Showing 231001 words to 234000 words out of 328222 words
Chapter 78 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
Mama ki barshi kawai har mu isa amma sai anyi da gaske don kada hakan yajawo
rikici barin dan faka in sayo mata lemo ko zataso shi nan ya tsaya ya fita naji
mama din tana ajiyan zuciya.
Kodaya dawo bai kara maganan ba har muka isa gida don waya da yakeyi a cikin
harshen larabci mota na tsayawa na sauka na barsu da mama din kodana shigo falon ba
kowa hakan yasa na nufi daki kai tsaye.
Nayi sallama na shiga yana zaune da matanshi ranan Nusaibace tayi girki tana
zaune tana bashi abincin don angamashi late evening sosai .
Ina shiga sukayi min ya jiki shike tambaya da hannu yaya nace da sauki na samu
waje na zauna saida yazid ya shigo min da magani da kayab marmarin da ya sawo muna
mai yawa ya aje a gabana yana fadin.
Ki kula da shan magani likita yace asha na kwana ukku a gani idan bai bariba a
koma Allah ya sauwaka yace zai leka part dinshi ya dawo.
Sai bayan ya tafine anty Asmau take min sannu da jiki na amsa gami da murmushi
ina gyara kwanci shigowan mama tayi muna sannu da dawowa take tambayan yaya jikin
nawa ?
Tunkan in bata amsa ta juya wajen mama tana tambayan me likita yace wahalan
jinyane ko ke damuna sai mama tace anya ban tsamanin hakan gaskiya ?
Don yazid dai akaiwa bayani an kuma auna fitsarina da jinina akai gwaji shinema
ya tsayar damu bamu dawo da wuri ba.
Awon fitsari kuma sai kace mai ciki daga zazzabi Nusaiba ta fada maman tudu ta
amsa da fadin abinda nake tuhuma ke nan saidai ban san me sukace dashi yazid din
ba.
In ma cikin ne dai Allah ya raba lafiya ya kawo masu albarka haba dai sai kace
wasan yara mama don Allah ku bari dai ina zancen ciki yanzu mijinta na kwance
haka ?
Anty Asmau ke fadawa mama haka cikin katse mata zancen da takeyi din ita kuma
saiba cewa tayi haba dai ciki a yanzu haka kuma drama ke nan ai ?
Ta fada tana wani mere baki ta juya zuwa cikin daki ta samu mijinta don itace da
girki a ranan ni dai ina kwance ina jinsu bancewa kowa komai ba.
Saidai a lokacin banda natsuwa don maganganunsu sun fara tsaya min a raina na
fara tunane barkatai a kan hakan ina yanke shawaran nisantan shimfidan yaya a wanan
maran kada wani abu yazo ya auku dani inga boni.
Yazid bai shigo ba sai bayan sallah isha,i ya shigo ya samemu dasu mama sai
anty Asmau yayi min ya jiki ya wuce zuwa wajen dan uwansa dake daki ya shiga ya
samu dan uwan nasa yana sallah ya zauna zaman jiransa.
Bayan ya idarne suka gaisa dashi nan ya zauna suka dan soma hira kafin ya fito
mashi da zancen daya kawoshi wurinshi din da farko cewa yayi dashi.
Ya dan uwa baka tambayeni abinda asibiti sukace game da matar kaba dazun da
mukaje don dana dawo akwai mutane a lokacin kuma maganan yana son in fara kebewa
dakai tukun.
Ya dago ya kalli dan uwan nasa alaman meya faru a fuskanshi yace don gaskiya
gwajin da akayiwa amarya ya nuna tana da shigan ciki na wata daya a jikinta shine
ke bata matsala a yanzu.
Cikin muryansa daya koma kamar a karye ya zaro ido yana fadin kana nufin cikine
da Rahama yazid din na kallon yanayinsa yace cikin gyada kai haka sukace dani gama
takardan daya bada result din nan.
Ya fito dashi ya mikawa yayan nasa dan murmushi yayi ya karba yana bin takardan
da kallo kafin ya tura karkashin filon da yake kwance.
I hope dai kasan da hakan ko kada rayuka su baci daga baya kai kawai ya dagawa
kanin nasa ya mayar da idonsa ya lumshe har dan uwan nasa yaso ya fita.
Saiga mama ta shigo dakin tana fadin ashe ka dawo yanzu naga mota a waje dazun
da kuka dawo ance kuma ka fita yace ehh na shiga garine .
Yanzuma sakamakon asibitin na kawo mashi to maleria ne ko yake damun ta yace a,a
kamar dai cikine sukace ga dai takardan nan hannunshi nabashi.
Ciki ciki name cikinta ke ciwo kome donni ban fahince ka ba ai kayi min magana
haka a dunkule yace mama me kike son in fada maki yanzu tunda nace ance shigar
cikine da ita yake sata zazzabi haka ?
Cabdi jam ciki ciki fa ita kuma yar nan a ina ta dauko ciki kuma a wanan lokacin
badai cikin Jafaru bane ko da sauri Yazid din yace wa,iyazu billahi mama ke kike
wanan maganan kuma kanar wace bata da aure mama ?
Hakan ya jawo hankalin mu a falo harsu mama suka taso da sauri zuwa dakin suna
shiga yazid na fitowa mama na biye dashi a baya.
Tana fadin kuji min wanan zance don Allah wai yarinyar nan cikine da ita ashe
take wanan laulayin haka ina Rahama din takene wai ?
Kiyi mata me zuwa zakiyi ki tambayeta dubu ta yaya ta kwanta da danki kome kike
nemanta kiyi mata yanzu ?
Asmau dake zaune a kusa dani dakin mama ta mike tsaye da danta a hannu tayo waje
ta saurara abinda ake fada lokacin mama dubu tana fadin.
Haba iya wanan ai abin a tsaya a dubane yaron nan kwance fa yake rai a hannun
Allah ta yaya zamu ganta da ciki ace hankali ba zai daga ba kuma ?
To kina da ja da ikon ubangiji ke nan dubu ko kin isa ki hana Allah ikonsa yadda
yaso a kuma lokacin daya ga dama wanan tambayan ba a bakinki ya kamata ya fito ba
har in ana zargin hakan awajen mijintane ya kamata ajishi bake ba ?
Akul naji wanan zancen ya koma fita a bakinki zan saba maki kafin ki shaganta
masu da daga bakinki bake ba kuwa duk wani baji ya fadi wani zancen aibancin daga
bakinsa a gidan nan kan zancen cikin nan zan fito masa a maryamuna ya sanni .
Shiru fslon yayi yayin da mama tace iya baki fahinceni bane gani nayi dai yaron
nan yana kwance haka mama ta ina zancen ciki yafito ?
Baki daddaraba ke nan dubu yarinyar nan da mijinta take kwana ko gadinsu kikeyi
da dare bahaushe yace tsakanin miji da mata sai Allah dama to ki kama bakinki da
zancen nan kinji na fada maki.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
7️⃣3️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Yadda naga dare haka naga safiya a ranan don ko ban runtsa ba har safe tunda na
idar da sallah asuba na dauko wayata ina kiran maria.
Duk da banso hakan ba nasan tana fama da kanta a wanan lokacin saidai haka ba
zaisa ta shareni da yawa ba nayi magana tace mijintane yace ta natsu a waje daya
saboda laluran cikin jikinta da take fama dashi.
Tana dauka na hau kuka ina fada mata cewa ni zan tafi abujane nagaji nagaji ba
zan iya ba hakkurina yana gab da karewa a gidan nan yanzu.
Subbahanallahi meya faru Ramaah ta fada cikin rikicewa ta dora da fadin kun
sake wani rigimane kuma yau din dasu ?
Bamuyi ba zamu daiyi nan gaba kiris don har mama wanan karon zata san halina
tunda bata kaunan mu to wai meya hadakune haka Ramaah ?
Saidai kinzo zakiji na fasa ina kashe wayata a cikin takaici hankalintane ya
tashi dan jin mena fada a lokacin don tasanni da karfin hali tasan halina idan na
rikice kuma.
Hakan yasa ta kira mijinta Habu take fada mai akwai abinda ke faruwa a can gida
don na kirata hankali tashe har ina mata ikirarin cewa zan tafi abujane ko wajen
ummah kaduna.
Cikin tashin hankali yake fadin ohh lord mekuma ya faru matan nan basu bari a
zauna lafiya baga Yazid a gida ba na kuma fada mai yasa ido a kansu.
Bari na kira yazid din naji abindake faruwa zan kiraki daga baya da hakan suka
rabu ya kashe wayan yana dannawa yazid don kira saidai bai dauka sai wajen kira na
ukku ya daga suka gaisa.
Suka gaisa sama sama ya soma fadin yazid meke faruwa a gidanne baka fada min ba
ko dazun munyi waya da kai ai ?
Wani gida ke nan yace nan mana yarinyar nan Rahama amaryan J ta kira hankali
tashe tana kuka yace gaskiya ban sani ba dan uwa .
Amma zan shiga in bincika yanzu habu yace dole akwai abinda ke faruwa gidan don
dai ta kira a cikin kuka dazun nan har sun kare wayan zai kashe yace wait dan uwa.
Kodai akan cikin jikintane suke magana dama nasan za ai hakan saboda jahilcin su
irin na mata amma bari na shiga inji dai ?
Ciki habu ya fada cikin mamaki yace eeh ciki gareta mana kuma na bincika na J
din ne so me zasu tsaya sunyiwa rigima kuma ?
Matarsa ce ba zina sukayi ba don me hakan zai zama abin tashin hankali kuma har
su sakata kuka akan hakan su barta taji da abinda ke damunta mana ?
Ciki fa kace habu a hakan har ta samu ciki dariya Yazid din ya kwashe dashi yace
miji da matane fa meye kakewa mamaki kuma sai habu din yayi murmushi mai sauti yana
fadin no banyi mamaki ba ai amma nayi kabar guy din nan inda kaganshi gaskiya J
yakai dan iska haka ashe kana kwance haka ka dirkawa diyar mutane ciki ka barta a
cikin tashin hankali da surutun mutane.
Bari dai in shiga din inji kome ke faruwa ya daga daga kwancen yana zura
jallabiyarsa a jikinsa zuwa cikin gida.
Duk da bai saba ganinsu hakan a part din da safe ba yasan dole akwai wani abinda
ke faruwa ke nan da gaske saidai ana ganinshi kowa yayi shiru sun gaisa dasu mama
ya nufi cikin dakin inda dan uwansa yake kai tsaye.
Ya jima a dakin suna tare dashi kafin ya fito ya fice daga part din don yayi
nazarinsa baiga wani abin daga hankali daga gareshi ba don haka ya kyaleshi bai
fito mai da zancen ba.
Mama tudu ta sameni a daki ina kwance take fadin wai ba zaki tashi ki fito
bane kina daki tun dazun kin dunkule ai sai hakan yasa baki gane jikin kiba ?
Tsayuwan da tayi a kaina yasa dole na tashi na fito zuwa dakin kwanan mu inda na
samu yaya J din shidaya a dakin yana kwance.
Haka kawai naji ina ganin bakinsa tare da takaicinsa lokaci guda naji gaba daya
ban kaunar ganinsa a rayuwata
Saboda yadda zuciyana yake raya min duk wani kunci da tsana da nake fuskanta a
rayuwa kusan nace saboda shine nake ganin hakan a yanzu.
Banda ganin kutse da katsaladan din shigo masu rayuwa da matansa suke ganin nayi
haka kuma a yanzu suke ganin na yaudaresu ko ina ha,intansa nakwaso ciki a waje
nace shine dashi.
Abu dai da yawa suka taru sukai min yawa a lokaci guda bake ganin gusawa daga
nan din shine kawai mafita a gareni da zaisa in samu sallama.
Ina jin muryanshi yana badaniyan magana dani dana shigo hakan baisa na juyo na
kalleshi ba lokacin na dauki abinda zan dauka zuwa ban daki na shiga.
Nayi kuka sosai a ciki kamar yadda na kwana ina sharban kukan a lokacin gab da
in gama wankan naji zuciyana tana tambayana akan yata din da yanzu shi meye nasa a
cikin zancen nan ?
Da har na hada dashi nake fushi mutumin da ko a kwancen da yake yana nuna ina da
muhinmanci a zuciyarshi aiko bai cancanci nayi mashi hakan a yanzu ba wata kilama
wani abu yake so na shareshi baki kulashi anya kuwa Allah ba zai tambayeni dalilin
hakan da nayi ba ?
Ga mama nasihanta a gareni kullum idan mun kebe shine kada in yarda a ji kaina
da mijina inyi hakkuri dashi dako wani irin hali na daure kada in taba bari a san
tsakanin mu.
Yau kuma sai taji akan abinda ba laifisa ba suji cewa ina fushi dashi har mun
samu sabani a tsakanin mu nasan ranta ba zai taba dadi dani ba.
Kodana fito abin mamaki yana kokarin dagawa daga saman gadon da kanshi da sauri
na isa gurinshi nace kai kuma meye haka idan ka fadifa kaji ciwo.
Maganan kamar an kwatoshi daga bakinsa yake fadin me akai maki meya faru naga
kinyi kuka binshi nayi da kallo nace ina turu baki gaba ni banyi kuka ba.
Ya koma ya zauna yana nishi na juya zan nufi wajen kayana haka kawai aka banko
kofan dakin kamar a cikin fushi duk muka bi kofan da kallo cikin mamakin ko waye ?
Saiba ce tana wani huci a fuskanta tana ganina taja tsuki tana fadin ai duk
abinda mutum keyi a boye Allah naganinsa kuma ba azzalumin kowa bane.
Inma wani kato yaba yarinya ciki take kokarin dafawa mutane sai Allah ya baiyana
maishi ta nufi wajensa ta aje kayan abincin data dauko na karyawa.
Ban kulata ba yi nayi kamar bansan ta shigo dakin bama a lokacin don ko
gaisawan dole da mukeyi da aka tillasta munayi a tsakanin mu bamuyi ba a lokacin.
Kokari nayi na taushi kaina ban kula mata ba na juya na fita bayan na saka
tufafi a jikina nakai kofa take fadin iskancin banza sai asirin yarinya ya tono a
gidan nan.
Azo ana daga muna kai ashe ba class ba aji nakowa clininc cema kowa ya hau ya
wuce hakan data fada yasa na tsaya na juyo ina fadin komai zaman mutum nakowa
ubanki yayi kadan ya shiga wanan clinic din.
Ke dawa kike wakike zagi nace da wanda ya amsa min da ita nakeyi kamar su mama
suna jirace sai gasu sun fado dakin ita da iya.
Kai kai lafiya wai meke faruwa hakane kuma daga shigowan ki nifa irin fadan nan
na cacan baki na kauyanci na fada maku ba a nan ba don bashine a gaban mu ba yanzu.
Har ita ta isa ta zagi ubana ita din me abin banza ke inkina da kunya har kina
da bakin magana banda abin kunyar da kikaiwa kanki din nan ?
Miji yana kwance haka sharkaf kije ki dauko mai cikin shege ki kawo mai zaki mana
mashi don an kiraki da yar iska zagi akayi ko halinki aka fada ?
Ai shine nace da ubanki mukayi iskancin ko don sune manyan gidan yan iskan da
muke zuwa,,,,,,,,
Muryan yaya jafar dake badaniya a saman gado ya dakatar damu duk daidai shigowan
mama da tawaganta yake fadi da karfi ba cikin shege tayi ba nine da kaina nayi
abina.
Yana fada yana kokarin nuna kanshi da hannunsa don a gane me yake fadi to kinji
abinda ya fada dai yace cikinsane abinda yake fada ke nan yayu wani kada kai alaman
ehh kamar wani tsohon kadangare dashi lokacin.
Yana kokarin cigaba da maganan da yake son fada kowa a dakin yai shiru yana
kallonsa yace saiba kiyi hankali idan kika kuskura kika sheganta min cikin nan zan
sakeki ya fada kamar maganar tana kwato mashi a bakinsa.
Haba dai wai meye hakane kin gani idan kika jawo muna wani matsala a cikin
zancen nan wallahi ranki zai baci sosai yaron nan tun farkon maganan nan ya nuna
cikinsane yasan da hakan ba shike nan ba ke meye naki a cikin zancen wai ?
Ciki dai Allah yayi lokacin zuwansa duniya yayi a haka ba wani mahalukin da ya
isa yace kar yazo yau ninaji karfin halin maye da hauka.
Akadara ma bash yayi cikin nan ba ke meye naki a ciki zancen nan yanzu tunda
aurene kawai ya hadaki damu yarinyar nan kina da karfin hali sosai wallahi.
Maman tudu take fadan hakan a cikin hasala iya dake salati tana fadin yanzu
yarinyar nan sheganta masu cikin nan kike kokarin yi ko me ta cabe zancen mama da
fadin.
Yarinyar nan wai hankalinta daya meye a cikin zancen nan ke kishiya tunda dubu
ta nuna kinfi kowa a wajenta har yakai zaki wuce gona da iri ?
Ke Nusaiba ku fita daga nan, na fada maki ai inma ba cikinsa bane ganewa za ayi
tunda ba a bace jinin gidan nan suke ba.
Ni dai nafice tare da nazarin lafazin kowa a wajen nayi koka sosai a ranan daga
baya naba kaina shawara akan zancen sai zuwa karfe ukku ya Habu da yanda suka shigo
gidan.
Ina jin muryansa suna gaisawa dasu mama suna tambayan yaushe ya dawo yace da
ranan nan ya wuce ya shiga wajen dan uwansa.
Ya jima a ciki ya fito yana fadin amma mama abinda yarinyar nan takeyi a gidan
nan yai yawa Yazid shima ya shigo ya sameshi suka hade nan wajen iya da mama din
suna fada muna daki da Yanda alokacin tana faman ban hakkuri.
Habu sai fadi yake ban taba gani kojin irin wanan abin ba su lokaci da sukai
cikin su wayayi kokarin