Showing 42001 words to 45000 words out of 328222 words
Chapter 15 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
gata ku godewa Allah da hakan gaku da yayyu
dake debe maku kewan baba din mu ina muka samu yayyu maza anty Yanda itace babba a
gidan mu sai yayana Aley saini sai umar sanda.
Ashe kuna da yan,uwa na dauka daga ke sai anty maria ce ai, nace a,a muna da
yan uwa maza biyu mu mata biyu su mazan suna tare da maman mu.
Kingani mu uku mata su maza su ukku yayan mu mace tana zamfara tana aure a gusau
sai ya J ya Habu sai Saare sai ya faruq saini.
Su dai ita babban kuce ban sani ba amma nasan ya faruq da mukazo gidan nan
lokacin yazo hutu mun hadu dashi.
Ita anty Rabi cikine da ita tsoho alokacin yasa bata zo bukin ba amma ance tana
tafe cikin kwanakin nan amma muna da yawa a gidan mu ai kinga hakan da idonunki
mukai ashirin da wani abu a wajen baban mufa.
Wai kuna da yawa kan gaskiya ko gidan nan ai munkai mu nawa a cikinsa tace da
matan su yaya ba suda suka cikawa mutane waje da bakin hali irin nasu.
Kinsan ita Nusaiba itace best friend din Asmau da suke school a wajen Asmau
tasan ya J shine daga baya ta nemesa ya aureta.
Budan baki sai cewa nayi amma yar iskace ko mijin kawarki zakice ya nemeki dole
biri yai kama da mutum ai bata da kunya ko kadan gadaranta yayi yawa wallahi.
Duk macen data san kunya ba zata taba haka ba ai ko kinyi kuwa iyayyen ki in na
arzikine ba zasu yarda da haka ba a rayuwansu.
Dole su dinga fada gaskiya babu shiri kuma har abada a tsakaninsu nikan kikai
min haka saina barki da mijin ku zauna inje gaba in samu wani mijin nawa.
A,a Ramaah baki san kaddara bafa Allah ya rubuto tun farko itama matarsace ya
kuma hada zamansu tun ba mijin a tsakaninsu.
Ita Asmauce wawiya ai ance ta fita harkan ta tabarsu da Allah amma bata da
hakkuri ga kazantar tsiya da rowa ita kuma Saiba ai kinga bata kai Asmau rowa ba
saidai cin mutunci da gadara.
Ga kuma hassada ko don hassada yasa tayiwa kawarta hakan na fada ina gyara zama
da yanzu itama Allah zai sakawa Asmau ya jefo wata ta kusa da ita ta auri mijin sai
kinga yadda zatayi haukan karya akai.
Ba hauka ba wanan ko mutuwa tana iya yi wallahi tana bal,ain son yaya fa aida
soyayyan da kissa ta samu ta yaudareshi wata ukune kacal a tsakanin su Salima ta
fada.
Zanyi magana Saare ta fado dakin tana fadin kai kai ina son yaya J yana gari
bakin ka zai more kwana biyu da dadi wallahi.
Kallonta mukayi gado ta fada tana fadin naso iya ta raga min amma tayi min
kwalelen shi yau don munyi rigima da ita dana sani da sai mun gama in bata amsa.
Sai kuma ta juyo tana kallon mu tace wai kuna nufin baku ci naku ba har yanzu
kuke nufi wai nazo mu koma wurin yaya mu samo wani nagashi da ledoji da yawafa zai
shiga part dinshi .
Kai amma anty Saare din nan wai kina nufin sai mu koma muce dashi wanda ya bamu
bai ishemu ba don munfi kowa kwadai ?
Wanan ma din da kika samu don bai shiga hannun marowatan matansa bane don
wallahi da guda daya zasu bamu kaf part din nan kuma dole a karba.
Balle zai fada masu basai sun kawo muna ba ya rigada ya bamu namu nan kinsan kuwa
ko kallo baki ishi Asmau ba .
Taja tsuki tana fadin ni yanzu ai nasan maganin su shiyasa nake shiga kai tsaye
in dibi abinda nake so a wajensu duk da kwakwazon da sukeyi kan hakan .
Ina jiran ranan da zasu kai karana wajenshi suga tsiya a gidan nan don zan nuna
masu nafi kusa dashi su godewa Allah da mama tana gidan nan aida sunga abu a wajena
.
Wayan ta dake ringing ya katse mata magana inda kowan mu yayi shiru a lokacin
tunane na fara akwai bambanci sosai rayuwan gidan nan dagidan su hjy fanna da
mukayi a Abuja don su komai moderate akeyinsa gidan .
Sabanin nan da akwai waddatan amma ana hadawa da akidan bahaushe mai ban haushi
akwai abin makin ayisa aci a wadace tunda Allah ya hore sai kuma a tsaya ana make
make dama idan mama na gidan za ayi komai a wadace kowa ya godewa Allah.
In bashi ba freezer part din yaya J din makil yake da nau,i nau,in namuka sunyi
kankara harsun gaji sai idan anyi tsiyar wutane sai su yoye su fara bashi su
wullakance a banza ba aciba.
Ban fita waje ba dana gama ko yar uwata banje na duba ba na samu waje na kwanta
ina faman kimtsa abubuwa da dama kasan zuciyata.
Washe gari na tashi nayi aiyukana yadda na saba ina gamawa nashige wanka don har
lokacin su ya Habu basu bude part dinsu ba balle naje mu gaisa da yar uwata.
Dana kwana da ita a raina ina faman tunanen yadda zata zauna tsayon wata shidda
a asibiti bata leko gidan ta ba.
Kamar Saare tasan tunanen da nakeyi a lokacin data shigo daki take fadin ni har
tausayi ya Habu da matarsa suke ban ace mace ta zauna asibiti har tsawon watani
shidda don Allah ?
Toke bakiji ance daurin mahaifa za ayi mata ba gudun kada ya balle a samu
matsala a nan gida yasa sukace sai dai ta zauna a wajensu ai.
Ras ras gabana ya dinga faduwa dan jin me suke fada ta yaya za a daurewa mace
bakin mahaifa an taba yin hakan kuwa ?
Dan lokaci na share a zaune wajen kamar zancen su bai dameni ba can na mike na
fita na hango part din nasu a bude hakan yasa nagane cewa sun bude.
Da sallamata na shiga suna falo sun shirya tafiya a lokacin don har mama tana
falon itama suna magana nashigo ina gaidasu da kwana.
Cikin harshen fulatanci nake tambayanta yanzu ita asibitin zata tafi ke nan ta
yarda da zancen likita bayan tasan daga inda matsalanta yake ?
Kamar ba zata ban amsa ba har na juya naji tana fadin yaya zatayi ita tunda
sunce aje can din dole tabi umurninsu ai amma koma meye ai mahaifiyar mu tana tafe
ranan.
Allah ya sauwaka ta amsa a zuciya ba,a fili ba don gudun rashin kunya garesu da
alkunyan nan ta fulani har yanzu ta ajini komai wayenwan bafillace kuwa.
Dakin ta biyoni banji shigowanta ba sai muryan ta da naji tana fadin Ramaah don
Allah ki natsu a gidan nan kada ki yarda ki canza a bayana kin dai san halin
mutanen gidan nan don haka ki kama kanki dasu don Allah banda kuma shiga abinda bai
shafeki ba don Allah.
Zan kula insha Allah ke kuma ubangiji Allah ya baki lafiya tace amin ga kudin
nan ki rike don kada ki zauna ba kudi a hannunki don Allah ki kula da kanki da
mutunci har in dan ya nufa ina da rabon dawo gidan mucigaba da rayuwan mu yadda
muka saba.
Kasa dago kai nayi in dubeta don hawayen daya cika min ido a lokacin gasu har
sun fara zubowa daga idona.
Ta gane hakan naji tace idan kikai kuka Ramaah zaki kara min zuciya nima har
mutanen gidan nan su dauka ban godewa gatan da suke min ba.
Likita yace yanayi na ba zan iya rike ciki ba don haka sai sun rikeni wajensu
suna bani kulawa daya dace daga yau din nan.
kinga kuwa ba yadda zanyi da wanan umurnin nasu tunda sunan sun yaya habu sun
yarda da tsarin nasu sunce ana irin hakan.
Muryan mijinta dake kiranta a falon ya katsemu ta fita ta barni nan ina kukan da
ba sauti itama din ashe kukan takeyi a lokacin.
Muryan mama dubu ce naji tana fadin asha assha maria yaya da kuka haka kuma keda
zaki neman lafiyan ki kuma zaki karawa kanki lalura.
Zaman asibitin naki ai kamar gida kike a can din babu takura ko kadaici sunfi
sone kawai su saka ma duk wani motsinki ido don yanayinki hakan insha Allahu aiba
komai bane.
Ina ji ina gani mama ta kirani nima tayi min fada sosai tare da kwantar min da
hankali kuma tana fadin wanan abin mu anan yanzu ba bakon abune ai mata nawa aka
kai suka haihu lafiya ?
Haka itama insha Allahu zata sauka lafiya ita da abinda zata haifa don haka kada
ku daga hankalinku har ku dagawa sauran yan uwan ku kuma.
Ni dai ban iya tsayawa naga shirin su shi mijin nata da itane suka shirya tafiyan
nasu ya hada mata komai da zata bukata yakai wajen mota.
Saida zasu tafine ta kwala min kira na fito da yare muke magana tana kara fada
min in kula da kaina a gidan sai gani nake kamar dai ta tafi ke nan ba zata dawo ba
daga wanan fitan da tayiwa gidan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
1️⃣6️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Sai da suka shiga part din ya J ita da su mama dubu da mijinta nasan sallama sukayi
dasu mijin nasu dake gari shine kadai ya fito har bakin mota yana fadin gashi nan
zuwa asibitin idan ya shirya.
Haka suka daga suka bar gidan duk kokarin dakewana saida hawaye ya zubo min ba
lokacin ya J yazo ya wuce mu zuwa part dinshi lokacin nake jin muryan Asmau na
fadin wai har sun tafine ?
Sun tafi Salima ta fada saita amsa da Allah ya sauwaka dama ashe bata da
lafiyane take yawan zama haka lukume a daki ko yaushe?
A daidai lokacin Saiba ke fadin wai har ciwo ma sai an boyewa mutum a gidan nan
abu har yakai haka muna gidan nan bamu sani ba ?
Koda yake ance kowa ya samu rana yayi shanyinsa cikin ne za ace za aje asibiti a
zauna har sai an haifeshi ni ban taba ganin irin haka ba gaskiya.
Na kula da lokacin da Saare ke nuna mata ni da idanu naji tace ai gaskiya na
fada Saare shi ciki ai har ka haifishi baka taba jin dadi a rayuwanka sai ranan
daka haihu.
Yadda take magana yasa naji ba dadi a zuciyana itako tacigaba da fadin kudi
yayiwa Habu yawa koda yake ba zafinsa bane tunda Allah ya kashe ya bashi ta dubi
kishiyanta tana fadi ita kuma tayi wani irin meda baki.
Sai naji Saiban na fadi a to mana ke inbashi ba dai naga mu duk lalura baisa
munje mun kwanta asibiti saidai asayo muna magani a hadamu dashi kawai ?
Amma ai kowa da irin yanayisa ko yanayintane yazo mata a haka ai ko ita bada
son ranta taje kwamciyan asibitin ba .
Tunda gashi ta fita tana kuka dadi zaisa mutum kukane Salima ke fadan hakan
cikin hasala data karbi zancen da yar uwarta ta soma yi dasu din.
Zo muje Ramaah kinji mama tace idan sun tafi mu gyaro wajen mu kulle masu ato
nidai ga gaskiya na gani ba za a hanani yin magana ba dai kan bamu tsaya karasa
saurarensu ba sai dai muna gab dashigane mukaji muryan mijinsu na kiran Asmau.
Shiyasa akace matan saure sunfi kishiyar miji daya kishi wanan ba karya bane don
matan ya J da suka fito fili suka nuna bakin ciki ga yar uwata ranan.
Ashe bani kadai naji haushin abinda sukayi ba din har da Salima don ina kitchen
ina hada kayan datace in kwashe zuwa cikin gida naji salima din tana fadin.
Shiyasa suke bakin kishi tsakaninsu ai ina abin dadi a zaman asibiti ga mutum
har wanan abin yakai zancen banza haka ?
Ciwone ai yasan kofan kowa sanda zaizo gunka baka sani ba tunda ba sallama maka
zaiyi ba ai munafuncin banza da wofi kawai ?
Ni dai banyi magana ba amma na rike hakan a raina akwai ranan magana matukar
muna raye na nasa hakan a zuciyata.
Bamu zauna ba nida Salima abinci muka dora don mama ta gargademu da hakan mu
hada abinci akai asibitin da wuri basai na can sunji yunwa ba za a kawo masu .
Kafin sha biyun rana mungama miya da abinci tana zaune tana yanka salad da kayan
had iya na zaune tana jan tasbaha a gefen ta .
Ni kuma ina kitchen na dora ferfesun da mama ta bugo waya tace a hada na kifi.
Ya Habu ya dawo yana tambayan makulin part dinsu da muka rufo masu naji iya na
tambayan ya mai jikin take ?
Naji yace sun bata gado sun fara dorata a dokan sun kuma hana a aita yawan sintiri
a wajenta don barcin da akeson ta dinga yi ko wani lokaci saboda lafiyan abinda ke
cikin cikin nata.
Bakaji ba mai lafiya yana zama haka don son rai ka zauna a hanaka mu,amula da
mutanen arziki su wa yancan sakarkarun sun dauka hakan wani abune har suna tsayawa
gulmam hakan .
Shi Jafaru ya sameku can ko zai fita don bai tsaya jin zancen nata ba ya juyo
yana fadin muna tare dashi iya shiya biya kudin komai ma har zuwa lokacin da Allah
zai sauketa lafiya.
Ai dama nasan ba zai bi kan matansa marasa kan gado ba tunda shiba sakarai bane
irinsu wai iya anyi wani abin ne ya dakata yana tambayan tsohuwar ?
Anyi mana Abu matan dan uwanka ke gani wai saboda makirci yasa yarinyar nan
karyan zuwa asibiti ta zauna a can don kawai ta,,,,,,
Haba iya ki bar yaya yaji da abinda ke damunsa don Allah matanda basu sawa basu
hanawa idan an tashiyi sune basu san Allah ba cikin zancensu Saare ke fadan hakan
ga kakan tasu .
Koya gane me take nufi da zancen ta yasa kai ya fice daga part din bai jima ba
ya fito a cikin shirinsa nan Salima ke fada mai mun hada abincin asibiti yace har
angama ta amsa da ehh mama tace kada mu makara ai da hada abincin.
Ku fito dashi na kai masu don kaduna zan tafi yanzu in sayo wani magani da za ai
mata amfani dashi nan ban samu oroginal dinsa ba.
Allah ya tsare mukai masa bayan mun saka kayan a bayan motanshi din muka nufi
cikin gida nikan Allah ya gani ban iya cin abincin ba a ranan don har lokacin ban
fahinci komai ga zaman da zatajeyi asibitin ba.
Mahaifiyar mu bata iso garin ba sai dare wajajen tara muna daki salima dai waya
takeyi ni kuma ina kwance naji ana mata sannu da zuwa .
Muryan ummah na tsinkayo a kunnena tana amsawa hakan yasa na dubi anty Salima ina
tashi zaune nace muryan ummah nake ji fa ?
Waye ummah ta fada tana kallona nace mahaifiyar mu tare da ita muka fito falon
tana zaune suna fira da iya dake tambayanta hanya ?
Sannu da zuwa muke mata saidai ni a cikin yare nake mata magana ina tambayanta
yan uwana tace suna lafiya taso tazo da umar sanda ai amma ta barshi agidan hardo
saboda karatunsa .
Ku kawo mata abinci ko iya ta fada sai ummah din tace sallah zatayi tukun a nuna
mata ban daki tayi alwala na mike tsaye don bansan inane zan kai ta ba sai Salima
ke fadin kaita bandakin mama mana ta sauka a nan.
Lokacin anty Saare na part din ya J bata sanda zuwan ummah namu ba ni dai a
yadda na dauka shine tana zuwa dan hirane part din.
Amma sai inji Salima na fadin don kwadayi da munafhnci take yawan shigewa matan
yayan nasu in bashi ba sau nawa suna masu wullakanci a baya lokacin da yayansu
baiyi karfi haka ba?
Amma yanzu wai duk anty Saare ta manta da hakan suta koma tana shigewa don suji
dadin wullakantasu ke nan kuma.
Dakin yana nan yadda muka gyarashi da safe nan ta shiga yayi sallah ta jima
bata fito ba salima ta dauki kayanta takai mata dakin ba wasu kaya bane sosai sai
manshanu da kindarmo mai yawa datazo muna dashi da nama soyayye.
Abinci ma da iya ke magana nayi murmushi ina fadin ummah ba zataci abinci ba
nan iya saboda kunyanki kinsan nan gidan surukintane ai.
Salima tace shine kikai shiru Ramaah ta mike ta suri kayan ta sameta dasu a daki
nan ta jera mata har da jawo kofan dakin don tasan babu mai shigowa hakan yasa ta
dan tsankwari abincin kadan ta aje.
Bata sake fitowa ba falon sai washe gari ta fito da shirinta tana dakon yaya ya
shigo ya tafi da ita asibitin da zata zauna.
Inda muke ta kokarin hada masu breakfast da za a kai asibitin haka kuma iya ta
lasa muna tare da mu za,a tafi mu dubasu a can.
Yasa mukai komai a gurguje inda na saka nonon kindarmon a cikin fridge na
rakumi datace min don yar uwata tazo dashi ta dinga sha na diba a cikin wani gora
da za akai mata ta dinga sha na kada a kulan kankara.
Mun shirya tsab koda ya fito yazo gaidasu iya da ummah