Showing 66001 words to 69000 words out of 328222 words
Chapter 23 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
tsakiyan
falon turus taja ta tsaya tana mamakina budan bakinta sai cewa tayi wai Ramaah ce
haka ?
Wanan da kinkai wata daya aiba zamu ganeki ba ke nan kin koma wata wise haka
lokaci guda haba dai kamar wace aka saka ga injin .
Gaida ita nayi ta amsa tana zama lokacin kuma naji mama dana hango damuwa a
fuskanta tana tambaya yaya ya samu harci kuwa ?
Wallahi mama baiyi barci ba yana nan dai kwance nasan ciwon ya lafa mashine amma
ba barci a indonsa fuskan kowan mu tausayi ya nuna mukai mashi fatan samun sauki.
Dagawa nayi na fara jidan kayana ina kaiwa dakin kwanan mu lokacin naji saaratu
na fadin wai mu hudu kenan zamu zauna daki guda yanzu ?
Ta sauka a dakina kafin yar uwarta ta dawo mana iya ta fadi hakan ba karin digo
Saare ke fadan waiki kai kayan ki dakin iya mu ukune yanzu a dakin anty nafisa tana
nan tare damu.
Jin hakan yasa na juyo cikin mamaki tace dakin iya zaki kai wanan shirgin naki
da kika kwaso ku kara cikin nata naji mama ta dan dubeta cikin damuwa tana fadin
banson iya shege Saare.
Kikai kayan naki dakin iya ku zauna tare dakin kunyi yawa yanzu nafisa na nan
tare damu saboda ciwon yayan ku.
Dakin iyan na nufa da kayan nawa ba laifi dakon don a gyare yake tas nasan wanan
iyatun dake zuwa yanzu ke gyaranshi amma dai akwai shirgi a cikinsa yadda saare ta
fada a gefe daya na tara kayan ban fito ba nashiga bayi donyin alwala saida na
tsaya na tsabtace shi na samu nayi amfani dashi nafito na tayar da sallah.
Kodana gama na fito ban samu su mama da iyan ba suna wajen dan nasu dake fama da
jikinshi a lokacin.
Tare da Salima da Nafisa muka shiga part din don gaida dan uwan nasu a can muka
samu iya tare dashi suna magana matansa duk suna zaune da yaransu daga mai waya sai
wace ke shan wani abu acup.
Gaidasu nayi na isa wurinshi ina gaidashi tare da mai sannu da jiki ya dago ya
kalleni cikin karfin hali ya soma fadin kin dawo ke nan ya kika barsu can ?
Lafiya kalau yaya ya karfin jiki kuma gabana saida ya fadi don yadda ya dago kai
mukayi arba dashi wurin ramin idonsa yayi wani iri na ban tsoro.
Bansan lokacin dana kai gurfane ba gabana yana faduwa a yadda ya kalloni ya rame
wajen idanunsa sunyi wani baki saboda azaban wahalan da yake sha a lokacin.
Ba zakice yaya jafar bane wanan dan gayen dana tafi na bari a cikin lafiyan shi
ko ince wanda ya kaini abuja sati biyu da suka wuce da kafansa ba.
Sai ki rantse da Allah wanan din ya jima yana ciwo a kwance ba Jafar bane ya
koma haka a cikin sati biyun sannu yaya ashe jiki kuma ba dadi haka ?
Hannunsa yakai a kai yana dafe goshin tare da fadin da sauki a wahalce bansan
hawaye suna zubo min ba saida naji Salima na fadin aiki bar kuka Ramaah jikin da
sauki sosai yanzu ai Ramaah.
Nidai zance har muka bar part din bawan Allah nan baya cikin hankalinshi saidai
idan an mashi sannu ya amsa da kai koda hannu baiko iya magana.
Gashi kuma suna fadin wai ai hakan da sauki sosai don dai shi musulmi da dangana
aka,sanshi ko wani lokacin bayan hakan baga ta inda saukin yake ba.
Allah sarki kallo daya zakiwa Mama da yaya Habu kiga tashin hankali karara a
fuskokinsu yanayin gaba daya nasu ba dadi a yadda salima ke fada min yaya Habu da
kawu dauda suna hanya ko yaushe cikin tashin hankali wajen malamai.
Kai duniya ina zaki damu mutum kamar yaya J mai alheri da mutunci ga duk wanda
ya sani yau kuma shine aka jeraba da wanan lamarin .
Sunce anje asibiti har angaji ana cewa ba aga komai ba amma za,aje sakoto ko
ibadan a aunashi don suna zargi a kwakwalwanshi abin yake inji likitawa.
Ranan monday zasu tafi talata ake awon yasa zasu isa tun monday din don suje
ayi booking kamar yadda aka shawarcesu.
Nisawa nayi daga inda nake zaune a hankali na furta wanan ba juttoro bane a
yarenmu ban zata wani zai jini ba lokacin.
Sai naji Nafisa tana fadim meye juma juttoro Ramaah ?
Nace a,a magauta nake nufi da hausa magauta kuma ni ai kin kara jefani a kwana
Ramaah ?
Kukan dai yaran yanzu baku san hausa ba magauta masu bin duduniyar ka take nufi
koda ance hakan ne ai ba a mussawa iya ta fada.
Iya idan hakane nima dai bance a,a ba don ko a cikin gidan mu kullum a cikin
hassadan su yaya ake duk da alherin da suke aikowa ana karbewa kuma ayi lalura
dashi.
Amma da an bada baya zagine ba godiya ba yake biyo baya a zagi mama a zagesu ana
binsu da sheri ni yanzu na hana inna shiga tare fadan suje suyi tayi donsu ke
komawa baya a kullum Nafisa ke fadan hakan.
Abinda nake fadawa dubu ke nan kullum amma tasa kada ta toshe kunnen yaran da
suka taso tun suna kananu ake binsu da sheri meye ba za a iya yanzu akansu ba Allah
dai ya kyauta kawai za ace.
Kin dauka don dadi ake shan tsamiya akwai dafa,in sanmu a cikinsa idan kana
amfani dashi lokaci lokaci yana da wuya wani abu ya samu jikinka.
Hirana da Dage dan baffa da nake tambayansa a wurin kiwo maiye amfanin tsamiyane
wai da mutane suke ta dibansa suna kaiwa birni ?
Washegari ganin yadda mama tayi laushi da yawa yasa na shiga kitchen don na dama
mata kunun tsamiya a hautsane na samu kitchen din komai ya barkace a cikinsa saida
kyat na gano ledan tsamiyan na dauko na wanke na jika.
Har na gama damawa suna zaune da kawu dauda suna magana na hado cups biyu na
fito falon dashi na aje gabanta ina fadin mama kunun tsamiyane na dama ko zaki iya
shansa.
Allah dai yai maki albarka Rahama yau kusan kwana nawa ina son in tsaya indama na
kasa samun sukunin hakan.
Naji kawu shima yana fadin a zaba min na dansha don Allah ai abin marmarine
saidai kunun da zafi hakan yasa tace don Allah in biyota dashi part din Jafar kila
shima a samu yasha kunun.
Ban fita ba saida na zubawa iya na dauraye kayan na fita na hango wanan matar
iyatu tana faman sharan tsakar gidan ga girma ga shekaru ina zata iya tsayawa tayi
yadda nake masa tsab.
Nikan na fito na nufi wajen ya J da kunun don bata kusa dani balle in gaida ita
ina saka kafa ina jin muryan saiba na fadin don ina kin rigani shigowa zaisa aje
dake idan na shiga motar gobe kisa in fito.
Saiba na fada maki idan banje ba kema babu inda zaki gidan mu zauna gaba dayan mu
a gida don ba fina kikayi ba da za a tafi dake a barni.
Wai menene haka don Allah har mijin ku yana kwance ba zakuyi ladab ku natsu ku
komawa Allah ba sai yaushe zaku girmane wai don Allah ?
Mamace ta leko daga dakin ita da kawu jin hayaniyan da sukeyi falo wai ashe cewa
kawu yayi mutum daya daga cikinsu ta shirya gobe aje sokoto da ita sai Asmau tace
ita zata wanan yakawo masu hayaniyar a tsakaninsu.
Ni dai ina tsaye saida kawu yace shigo muna dashi nan kinji yar nan wanan ne
kuma karo na farko dana taka zuwa dakin part din shi maigidan nasu.
Yana kwance shida wani abokinsa dake zaune saman kujera na gaidashi ya amsa ba
tare daya dago kai ba na aje kawu ke fadin a dan zubama kunun tsamiyane ta damawa
dubu ko zata gyara bakinta a zubane kasha Jafar ?
Sai lokacin ya sauke hannunsa daya dafe kai yana fadin a zubo kadan kawu kawu ya
dan kalloni yana fadin zuba masa ko Allah zaisa ya yasha din.
Yana da zafi kunun don haka na tsaya na dan huhuta masa na mike zuwa wajensa
ina fadin yaya ga kunun da kyat ya sauke hannunsa yana kokarin karban kofin faga
hannuna.
Abokin nasa ya taso da sauri ya karba yana bashi yake kurba a hankali yayin da
nida kawu muka zuba masu idanu sai ya shanye tas ikon Allah Allah dai yasa ya
zaunama a ciki.
Amin amin abokin ya fada na fito da cup din na dauraye wanda aka kwana dashi
cikin wani hali sai gashi ya fara karyo zufa a jikinsa.
Mama dake shigowa ita da iya da suka gama rabon fada take fadin ikon Allah meya
faru yake zufa hakane ?
Kunun nan da yarinyar nan ta dama aka zubaf mashi shine yasha yake wanan zufan
haka Allah dai yasa ya zauna mai a cikinsa.
Na dawo da kofin dana daurayo yayi yunkurin amai suna fadin subbahanallahi aman
dai yana nan ke nan sai ya koma ya kwanta ya daina yunkurin da yakeyi da farkon na
aman.
Sannu a hankali yayi lamo a yadda ya dan kwanta din ganin haka nikan na fice
daga wajensu babu kowa cikin matan nasa duk suna dakinsu a lokacin.
Na samu yan matan mama sun tashi suna falo zaune su ukkun don yanzu zaman
nafisa an karu a gidan ban dauki komai ba nake gayar dasu da kwana suka amsa min.
Aina zata kina kwancene har yanzu nace a,a kunu na damawa mama nakai mata part
din yaya J wai meya hadasu fada da safe haka ?
Wallahi ban sani ba na fada Saarece ke tambayana sai naji tayi tsuki tana fadin
ni wallahi halinsu ya fara fita min rai mutane kamar awakai sai surutu tsiya haka
abu ba abu ba fada.
Mutanen kine ai kunfi kusa gashi tun dawowan Saiba ta dora gaba dani don kawai
na fadi gaskiya akan me zamu zauna kamar muna tsoronsu kullum.
Ban fahinci zancen ta ba na danyi yan mintuna naji tanawa anty Nafisa bayani
akan abinda ya hadasu fada ita din wanda nayi mamaki kwarai jin cewa akaina ake
wanan abin.
Bafulace da rikon gaba a take naji gaba daya na tsani wanan Saiba din don haka
na mike ban karasa jin sauran maganganun da sukeyu ba na shige dakin iya na kwanta.
Barci nayi don ba aikin da zanyi sai bayan azahar mama ta shigo tana tambayana
daga dakin na amsa mata take fadin to yayan ku yace a kara dama masa irin kunun
dazun din nan.
Ai mama da zamu samu ganyen tsamiya fresh muyi amfani dashi da zaifi jin dadinsa
sosai ace wanan garin kuma sabon dakane zaifi jin dadin shansa.
Ni dubu Rahama yanzu ina zamu samu ganyen tsamiya a garin nan tsamiya da mutane
kejin wahalan dibansa .
Sai abin ya ban mamaki na tareta da fadin tsoro kuma mama niko hawa nake na debo
to ai kuma kamar mutanen boye kuke Rahama in bashi ba yaya za ayi ku kwana dokan
daji ku kadai.
Kodana dama nakai yana zaune saman gado ya hade kai da gwiwa jikinsa saye da
singlet fari na maza mai yan hannuwa iya damtse.
Na samu matan tare dashi da iya na shigo dashi ina gaidasu na aje a gaban Asmau
na fita ya kallota yana fadin ta zuba mai tana zubawa ta mika mashi ya bita da
kallon mamaki kafin yace cikin karfin hali ba zaki iya fifita min ba ?
Na dauka da zafi kake son shi ai ta fada tana mayar da kunun gefenta tama rasa
yadda zata fifita kunun saida iya ta fada mata yadda zatayi.
Yana sha yayi gyatsa ya koma ya mike zuwa falo saman dogon kujera hakan yasa
suka fito daga dakin iya dai na zaune don mama sun fita da kawu a lokacin.
Ganin basu da niyar gyara mashi dakin yasa yace da Asmau sai magariba ba a gyara
min dakin ba ko ?
Washegari dai suka tafi sokoto don yafi masu kusa jikin kuma gaskiya da dan dama
sosai ya habu da kawu da mama suka tafi dashi sokoto din.
Matansa an barsu a gida ba aje da kowa ba saboda fitinan da suka soma na wace
zata yasa mama ta tafi ita aka barsu a gida.
Asibitin sunyi aune aunensu basu gano komai a cikin kan nasa ba komai nasa yana
normal hakan yasa dole washegari suka nufo gida.
Nikan da yamma ina gyaran dakin iya da duk na gyara tulin komatsen dakin irin na
tsofi ina wayan mopping dinsa lokaci lokaci sai dakin ya canza ma,ana a yanzu .
Muryan Anty Nafisa naji tana fadin su mama sun dawo fa hakan yasa muka fito gaba
dayan mu zuwa taron su yanayin mama kawai zaisa ki fahinci tana cikin tashin
hankali lokacin.
Gaba daya muka nufi part din ya J wanda yaya Habu ya rike mashi hannu zuwa
cikin part din a hankali suke tafiya dashi a falo aka zauna.
Kallo daya yaiwa part din ya kau da kai idan ba karya zai fada ba yana ganin
tun tafiyansu ba a share falon nan ba.
Duk da yana cikin halin ciwo tsabtan nan nasa yana nan mashi har yanzu gashi kuma
Allah ya hadashi da kazaman mata a rayuwanshi.
Wanan dawowan kan sun bazama wajen neman magani sosai idan kinga ya habu ya
fita yacinsa sosai a yanzu don tashin hankalin da suke fuskanta na dan uwansa.
Nikan sosai na mayar da hankalina wajen yar uwata da mahaifiyata zanyi girki a
part dinsu in kwashe in kai masu sai iya da nake zubawa don mama ba zama takeyi ba.
Wanan yasa koya kira yaji lafiyan matarshi take fada mai komai ina kawowa basai
ya damu ba Allah yaba yaya J lafiya.
Don sun kwasa sun tafi wani gari dashi a cikin Niger state nima kuma akwai kudi
a wajena wanda shi ya J ya ban daya kaini Abuja.
Ga kuma wanda mijin anty salma ya banda sallah da zan kuma dawo hakane ya kara
ban kudi masu tsoka gidan daddy ma haka donshi banda wani matsala da kowa yanzu
gidan balle in tsaya ina rabe rabe.
Dakinsu kuma ban shiga ba tun wanan koran wullakancin da Saare tayi min na kora
da hali abu daya shine na shiga na kwaso kayana dana bari a dakin.
Na kwashi wanda na dawo dashi nakai duka can part din yar uwata na aje abina don
haka na koma banda case dasu indai ya habu yana gari zan zauna nan wajen iya din
amma kayana nacan wajesu.
A can inda suka je wani kauyen agaye wajen wani banufe da wani ya turasu shine
yayi masu bayanin jifansa akayi jifa kuma mai karfi koya mutu ko ya haukace ya koma
bai moriya.
Dalla dalla mutumin ya soma masu bayani yana fadin uwarsuce tayi sakaci har
hakan ya faru ba kuma J ba kadai har duk diyanta ana kokarin ganin an raunanasu ga
baki daya.
Abin mu na mata abuna farko dayazowa mama a rai shine abokan zamanta mutumin
yace ko daya suma gasu nan suna kallan nasu amma wanan ba irinsa bane.
Don hadashi akayi da dodon tsafi dake shan jinin jikinsa don ma yana da tsarin
ubangijine basu samu yadda suke so dashi ba ai.
Ka tuna mutumin daka gaisa dashi ya kama maka hannu da sunan yana tayaka murna a
yan kwanakin da suka wuce ?
Shiru J din yayi yana tunane ko waye yace kadai tunana gashi nan baki gajere
mai dan fadin kai da tumbi baida tsawo sosai dai haka dashi kafirine bai sallah bai
chochi ?
Still yana shiru yana tunane na dan lokaci don ya kasa gano ko waye wanan
mutumin da akai masa kwatancensa saboda abokan hurdan nasa ai yawanci kafiraine.
Hjy kinyi sakaci sosai akan yayan ki akwai matar data so fada maki gaskiya a
baya amma baki mai da hankali ba kan hakan ?
Itama mama nunawa tayi bata gane matar ba a daidai lokacin da J yace malam
kwarai kuwa na tunashi tabbas anyi hakan bayan shan ruwa na fito na sayo abinda
zanyi buda baki bakin wani shago na hadu da wani daya kira sunana ya nuna min sani
ban sanshi ba amma shiya sanni.
Yake min murna da cewa shiya dade da sanina ai muka sha hannu dashi sai malamin
yace a lokacin ya shafama abin don da shirinsa ya fito dama.
Yanzu malam yaya za ayi yace Allah shine maiyi mu saidai mu danyi namu dubarun
da Allah ya hore muna ai.
Yana ta jan tasbahan da yake aikinsa dashi kafin yayi murmushi yana fadin dewa
ya,i wanan yarinyar da karanbani take saidai ba zasu iya komai da ita ba.
Wace yarinya ke nan kawu ya tambayi mutumin yace gata nan dai a cikinku take
wata mai dan tsayi da manyan idanuwa saura kiris ta kai ga nasara a shirinta.
Amma baku bata daman hakan ba da zaku bata dama da anyi nasara koda baku zo nan
ba saidai tana shakkun wani abu a zuciyarta kuma.
Wacece ke nan malam gasu nan dai a tare daku su din alherine a wajenku kasan
wani lokaci Allah kan muna wani baiwa amma bamu fahintar hakan sai muyi sakaci da
abin.
Amma shi nan gaba zai fahinci komai kai yake jijigawa yana fadin yarinyar tana
da gwargwadon sani amma a yanzu tana tsoron aiki da hikimarta .
Nafisace ko mama ta fada wata kila itace inji kawu ya fada daga gefenta sai
mutumin ya dora da fadin hjy lalai ki samu wanan matar dake son maki bayani don
tasan komai.
Ya dai basu magani bayan surutan da yayi tayi a ciki harda zancen