Showing 150001 words to 153000 words out of 328222 words

Chapter 51 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

yana fasin zamuyi waya na amsa saida yaya habu ya fita na iya
fitowa falon na dan labe ina mashi Allah ya tsare suka fice daga gidan.
Sai kuma lokacin naga gidan yayi min girma duk da ga yarinyar nan biba daya kawo
min ga kuma maigadi a wajen gidan.

GIDAN KAWU
Kawu dauda dake zaune yana lissafin kudi jin motsin matarsa hausatu yasa ya
maida filo saman kudin ya taushe saidai yayi shuka a idon makwarwa don hausatu taga
abinda yake nufi lokacin.
Jug din furan data dauko wanda yaji nono da sukari tana ajewa ta mike tana fadin
malam meye duniya naga tun shigowan kudin nan ka tsiro wani sabon dabi,a a zuciyar
ka.
Kana nuna baka son ma inmatso balle insan komai dangane da kudin nan karka manta
komai daya faru har kudin nan suka shigo hannunka nice na shiryashi gidan nan ?
Kai ya dago yana fadin yanzu me kuma nace ko nayi hafsatu me nace akan kudin nan
dole in kula da dukiyan mutane ai don yaran nan kinsan ba kirkine dasu ba.
Zasu iya hada kai nan gaba su binciko kudinsu a wajena donshine bani son wasa da
wanan kudin kike ganin kamar wani abune hakan ?
To yanzu dai ba wanan ba malam ta kai zaune tana fadin kasan dai Allah ne yayi
damu zamuci kudin nan muma a gidan nan tunda ya kwatosu ya dawo muna dasu hannun
mu.
Katseta yayi da fadin to sai akai yaya ta kara gyara zama tana fadin to shine
nakema tuni da yaran nan mardiya da dija kasan dakunan su yana son gyara ko kwashi
muje din nan na bakin titi da ake kafawa aka kwasan masu zasuji dadi kasan mazan
yanzu basu son ganin daki ba komai sai wullakaci da raini ya shiga tsakanin miji
da mata.
Ko wani miji dai a yanzu so yake yaga wurin kwanci gyarare da kuma mace mai dan
maiko ba yar bani bani ba kadai san komai basai na fadama ba .
Shi kuma yaron nan sale a samu abinda aka bashi ya huta da yawon tasha din nan da
yakeyi idan kayi hakan ni kayi min komai wallahi nasan naci a gida ni in koshi
tunda kai naga ba irin mazan zamanin nan bane da suke son ganin daki yana walkiya.
Hakane fa to zan duba saidai zancen Sale gaskiya ban maki alkawari ba tunda ko
an bashi a wajen shan wiwinsa zai kare don me zan dauki dukiyan mutane in danka
mashi da sukarye a banza.
Malam yau dai kome sale ya zamo dankane ba a canzawa tuwo suna su wa yan nan
daka rike suka zamo abin kwarai ai yanzu sun gujeka sun nuna maka halin yan duniya.
A,a hafsatu muka dai nunawa juna mu dasu tunda yakai har yaran nan yanzu kamar
sungane me muke kullawa a kansu don gaba daya yanzu Jafaru ya daina fada min komai
nasa kinga kuwa kamar ya ganeni ke nan yanzu.
A bakin yan gari nake jin wai,wani harka ya samu na ma,adaine shine yaje gun
sarki ya gabatar da kansa kinsan ko tunda kikaga hakan harkace babba amma yai bugun
gaban kanshi yake gabatar da komai ba tare da sanina ba a yanzu.
A,a,a,a aiba ido zamu saka mai ba son mun kwaci wanan dan kudin a hannunsa yanzu
dole mu sake shiri a kansa a nemo makashi kamar baya ?
Nagaji da wanan abin hafsatu tunda yaran nan ba mantawa sukayi dani ba gara dai
in sun tuna dani inci din yanzu abin nan dana rufewa Halima yana damuna a raina
tunda duk yadda nabi a karshe dai kwaliya bata biya kudin sabulu ba kan yaran .
Kai ke ganin haka malam da badon hakan ba aida baka samu kansu hakan daka gama
fadi ba a baya saidai kaima ka koma cikin yan kallo a yanzu.
Haka dai ta gama dadin bakinta ta matsa mashi yasha furan yace zai sha don a
yanzu ya fara zargin tana mashi asiri don bai iya kyatare zancen hafsatu din har
wani shakkunta da tsoro yakeji nata idan ta fadi magana dole a bita koba dadi.
Yanzu ko ya daura dammataran kwato kanshi kan abinda ya dade yana buri a
zuciyarsa duk da yasan hakan ba karamin abu bane wajensu hakan zai jawo masu.
Itama dai a bangarenta mikewa tayi cike da tunanen mijin nata da a yanzu yake
kokarin juya mata baya don ganin ya damki kudin da suka dade suna shiryawa akansu
sun shigo hannusa yake kokarin juya mata baya a yanzu.
Yazama dole ta kara shiri akan malam din don bata tsamaci kudin ba a hannunta
zasu zauna ba sai gashi duk da suna wajensa yana kokarin karta ganima da idonta
hakan me yake nufi ke nan ?
Takai wani lokaci a wajen tana tunanen hanyar da zata fitowa malam din dashi
kafin ta mike ta shiga aikin gabanta tanayi tana saka da warwala a zuciyarta.

Musalin karfe dayan rana Salimace data gama shirin ta tsab ta fito daga dakin
kwanan su da yar karamar jakkar hannunta saidai ganin saiba tare da mama yasa ta
kasa magana lokacin ta zauna.
Kamar hadin baki saiga mariya ta shigo da abincin ranan data girkawa su mama din
ta fara gaidasu iya ke fadin yar albarka yar tofon lada kamar kinsan tun dazun
yunwa nake ji wajen nan zaune.
Ruwan shayi da biredi mai zaiyiwa mutum a cikinsa ba wani abu mai nauyi da mutum
yaci tun safe malalatan yaran nan sunki su girka abin kwarai da mutum zaici har
yayi sauransa yaci da safe ya dora a cikinsa don kiuyan banza irin nasu.
Amma iya ai kinji ina masu fadan dafa dukan da sukayi jiyan nima ba sonsa nake
ba amma tace min wai ta zuba ko dole na kyaleta.
Iya bata tankawa mama din ba dake magana tace bude min nan kinji ban iya bude
abin nan takecewa maria din data aje abincin gabanta.
Maria ta duka ta bude da sauri iya ta kyalla ido kan abincin tuwon alkaba da
miyar danyan kubewa sai manyan nama guda biyar da miyan ja da ya cika kulan miyan
bata san lokacin da hannunta ya dafa kan maria din ba tana fadin Allah yai maki
albarka yar nan ya kareki daga idon mahassadanki alherin Allah ya bi rayuwan ku har
karshen duniya.
Kaji iya da wani zance shi kuma mijinta daya kawo abincin fa mama ke fadan hakan
?
Iyan ta dago tacewa mama din ai kinji jam,i nayi mata ai bance rayuwanta ita
kadai ba har kowa nata nake nufi a zancena dubu.
Idan nayi mata kamar habu din nayiwa ai don duk daya suke wajen mu daya kuwa iya
mama ta kara fada iya dai tace miko min plas in diba kinji takecewa yanda din.
Ta mike zuwa kitchen da dauko mata plate koshi saidata tsaya ta wanke tas ta
fito ta kawowa iya din ta zuba mata duk saiban tana zaune tana kallon abindake
faruwa.
Maria din ta mike tana fadin ke kuma gaki da jakka a gabanki mana kamar me
tafiya tana cewa salima ?
Kamar kinsan tafiya zanyi zan tafi Abuja yau din nan inje in huta da surutun iya
da sauri suka kalleta suna fadin Abuja kuma ?
Tace ehh gidan Rahama zan tafi dazin mukai waya da yaya yace ya wuce can zani na
dan zauna da ita kwana biyu kafin ya dawo nan ai lagos ne gidan kwamacala gidan
kowa da kowa can ko ai kinga gidan hutawane nayi.
Maria kan tunda ta daga batace komai ba tasa kai ta fita tabarsu nan suna
karawa da Salima din da Saiba dake fadin ohh dama nufin ku ke nan ashe gidan
hutawane can din.
To bari yayan naki ya dawo muji in hakane kowama ai yana son hutu a rayuwansa wa
zaku mayar dan kauye bakauyama kun kaita abuja balle mu yan birni.
Ke Nusaiba fita batun Salima don Allah shirmenta take fadi shi abujan dame yafi
lagos din ?
Yafi mana mama Saare ta fada daga gefeb da take kwance ai tunda kikaji Salima
ta fada nufin yaya ke nan can ne gidan hutun nasa nan kuma na kwamacala.
Wanan karon kingansa gidan nan sosai kamar yadda ake ganinsa idan yana gari komai
dai mutum zaiyi ya tuna da Allah .
Halan Rahama din tafi wanine ko wata kai da za a tsabareta a gefe daya a rabata
da yan uwa akaita can mama don bakiga gidan bane fa shiyasa ba zaki gane gaskiya
Salima na tafadi ba irin ginan zamani din ban komai tsone a gidan gwanin ban
sha,awa.
Kai haba don Allah akan dan uwanki kike fadin wanan maganan haka yar nan iya data
cika baki da abinci take fadin hakan ga Saare din.
Ta samu ta hade tana fadin shike nan Allah ya bashi ba zai nuna ba akansa aka
fara hakan ina nan kukaso ku tozarta shi kuga inda zai saka yarinyar nan yayi maku
bazata akan hakan.
Yanzu kuma kuna son kakaro wani zance salima tace nima iya bada wani manufa na
fadi hakan ba wallahi sheri dai nakewa mariya din ita kuma saare tana son maida
zancen babba ta mike zata fita da jakkarta mama tace da ita dawo.
Da sauri iya tace ta dawo kamar ya ke jeki Allah ya tsare ki gaida ita sai munzo
duk sukai shiru sai Saarece ke fadin toke iya ina ruwan ki ai gara a hanata zuwa
din don bata san ciwon kanta ba gidan kanwar bayanta zataje ta tayata zama gototo
da ita Rahama sa,artace don Allah ?
Ke ya isa haka don Allah mama ta fada a hasale sai saare din tayi shiru amma
mama kin daiji abinda ake fada ko a bayan mu yau shi salima ta fada a gabana ko ?
Don salima ta fada mijinki ya fada maki hakan wai akankune aka fara hakane miji
ya raba gida in kubi a sannu indai Jafarune Allah yai masa budi tunda kukaga hakan
koku yana da niyar raba maku din mutum ya kasance mai hakkuri koda yaushe ba gagawa
ba zancen yaran nan zaki dauka ya wahal dake a karshe to ki zuba mashi ido inkinji
ta tawa.
Ta dade zaune kafin ta mike ta fice zuwa part dinsu a hasale take har lokacin
tana shiga saiba na zaune tana cin abinci take fadin kinji ni da yar iskan nan
Salima ?
Me tayi Asmau ta dago tana tambayanta taja tsuki ta zauna tana fadin wai nan
gidan shine gidan kwamacala don haka lagos ne nan can kuma gidan daya kai yar iskan
nan shine Abuja gidan hutu.
Dariya Asmau ta kwashe dashi tana fadin kai lalai salima dai yar takalo zancene
yayin da nusaiba din kewa Asmau kallon shasha,sha tace wai ke ranki bai baci bane ?
Tace akan me shi kanin miji kana fushi da zancenshine Nusaiba ai lokacin daya
gane kana fushi da abinda yake ma lokacin zai kara abinda zai bata ma rai .
Ina ruwan mu da Abuja ko lagos tunda nan ma bamu rasa komai ba nifa kinga raina
bai baci da wanan abin bacin raina dayane shine ace shi mijin ya juya muna baya ya
fita zancen mu bai kulamu bai damu damu ba amma ni duk wanan abin nasan wata rana
kamar mu zata koma itama a dai fara aje yaya ki gani itama tabi layin mu din.
Kafin tabi kina nufin mu zama yan kallo Saiba ta fada tace dama ai haka abin
yake kin sani dole in ankawo wata kayi hakkuri don baka zamanin ka kaina wani ni
wanan yasa kikaga ban wani damu kaina ba tunda nasan haka abin yake dama .
Ohh Allah hakane ai bansan da cewa ni kadai ke yakina ba gara da kika fadi naji
yanzu kai nusaiba ke nan da wani zance kike to ke wanan abinda kikeyi riban me
kikaci wajen sa don Allah ?
Ta mike zuwa daki tabar Asmau din data bita da kallo zuwa kurewanta tayi
murmushi tasan abin ya taba mata zuciya amma ta godewa Allah data taushi zuciyar
nata kan abinda take ji din.
Da badon yan uwanta da iyayyenta da suka tsawata mata ba da haka zata biyewa
Saiba din suyi ta hauka ana masu dariya tare miji dai na kowane ba na mutum daya ba
don haka kowa tashi dabaran ta fitar dashi a gidan.
Suna isa Abuja direct airport ya nufa dashi don saura kiris jirgi ya tashi yana
fitowa daga mota kirana na shigo mashi ya dauka yana fadin.
Amaryata ya kike ?
Saida na sauke ajiyan zuciya na amsa a cikin sanyin murya da lafiya lau yayana
yaya hanya yaya ya habu ya amsa da yaya habun ki lafiya lau yake Rahama to ya
akayi.
Na dan kashe murya ina fadin ba komai yaya sai dai kewa gidan yayi min shiru ya
ba dadi sai naji yace ohh god ko in dawone to ?
Ke Rahama ba zai dawo ba ki koyi zama ke kadai mana ita maria da nake tafiya na
barta kin fitane da zaki wani marairaice murya da sauri na kashe wayan na kifa
kaina a filo.


ZAINANB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

5️⃣1️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Saiba kuma ya habu ya fada don ganin Saiba again tana kiran dan uwan nasa a lokacin
ya fadi hakan yana mikawa yayan nasa wayan.
Ya karba yana mannawa akunnesa yace hello Nusaiba wallahi J sai Allah ya isar
muna mucuci kawai azzalumi don yarinyar nan kake kokarin nuna mu ba komai bane a
yanzu wajenka ?
Yau har yakai a na fada muna cewa wai mu din kayi doping din mu ka koma wajen
wace ake ganin tafi mu wallahi kai azzalumine J sai ,,,,,
Dakata Nusaiba wanan wani irin zancen banzane kika kirani kina min mara amfani
ina kan hanyar tafiya neman kudina ko wani yace daku da Rahama nazo tafiyan nan ?
Aiko da itace ba a mussun hakan don zaka iya yin hakan a yanzu tunda ka iya ware
ta daga cikin mu ka nunawa duniya tafimu wallahi ka dawo ansan wace za ayi don ni
ba zan yarda da hakan ba kaji na fada maka.
Ok ai ba sai na dawo ba Nusaiba ko yanzu kije gidan ku ba matsala na sake ki wuf
Habu ya karbe wayan daga hannunsa yana haba dai J zaka biyewa haukanta ku zama daya
?
Duniya ta zageka a kuma zagi Rahama a banza da bataji ba bata gani ba irin wanan
abubuwan naji maka tunda ka kawo zancen auren Rahama a wajena .
Nasan dama sai kun kwasa da Saiban sosai akan haka don haka don Allah ka kara
hakkuri ka daure ka fita zancen ta kawai kaba banza ajiyan ta don Allah .
A zaria ihun da Nusaiba tayine ya tayar da Asmau dake barci a falo ga yara sunyi
kaca kaca da falon nasu da shinkafan da sukaci sub watsar ko ina sun zubar da ruwa
samab center carpet din duk kiriniyarsu a lokacin baisa ta tashi daga barcin da
takeyi ba sai ihun da saiba tayine ya tayar da ita agigice.
Lafiya take fada tun kan takai dakin Saiban tayi dirsha kasa tana salati tana
shiga take fadin lafiya maman ikiram ?
Ita inda ranta yakai shine mijinsu wani abu ya sameshi tunda shine ke hanya a
lokacin don haka tasa shi wani abin ya sama dai.
Yaya J ne ko me ta kara fada tana matsawa kusa da ita a hasale ta dago ta
kalleta tana fadin don Allah ni kin cikani da tambaya shine din.
Burin ku ya cika yau tunda ya furta min saki amma ku sani wallahi yadda na rabu
da J kowanku sai ta rabu dashi rabuwa na har abada gidan nan.
Ba daini akaiwa haka ba to wallahi ki rubuta ki aje na fada maki har bafilatan
nan da yar uwarta saina fitar da ita gidan nan dukkan ku .
Wai me kike fada hakane don Allah meke faruwane sai wani magana kikeyi kamar
wace ta samu laluran kwakwalwa ?
Ehh hauka nayi ki fita kawai ki ban waje don Allah Asmau banson gulma tunda kinji
meya faru dani ko ?
Fita tayi daga dakin kamar yadda tace saidai bata zauna ba part din iya ta nufa
ta samu Saare take fadin kijefa ina ganin mutumiyarki ba lafiya tsakaninsu da
yayanki
Ita da yaya kuma shida bai gari koya dawone tace ina ganin kiransa tayi da cin
mutunci dai amma ki daije kiji ko meye ta mike da sauri ta fita daga falon iya din.
Asmau takai zaune wajen iya tana fadin Nusaiba bata ji saida na bata magana nace
tabar zancen nan taki nasan ta kirashi a wayane sukai cin mutunci ya saketa.
Shine wai gaba dayan mu har mariya sai mu bar gidan nan yadda aka saketa daga
kawai naje ina bata magana ta dinga fadan hakan akaina.
Nasan za akai ga hakan don yarinyar nan bata da kirki ko kadan badai kan dan
zancen nan da Salima tayi bane ta hakeshi ta kirashi da cin mutunci.
Shine kuwa nasan ma shine iya saiga mata ta fito daga daki take tambayan meke
faruwa kuma nan suke mayar da abinda ya faru ta mike tana fadin saki kuma ?
Sakifa shi jafar ina ya koyo sakin mace daga dan magana ko da gaske kansa ya
burgene ban sani ba kan yarinyar nan ?
Wani irin zancene haka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login