Showing 138001 words to 141000 words out of 328222 words

Chapter 47 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

kaishi don
Allah.
Jin alarm din wayansa dake sanar masa da lokacin sallah ya mike zuwa masallacin
nan unguwarsu inda suke bi sallah.
Ana idar da sallah ya shiga motarshi yabar gidaa tudun wada ya nufa ya gaidasu
mama kana ya nufi gidan anty Ai da yake son zuwa ya ganta.
Yana gidan Habu ya kirashi a waya yana fadin J kana ina gasu malam sun iso aina
dauka kana cikin gidane saida na aika akace kafita.
Habu kuyi yadda ya dace gani nan tudun wanda daga nan kuma zamu fita da Nurane
kai habu ya daga ya dubi su mama da sauran jama,an dake wajen.
Baiso ace J din baya wajen ba za ai wanan rabon amma zai dage yaga an fitarwa
kowa hakkinshi yadda ya dace .
Aka bude taro da addua tare da bayanin abinda ka,idan kado ya bada ikon abawa ko
wani mai hakki kafin habu ya dora da kara masu haske kan yadda dukiyan nasu yake.
Masha Allah wanan bawan Allah yayi kokari matuka abin a jinjina masane sosai
duba ga irin rikon amanan da yayi da kurciyanshi.
Abune mai wuya a samu kudi har riba a wanan shekarun don haka su godewa Allah su
kuma godewa wanda yayi wanan jajircewan a garesu.
Habu yace ba wani bane illa yayan mu jafar shine aka dankawa kudin tun lokacin
akan ya juya har ya fara daga baya yayi shawaran gara ya bada wa yan nan kudin ga
wani ya juya ya fara sana,an kanshi amma yana bibiya ko wani lokaci malamin yace
Na,am .
Shine dalilin da yanzu da yan uwan mu suka bukaci kudinsu aka fito dashi aka
lissafa mun samu kudi ya ninka ninkin ba ninkin muke so a warewa kowa nasa kaso a
damkawa masu shi abinsu.
Daidai lokacin kawu ya shigo falon don bai samu karasowa da wuri ba saboda kauye
daya tafi duk akan rabon kudin don yana son a daure bakinsu wai.
Duka kudin su dawo hannunsa ba tare da an samu wanda ya mussa hakan ba a cikinsu
don ya kula yaron sun soma sanin ciwon kansu a yanzu.
Yazo ya zauna sai cicika yakeyi yana batsewa don me za a fara bashi daga baya
daya fahinci ba a soma kasafin kudin ba ashe shine ya dan washe fuskansa.
Malami na farko ya gyara zama yana fadi to ai abune mai sauki yanzu tunda da baya
an raba ansan yawan abinda kowa a nan ya mallaka daga mazan har matan sai a soma
cirewa kowa nasa kason ko kuma alabashin kasafa kudin a yadda wanan can kadon na
farko yake har riban da kowa ya samu zuwa yanzu.
Da yake aikinsune sun saba nan da nan aka fara lissafin yadda ya dace ana ajewa
kows nasa gefe daya da sunan da mama aka fara sai su maza kafin a debewa diya matan
akasafa masu yadda ya dace.
Ba wanda aka cuta a cikinsu rabo na tsakanin da Allah malaman suka tsaya sukai
masu inda Habu ya mika hannu ya dauki na farko yana fadin wanan na J ne.
Jafaru kuma a yanzu ai baida abinda zaiyi da wanan kudin kan a,a hjy ba yana
cikin magada ba ?
Suka amsa da yana ciki malam yace don haka a kwashe mashi tunda yana da hakki
anya Jafaru bai yafe kudin nan ba kuwa ?
Anty baraka ke fadin malamin ya sake fadin babu zancen yafiya a nan tunda ya
gada shima dole a bashi hakkinsa ai.
Sai kuma wanan nawa saina yazid daya mika hannu zai kwasa mama tace kada ka
dauki na yazid habu ka barshi za aci gaba da juya mashi kafin Allah ya dawo dashi
lafiya ya karba mama ke fadin hakan.
Kallonta Habu yayi a cikin mamaki kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru ya kasa
furta komai daga can Salima take fadin amma yaya Yazid yace abawa J nasa kason ya
rike mashi a hannusa idan an raba ai.
Nina haifi yazid ba wani ya haifa min shi ba don haka nina san yadda zanyi dasu a
wajena ta fada fuska daure habu ya ciro kudi daga Aljihunshi yana fadin wanan na
maine J yace a baku ai maku godiya.
Ya hada kudinshi zai fita yaji salima tace yaya Habu kada ka fita kudina nace a
ba ya j ya aje a hannunsa fa ?
Ba zan bashi ba akwai wanda zan ba a cigaba da juya maku kudin nan mama ta fada
a tsawace ga salima din.
Dakata hjy malamin da zai fita falon a karshe ya fada yace wanan hakine fa
yarinyar nan yanzu ba yarinya karama bace don ko wace ta mallaki hankalin kanta a
yanzu.
Don haka yau ko cewa tayi ita zata rike abinta a hannunta za a iya danka mata
dukiyanta don ita ta gaji abinta daga mahaifinta.
Kawu ya hade wasu yawu yana gyara haban babban rigansa sai aikawa malamin harara
yakeyi daga inda yake zaune ganin malam ya tsaya jawo dogon aya yasashi magana.
Malam ina ganin kunyi abinda ya dace yanzu ai kowa yasan hakkinsa kamar yadda
suka bukata don haka abarsu suyi shawara da uwarsu kuma.
Ni wallahi ba wani shawaran da zanyi ya habu ka dauki kudina kaba yaya J na fada
mai abinda nake sonyi dasu nan gaba.
Salima zan safa maki fa ina fadin magana kina musayawa mama nace abu zan saya
dasu idan sun kara yawa kuma har na nuna mashi abin ya sani .
Habu ya dawo ya tsaya gaban kudin yace baraka kwashi naki ke saratu ki dauka a
ban na salima din tunda abu take son saya da kudin.
Idan abin bana amfani bane na tabbatar da J ba zai yarda ba baraka ta kwasa sai
saratu ya duka ya dauki kudin Salima din ya fita dasu zuwa part dinshi.
Ranan Salima tasha fada sosai wajen mama Allah ya gyara batayi maya baki ba duk
abin nan anyishi iya bata wajen don kamar an kadata fita unguwa tabi J ya sauketa
gidan wani dan uwanta dubiya.
Yanzu yaya kaga yadda abu ya kaya kuma yaran nan kamar abin hadin baki kudin nan
daga nawa saina Yazid koshi don bai nan,ne .
Nasan da haka za ayi shima karban abinsa zaiyi sai na saratu itama naga take
taken ta tun kan a raba take fadin sana,a zata fara tunda karatun yakiya gareta ko
Allah zaisa mata hannu.
Ni yanzu ai lissafin ya tsaya min saidai a kawo mu gwada ko zasu fara daukuwa a
garemu hakana bai bar gidan ba ranan saida ya karbe kudin mama da yazid din.
Dana saratu da mama ta raba biyu ta boye rabi ta mikawa kawu sauran ya daure
leda ya tafi yana mata sallama kada iya ta dawo ta sameshi .
Zance ya lalace yasan ko wanan rabonsane shiyasa yayi dabaran daya izata zuwa
gidan dan uwan nata a ranan ayi a kare bata nan.
Habu ne bayan fitansu ya dawo raka malaman yake waya da j yana fadin gaskiya j
akwai abinda yake damun mama gaskiya.
A nan dai ya kwashe komai daya faru wajen ya fada mai murmushi j din yayi yana
fadin ba komai matsalanta a yanzu kawune.
Iya ta fada min dazun a hanya cewa kawu shiya matsa a fito da kudin nan a raba
don kawai wata bukatanshi.
Dama ina hasashen hakan daga kawu mutumin nan ya kamata mu nuna mashi musan
nufisa akan mu yanzu.
No kada ka soma ba yanzu ba Habu idan kayi hakan ranka zai bacine da mama don
haka ka kyaleshi har gaba.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

4️⃣7️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



Zaune yake falin yaya Ai itama a nan cikin tudun wada gidanta yake saidai akwai dan
nisa da family house dinsu din daga gidan daya sauke iya daketa bashi hakkuri akan
rayuwa da kuma iyayye da yan uwa ya nufo gidan yaya Ai din.
Da murnanta ta rasa ina zata sakashi a lokacin don jin dadin yau dan uwanta
yazo wajenta abinda basuyi mata ke nan kamar yan uwana na gudunta take gani saboda
talaucin da Allah ya dora masune.
Don ita yaya Ai din mijinta dadtijone sosai kila kuma gami da talaucine yasashi
tsofa a zamanin kurciyarsa ya danyi tashen kudi saidai irin na rufin asiri din nan
za ace.
A haka kuma iftila,i ya sauka,mashi a hanyansa na zuwa fatauci lokacin ya hadu
da barayi suka karbe duk abin hannunsa tun lokacin yake fama da rayuwa shi da
iyalinsa.
Kasane bana hadin kai ba aure abu zai samu dan uwa maimakon a samu yan uwansa
yan kasuwa su tallafawa mutum a dagashi sai dai a sakawa mutum ido har sai yakai
kasa waras kamar jira ake hakan ya sameshi dama.
Na tabbatar da mata Allah ya umurta da kasuwanci kamar maza za a ga hadin kai da
taimakon juna a tsakanin suπŸ™‹.
Sai ya kasance yan uwa ma sam basu damu da ita ba da iyalinta don bata da komai
a rayuwanta saidai duk sallah nasan idan an fita ana zuwa gidanta boyan Allah ga
son jama,a saita rasa ina taka saka mutum idan yazo wajenta.
Yanzuma da J din yazo sai godiya take masa daga ita har mijinta da kishiyarta
kamar wanda sukaga yazo masu da wani abu a lokacin duk da hannu sake suka ganshi
amma sunji dadin hakan sosai a lokacin.
Ta kakabe wajen da zai zauna tukun a dakin nata da babu komai a cikinsa sai dan
gadon katako mai dungu da wani tsohon zani gado shimfide duk ya kode.
Gefe guda wani tsohon kujerane da tsufanshi har yasa katakonshi ya fito fili ya
zazzage an tula raga don ya danyi taushi.
Nan aka gyara mashi ya zauna suka fara gaisawa da yar uwar nasa dake mashi sannu
da zuwa a lokacin take tambayan dazun nake jin kana gari a wajen malam yake fada
mun yaji ance kaine kabada gyaran massalaci kofan gidan mu .
Yace shekaran jiya na shigo da dare jiya kuma abubuwa sun min yawa yasa ban samu
zuwa nagai dake da gajiyan buki ba.
Haba dai aiyiwa kaine ya kara mata da godiya take fadin Jafaru aini ka karrama a
zancen nan da har ka tuna dani baka kyamace niba ka turo ayi komai a gidana akwai
abinda yafi haka dadi a wajena.
Wanan ai yafi dan uwa yazo ya baka kudi indai ana zumunci haka da zumunci bai
taba lalacewa ai a duniya amma ina su isa gamu gari guda a waje daya sai inyi
shekaru ban saka kowansu a idona ba garin nan kuma ana raye inaga yaya in sun taso
kuma kaga ba zumunci ke nan ai a tsakanin su idan sun taso.
Hakkuri ya bata yana fadan in sha Allahu za a gyara yaranta da suka dawo daga
islamiya suka shigo su uku mata maza biyarne ta haifa a gidan.
Wanan yasa tsufan wahala ya taso mata saika rantse batayi primary ba balle
secondary idan ka ganta lokacinsu sune yan mata masu tashe a gari duniya ke nan
yanzu saboda talauci da yara ta koma haka abin tausayi.
Ya Allah ka duba muna wanan zamani cikon tausayinka ya Allah ka sakawa duk wata
uwa da alheri kasa albarka ga zuria wa yanda suka kauce kuma ga tsufa ga zuria
Allah ka shirya munasu badon halinsu ba ya Allah mun tuba kaiwa kasan mu da
musulman kasan mu agajin wahalan rayuwan da ake ciki Amin ya Allahu.
Yaya Ai me malam keyi yanzune na ganshi a gida a wanan lokacin ko har ya taso
daga kasuwan ne ko yake tambayanta kan mijinta din ?
Haba ta kama tana fadin malam kace Jafaru ai malam yaushe rabonshi da kasuwa yau
kusan kimanin shekaru goma sha,ai tun wanan abin daya faru dashi.
Da yana dan zagaya abokan hurdanshi na kasuwa don samun abinda mukaci a gidan har
yakai sun gaji dashi sun fara kyamatarshi yazo ya daina fita yanzu dai sai abinda
Allah ya kawo muna idan rabon mu ya ratsa.
Innalillahi yake nanatawa a zuciyarshi har yakai fada a fili ya gyara zama yace
yanzu kina nufin haka kuke zaune bai sana,an komai ?
Haka muke Jafaru aiko nayi mamaki da baka san hakan ba duk zuwan nan da kukeyi ai
kuna ganinsa gidan nan ko ?
Na dauka dai don sallah ne kinsan nafi zuwa nan da sallah wani lokacin a,a
wallahi halin da muke ciki kenan ai shekara da shekaru kai dai Jafaru.
Allah ya sauwaka ya fada yarta datazo a karshe tana gaudashi zata kai shekara
goma sha uku da haihuwa yake fadin wana takice tace tawa ce ita autata take biwa
takwaran iya ke nan ai Habiba.
A,a,a ashe kin samu mai sunan nan kema tace ina da ita ai gata nan yace ina ga
ni zan dauketa kuwa ko ita ko wanan autan naki ko inbawa Amaryata rikon ta su zauna
tare idan zaku ban don banson zamanta ita kadai don ni ba mai zama a garin bane
sosai wanan yasa yanzun nan naji hakan ya fado min a rai.
Amma abinda ya kawoni nan shine ina son dake da anty Rakiya kuzo wanan gidana da
amaryana take ku dauki kayan tausan gaban wa yan nan kukai masu duk da nasan na
daiyine kawai amma sai kuma yai shiru bai karasa fadin abinda yayi niyar fadi ba
din.
Sun dan jima ganin magariba daya gabato ya mike suka fito bayan ya aje mata
kudi yan dari biyar biyar ya samu kishiyar ta tana bakin murhu ya ciro dubu ashirin
ya bata ta bata ai kuwa suka shiga godiya.
A waje ya samu malam sule na masa gadin motarshi saboda yaran unguwar sun dan
jima dashi kafin ya fada mai makasudin zuwansa din gidan.
Yaji dadin hakan don daga mijin har matan mutanene masu son zumunci saidai babu
karfin yin hakan a yanzu dole yasa suka lafa.
Shima dubu hamsin ya bashi ya barsu cike da tausayinsu a cikin ransa masalacin
kofan gidansu da mahaifinsu ya gina da yake raye nan yayi sallah magariba tare da
jama,an unguwar.
Ana idar da sallah ya sulale ya fita bai zo gidana ba saida ya koma gidan daya
sauke iya ya dauko ta zuwa gida haka kuma yana son yai ma iyalinsa saida safe duk
da ba dadin rai ya samu ga hakan ba .
Bai shiga part din iyan ba kodaya fito ya ja motarshi ya bar gidan don Nusaiba
bata ko amsa sallamashi ba daya shigo.
Sauri yakeyi yaje yaga halin da yar mutane take ciki donshi bai tsatsaya ba ya
juya zuwa gidan amma duk damuwa akan halin daya samu yaya Ai su ya daga mashi
hankali.
Wa yan nan sune abin taimako a duniya shine amfanin samu a cikin dangi ina
amfanin kana dashi dan uwanka na cikin irin wanan rayuwan kuma ?
Tun fitanshi na shiga kitchen na dafa ruwan dumi na saka a flask na juye saura
naje bandaki dashi naji dadin tsarki da ruwan dumin sosai don haka na kai har
magariba ina gasa kaina da ruwan dumi hakan da nayi yasa na samu walwala na iya yin
girkin dare dan abinda zamuci da dare din.
Ko kafin ya dawo nayi tuwon semo da miyar busassan kubewa don shine gareni
lokacin amma nayi amfani da nama dake shake a cikin freezer kitchen din.
Inda na dan cika tattasai da albasa da dab attah kadan sai kayan yaji dana
barbada don kamshin miyan yabada dan dano nama kuma na dafeshi sosai tunda miyar
yaukine nayi ga kamshin daddawa dake tashi a ciki na hada komai na shiga wanka a
gurguje na dade zaune a ruwan dumi kafin na fito nayi wanka sabulu da soso na dauro
alwala na fito na tayar da sallah ina idarwa na mike kada jikina ya bushe sanyi ya
sauka min na nufi mirro na gyara jikina sallah isha nayi na saka wani dogon rigan
cotton mai mayafi rigan anyishi mai sharp na saka hula kalan kayan sky colour na
dan yafa gyalen shi a wuyana.
Nasan don inda yake a lokacin ya kusa dawowa gida hakan yasa na kara feshe ko
ina da air freshener take gidan ya dauki kamshin dadi ban shafa turare a jikina
saidai roll on a arm dina zuwa wuya don zufa.
Karan bude get din gidan dake bada wani sauti saboda nauyinsa yasa na gane ya
dawo a lokacin.
Yana shigowa direct dakina ya nufo ina kwance nayi rigingine saman gado da
littafi a hannuna da nake dubawa ya shigo dakin da sallama.
Na dan dago kai ina mashi sannu da zuwa na sauke kafana daga saman gadon don in
mike in karbi ledan dake hannusa don malaman mu Lubbunah ta fada muna hakan waje
biyu yake da amfani karban kaya a hannun miji.
Na farko ladan da zaki samu daga Allah don girmama mijin da kikayi da aure sai na
biyu kuma hakan na saka wani irn kauna a tsakanin miji da mata na ban girma donshi
ta horemu dayin hakan komai kankanta abu muyi saurin karba daga hannuwan mazajen
mu.
Mu,sanman mazan mu na hausa dake amfani da addini da al,ada lokaci guda hakan ya
zama addini da dabi,an malam bahaushe.
Ya gane me zanyi don idona na kan ledan hakan yasa da sauri yace No ki zauna
abinki ba wani abu bane ai a ciki kazace sai fresh milk na kawo maki kisha.
Ban dai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login