Showing 318001 words to 321000 words out of 328222 words

Chapter 107 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

suka tare ke nan ita Rahama har yanzu
tana gidanta daban koya hadasune ?
Haba dai tana nata gida Asmau kuma tana sabon gida saiba fa shiru salima din
tayi bata bata amsa ba ta kawar da kai hakan yasa ta juya ta dubi mahaifiyarsu.
Saiba fa mama bada ita aka tare bane a gidan mama din ta nisa kafin tace jiya
ta tafi ta koma gidansu kaduna jiyan .
Gidansu kuma a to tunda tace bata da mutunci bata iya bin abu sannu ba sai tayi
tujara ai taga karshen tujara a wajenshi kuwa.
Nifa ban gane ba don ta kwana biyu bamuyi waya da ita ba ranan ma na kirata waya
na ringing bata dauka ba nace ko bata kusa da wayan ne ?
Ta dauka tunda kowa laifin ya shafa a wajenta yanzu rashin mutuncinta ya karanto
mata karya kuwa a wanan lokacin don cikinta yayi.
Kema banga dalilin kiranta ba kina fada mata sirin ki tana baradaki a gari tana
yawo da sunanki kan cewa bakiyi dacen gidan aure ba ?
Mama ta juyo a hasale tana fadin ita data dace ai halinta yasa ta zauna a gidan
daula ko banda dai sherin kishiyoyi ai ita Saratu ba a ji tayi cin mutunci ba.
Wai mama meyasa ta koma kaduna kuma ana zancen tarewa sabon gida ko sunyi fada
da yayane kuma yace ta tafi ?
Salima ta mike tsaye tana fadin kin damu da ita ke nan matar da tabi kowa tana
fada masu duk abinda kike kiranta kina labarta mata a waya zaki tsaya jin meya faru
?
Ko ba,a fada ba aikin sani rabuwa sukayi mana dashi zata kawo mai iskanci ya nuna
daidai yake da ita ya sallameta ta kuma koma ganin laifin mamanki a karshe ta
hadasu ta zage tsula har tana fadin mama ta tanka in bata shigo ta murjeta ba a
falon nan.
Yau ga yar iska mama din zata duka ai ga mama din kiji a bakinta in,ni baki yarda
da zancena ji da kanki don Allah fita batun wata mara mutunci can .
Mama wai don Allah da gaske salima takeyi haka akayi ta dago tana fadin Saratu
don Allah kiji da abinda ke gabab ki bar min zancen wanan yarinyar mara kan gado.
Eeh lalai kuwa Saiba takai yar iska mamace zata zaga har da fasin ta yi magana ta
murjeta duk halarcin da mama tayi mata a gidan nan.
Aita manta hakan yanzu tunda dan mama yafi karfin mama tace don yabar yarda da
ana labawa ga mama ana tauye mashi hakkinsa .
Nikun isheni da rashin hankalin ku don Allah mama ta fada a tsawace garesu
shigowan iya yasa duk sukai shiru a dakin.
Wa nake gani nan iyan ta fada ta amsa da nine iya ko baki shedani bane kema
zamani ke amarya har yaushe aka kaiki da zaki zo gida ?
Jiya ta amsa ma iyan tana daure fuska don ba shiri sam tsakaninsu wai yaushe
tazone iyan ta juya wajen salima tana tambatanta kafin ta mayar da idonta kan
kayanta dake gefe daya aje.
Iya dazun nan ta shigo mama taba iyab amsa takai zaune tana fadin lafiya dai ko
sai saratun ta mike taja bag dinta zuwa daki tabar mama na mayarwa iyan da zuwanta
din.
Kwance yake yana barci a dakin matarshi ta biyu yaji sallaman uwargidanshi a
kofan dakin ya mike zaune yana fadin shigo mana fati ta karasa shigowa daga ciki
tana gaisheshi cikin hade rai wanan dabi,antane matukar ba dakinta yake ba yana
wani dakin har in ta fahinci ya kwana da mace zata wuni tana hade mashi fuska a
gidan .
Bashi ba har yara a wunin ba zasu gane kanta ba lokacin gata haihuwansu takwas
amma yana bala,in shakkunta ta riga data shige mai gaba sai abinda tace za ayi a
gidanshi.
Hakan yasa sauran matan da suka san irin rayuwan kishinsu sukaci maganin zama da
ita suke binta sauda kafa don a zauna lafiya.
Amma ita saratu taki hakan ta dubeshi tana fadin ina ganin fa amaryanka kamar
bata kwana gidan nan ba jiya ?
Da sauri ya dubeta yace bata kwana ba sai wanan matar da yake dakinta tace ta
kwana mana don ko dazun da zan shiga bandaki na ganta har mun gaisa.
To zan mata karya kika nufi ko mai dakinta dai a rufe take inko ta kwana ina take
yanzu shiru matar tayi kada a dora mata laifin daba nata ba a kai.
Ya mike tsaye yana fasin ina zata amma koni naga haske a dakinta da zanje sallah
maganan jamilata sai dai inda sahena tabbar gidan ya mike zai fita ta hararoshi
tana fadin in kuma zaka ?
Ya koma ya zauna da sauri yana fadin wai da in dubuta ko tana gidan su ladi don
can naga ta lakanci shiga kwanan ga ?
Na tura ance batazo ba yasa nacema bata nan ta juya ta fita sai lokacin ya samu
ya mike tsaye yana zura riganshi dake rataye.
Dama naji tana waya tana fadin ita gida zata bata iyawa sai ya hauta da fada da
kinkaji shina baki fadamin ba ai dauri ki hwada min in sani.
Ya fita yaga dakin kargame da kwado ya nufi wajen gidab nasu ya tsaya idon matan
dake zaune waje suna aiyukansu duk a kanshi bai damu da hakan ba wuce wajen gidan
yana dube dube.
Allah ya gani yana son saratu amma ba yadda ya iya da fati matarshi ta farko don
macece ita mai tsananin kishi da dokoki matukar bata amince da mace ba, bata taba
zama gidan.
Don ta shiga gallaza maki ke nan sai kinbar gidan don kanki kuma iyayyen miji
suna matukar son ta don ta iya kissan sace zuciya.
Ajiyan zuciya ya sauke ya dawo cikin gidan hankalinsa tashe yana bada baya yaji
matan sun kwashe da dariyan shakiyanci gareshi baidai juyo ba ya shige dakin daya
fito.
Wayanshi ya dauka ya kira layinta ana cewa layin a kashe yake haka ya wuni kira
ko wani lokaci amsa dayane shine kashe layin nata yake.
Ya kira layin yaya J shima ance mai baya samu nan hankalinshi ya kara tashi kada
yar mutane ta bata a hannushi ya daiji idan ta isa gida hankalinshi ya kwanta.
Bashi ya samu wayan nata yashiga ba sai wajajen goma na dare kuma taki dagawa ya
tura mata text tana ina ta bashi amsa da gidansu zaria sai lokaci hankalishi ya
dan kwanta.
Ina kwance a falo muna hira da mama Aminu ya shigo cin abincin dare don duk
fitanshi bai wuce karfe takwas a waje ya dawo gida.
Shikewa mama hira da cewa ashe mummy saratu tazo ne dazun na ganta da naje gidan
su kauwa anty salima sako wai yau din nan tazo .
Na dago kai nace Saratu fa kace tazo yace wallahi na ganta har mun gaisa ita
kuma matan uncle ance jiya tabar gidan bayan taciwa mama da uncle mutunci ba irin
zsgin da batayi masu ba.
Kai Aminu mamafa taciwa mutunci kace to ba zata iya bane don ance taciwa dubu
mutunci aiba abin mamaki bane tunda bata samu yadda tayi tsamani ba yanzu.
Dama shirin aiba na Allah da Annabi bane akeyi na munafuncine dama yanzu kuma
Allah ya nuna masu abinsu sai haka zai biyo baya rabu da abinda ba a farashi da
gaskiya ba dama a haka ake karewa.
Mama dubuce ke dogon sharfin da yasa duk muka tsaya muna saurarenta shi Aminu ya
dora da fadin wai har cewa tayi mama ta tanka a dakin nan tashigo ta murjeta.
Kai fa yace iya ke ban labari kinsan iya ta tsani wanan matar donshi tace azo a
sakawa kofansu makulli kada ta dawo tace zata zauna nan yake bamu labarin taje
gidan da suka koma maigadi ya hanata shiga don an fada mashi ya kulle gida yace ba
zata shiga ba tayi cin mutunci ta dawo gida kuma ta dora wani don mama tace tayi
hakkuri ta hau zagin nama din har kowa bata ragawa jiyan ba.
Shine yau tunda safe ta tafi tana fadin ga gidan nan tabar masu abinda mama da
danta sukai mata sai sungani a rabon su kuma wallahi sai ta hanasu zaman lafiya a
rayuwansu.
Bata isa ba maman tudu ta fada tace yarinyar nan bata da mutunci ko kadan
aniyartane ya koma masu daga ita har dubu din data marawa karya baya.
Dama ta dawo gidan nan da niyar fitar da Rahama dakinta sai Allah ya nuna masu
yana bayanta duk abinda sukeyi bai taba samunta ba kuma baisa ta saduda ba ga hakan
rabu da wanda Allah ya tsarkake zuciyarsa kaji.
Wai koda ake cewa na fadawa yarinyar nan ta tashi tsaye tayi hankali da ita sam
ban taba fada mata ba balle hankalinta ya tashi hakan yasa nayi murmushi ina fadin.
Mama nifa bafilatan asalice bani sheri ga kowa in kaimin ya bika haka nima idan
nayi ba zai barni ba donshine mu fulani bamu damu da yiwa mutum mugunta ba muke
kuma cikin daji zaune da dabbobi lafiya.
Kai Anty kikace fulani basu mugunta karshe ke nan Aminu ya fada yana dariya
Aminu bamu mugunta saidai ramuwan gaiya a cikin fushi.
Bafulatani duk ka cuceshi da safe shi kuma zuwa yamma sai ya dauki fansa ko
shekara nawa akayi sai mun rama abu ga mutum don bamu mantuwa.
Saida ya tashi mama ke fadin akwai dai ba banza yarinyar nan saratu tazo gida
ba dole akwai dai don in zatazo ai tare da mijinta ko wani nasa ya kamata ace tazo
zuwan farko.
Amma haka kimkam ace Saratu tazo dole akwai dai ba bamza ba gaskiya koma meye ai
zamuji bari dai mijinku ya dawo zamuji ko meye don duba ba zata fada ba yanzu.
Allah ya sauwaka nace na dora da fadin ni nazata tazo ganin gidane tace wani
ganin gida har yaushe tabar garin nan da za ace tazo boyewa sukeyi amma auren ba
dadi tunda aka kaita.
Can dana je gida nake ji wai ashe yazid yasa an kulle kawunsu gidan yari ko
kudinsa ko fursuna yanzu jafaru ake jira ya dawo aji.
Kuma ance shi yazid din ya koma abuja abinshi ya zauna bayan yasa an kulleshi
amma ai kinga dubu bata fada muna ba sam bata son asan komai kan diyanta.
Shi kuma mijin ku bayayi saida yan uwansa yanzu shi yayanku shike kokarin a sako
kawunku din amma suki sunce sai wanda ya kawoshi kara yazo nasan kudi ya basu don
suyi mai haka din.
Yayan ku yace Yazid ya fada mai kudinsa yaci yaki fitowa dashi idan yaji matsi
zai fito mashi da abinsa so yake a bada hakkuri a manta zancen ya cinye kudin daga
baya shiko bai yarda da hakan sai ya bashi kudinsa koda zai sayar da gidansune.
Kaj amma yazid bai kyauta ba kawu zaisa a kulle ai yaci ragowa a wajensu ko don
mahaifiyarsu dan uwan haihuwantane fa ?
Baki san yazid ba ko yazid baida kunya haka ya tashi da rashin mutunci tun yana
karami zuwa karatun nan da Alh ya turashi waje shinema saukinsa yanzu .
Nashiga daki ina mamakin wanan rayuwam na mutanen gidan mu na yau daban na gobe
daban kullum a cikin rikici suke zancen kudin nasan dashi na dau boyewa mamane
kamar ban sani ba ashe abin har yakaisu ga haka.
Ni yanzu a kwanakin nan ba abinda nakeyi sai tuno da yan uwana da muka bari a
rugga cikin wahala musane ya taba zuwa maria ta haushi da fada lokacin don me yazo
ace mun taru mun cika masu gida .
Haka tashi gaba muna kuka ta sallameshi washegari ya koma gida tun lokacin bai
kara dawowa zaria ba banjin koda mama tayi aure kaduna sunzo kin san mu fulani da
rikon tsiya a zuciyar mu.
Saida naba matan hardo sako da sukazo sunan Amir akai masu tare da wasika a ciki
nace su kirani har zuwa lokacin banji kiransu ba ni duk yadda yaya jafar yake da
yan uwansa ina son yadda suke rayuwansu a waje daya din nan amma mu tamu kaddarance
mu taso ba tare da yan uwan mu ba.
Dan uwa fa rufin asirine yau da dayansu zaizo ba zan taba korashi ba zan rike
abinane duk abinda mama zatace saidai tayi matukar ba mai gidanne ya koreshi ba.
Amma ita tsoro da zurfin ciki yasa tayi masu abinda ba zasu taba mantawa da ita
ba a lokacin saida mukai karamin gaba da ita na gaji na sake zancen yanzu ko ina
son ganin su sosai a raina.
Ina dadin muna cikin daula su suna cikin wahala ba tare da mun taimakawa
rayuwansu ba sun fito fili tunda tare mahaifin mu ya barmu dasu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/13, 09:24] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

9️⃣9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Dare daya Allah ke nashi ikon idan ya tashi ba wani mahalukin daya isa ya hana
wanan faruwa a duniya saishi daya bayar ya isa ya karbe abinsa duk lokacin dayaga
daman hakan ga bawa kamar yadda ya bayar din.
Wanan tafiyan da yaya yayi sati biyu kacal ta daukeshi ya dawo a cikin tarin
dukiya mai dinbin yawa tare da abin arziki ga yan uwa da masoya don tafiyace data
zamo wace ba za a manta a cikin tarihi ba.
Wani lokaci Allah kan jerabi bawansa ya dora mai jerabawa a rayuwansa wace zata
zamo mai alheri a gaba matukar bawan nan ya iya juriya ga hakan ya samu ikon cun
jerabawansa da hannu biyu a karshe sai Allah ya juya hakan ya zama mai alheri a
rayuwansa.
Don kuwa zance da ciwon yaya da shiga fatarsa da ganin wasu halaiyan da bai zata
ba ga yan uwa duk hakan jerabawane daga ubangijinsa Allah.
Don sanadiyan wanan ciwon da yaya J ya kwanta abubuwa da dama Allah ya jerabeshi
dashi yaga duniya sanadin hakan dukiya ya salwanta lafiya ta kubce masa yan uwa sun
gujeshi don baida iyali sun nuna nasu halin a gareshi abokai ba kowa ke saurarenshi
ba duk da halarcinsa garesu a baya.
Sai gashi Allah ya dawo mai da dukiyansa inda ubangiji yayi ikonsa kayan sun
ninka kudinsu sama da lissafin mai lissafi abin baiko faduwa.
Wani saurayin Maibe dake can ya adana kayan a wajensa kamar yadda ta bukata
yayi daga baya da suka samu labarin jin saukinsa aka baiyana mashi inda kayan suke
yabi kuma suka shiga a cikin lokaci aka samu alherin daba,a taba tsamanin hakan ba
gareshi.
Ruwa aketa shega muna a garin hakan yasa bamu tsaya wani dogon hira ba duk da ba
matsalan mu da ruwan muna cikin rufin asirin Allah mu bamu ganinsa balle ya tabemu.
Amma yanayi yasa mun kwanta da wuri a ranan nagama shirya Amir nima na kimtsa
kaina zan kwanta naga wayana yana haske na dauka.
Yaya nagani yana kirana lokacin na dauka yaron kuma yana min kukan nono na fara
daukan wayan nakara a kunnena kafin nakai hannu na dauki yaron ina mashi sallama
naji yana fadin kun rufe gidane nace ehh yaya ki bude min gani nan zuwa ya fada.
Na amsa da to cikin mamakin yadda ya iya tafiya a cikin wanan ruwa ga dare haka
duk da shadaya ake nema a lokacin amma gari yayi tsit a lokacin.
Na saba yaron a kafada na fita zuwa falo na bude kofan a daidai lokacin maigadin
mu ya bude get din gidan motoci ukku suka shigo a jere lokaci guda haraban gidan.
Dawowa nayi na zauna don Amir daketa tsala min ihu hakan kuma ba halisa bane
shi yarone mai hakkuri yana da wuya kiji kukansa sai can ba a rasa ba amma akwai
zuciya gareshi mama kance ya gado na fulanin a gareni watau zuciya.
Haka ya shigo ya sameni zaune na fara ba yaron nono yana tambaya ina key din
dakunan boys quaters suke na mike na dauko mashi ya fita na zauna nacigaba dabawa
Amir nono a falon.
Ya dan jima ina falon zaune ina tunane a cikin raina Aminu ya dinga shigo da
wasu manyan jakkuna shida mai gadin gidan kusan biyar kafin shiya shigo daga baya
don ruwan ya dan tsagaita a lokacin.
Tun kafin yakai zaune yake tambayana mama fa tayi barcine nace ta kwanta tun
dazun nima wanan ya hani barci yau da sauri yake tambayan meya sameshi kuma ?
Nace dashi yau dai kuka yakeyi tun yamma mama tace kila cikinsa ke ciwo anbashi
balma kuma bai bari ba.
Ya mika hannu ya karbi yaron nace abinci fa yace bar zancen abincin nan yanzu
bamu da yunwa hankalinshi na kan yaron yana dan dube dube a jikinsa yake ban amsa.
Yakai zaune yana fadin ko zamu kaishi asibitine a dubashi da sauri nace da daren
nan a dai bari da safe mugani yanzu ko mun fita a cikin ruwan nan wa zamu samu a
can ?
Baki da tausayi don ciwon ba a jikinki yake ba zakice har saida safe idan bai
bar kukan nan ba dole mukaishi asibiti nayi sa,a yarin yabar kukan shima ya mike
zuwa dakinshi yana gyara kayan da suka shigo dashi din ciki.
Yaron na goye a bayana na shiga na sameshi ina fadin yaya bafa gidan nan zaka
zo ba naga kazo muna a cikin daren nan baiyi magana ba saida ya gama dora kayan ya
juyo yace Allah


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login