Showing 228001 words to 231000 words out of 328222 words
Chapter 77 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
basuga abinda ke damunsa ba suke fada.
Barci yakeyi yanzu sosai tun bayan shigan wanan ruwan a jikinsa idan na bashi
magani da safe zai koma yayi barci mai nauyi na tsawon wani lokaci idan ya falka in
bashi abinci yaci .
Allah sarki a hakan kuma fa tunda ya fara dan motsi sallah baya wuceshi zai min
kwatance da zaiyi sallah a dagashi yayi idan ya idar kuma ya koma kwancensa.
Kan zancen nan saida yan gidansu Saiba suka shigo zaria suka nuna bacin ransu
ga abinda ya faru suka bada hakkuri yazid yana zaune yace ai su batayi masu laifi
ba wanan tsakaninta da wanda ya ajetane da kuma Allah.
Tun daya fara jin sauki yake cin abinci sosai a yanzu don ya fara karban abinci
da alaman ma kokon dayake sha ya gunduresa a yanzu din.
Asmauce a lokacin take bashi abinci don ita ta girka duk wace ta firka zata
zauna ta bashi yayin da kuma wace bata girki zata zauna dashi a wunin .
Sai tsarin hakan yayi min dadi sosai don jikina ya fara nauyi da laluran
gaskiya a yanzu ko ina samun hutu sosai inyi ta barci.
Ina zaune a gefensa Asmau tana bashi abinci dan Asmaun na goye yana a hannuna
ina mashi wasa a gefe yaron yasa kuka uwar tana tsaye a gaban mijinta tana fadin
saita gama ta kamashi.
Sam yaron baida yarda da kowa hakan yasa uwar take dauke dashi ko yaushe mikewa
nayi dashi ina jijigashi a cikin kafin naji yana badaniya da nufin na mika mata dan
ta karba mana kukansa ya isheshi ke nan yake nufi.
Ni kaina karfin hali nakeyi a lokacin don warin abincin nan ya isheni a hancina
ina jin kaina wani iri a lokacin.
A wurin karbansane na shaki turaren dake jikinta kuma wani irin amai ne naji
yazo min lokaci guda karo na biyu ke nan a yanzu dana ji abu mai kamshi zanji
zuciyana yana tashi .
Da sauri na mika mata na nufi bandakin nayi mamakin irin aman da nayi a lokacin
duk dan abinda naci a lokacin saida na amayeshi a wajen haka na fito a galabaice
ina share fuskana .
Idon su a kaina yake na samu waje na zauna a gefe tana min sannu kamahin ne ya
kara dakan hancina na mike da sauri na koma bandakin idonshi yana kaina har na
shige ina kakarin aman da ba abinda ya fito min a wanan karon.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
7️⃣2️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
A galabaice na fito daga bayin wanda yakai har mama tudu saida ta shigo tana min
sannu yayin da gogan ya wani tsareni da ido yana kallona daga kwancen da yake din.
Mamace cikin kidima take fadin me kikaci ko baki da lafiyane nace ina ganin
zazzabi ke son kamani don harda kaina yake min ciwo sosai.
Jam aima kikana da karfin jini ko yaushe kina tsaye tunda mukazo laluran nan ban
taba jin kince ga inda ke maki ciwo ba.
Bari a duba in akwai panadol saiki sha ki kwanta ko zai fada maki ta kara min da
sannu na amsa da kyat tare da fadin nagode.
Asmau take fadin balle kwanakin nan akwai sauro ko jiya saidana kunnawa yaran
nan maganin sauro muka samu barci dasu.
Ina gama shan maganin na nufi dayan dakin na kwanta barci mai nauyi ya daukeni
har yamma ban falka ba don na samu barci mai dadi a lokacin.
Kodana falka na danji dama wanka nayi na dauro alwala na fito na tayar da sallah
ina jin marata tana dan yanka min lokaci lokaci hakan yasa stil nake expecting din
zuwan period dina na monthly da mata keyi tunda yakan zo min da ciwon mara wani
lokacin.
Abinci kasa ci nayi duk yadda mama ta matsa min kan naci amma na kasa ruwan
zafi nasha na samu waje na kara kwantawa banyi barcin dadi ba a ranan don yadda
jikina ya gashi nake jin zazzabi.
Cikin ikon Allah zuwa asuba ya fada min sai gashi na tashi nayi aiyukan dana
saba na dauraye mai jiki yadda na saba yi masa don ban yarda in barshi da najasa a
jikinsa ko datti hakan kan kasance ko da mun yi aurataya nice zan masa wankan
tsarki bayan na umurceshi da daura niya kafin kowa ya fito na gyara ko ina kamar
komai bai faru ba tsakanin mu.
Koda gari ya kara haskawa na gama da daki har falo lokacin ne mama ta fito tana
fadin yar nan keda kika kwana da zazzabi kece ke aiki haka tunda safe daki bari ai
zan iya in kama maki ai ?
Murmushi nayi na dago daga sharan da nakeyi nace naji sauki mama na gaida ita da
kwana take tambayana karfin jiki nace Alhamdullahi .
Nagama komai na shiga nayi wanka na saka wani dogon riga na samu waje na kwanta
a dakin duk wanda ya shigo a gidan zamu gaisa dashi yayi min yaya jiki ?
A haka har aka kawo abin karyawa ina jin iya na fada tana fadin doya haka a
bushe babu komai da zaca hada dashi kaci ya gogema makoshi.
Hakan yasa banji sha,awan fitowa na karya din ba don nasan kayan takaici zan
sama a wajen yasa banko fita da sunan karyawa ba a lokacin.
Barcina nayi sosai a ranan don idona dama da barci ban samu barci da dadi ba da
daren don zazzabin dake damuna din.
Muryan mamace dake tsaye a kaina take fadin ki tashi haka tun safe baki karya
ba kina kwance ko jikin ne har yanzu ?
Na daga ina fadin a,a na mike da idona da sukai min ja zuwa bandaki nan kuma na
kara jin aman yazo min saidai ba komai a cikina haka na wahala na fito daga bayin .
Dashi muka fara arba ya kura min idanu yana bina da kallo kamar maye ni kallonsa
har damuna yake a yanzu idan ya kafeni da idanunsa.
Wai Rahama aman ne har yanzu badan mijinki na kwance haka ba ai sai ince ko Abba
ya samu kani ne Asmau ke fadin hakan.
Duk da gabana yayi wani irin faduwa amma saina dake nayi murmushi a fuskana
kawai na samu waje na zauna ina goge fuskana da dan kwali a cikin wahala.
Ki samu abinda kikaci kisha magani ya fada yana mai bina da kallo na dan sauke
ajiyan zuciya na mike tsaye na fita zuwa part din su mama.
Suna falon mu ita da mama da iya dasu inna na gaidasu na fita zuwa wajen anty
Salima ko zan samu abinda naci a part dinsu don ko shayi ba zan iya sha ba a
lokacin saboda yadda zuciyana ke tashi.
Nan ma din ba wani abinda suka dafa a lokacin ma take girkin abincin ranansu
take fadin bari ta hada min tea da sauri nace a,a ta barshi nashiga dakinsu na
kwanta.
Ina jin zazzabin na son ya dawo min haka na daure nayi sallah na koma na kwanta
sai gata ta shigo min da furan gora mai sanyi shi nasha sosai don yayi min dadi a
bakina sosai lokacin.
Barci na koma sai zazzabin ya kara rufeni kuma mama tudu ce mai tambaya ina ina
don bata ganni ba ake fada mata ina can dakin su salima kwance.
Duk mun dauka dai zazzabin gajiyane haka kinsan halin malam ba haushe ba komaine
ake saurin kaiwa asibiti ba sai anga yan dabarun gida sun kiyane za a kai kafa
asibiti.
Don kuwa ciwon kwana biyu ina kwance ragaraga dani abani wancan a bani wanan sai
yayi dan sauki zai dawo kuma gashi banson yawan hayaniya ga tara miyau a baki saina
faki ido na zubar shiyasa ban ma zama a cikin mutane a kwana biyun nan.
Na idar da sallah a dadafe na dawo part din mu inda na samu su mama dashi a
zaune shi kuma yana kwance a inda yake tunda na shigo mama ta bini da kallo tana
min sannu ta dora da fadin.
Ni dai ko ince an samu dan jinyane wanan ciwon Rahama kamar na mai shigan ciki
haka komai kaci baya zama a ciki sai an amayeshi ?
Daga inda mama dubu take zaune ta dago kai da sauri tana fadin ciki kuma yaya
don Allah ki daina zancen nan .
Wanda ke kwance haka rai a hannun Allah ina zancen ciki kuma ya fito nan gareta
kuma ciwon daine yazo a haka balle dama wanda yai jinya haka ai sai yaji jiki daga
karshe shima.
Dadina dake sai ki dinga magana kamar karamar yarinya dubu to ko cikin ne Allah
ba yana iya kawosa ba ko a hakan akwai abinda ya gagari Allah ne ?
Iya ke fadan hakan ga mama din mama tudu tayi murmushi tana fadin shi dai
nagani nawa akayi irin hakan muna gani dan wajen Rakiyana da mukaje jinya sokoto
kwanaki da kariya ba sai anyi dori ya gwauce ba sai daga baya likitoci suka gano
inda matsalan nasa yake dole aka rabashi kwana da matarsa a dakin .
Ai kariya kikace yaya wanan da yake kwance haka shatkaf dashi bako motsi ina
wanan zance ya fito haka kuma ki tashi ki danci wani abu kafin ki kwanta ta fada a
karshe.
Gabana sai faduwa yakeyi duk da zancen ban dauka zai iya faru haka ba na mike
zuwa falo ban iya kallon abincin ba na samu wuri na zauna nayi tagumi.
Sai a wanan ciwon na tsani halin maria ta da mama ke zaginta dashi ina kareta
ashe wani shirun idan yai yawa wa mutum akwai illa don bata iya tabukawa kanta
komai balleni ni kadai ta bari ina zugata a cikin dangin miji tana gefe ta fake da
laluran ciki ta fita batuna yau wa zan tunkara in fadawa wanan magana.
Ban koma dakin ba saida su mama din suka fara fitowa don neman wurin kwanciya a
nan falo suka sameni kwance maman tudu take fadin ayyah dama aina fadi mu baki waje
ki kwanta .
Na dai daure na kawar da kayan da komai dana saba na koma dakin kwanan mu na
fara shirin kwanciya a ranan har wani sanyi nake ji a jikina hakan yasa na nemi
waje na kwanta na lafe a kujera.
Da farko na samu barci amma da tsakar dare barcin gagarata yayi na soma kaduwa
hakan yasa ni kuka ni kadai a inda nake din.
Cikin karariyar muryasa naji yana kiran sunana yana tambaya yayane nace ba
komai na kara nadewa don komai haushinsa nake ji a lokacin.
Dole ya gaji ya kyaleni don bai iya tasowa zuwa inda nake nasan yadda banyi
barci ba shima baiyi barci ba a ranan haka ya nade dai don ba yadda zai iya.
Washegari mamace ta shigo jin bataji motsina ba tashigo tana tambayan ko jikin
ne da kyat na iya daga kaina na bata amsa takai zaune tana dafani tace kina ko shan
magani Rahama ?
Na dai amsa mata ta dade zaune tana kare min kallo kafin ta mike ranan ita da
kanta ta gyara muna part din su suna aikinsu na karfi yayansu daine sai a hankali
gaskiya kuma abin kamar a jininsune yake haka gaba dayansu yayansu mata basu da
moriya sam.
A ranan itace ta bashi abinci na dai daure na gyara mai jiki da shimfida na koma
na kwanta sauran aiyukane har bashi abinci duk mamace tayi a ranan tana falo tasa
min kira nazo mu karya dole na taso nazo din.
Cibi daya nayi na taliyan da aka dafa muna wai abin karyawan safiya na dawo
dashi da gudu naje na amaye na jima na fito ina haki na kwanta mama ta dubeni tace
anya Rahama kuwa.
Yanayin ki ya nunafa kamar cikine dake komai da kikeyi na masu cikine fa Rahama
baki na turo ina fadin haba mama na gyara kwanciyana .
Ina wajen nade na dunkule yazid ya shigo suka tsaya suna magana dasu mama da
matan yaya Jafar yake fadin
Ke yaya dai mijinki yace nazo na kaiki asibiti baki da lafiya gata dai kan kamar
maman biyu zazzabi kamar na mai ciki haka ta kwana tana wahala .
Ciki kuma mama kamar wace tasha a ruwa aida an saka mata ayan tambaya akan
cikin nan kuwa Saarece ta fada tana turo baki gaba har ta fara tafiya ta nufi dakin
ta juyo tana fadin watan yaya J na takwas ke nan fa mama hakan kwance ake zancen
wani ciki kuma yanzu gareta ?
Dakuwa mama tayi mata tana fadin ja,ira mara kunya kinbi kina wani hakilo inma
cikinne ina ruwan ki yarinyar da mijinta zaki kama wani zance can ?
Har ta shige mama tudu naci gaba da fadin nina rasa menene tsakanin yar nan
Rahama da saratu sam bata kaunar yarinyar nan da alheri ko kadan wallahi.
Daga inda iya take zaune ta karbe da fadin ina zata kaunaceta tunda sheri yana
ranta ita saratu watake so Amina ai banda wanan mara kunyar da halinsu yazo daya
banga wanda saratu ke kallo da gashi ba gidan nan har yan uwan nata kuwa.
Abu kamar asiri zakice yarinyar nan ta asircesune ita da uwarta yadda suke kafa
kafa da zancenta yanzu ba taji hakan ba tana fita zakiga takai zancen nan wajen ta
su dinga yiwa yarinyar nan kwakwaf inma cikinne ai Allah ya kawo abinsa.
Ina lafe ina jin duk abinda suke fada a lokacin gabana ya soma faduwa ina tuna
taraiyan mu da yaya a asirce wanda mukeyi a yan kwanakin samuwan saukinsa wanda
daga Allah sai mu muka san abinda muka aikata din .
Kai ina hakama ba zai yuyu ba har wani abu mukayi da za ace ciki ya shiga ga
hakan mutumin da baida lakkan wani abin kwarai karfin haline irin na maza da yan
adam kawai na kwakwa a wajensa.
Barci nayi abina bansan wainar da ake toyawa ba a gidan saida wani zazzabi ya
tayar dani na falka ina makyarkyata babu kowa a part din sai mama da shi dake
kwance dakin na koma wajenshi na kwanta agefensa na dunkule.
Ya zuba min ido da kyat ya mika hannunsa a kaina jikina ya gashe yayi zafi kamar
garwashi ya soma fadin on tashi a kaini asibiti sai naji sam banson zancen wani
asibitin nan da suke min kamar yana son a kara tsanatace a hakan gashi na fara jin
zancen banza a bakunan su duk da banda yakinin cewa ga matsalata nasan kuma
zazzabine kawai na wahala ba komai ba yake damuna.
Shigowan mahaifiyarsu part din don ba kasafai take zama ba a nan saboda mama
dake mata kara takanas ta baro komai nata ta dawo nan ta tare saboda danta dole ta
kawar da ido tayi kawaici akan hakan dama kowa yasan jafar dan maman tudu ne inbada
dan hatsaniyar rabon gado ya dan shiga tsakaninsu ba a kwanaki bayan rasuwan
mijinsu yanzu ko an daidaita hakan an koma kamar komai bai faruba a baya.
Yar nan ku kaita asibiti fa muryan mama dubu naji tana fadan hakan a gefe taci
gaba da fadin ciwon nan kada yaci jikinta duba yadda ta fada a cikin kwana biyun
nan ?
To shi dai da zai kaita gashi a kwance yana fama da kansa tun safe yaiwa Yazid
magana tunda ya fita da motan bai dawo ba tun dazun.
Dama yazid zai kaita aiko dai ya fita da nasa iyalan tun dazun nan J din ya fara
danniyar fadanshi akan dan uwan nasa a cikin karfin hali ya jawo wayarshi ya tura
mashi text ba a jima ba sai ga yazid din ya shigo yana fadin afuwan madam mijikin
ya hauni da fada na bar mashi mata na ciwo a gida ?
Sannu tashi muje asibitin please ba zai barni in huta ba yadda ya hasalan nan
dani yasa kai ya shiga dakin wajen shi na mike ina son shiryawa mu fita.
Tare da mama muka tafi asibitin itace tayi min rakiya zuwa ganin likita da zanyi
ancewa na kawo fitsari aka kuma debi jinina tun lokacin nashiga damuwa .
Ni abu biyu najiwa tsoro na farko kar zancen ciwon ya J ya zamo gaskiya abinda
kawai ya fado min a rai ke nan yasa sukace zasu dibi jinina .
Munyi zaman jugun muna jiran sakamako saigashi anfito dashi ankaiwa likita Yazid
ya shiga akai mai bayani cewa ai akwai shigan ciki a tare dani dan wata daya.
Abinda yaba likitan mamaki shine da yazid dake fadin likita kun duba da kyau
kuwa don mijinta fa yana kwance baida lafiya almost eight month ke nan yanzu.
Shine me hakan bai iya ganetane ko bai sheda kowane har yanzu jin hakan yasa
yazid din yin shiru na dan lokaci ya mike yana murmushi sukai sallama da likitan
bayan ya bashi takardan da za a sai min magani.
Tunda ya fito yake min wani irin kallo daya sani tsarguwashi dan irin yadda yake
kallona din mota muka koma nida mama muka zauna shi yaje sayen magani.
Ya dawo muka bar sibitin saida muka dauki hanya da kyau naji yace mama akwai
matsala fa don nasan za ayi tsiya da sauran yayan ki idan suka samu labarin abinda
ke damuwar yarki.
Subbahanallahi akan me za a samu matsala kuma wai wasu yayan nawa kake magana
ban fahince ka ba ?