Showing 183001 words to 186000 words out of 328222 words
Chapter 62 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
min jikina yau.
Ni dai yaya saida safe don Allah kada kasa mai girki tace ko a can kana tare
dani manne a waya ina fadan hakan naji yana fadin .
Baki yarda da abinda na fadaba ke nan kashe wayan nayi ina jan tsuki na wurgata
gefen filo waini yaya ya mayar karamar yarinya ya faki odon matansa yazo yana min
dadin baki .
Nasan zai kira yaji wayan a kashe kamar yadda na saba tofe dakina da addua haka
nayi don tunkan inshigo na rufe ko ina na gidan biba kuma zata kwana da iya don
tare suke kwana a dakin dama da ita.
Haka na kwana ina juyi washegari na tashi kamar kullum karfe bakwai duk nagama
komai har na shirya don tafiya karyawa ne ya rage muyi nida Biba .
Ina saka hijab naji muryanshi a falo nayi mamakin hakan sosai yadda ya baro can
gidan a wanan lokacin haka ?
Ya leko dakin yana waya na dake ina mashi ina kwana ya amsa ya kashe wayan yana
fadin meyasa kika kashe min waya jiya Rahama nazo kuma na samu kun rufe gida ?
Kazo fa yaya haba dai kadai fada ina zakazo karfe goma fa da yan mintuna lokacin
ai Oh kina zaton karyane banzo ba din to ki tambayi maigadi idan kin fita.
Banso ina waya da mutum ya kashe min waya hakan yana bata min rai sosai wallahi
ba wani gargada nace dashi iam sorry gani nayi zamu shiga hakkin wace ke tare dakai
lokacin.
Ni hakkina da sukeci fa ya fada yana nufoni sai muryan iya mukaji tana fasin
wai Jafarune da safe haka ince dai lafiya ka fito gida wanan lokacin kuma ?
Iya nine ya fada yana kutawa ya fita ina jinshi yana fadin nazo nakaisu
makarantane kada su makara don da motarsu na tafi can jiya din.
Allah sarki nikan nace to lafiya ka fito a yanzu da safe haka to ya kwanan
mutanen gidan ya amsa yana zama falon yace lafiya kowa yake sai yaron nan Abba dan
wajen Habu shine dai jikinshi ba dadi har yanzu wallahi.
Yo ina zaiyi lafiya dama yasha allurai da kwayoyi tun a cikin uwarshi dole sai
an zuba mashi ai yayi lafiya ai illan asibitin ke nan dama irin hakan baku ganewa
ne dai .
Banji dadin jin Abba ba lafiya ba don mijin yar uwata bai gari shi yanzu habu
sam baya zama gida ko kadan ko yaushe yana wajen aikinsa ni har takan ban tausayi
wani lokaci saidai ita sam bata damu da hakan ba.
Naji kamar in tokesa ya kaini idan mun fita saidai kuma zan iya makara idan
nace hakan muka karya a gurguje muka fito munawa iya sai mun dawo.
Tun a gabana yake fadin zan biya gida in dauko maki salima tazo ta tayaki zama
kada a barki ke kadai .
Amma sai naji iyan tace ka barta zanyi ibadana idan nagaji kuma sai in dan kwanta
kafin su dawo tunda ba har dare suke kaiwa ba a can.
Muna gaba zaune biba tana bayan mota zaune yaja motan muka fice a gidan saida
muka sauke biba yaja mota banyi aune ba naji hannusa cikin nawa yana tuki da hannu
daya kallonsa nayi na dan sauke murmushi naji yace dani.
I love you with all my heart yana lumshe idonshi naso ki rubuta exam ina garin
nan gashi zan koma next week don kayan mu ya kammalu.
Yanzu mutane su fara gane harkan donshine bamu tsayawa bata lokaci da zaran
kayan ya kammalu nake mikashi can wajen masaya.
Zan barki da iya don zamanta a nan tare daku hankalina yafi kwanciya da hakan
nasan babu wani wanda zaiyi ganganci zo maki gida da izgili tunda tana tare dake
yanzu duk da nasan mama ba zata yarda da hakan ba amma zan fara zama da iya din
inji ra,ayinta.
Nasan ba zataki ba ai saidai idan taki kada ka matsa har ayi tashin hankali Allah
yana tare damu ai ba abinda zai samemu in sha Allahu.
Tafiyan da yakeyi da motan a lokacin ba wani gudu yakeyi ba har muka kai muna
zance guda ya saukeni nayi mai godiya yaja mota ya tafi.
Kwananshi hudu can gidan tare da iyalinshi inda nayi kokarin danne zuciyana ban
yarda na nuna hakan ya dameni ba a fili amma kasan raina akwai kishin hakan sosai
da nake ji.
Don idan yazo yana dan kame kameshi sai na dinga jin haushin hakan bayan ya gama
masu abinda kilama yafi wanda yake min nan zai dawo yana nuna min irin damuwan da
yakeyi dani din.
Ranan da zai dawo gidana duk shawaran da anty salma taban shinayi na kuma ga
farin cikin hakan a tare dashi sosai don ga iya a falon amma duk inda nabi idonsa
yana kaina tunda yazo kuma bai fita zuwa can gidan ba kamar yadda yakan muna zai
dawo yakai goma ya koma gida sai kuma da safe idan ya dawo.
Niko nasan nayi shiri din don ni aka bari da tsamin jiki a karshe inda Allah ya
taimakeni ranan ba school donshi na dan kai wani lokaci kwance ban fito ba sai
takwas da rabi.
Inda nafito na samu Biba har ta dafa ruwan zafi tana fere dankali donshi a
rayuwanshi nafahinci yafi son dankali irish da safe wanan yasa nake kokarin soyawa
wajen karyawan mu.
Nakan sarrafa masashi nau,i nau,i wani lokaci haka kuma duk yadda na sarrafa din
zai zauna yacishi sosai da safen .
Faten dankalin da kayan cikin da nasa biba ta yanka kanana nayi muna inda na dan
sakewa dankali ruwa sai kuma muka hada ferfesu kai shanu da ya kwana saman wuta a
hade.
Sai ruwan shayi mai kauri da yaji kayan kamshi wanda mukeyi a gidan maman Abuja
mun kammala na jera a dinning din don ko iya ban dibar mata nata daban ba a ranan
saboda ina son mu zauna a karya gaba daya yau a gidan.
Wanka na shiga na tsala kwaliya a cikin atamfa da akai min dinkin buje da riga
kayan yayi matukar karban jikina sosai dan takalma flat na zaman gida na fito dashi
zuwa dakinsa.
Barcinsa na samu yanayi hankali kwance na kai zaune a gefenshi yadda zaiji
motsina a lokacin.
Hakanne ya faru don ko second banyi da zama ba naga ya dan bude idonsa dake cikin
nauyin barci yana kallona murmshi na sakar mashi ina fadin barcin ya isa haka yayan
mu ka tashi ka watsa ruwa iya tana jiran ka mu karya don tare zamu karya yau da
ita.
Ido naga ya lumshe yana jawoni zuwa jikinsa na dan fada ya sauke nufashi yana
fadin bason haka ba sai ince ki bari in biyaki kudin wanan kwaliyan naki don
Allah ?
Ba saika biya ba tunda ka yaba ka tashi dai a karya kada iya taga nawana wajen
bata abin karyawa yau ta dauka ban damu da ita bane.
Yau ba school ke nan nace ehh ina mikewa ban faye shiga ba irin yau don lecture
gudane gareni malamin ma kuma ance baya gari yayi tafiya.
Ok ya fada yana miko min hannayesa biyu da alaman wai in dagashi daga kwancen
banki ba na mika mashi hannayena din ya mike zaune bandaki ya shiga na mike na wce
wajen iya.
Tana zaune tana dan hira da biba nashigo ina gaida ita da kwana na samu biba
tayi wanka tana shafa mai nace kiyi ki shirya ga uncle nan zai fito muje falo mu
karya a can yau.
Bidiri yau da mai gidan za a karya ke nan nayi murmushi nace iya ai hakan
sunnane a musulunci zama tare da iyali a danji korafin kowa hakan yana kuma kawo
shakuwa a tsakani akace .
Don sammakon da mukeyine muna fita yasa ba a samun yin hakan wani lokaci don
yadda muke karyawa a gurguje kadin mu fita.
Dolene miji ya kulaka ai yar nan duk sauri da abinda ke gabanki baki gaza bashi
kulawanki haka nima nan da yar nan me zai hana mace ta sace zuciyat mijinta tana
hakan.
Abinda suka gaza ganewa ke nan ba asiri bane ke sa miji karkata sai tsaban
kulawan mace wata mace bata dogara ga asiri ko wani siri ba akan miji sai zalla
tsaban kyautatawa da take masa yake sa miji ya ahagala a kanta haka .
Dan zaman na fahinci komai game da zamantakewan ku gidan nan akwai banbanci sosai
a gidan nan da can gidanmu .
Wa zai zauna ya baka kulawansa irin hakan da kikeyi mace tasan muhinmancin da
darajan namiji haka ace miji ba zai bata kulawansa ba wanan ai karyane.
Barsu can su zauna suna kishin hauka da bai fishesu ga abinda ya dace suyi amma
haka zasu barshi har sha daya wani lokacin wai ba a gama abin karyawa ba.
Toke iya waya tambayeki muryan Biba ya katse mata maganan ta mika mata dakuwa da
hannu daga inda take zaune tana fadin ungo naki nan yan nema idan zaki mai da
hankali ki koya a wajen yarinyar nan gara ki koya ki tashi da wanan halin duk da
naga kina da kwazon kima kinayin komai yadda ya dace.
Ni dai ina gefe zaune bakin gado ina murmushi nace iya kinsan taji kina zancen
iyayyenta shine ranta ya baci.
Kai anty ni da nake shan harara wajen mummy ko ranan sunna gani zaune tana raba
abu data kawo kaina ta tsalakeni taba ta kusa dani ko ruwa saida dare mummy salima
data ban abinci nasha ruwa a gidan nan ranan.
Kinji ko ai kinji tsiyar basu da hankali ke meye naki a ciki ina mijinsu ya
kawoki nan zama ko wajensu kuma yana iya kaiki ai inga halin arziki ai.
Sun kasa gane hakan da sukeyi suna bata kansune a wajen yan uwa duk da yan uwan
suka nuna masu sunfisu daraja bakomai bane kuma hakan sai kwadayin duniya.
Ai kinga uwarki da yar uwarta da suka kama kansu inba wani dalili mai karfi ba
basu zuwa gidan balle su shiga shirginsu din bakiga suna mutuntasu ba dole tundai
Rukkaiya da bata daukan raini.
Shigowansa ya katse masu zancen yashigo yana fadin iya kedawa ke fada haka tunda
safe tun ina falo nake jin muryan ki ?
Nida sarakunan kishin nan mana matanka su nake zankada tunda safe matarka tace
damu yau tare zamu karya dakai shine abin yaban sha,awa nake fada dasu.
Murmushi yayi yana kallona yace haka tace ta hanani barci wai in taso kada mu
barki da yunwa kiga laifinta ?
Ina laifi yar nan kin maisheni kamar basaraka ko sarakuwar uwarku ban samu rabin
gatan nan a wajenta ba gashi na samu ga jikokina.
Iya ai dole muyi maki kece fa gatan mu ga baki daya in ba ai maki abinda zakiji
dadi ba aiwa,washi iya na fada na mike ina jin tana fadin cikin raha ashe gaskiyane
akwai mata masu tsoron kishiya gashi ko nagani a yau.
Falon muka fito gaba dayan mu nan aka zauna saman babban shimfidan da nayi
maimakon danning din saboda tsohuwar na fara zuba abincin sai kamshi ke tashi .
Yayin da iya ke faman zuba cikin washe baki da jin dadi muna tsaka da cin abincin
sai sallaman mama mukaji da kawu sun shigo.
Kawu yana fadin a,a lalai iya kan ba zata koma gida ba ana haka duk wanan
didiman haka iya ?
Kayi bakin ciki da hakan ne tunda ka kasa danka ya dauka yanayi ko iyan ta fada
na yunkura na mike ina mai barin abincin tare dayi masu sannu da zuwa.
Na gaidasu suka amsa kawu yana fadin nina isa in bakin ciki iya tunda jafaru ya
kama muna ni dama nace da wuya iya kiyi zancen gida a yanzu tunda mukajiki shiru
haka ashe dadi jafaru ke narka maki a nan haka ?
Ta sake fadan kayi bakin ciki ke nan nace aka kwashe da dariya mama idonta yana
kan plate din abincin kowa take fadin.
Ai dole ta koma gida tunda a can take gamu sai zaraya ta barmu munayi zuwa nan
dubanta sai iyan tace na hutar daku ku zauna gidan ku nan kan banda ranam bari inma
daukana kukazo yi to ba zani ba.
Kitchen na nufa na barsu suna drama da tsohuwar tasu har na dawo na aje plate
din a gabansu ina kokarin zuba masu abincinne mamatace nikan a koshe nake ban fito
da yunwa ba.
Ai badon yunwa zata zuba maki ba dubu tunda tasan mijinta bai kaza dake ba
kamar yadda ya bayar nan ya baku a can ai.
Amma karrama bako yana cikin koyi da sunnan ma,aikin Allah ai ko kin isa kija da
hakan kuma yanzu baki zuwa gidan nan kice wai a koshe kike baki fito gidanki da
yunwa ba ke ?
Iya idan ban koshi ba ai zanci koda yaya yazo daukata ya samu ina cin abinci
gashi nan ki tambayeshi ?
Amma ba irin wanan bako nidai na zuba nakai plate din a gabansu ina daukan nawa
na mike inacewa biba ta taso muje daki muci.
Shidai yana zaune yana jinsu sai abincinshi yakeci kawu ya fara jawo nasa plate
din ya kawo gabanshi ya soma ci ya fara fadin dubu kici abincin nan kada mu kwareki
don Allah.
Ina iya zata yarda ta koma can tana hada wanan a rana haka kafin yakai karshe
tsohuwar tace ance kaci mai dadi idan ka samu daman hakan.
Can babu mai dadin ne iya wanan ai sai a dauka can bamu da irin cimar nan a can
din sai dai ace kawai gyaran ba daya bane kawai.
Ina gyara zaizo daya dubu tunda ilimin abin ba daya ba kefa dubu duk abinda zaki
fada iya ba jinki zatayi ba a yanzu don haka kiyi shiru kawai da zancen nan .
Iya munzo akan maganan yaron nan Yazid ne da Jafar ya sanar damu dawowanshi wai
kuma har da iyalinsa yanzu iya ga Jafar fisabilillah abinda yaron nan ya aikata
muna yayi daidai ke nan ?
Ace wai yazid daga zuwa karatu yaje kasan mutane yayi aure a can bada sanin kowa
ba a cikin mu ina shi ina zuwa auren wani kasa iya don Allah ?
Zakija da ikon Allah ke nan ko duk abinda bawa yayi mukkadarine garesa dama
dalilin hakan yaje kasan da sunan karatu don ya hadu da matar nasa hausawa sunce
matar mutum kabarinsa ai .
Koda rarafe sai yaje tunda Allah yayi a can matar nasa take kuma dan uwansa ya
fada maki dalilin hakan to meye na damuwan zuciyarki ke a yanzu ?
Iya ba hakana bane naga kayi aure a gida ka auri matar da akasan dabi,u sunzo
daidai yaya aka kare balle ka dauko a wani kasa kazo da ita nan ?
Idan yazo kuma yace saman kanki ko a karkashin wani zai zauna da iyalin nashine
wai meyasa kukewa aure shigan kutsu dubu aurensane bancin ranki a yanzu ko
dawowansa kusa daku ?
Iya abinda nake son ki fahinci dubu a nan shine da yaron nan ya dawo gida yayi
aurensa a cikin gata kamar yadda kowa keyi zaifi mutunci kinsan halin mutanen yanzu
da maganan da bai shafesu ba iya.
Sai abarsu suyi tayi yanzu ai tunda aikin gama ya gama ko aure harda haihuwa
biyu yanzu meya rage don Allah ?
Ni kawu banga abin tayar da hankali ba a nan tunda shi zai zauna da matarshi na
fadawa mama addua kawai zata bisu dashi yanzu don Allah.
Yaron nan da karatunsa inma yace bai sana,an nan sai aikin gwaunatine yana dai da
ilimin sa ko da zai iya rike iyalinsa tunda acan aiba mu ke rike mashi dasu ba.
Yarinyace karama kwarai matar nasa yar wani malaminsune yaga kirkinsa ya aura
mashi yarsa ba ba tare daya san kowa nasaba fa mama .
Yanzu kuma munan sai muce hakan bai muna ba mu nuna bamu ksunat yarsa mu don
kawai bata fito cikin nahiyar mu ba amma dai ai musulmace ko ?
Nasan dama bakin ku daya dashi tunda kai ya iya fadawa zancen ai dole ka fito da
wanan zancen yanzu baka son a fada tunda kuma kun auro matanda suke son sunfi
karfin mu.
Zancen duk a kunnena yake muke nan mama ke nufin muna son fin karfinsu da mukai
mata me na rashin mutunci don kawai mun fito yayan fulani ba zage zagi ba kome ?
Saidai kafin nakai karshen maganan zucina naji iya na fadin shi auren kabila ai
ba bakon abu bane don kowa yayi a cikin mu dagani har ke kuwa dubu ?
Mahaifinki ai asalinsa banufene suka dawo nan da zama aka saje kuma na aurensa
tun asalin yarensu bai bace ba haka kema kuma kika auri mahaifin yaran nan kowa
garin nan yasan zuwa Alh yayi garin nan nema daga Adamawa koba haka bane meye
bambancin zance a nan ?
Sai mama din tasa kuka don me iyan ta fadi hakan Biba najin kukan mama ta mike
tsaye kamar zata fita a dakin na zabga mata harara ina fadin karki soma haka ace
dake munafuka.
Yaya irin abinda nake gudu ke nan tunda Habu yazo da zancen aurensa naso hanawa
amma ka daure masa gindi akan babu komai gashi.
Jin dadin auren har kanwarta ta cinnawa shi Jafar a yanzu gaba daya kowa yasan
yaran ran sun juye min kan yara don ba haka na tarbiyarta da yarana ba duk kun sani
a nan ?
Dubu ki shiga hankalinki wallahi kafin na saba maki a wajen nan meye hadin auren
Yazidu dana jafaru kona habu yanzu ?
Kin fa kusa kai yaran nan makura akan zancen nan idan yaran ku sun sauya ku
kuka sauyasu