Showing 324001 words to 327000 words out of 328222 words

Chapter 109 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

aka dorawa ciwon bashi ba.
Akwai soyayyan dayafi wanan har dan uwanka zai sadaukar da ransa akanka ka kasa
mashi komai matar nan tana iya kokarinta damu tun muna kanana yanzu haka yadda
yaran mu suka saba da maman tudu mama basu saba dake ba hakana don hattaransu da
kikeyi akan uwayensu mama kikan manta da yayan mu jininkine su ?.
Shi kuma kawun da kike magana a kai kowan mu nan yasan irin ta,asan da kawu
yaiwa rayuwanki ya haniki zaman lafiya damu yayan ki haka kuma bai son ganin
cigaban mu wanan a baiyane yake kowa ya san hakan mama don haka kada ki matsa muna
kan kawu don Allah kawu dan uwankine ba dan uwanmu ba .
Kai habu ka shiga hankalinka kafin na fyatoka daga hancina ba yau ba na kula
dakai da tsatsauran ra,ayinka akan yaya idan kai ba zaka taimaka mashi ba ka bari
wanda yayi niyar hakan yayi.
Tunda shi Yazid yace ba zai taba yafe kudinsa dake hannun yaya ba ga kuma Saratu
yanzu ta taso da zance kudinta take so ta koma gidan mijinta tunda kunki taimaka
mata ku .
Yaya J yana zaune yanata charting bai dago kai ya dubesu ba amma hankalinsa na
kan abinda kowa ke fadi wurin a lokacin saida yaji yazid yace mama kudin nan
kudinane fa ?
Ubana ya mutu yabar min gadon su kuma banyi da kowa nace abashi kudina ba wanda
yai fushi da matakin dana dauka ya biya mashi man in rabu dashi matukar bai biyani
ba wallahi sai yayi fursuna akan kudin nan haka kawai zaiyi na iya kyaleshi koshi
sai ya biyani a lahira don ban yafe mashi ba.
Nasan zaka aika donshi nake son dan uwaka ya biya kudin tunda na fahince kai
abin kunya baya gabanka yazid nemansa ma kakeyi ka yafa.
Aban kudina in rika mama yadda kowa ya rike nasa nima in rike abina nagaidai
babu ruwanki cikin zancen idan kuma za a biya mashine a ban kudin yanzu.
Shirun da yaji anyi a falon yasa ya dago kai kallonshi sukeyi a lokacin yasa
yace wa wai dani ake maganane banji ba ?
Ka daiji abinda yake fada game da kawunku idan ya matsa zankai ga mashi baki
yasa nake kyale yazid da iya shegenshi.
Baki kuma mama akan kawu zakiyi mai baki har idan kinyi muna hakan ai kamar kin
cutar da rayuwankine mama ka bashi kudinsa tunda tozarci yake neman muna.
Ni mama a,a ba wanan akawarin a waje ko kin manta daga ina kudin suka fito suka
koma hannun kawu da har yanzu kudin suna hannuna da sunfi abinda ake nema yanzu a
kawu.
Kawu da munafuka din nan saratu nan suka tasaki gaba da sunan cewa kudin nake
wandaka dasu har naje na auro Rahama.
Ni auren Rahama gareni alherine ba tsiya ba tunda ina ganin haske ga taraiyana
da ita akan me zan dauki kudina ince na biyawa kawu kudin yazid .
Ai gara in nayi niyar taimakawa yazid din insan kyauta na bashi kudin da biyan
bashi ba mutumin da bai kaunar ya ganni da rai zan biyawa bashi mama ba wanan
zancen kuma tsakanina dashi gaskiya inda yakai mashi kudinsa ya fito dasu don sunan
a boye tunda ba abinda yayi dasu.
Barakha dai tunda ta rokeni gafara ta kuma fada min dalilinta na goyon bayan
haka ita kan bance ban taimaka mata ba yanzu.
Auren Rahama bani kadai ba duk wani wanda yake tare dani ya karu dashi amma aka
rufe ido akaso tozartani cikin duniya saida Allah ya rufa min asiri ban taba taba
wanan kudin ba da sunan wani abu a rayuwana don nasan irin azabab da Allah ya
tanadar akansu.
Ya basu kudinsu ko kuma yaje gidan yari akansu ni wanan ba zancena bane gaskiya
don ban cikin maganan tun farko an tsameni a zancen yanzu ko idan nasa kaina ninaso
hakan .
Duk abin da kowa yayi min ina sane ina dai hakkurine a zauna lafiya amma kada
mutum ya daukan ban fahinceshi ba kai Habu kwanan nan bada jimawan nan ba na kiraka
akan ka taimaka min da kudi muna asibiti da Rahama za ayi mata aiki kememe kaki
kulani balle ka taimaka min.
Shiko yazid dana kirashi cewa dani yayi shi ina yaga kudi zai dai turo min dan
abinda yake dashi ya turo min da dubu hamsin sai bare wanda ban hada komai dashi ba
ya iya ban dubu dari hudu lokaci guda ga barakha da bata aikin komai sai sana,an
hannu ta iya turo min da dubu dari.
Kai ammako anji kunya haka akayi baka fada ba iya kona fada maganin me fadin
zai min a lokacin tunda badashi banda wanda zai ban .
A tunane shi dan uwa Allah kan baka sune don rufin asirin juna sai yanzu na
fahinci abin a yanzu ba haka yake ba don kowa kanshi ya sani a yanzu.
Wanan zance kamar almara fa Jafaru daga habu har shi yazid da bazarwa suke rawa
a yanzu bada taka ba da har zaka shiga hali haka su kasa taimaka maka ?
Gasu ai shiyasa na fada a gabansu yanzu ba kawune kadai yayi min abinda ba zan
manta ba har dasu da nake gani rabin rayuwatace su don na shiga jerabawa suka iya
min hakan.
Dubu kingani ko kinga irin abinda nake fada maki ko kinga abinda matsalolinki
suka jawowa rayuwan ki tun kina raye kin daiji irin abin ko ?
Na fada maki irin halaiyan nan na banza bi mutum suke su nadeshi su shafi har
wanda baiji bai gani ba yau ina laifin yaron nan a wajen ku ?
Kai Habu ya dago da idonsa da sukai ja yace ni nasan anyi hakan amma ban dauka
cewa abin serious bane sosai a lokacin yasa ban turo kudin ba amma yayi hakkuri don
Allah ?
Ba dole ba dole yayi hakkuri idan baiyi hakkuri ba kasheku zaiyi tunda hamnuka
bai rubewa ka yarda.
Wai iya baki bari ayi magana kin hana sai kace kece mama dakuwa tayiwa salima
din tana fadin daga uwar naku harku waye silan zuwanku duniyan nan.
Iya munzo akan zancen auren salima ina son kafin tafiyan ku insha Allahu za ai
aurensu jin hakan yasa mama dagowa da sauri tana fadin sati biyu kamar hauka ?
Aure haka ba shiri komai a dai bari har Allah ya dawo damu lafiya zaifi yace
wani shiri mama ki dai sakawa yarki albarka amma duk wani shiri ai an gama komai
ina ganin yanzu abinda ya saura sai wanan cincin din da kukeyi din nan ai koshi na
gama da wanan bangaren ko insha Allahu komai na saya.
Shine zuwa kanon da mukayi kwanaki dasu zaman su gida haka yana damuna saida ta
nisa tace angama komai kace fa a bangaren ka ko shi ya gama ginansane ?
Ya gama ina ganin yaushe sukace zasu kawo kayan akwatunama yana tambayan kanwar
tashi tace yace a cikin satin nan dai zasu kawo.
Allah dai ya saka maka da alherinsa yasa kafi hakan a rayuwanka jafar kayi yadda
duk akeso ayi Allah ya baka zuria masu rama maka ya amsa da amin .
Itama mama ta amsa tare da fadin har ita Nafisan ke nan yace insha Allahu wanan
dan uwan mahaufiyarta dayaje karatu waje ya dawo dashi za ayi a nan kaduna zai
ajeta.
Wani nisawa mama tayi ta shiga dogon tunane can ta dago tana fadin amma wanan
duk tsarinkane ko tunda ka gaji da ganinsu gida ?
In ma tsarinsane aina alherine tunda aure ya hada Allah kadai yasan ladan da
zai samu a wanan abinda kayi Jafaru Allah ya biyaka da alherinsa kaji.
Mikewa J yayi yana fadin to mama mu zamu tafi wa yan nan dana lissafa maku sune
zaku tafi tare bana saudiya insha Allahu badi kuma idan ranmu yakai sai a duba wa
yanda ya dace suje.
Mama bata iya magana a lokacin don yadda zuciyarta yayi mata nauyi da zantukan
da sukayi dasu na kawu yafi tsaya mata a rai yadda har suka tashi yaran gaba daya
suka tsani dan uwanta a yanzu.
Yadda yace hakan ya faru ansha buki ankai amare komai nasu iri daya saidai kala
daya bambamta da kuma abinda kowa ya sayawa kanshi anyi lafiya an kare lafiya amare
sun tare dakinsu abin gwanin ban sha,awa dasu.
Saratu kuma tasha zunde hakan yasata zama daki don ta zama mujiya a cikin mutane
yawan zunde yasata boyewa don wanda ma bai sani ba sanadin bukin nan yasan abinda
ya dawo da ita gida.
Bayan an gamane dama mama tun kafin bukin ta koma gida don tafiyansu daya gabato
munji kewanta sosai a lokacin.
Ina kitchen girkin rana nakeyi dan aiki nawa yakaini rana naji wayata tana ta
ringing bibace ta dauko wayan ta kawo min na fito ina amsawa don ganin wace ke
kirana din a lokacin.
Yandace na daga da sallama ina gasheta ta amsa a gurguje take fada min wai nasan
me su yan uwan mu suna cikin garin nan kwana biyu ke nan suna neman gidan basu gane
ba ?
Suna ina nace mata cikin zakuwa tace gasu suna cin abinci nace dasu in sunga
nikan zan basu kudin mota su koma ko suje wajen mama aji yadda za ayi amma ban
yarda yaya habu yazo ya samesu a nan ko mama taji ta soma fadan nan nata.
A cikin wani murya mai kama da tsawa nace da ita kada ki soma turo min su nan
gidana koda yake bari Aminu yazo ya dauki min su.
A,a Rahama kinsan halin mutanen gidan nan yanzu da angansu kuma sai ace munji
dadin waje muna kwaso yan uwan mu yaya muka kare dasu balle kuma mun dauko wasu ?
Maria su kore mu udan sunce basu zama da yan uwan mu saidai mijinki ba amma ni na
jima da aje magana a kansu da yaya Jafar.
Allah ya yanke muna wahala ya turo muna su nan likacin daya kamata su din a,a
Rahama ki bari na basu kudi su koma gida din Allah ?
Gida wajen wa suje suyi ta aikin bauta mu muna nan cikin daula suna can suna
bautawa kawu ga Aminu nan zuwa yazo min dasu na fada ina katse wayan.
Sam banji dadin wanan zance nata ba ba a dauki lokaci ba Aminu ya dawo min dasu
zabar tausayi saida nasha kuka dana gansu lokacin.
Aminune ya duko gefena yana fadin anty bari na kaisu dakina suyi wanka in basu
kaya su muje suyi aski sai mu dawo ina jan majina a hancina saboda kukan da nayi
nace dashi bari na dauki maku kudi kaje dasu ka sayo masu kaya yace to anty don dai
kince da kayane dan aski kawai ai ban rasa kudin da zasuyi aski a wajena.
A,a tsaya in dauko kudi ku dan sayo kaya su samu na canzawa nashiga na dauko
kudin na mika mai suka fita kuka nacigaba dayi ina waya da mama da hankalinta ya
tashi.
Take fada min mijinta bai yadda da yaya mazan ba ya daifi yadda damu matan ita
bata san abinda yasa baison ayi zancen su ba ?
Ni da kaina na kira yaya ina kuka na labarta mashi zuwansu din da yadda abin ya
faru cikin karaji naji tace yanzu suna ina ?
Aminu ya kaisu suyi aski ya dan sayo masu kayan sauyawa yace barin nemi Aminu
din ajiyan zuciya na sauke dama nasan yaya ba zai taba kinsu ba.
Don sauda yawa yana min hiransu lokaci lokaci yakance dani yakamata a dubu su ko
ya kira hardo ya tura masu sako duk da nasan hardo zai basu amma baffa amshewa
zaiyi.
Tare suka dawo gidan dashi sayayya sosai yayi masu suka shigo yanawa musa sheri
da ke ashe kanin naki aure yayiwa gudu yazo nan saida yaga za ayi mashi auren
dolene ya tuna damu.
Harshe na juya ina tambayanshi yake fada min yadda akayi raina ya baci sosai da
kawu abinci na mike na kawo masu sukaci suka dasa wani hiran dashi.
Dakunan daba kowa a ciki na boys quarters yasa Aminu ya bude ya saukesu a ciki
da yake ba nan gidan mu yake ba saida zai tafine yakecewa dani ina ganin fa nan za
a kawo yaran nan idan uwarsu zata saudiya.
Su basma yace eeh don ban yarda da cewa da tayi wai akaisu gidansu ba Allah ya
kaimu nace ban yarda na nuna komai ba ga hakan.
Amma nasan akwai ta don yadda yaran suke basu jin magana kuma ba a tsawata masu
amma ba komai zanyi iya kokarina dasu insha Allahu.
Aikuwa hakan ya tabbata don kuwa tun ana saura kwana ukku su bar kasan sai
gashi da yaran yazo min ban ko san da zuwansu ba ya kwasosu zuwa gidana ba yadda
zanyi dole na rugumesu .
Irin wasan da sukeyi ya fara daga min hankali wasane na alaman ba kwabo din nan
ga yaro nan muka fara kwasa dasu nayi masu serious warning akan hakan.
Ban yarda na sake masu ba sam da safe kuma zan tayar dasu suyi sallah akan
lokaci idan angama kuma nasa suyi brush biba tayi masu wankan safe.
Gaida mutane akan Aminu na fara koya masu hakan ya shigo suka bishi da kallo na
daka masu tsawa su gaidashi daga zaune inda suke sukace ina kwana nace ba zaku
tashi ku gaidashi ba bakuga yadda biba ta gaisheshi bane hakan yasa suka mike daya
bayan daya suna gaida shi.
Nace duk wanda yazo baku tashi kun duka kun gaidashi ba saina tsunkewa mutum
kunnensa da yuka .
Haka sunso su dinga irin barnan nan da sukeyi su halaka abu ana kallonsu ba kwabo
su barnatashi ana kallo haka zasu barna abu.
Shima cikin nasiha da fada na hana wanan da mamansu tazo gidana muyi ban kwana
wai daga gidansu take shi yaya ya kawota yadda suka gaida ita ya bata mamaki.
Har take fadin wai basmace nan kuwa a,a yan matan anty kece nan harda su makeup
a fuska koba kwali kika shafa a indonki ba.
Ina jin mijin tace mata waye anty ita ba zasu iya kiranta da mummy ba ko mama
karna kara jin wani anty can daga yau nace dashi ai haka suke kirana tunda sunji
biba na fadan hakan.
Tana dan murmushin yake a fuskanta yace ki duba don Allah dan kwana biyun da
yaran nan sukayi a nan yadda suka koma keda suka gaidake da zuwa bakiji dadin hakan
ba yanzu ?
Toni yaya me zance kai kome nayi ai banyi daidai bane a wajen ka kasan halinsu
baji sukeyi ba nan ma dai don suna shakatane ai to kada ki koya masu din ni ai
nasan matakin da zan dauka don ba zan yarda ba gaskiya.
Basu jima ba yace su tashi suje nasan don ganin da yayi yaran sun narke a
jikintane saida ya mike yake cewa dani ki shiryasu idan na dawo zamuje can gida ku
sallami su mama.
Hakan ya faru don kafin ya dawo munyi wanka mun shirya tsaba duk da kayan yaran
ga kaya na kwarai sabbi amma duk sun nakashe daga wanda ya yage a tsakiya sai wanda
zip dinsa ya lalace hakana dai muka samu aka saka aka fita ina yaba sakaci irin na
wanan matar a raina wai kuma harta iya hado wanan kayan haka azo dashi.
Munje gidan ba laifi don mama har daukan Amir tayi tanawa mashi wasa da wakan
yabo na mai sunan, baban nasu yana murmushi ta dubi yaran tace indai ba idona ke
gizau ba sai ince yaran nan sun sauya a dan kwana biyun nan da sukayi.
Tunba Siyama ba ni dai har kiba naga tayi ai dole yanzu ta rage wanan alaulayin
nata Saratu dake neman shiri da dan uwan nata ke fadin hakan .
Yawan cuwon nan da kwanciya naga duk ta dainashi yanzu uban ya fada mama tace
dashi aiko yunwa ya isheta yaushe suke tsayawa su kula yara?
Jiyama nake ji ance anga uwar wai a nan garin na dauka ai duban tar tazo ko tazo
ina zata ganta nayiwa maigadi kashedi idan ya bari tazo min gida bakin aikinshi
ranan.
Ni dai banyi magana ba ina zaune ina jinsu aka gama yace mu tashi muje da zan
fito na mikawa mama dubu biyar iyama dubu biyar muka fito.
Naso na rakasu har kaduna amma yaya Auwal yace kowa ya zauna gida sun gode sai
mazan su suka rakasu zuwa kaduna a ranan kuma akace sun tashi da dare don saida
suka daga suka dawo gida.
Gaskiya munji kewa sosai gidansu mama Saratu aka bari da matar Yazid duk ita
da ita da babu dukka dayane tunda bata fitowa kullum suna ciki rufe.
Sai su Aminune isah yaya yace zasu dinga kwana gidanshi shi kuma musa a gidan
su mama haka ya rabasu ni dai najawa yaran kunne sosai a lokacin.
Nayi ta jira inji wani korafi daga mama game da yan uwana din sai baniji ba yasa
na saki zancen a raina suma basu da rugima sai hakan yayi min dadi.
Sana,anmu da Nafisa a yanzu ya bunkasa sosai don ba zannuwan gado kawai muke
daukowa ba har da kayan kitchen masu kyau sabbin yayi muke daukowa hakan yasa muka
fara shawaran bude shago a asirce ba tare da kowa yasani ba.
Ni da wata kawata da muke unguwa daya zata bude shagon kayan mata ni kuma nace
na kayan kitchen din da sauran abubuwan mata.
Na nemi shawaran yaya na fada mai ya yarda da yace zaiyi magana abokinsa ya
nema muna shago a bakin tiri inda za afi samun kasuwa.
Ni dai nasan baiyi niyar zuwa saudiya ba sai gashi kwatsam yazo min da zancen
zaibi jirgin yawo ya cin masu don hankalinshi bai kwanta ba tunda suka tafi.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login