nan mata da yawa suna fuskanta bacin rai a zaman aurensu koda ya
kasance kuwa miji na aon matarshi uwa ba zata bari a zauna lafiya ba irin haka aji
dadi.
Abin mamaki na zata maria zata dan zauna dani ta kara min shawara ina tsaye
wajen bayan wucewan su daddy saiga Habu ya fito yana cewa da ita muje ko tsayuwan
nan kada yai maki yawa.
Haka suka shiga mota suka tafi suka barni ina kallonsu a cikin mamaki har suka
bacewa ganina naja kafata zuwa ciki inda na samu mama da iya zaune a falo suke
fadin Allah sarki mutanen kirki sun tafi Allah ya saukesu lafiya.
Amin kawai na iya fada na shiga dakin yana kwance shi kadai a dakin yayi shiru
yana kallon saman dakin yanayin kwanciyarsa zai nuna maka cewa ya shiga zurfin
tunane a lokacin .
Kwanciya nayi ba tare dana kallo inda yake kwance din ba nima na fada nawa
tunanen muna wajen a haka har aka kira sallah magariba.
Na mike zuwa bandaki na hado komai da nake mashi alwala na fito saida nayi mai ya
tayar da sallah nashiga na dauro alwalata nima na fito.
Falo na koma ranan nayi sallah haka kawai nake jin tsanarshi na karuwa a zuciyna
ina zaune ina addua wayata ta dauki kara bayan na duba naga ummah ce a layin
lokacin na dauka take fadi bayan mun gaisa.
Ramaah yaya na batku dazun kiyi hakkuri kinji kowa da tasa kaddaran kar kiyi
mamaki duk sanadin wanan cikin Allah ya kwantar da mijinku jinya irin haka saboda
hakan kawai ya faru a tsakani ku.
Wani dan, taurine dashi kafin yazo duniya sai uwa da uba duk sun girgiza wani
lokacin ubane kan fara laulayi da jinyar ciki kafin a sakawa uwa ta karasa saukin
haka manya suka fada.
Ance sai uba yayi jinyan fitar da kwansa kafin ya samu ya fito daga jikinsa
kamar yadda mace kanyi wahalan haihuwa suma maza din suna da tasu jinyar kalan
fitar da kwai a jikinsu.
Don haka nake ganin duk wanan jinyar kamar ta wanan halittan dan da a yanzu kuka
samune dashi sai kiga in har hakan gaskiyane a cikin yan kwanakin nan insha Allahu
mijin ku ya samu lafiya ya mike kamar bashi ba.
Ta jima tana rarashina kafin mukai sallama ina aje wayan kiran mummy yana shigo
min a wayan na daga itama din dai hakkuri ta bani kamar yadda duk wani masoyina iya
hakkuri zai iya ban a yanzu kawai don dama shi muka gada tun kakanin a arewa.
Na dai idar da sallah ina zaune naga shigowan mahaifiyarshi hakan yasa ban damu
dana koma ciki ba na zauna a falon abina ta jima a ciki zaune kafin ta fito da
bacin rai ta fice daga part din.
Ikon Allah naji maman tudu ta fada daga bayana don iya bata falon namu lokacin
zuwan Yazid da family shi yanzu bata faye zama damu ba ko yaushe.
Amma akwai aiki a wanan rayuwan kice komai yaro keyi da iyalinsa idon ki yana
kai a wanan zamanin ka kawar da idonka ma yaya aka kare dakai balle kace saka ido
zakayi.
Dubu tana da wahala a rayuwanta zancen nan da mutumin nan ya fada shine yanzu
take faman hasala akai duk da yaron nan yana kwance bata duban hakan ita.
Saida ta sameshi da wanan zancen bata duban zancen nan bana yau bane balle ta
duba halin da dan nan yake ciki ta tausaya mashi ga hakan.
Amma wai haka dubu ta rutsa yaron nan yanzu akan zancen nan dubu sam bata kaunar
diyanta suna alheri wayema me alherin ciki banda shi jafar din ?
Jafar din dai mijinku shine ya buwayeta yake alherinsa ba tare daya fada mata ba
kada ki dada ki kara a wanan tsanar da tayi maki a yanzu kan rilon yar nan diyan
baby da kikeyi yana daga cikon abinda yasa ta tsaneki haka ?
Ta dauka ban sani bane har mutunci taci masa daya dauko maki yarinyar nan ta
manta Nafisa na gidan take fadin ta rabasu hurda da duk wani dan uba nasu amma baya
jin hakan .
Tunda mutumin nan yayi zancen gida a gabanta nasan ya bambarowa yarshi magana
har su kuwa indai dubune ki zuba ido kiga yadda zasu kwashe da ita a gidan nan
yanzu.
Ai tunda ta gane inda take hasashen yana narka kudinsa ba a nan abin yake ba yar
nan a yanzu nata ya sameta kuma da dubu a gidan nan zakice na fada maki wanan zance
kuwa indai itace .
Sai lokacin na dan murmusa ina gyara kwanciya tace aiki barsu zakice na fada
maki don sai ta zazzagewa yarinyar nan fushinta tas zataji saukin hakan a ranta
yamzu.
Sukan ba zakice tsohuwar nan iya ta haifesu ba son sam basu dauko halin iya ba
ta ko ina sai jikokin ne suka dauko iyan a wajen sanyin hali sam iya baka rashin
gaskiya ita a gabanta.
Ni dai har barci ya daukeni ban sani ba a wajen sai dare sosai naji mama din
tana tayar dani inshiga daki na koma daki na kwanta sai safe.
Kamar yadda na saba a kullum hakane ya faru a wanan karon nayi sallah ban zauna
ba na shiga aiyukan cikin daki saida na kawo wirin gada kamar a mafarki naji ya
rikeni da hannusa da bai iya dagawa lokacin sai gashi ya rikeni dasu gam.
Na dago ido ina kallonshi shima ni yake kallo idonsa a cikin damuwa yake magana
fushi kike danine Rahama da nayi maki laifin me kike wanan fushi haka dani ?
Ni ka sakeni ba fushi nakeyi ba na fada ina kokarin kwace hannu na daga rikon
dayayi min din sai naji ya sasauta rikon yana murmushi yace.
Da kina da wayau Rahama da baki fushi dani ba a wanan abin ko kinyi fushi dani ni
bana fushi dake saidai ina son ki sasauta fushin nan naki don bake daya ke rayuwa a
yanzu ba.
Hakan daya fada yasa na kalleshi a lokacin ya daina kallona hakan yasa na
kyaleshi na share dakin ruwa na hado nazo nayi mashi wanka dasu yadda na saba
nagama na goge dakin na saka kamshi kafin na hado magani na zauna nayi mai addua na
bashi ya sha na kuma hada mashi tea mai kauri kamar yadda na saba yi mashi kafin
duk su kawo abinci sai na tabbatar da yaci wani abin a cikinsa kafin na bude kofa a
kullum.
Bugun kofan da akeyine yasa na nufi kofan don in bude saidai kafin na bude din
naji muryan maman tudu tana fadin haba wanan dukan ai sunji dole a bude indai
Rahamace yanzu haka ita ta tashi tunima tana aiyukanta ai.
Ina budewa Saiba ta kutso kai a cikin dakin kamar zata bankeni naja gefe daya ta
kutsa kai ciki tana fadin munafuncin banza da wofi kawai.
A labe da sunan yaudara ana ha,intan mutane ga hakan Allah dai ya tona maki asiri
ai kowa ya gama ganin ki da abin kunyar da kikayi .
Abin kunya ai yana a gindin kowa don gara da nawa bada katon waje nayi ba da
mijina nayi wasu kuma zarginsu akeyi da mazan waje ai ?
Allah yafiki yafi sherinki nusaiba don ya kwatoni daga sherin da kikaso ki kulla
min shigowan mama ya hanata ban amsa don mama ta shigo cikin daga murya tana
fadin .
Yarinyar nan kina da hankali kuwa ina zancen nan an kasheshi tun jiya yanzu kuma
kizo da farar safiyan nan ki tayar da mutane da fitina haka ?
Aina fada maku yar nan bata da mutunci dama nasan ba zata bar zancen nan ba ai
kishin mahaukata kawai ta iya ita.
Niba fitina nazo yi ba nazone a raba kwana abawa kowa hakkinsa tunda ba ita
kadai bane kuma bata fi kowa da za a barta tana abinda taga dama haka ba ?
Kanki daya kuwa to anki a raba kwanan yadda aka saba din haka za ayi ai dama ba
wanda ya hanaku halinku shine ya koreku ba wani ba ko kun tsaya din me zakuyi
mashi?
Ki duba ki gani yadda yarinyar nan ta tsaya ta gyarashi ta gyara mashi muhalinsa
a cikin ku wa zai iya wanan din ?
Keko Amina tace hakan mana sai an raba kwana a yanzu mana tabi dare tayi mai
fyade