Showing 105001 words to 108000 words out of 328222 words
Chapter 36 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
donshi don Allah kawu a bari sai munje
can din idan mun dawo idan zaka fadawa mama din sai a fada mata abinda ke nan.
To shike nan tunda kaga haka yafi Allah ya tabbatar muna da alheri shi lamarin
aure da haihuwa haka mutuwa ba a son baki yai masa yawa.
Yanzu yaushe zamu tafi kallon Jafar din Habu yayi sai kuma ya koma yace da kawu
din ko gobe in Allah ya kaimu ai muna iya zuwa tunda kowan mu yana da tsabgogi a
gabansa da zaiyi zuwa jibi.
To shike nan Allah ya kaimu karfe nawa zamu fito ke nan da zaran an sallame
sallah in sha Allahu zamuzo mu daukeka mu tafi da hakan suka bar gidan kawu din da
wanan zancen.
Nikan nayi jira banji kira ba karshe ma fita tayi zuwa wajen tsabgoginta ta
barni gida da yara da yake weekend ne ranan.
Don haka banji komai a gareta ba barxcin mu mukayi sosai saida Yanda ta kira
wayana na falka muka gaisa take tambayana anty salma nace ta fita unguwa.
Muka danyi hira take fadin tana son zuwa gidan maman mu kaduna, saidai bata son
zuwa a yini kwana take son tayi idan taje ta dan huta.
Kai ni gaskiya ba zan iya zuwa in kwana biyu wanan gida ba ko yaushe fa mijinta
yana gida bai fita ko ina shi ni gaskiya saboda shine banson zuwa din.
Kaji da wani zance kuma ?
Ina kike son ya dinga zuwa dama banda abinki ai hakan ma mutuncine bai fita ba
balle a ce yana dattijo yana kuma yawo a gari bai kama mutuncin kansa ba.
Nan dai muka kauda zancen take fada min ai yaya J ya dawo shekaran jiya yanzu
haka yana gari sunyi tafiya ma a ranan da yaya habu nace Allah ya dawo dasu lafiya.
Take fadin yan iskan ai ance har yanzu fushi yakeyi dasu salima ke fada min
dazun data shigo nace wai ita anty salima bata koma bane har yanzu ?
Ai tayi relocation ta dawo garin nan da services din nata wai shi yaya jafar din
ya hanata komawa kasan iyamuran tace.
A raina nace tabdi nikan ai ba mai kawo min wanan idan na tafi na tafi ke nan ma
saina gama indawo gida baki daya don ba zan yarda da irin haka ba.
Iya fa na tambaya ta kwashe da dariya take fadin iya na nan shekaran jiya mun
jima tare ai don na shiga wajenta gaida ita da kafa.
Take min kwarmaton matan yaya din tace tana ganin yana gab da kara aure nace
Allah yasa yan iska ya auro masu wace zata zama masu karfen kafa a gidan.
Ke nifa Saiba nan takai min ko ina na rasa mena tare mata a gidan nan har Abba fa
ta hada cikin rigimarmu donni har yanzu batayi min magana nima banyi mata.
Sai gashi fada ya kaule tsakaninta da salima wai akan Abba don ya dauki tedy din
yar ta da suka shiga part din tace ya aje aiba ubansa ya saya ba .
Ita dai ta sani zata samu daidai da ita koba namiji ba aiya fita sanin kan sheri
tana nan ta kasa zaman lafiya da kowa a gida sai masifan tsiya.
Mun dan jima kafin muyi sallama duk tambayan da take min akan yaushe zan dawo ban
fada ba don bazan iya cewa ba zan dawo ba ai saidai taji a bakin anty Salma.
Su hudu sukai tafiyan zuwa Adamawan mu na cameroon wajen hardo wanda tun safe
suka tashi sai da yamma suka isa ruggan hardo.
Duk da garine harda wutan Nepa akwai dan kauyen namu taro na sosai akai masu
tare da mutuntasu sai bayan sun hutane don a ranan zasu dawo.
Kawu ya gabatarwa Hardon abinda ya kawosu watau neman auren diyansu da maria
matar Habu take riko wanda kuma shi yayan habu din ne yake neman auren.
Daga inda Hardon yake zaune sai faman girgiza kai da yakeyi yana fadin Allahu
akbar tokai kawun yara a kwashe duka a baku gida daya.
Muma nan ai muna da bukata hadin irin bawai muyi abin rashin hankali mu dauki
yara har biyu ciki daya mu mikawa daki daya ba kuma ?
Hardo ai Allah bai hana ba kawu ya fada hardon yace na sani ai donshine bani da
ja dan sunnah ce babba hakan garemu musulmai.
Maganan manya rabi da rabi hirace har da hiran jikin yaya da yai fama dashi suka
tabo cikin zancen nasu hardon ke fadin Allahu akbar.
Kawu dai yana ta masa hira a cikin hikima yana kara cusawa hardo zancen a zuciya
hardon yace to ai baku fada muna ba da munyi namu na nan mugwada a gani ko za a
dace.
Kuna zube diya haka cikin duniya ba tare da kun tsumasu ba tayaya mutum na wanan
irin shiga mutanen za a sakeshi kara zube yayi alkawarin zai basa sayyun itatuwansa
yaje yacigaba da gwadawa har habu da kowa nasa zasu iya amfani dashi.
Yasa murya ya kira shatu tazo yace ta debo masa wasu magani a cikin yaren mu na
fulani ta juya taje bata jima ba sai gata dasu ta dawo.
Ta mika mashi ko wani saida ya tsakura ya dandana yake masu bayani don su gane
tare da aikin maganin .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,
3️⃣7️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Wanan dalilin karban maganin a hannun hardo don gaba dayansu sunsan cewa maganine
mai tasiri wanda sunsan zai amfane su sosai nan gaba.
Don akwai magani sahihi a wajen fulanin asali dama ance ba a hardon banza sai
wanda yasan abinda ya taka yake zama hardon kewaye.
Don haka suka dakata da tafiyan nasu aranan a nan ruggan suka kwana suna ganawa
da hardo don kawai su mallaki maganin daga hardo .
Wanda shida kansa hardon ya kwadaita masu din don ganin a yanzu yaran sun zamo a
halinshi tunda suna auren yayansu.
Yaga ya taimaka masu da abinda zasu kare kawunansu dashi daga magautansu wanda
su basu san hakan ba sai kaura da kai da suke faman yi tare da makiyansu.
Mussanman kawu dauda da abu yake cinsa a zuciya da dadewa game da diyan yar uwar
tasa duk da bai fito fili yayiwa hardo bayanin akansu yake nema ba amma shi hardon
ya san hakan ya boye mashine kawai .
Kallon kawu din yake karr don hakane ya taya masu maganin da bakinsa da suka
fito da zancen jifan da akewa ya jafar din kuma jifan yana cinmasa har yana kaishi
kwance kamar ba za,ayi dashi ba.
Hakan yasa irin hikimarsu ta manya ya fara kebewa da kawu yaji ta bakinsa inda
ya bashi iya abinda zai iya bashi don shi kawu din cewa yayi a taimaka masa da
wanda zai rika karban abu wajen wanda duk ya bukaci abin hannunsa an kuma bashi
din.
Saida kawu zai fita yace ya turo mashi Jafar yai wani magana dashi daya shafi
zancen wajen aikinsa hakan yasa kawu din ya fadawa Jafar da ya shiga zai gana da
hardo.
Jafar din ya dan tsaya jim yana dauka akan zancen Rahamane kawu ya gana da hardo
din sai bayan ya shigane yace aida sun shigo tare da Habu inda ya kira wani yaronsa
ya nemo habu yazo shima.
Bayan sun zaunane ya soma magana yana fadin ku saurareni kuji abinda zan fada
maku don yanzu kun zama yayana tunda kuna auren jinina.
Don abinda yasa na nemi ganawa daku shine kuna tafiya inwanku a waje don haka
kowa ya taka ku lokaci daya zai sameku don ku din kamar yayan rokone.
Suka dubi juna a tsakaninsu yace akwai wani abu da mata keyi yayin da Allah bai
basu haihuwa ba sai su kasa hakuri suga kamar Allah ya manta dasune.
Idan mace ta tsunci kanta cikin irin halin nan zata daga hankalinta har na tare
da itama a lokacin kowa yace ya iya zata kai kanta gareshi neman haihuwa don ta
samu taga jininta a duniya.
Saidai kash irin hakan akwai hatsari a cikinsa indai ba malamaine suka bada wanan
sa,an ta wani is,simin sani da baiwan da Allah yai masu daga Al,kur ani mai,girma
ba.
Mafi yawan mata suna halaka zurian su ta wanan hanyan zuwa wajen malaman tsubbu
da yan bori dake aiki da aljannu da sunan samun sa,a su wa yan nan diyan sune yayan
roko da nake nufi.
Wani irin zufane ya tartsowa habu a gaban goshinsa take kuma mafalkinsa na baya
ya fado masa a rai har hankalinsa na neman gushewa a garesa lokaci guda.
Muryan hardo ya dawo dashi daidai hardo dake fadin irin hakan uwarku tayi shine
kuma a yanzu yake shafan dan uwanka kai habu harkai baka tsira ba saidai saukinka
gudane haduwan auren ka da maria shine hasken taurarinta ya hasko naka din.
Zama ya gyara yana fadin nasani baba nasan hakan tun ban hadu da maria ba don a
ranan da zan taho cameroon wata mace ta fada min kusan hakan a dunkule.
Nan ya kwashe komai har da zuwa neman matan da sukayi da mama dubu da kuma
mafalkin da yayi daga baya har yazo zancen bada maganin da nayiwa ya jafar din.
Sai lokacin Jafar da yayi suman zaune ya iya budan baki yana kallon dan uwan nasa
yace yanzu habu kasan da hakan kaki fada min komai na tashi tsaye inata wahala ?
Baisan komai ba iya abinda aka sanar mashi ke nan amma shi wanan kawun naku
yasani yasan komai a game daku saidai nasa manufan akanku ya hana ya fadawa uwarku
gaskiya don amfanin kansa da yakeyi daku yanzu.
Sanda dake gefensa ya dako ya aje a gefensa yace kunga haka hakan kuke
tsakaninku dashi ba zaku iya komai ba saida izinin wanan mutumin.
Saidai ku a wajen ku hakan biyayyane a gareshi wanda ba haka bane tsananin karfa
ce dake tsakanin ku dashi yanzu dai idan Allah ya maida ku gida lafiya ku san yadda
kukayi da mahaifiyar ku takai wanan sadakan da aka umurce ta dayi shine maslahan ku
dasu haka shima abinda yayi a kanku din duk zai karye.
Kofa habu ya duba kamar kawu din na tsaye yana sauraronsu yaji Hardo din yace
wane shi nan ai tuni na hadashi da abinda zai sakashi kwana ba zai taba jin abinda
muke fada ba a yanzu.
Ku saki jikinku kuyi maganan da duk kuke son yi a wajen nan kun dai san baku
tambayeni ba nice naga dacewan in fada maku gaskiyan abinda ke a duhu gareku.
Shiru wajen yayi kafin habu din ya fara kawar dashirun da fadin baba na rasa me
yake damuna haka kudi zasu shigo amma ban iya abin kwarai dasu zasu lalace min
h,,,,,,,,
Wanan sherin wanan kawun nakune da matarsa dake dorasa a hakan aiba halinsa
bane sherin matane matarsa ce matsalan taku tana hassadan da za ace uwarku ta fita
sa,an haihuwa.
Jin zancen hardo sukeyi a wani bakon yanayi da basu taba zato ba a zukatansu wai
kawune da wanan halin hardon ne ke magana yake fadin.
Aishi baffa tsoron Anini yakeyi shine ya saka ya jata a jiki fiye da yar uwarta
don da tana wajen shi har yanzu na tabbatarda sai Anini ta karya duk wani shirinsa
akansu.
Nan ya kwashe tarihin mu kaf yabasu da irin yadda baffa yaci kurwan dan uwansa
mahaifinmu a cewarsu ya gwada na yaran saidai tasu kurwan duk a boye take don duk
aka haifesu sai na boye inwarsu.
Shiko dan uwansa ya samu nasaran samun damansane a cikin abin sha da magariba
sa,an mugun duk wani mugunta da magariba mugu ke aiwatar dashi don a lokacin
mumunai suna gagawan saduwa ne da ubangijinsu sun sake komai a lokacin.
Taurarin Anini yafi duk taurarinsu karfi shi baffan nasa ya sani yau ko katsa ta
diba taba mutum da sunan magani sai karbu ga mutum balle wanan dafa,in mai karfi.
Sai daga bayane suka fahinci wace hardo din yake kira da Anini sunana na gado da
suke kirana dashi a ruggar tamu ke nan.
Zaka samu alheri sosai dan samari zaka ji dadin zabinka sosai koma ince haka
dukkan ku auren ku da yaran nan alherine gareku babba.
Saidai a hada da hakkuri yana fada ya dauko wani dan kullin magani a cikin
jakkarshi ya banye kullin yake fadin habu ya miko mashi hannunsa ya dinga murza
mashi abin a tafin hannunsa yana fadin da bafullace kake sai kowa yasan garakanka a
nahiyar ku amma yanzu kai bansan abinda ka dosa ba.
Hakan yasa Habu sakin murmushi yana ajiyan zuciya hardo na daure maganin Jafar
yace nifa hardo saida hardon yayi murmushi yace wai ta Allah ta isheka bari dai
kagani kofafinka zasu bude nan ba da jimawa ba da zaran kun hade da matar taka ai.
Ai wanan baiwan taka yaja maka haduwa da hadadrun da kake fuskanta saidai Allah
na karekane don ibadan da kake dashi hakama mahaifiyar ku.
Duk da ana bata karfa kullum amma bata yarda tayi sakaci da ibadanta ba wanan ne
ubangiji yake kwato ku har zancen dan kabilan ibon daya jefeshi a kafa ya kumbure
saida hardo ya fada masu da zancen kawu dayasa suka kara shiga natsuwansu akanshi.
Kusan dai raba dare sukayi a wajen hardo din koda suka koma masauki sun samu
kawu yana ta sharan barci ba kwanciya sukayi ba alwala suka dora kowansu ya tayar
da nafila.
Washegari dasu akai sallah asuba a ruggan an idar jama,a zasu watse hardo ke
fadin akwai daurin aure a kofan gidanshi da karfe bakwai na safiya.
Gabadaya kowa yayi mamaki dajin sanarwan hardo din inda suka fito da mamakin
hakan sam basu kawo cewa sune da auren ba don gidan hardo gidan jama,ane.
Hakan yasa suka dakata da tafiyan don kara gasu hardo din sai da akazo daurin
aure ne abin ya basu mamaki da hardo ke fadin kawu ya matso ya amsawa dansa auren
Anini din.
Sukuma sune waliyan amarya su kawo sadaki dubu hamshin daga garesu kowansu yayi
mamakin hardo nan danan habu ya kirgo dubu dari ya mika a matsayin sadakin hardo
yace baiki ba amma jafar ya bayar da kansa yake so don shine mai aure.
Ya saka hannu ga aljihunsa ya ciro dauri biyu na yan dubu guda ya aje a gaban
hardo din ka shiga hidimar daurin aure kamar yadda sharia ya gada.
Kamar ance habu ya dago kai ya kalli kawu yayi mamakin yanayin daya hango kawu a
cikinsa ya dan radawa J din daya dubi yanayin kawu din a lokacin.
Anyi lafiya an watse sai lokacin sukaje godiya wajen hardo nan yake fada masu
cewa idan sun koma sun saka ranan tarewa sai ummah ta bugo waya mata suje ayi bukin
acan wajenta kaduna tunda tana kusa dasu shidai yayi nasa na uba a nan.
Haka suka bar rugga cikin jin dadin halarcin hardo garesu suka nufo gida cike da
farin cikin sa,ar tafiyan tasu zuwa ruggan mu.
Har suka iso gida ba wanda suka fadawa ga abindake faruwa tsaraban da suka dawo
dashine irin na wajen mu yasa Yanda tambayan ga kaya kamar na wajen mu dai ?
Yana daga kwance yake fadin daga can suke ai har can din muke hardo ya hadomu
dasu akawo maku.
Yanzu yaya Habu zaku rugga shine baka fada min na bada sako zuwa wajen hardo ba
saidai naji kunje kawai kun dawo hannu sake ?
Waya fada maki hannu sake mukaje maria kinsan koni bankai abuba J zaikai don bai
saba zuwa waje haka hannu sake ba,shi.
Tashiga juya abin da mamaki saidai babu daman magana don haka ta kyaleshi ta
shiga kawar da kayan zuwa kitchen dinta.
A part din iya kuma washegari da aka shigo da tasu tsaraban take fadin kasan
fulani kukaje ke nan daga zuwa tafiyan wuni sai kuma kwana haka matar dauda ta
ishemu da waya bataga mijinta ba.
Kamar wani yaro kuma yaran matanku basu damu kamar yadda ita ta damu ba ni
Hansatu na rasa wani irin so takewa dauda haka har tsufa.
Jafar ne ya shigo cikin wani dinkin shadda mai maiko ga laushi da santsi kallan
ruwan konanen kuka sai kamshi dake tashi a jikinsa ya kafa hular data dace da kayan
da bakin takalma half cover ta maza
Ikon Allah wanan shigafa haka Jafaru sai kace wani ango dakai can kana zuba
kamshi ya washe baki kafin ya kai zaune yana fadin ai ango nake Iya tsohuwa.
Kema dai shigar tawa ta burgeki kenan iya ina amaryan tawa zataga shigan nan ta
yaba haka kafin ke iya ki gani ki yaba din.
Kunji ja,iri ni ba amarya bace ke nan kakarai ka fada wanan matar taka Nusaiba
taji tayi muna dariya ko ita dai na rigata ganin wanan shigar tunda ita bata yaba
ba.
Ba zata jimu ba iya koda taji din ma ba zata samu hakoran dariya gareki ba a yau
iya don nata ya sameta tunda kin kirani da ango ya fada don ganin irin kallon da
iyar tayi mai.
Itama iyan murmushi tayi tana fadin jafaru na dai gane kamar kana son kara
aurene a yanzu don abinda yaran nan sukai maka ?
Da dai kayi hakkuri dasu hakana don koka kara auren wa yan nan