Showing 12001 words to 15000 words out of 328222 words

Chapter 5 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

Dariya ta kwashe dashi kafin tace waiko ka fara kishi akainane haka da har zaka
ganni kaki min magana wani kallo ya watsa mata na takaici ya karasa fitowa cikin
motan yana facing dinta.
Gata bakace bata shafa mai da matan yanzu suke yawan shafawa jikinsu su canza
kala ba ita tabar bakinta na natural maikyau saidai gaskiya idan ace ta girmeshi da
kusan shekara bakwai zuwa takwas ko goma ba zai musa hakan ba amma kuma wai sonshi
takeyi a hakan ita.
Yana dai son su rabu lafiya hakan yasa yake dan tsayawa ya biyewa shirmenta
wani lokacin idan mutanen arzkin na kansa ayi hai hai a watse lafiya.
Handsome dama ina son ganin ka muyi wani magana naga kai mutumne mai harkan
bussiness so akwai wani brother nawa dake wanan harkan acan porthercout nake son in
hadaka dashi amma kaje kayi tunane idan zaka iya don harkane dake son natsuwa sosai
a cikinsa.
Na yaba da hankalinka da irin natsuwan ka yasa nayima sha,awan wanan harkan ya
dade yana neman dan arewa dayake da amana wanda zasuyi wanan harkan dashi sai
nayima sha,awan hakan.
Kallon ta yayi a tsanake yana karontota a zuciyarshi ba wasa a cikin lamarinta
don haka shima ya natsu ya maida hankali kanta budan bakinshi tambayanta yayi da
why me ?
Sai yaga tayi murmushi ta dan kara matsowa kusa dashi tana fadin you deserve ita
handsome kana da natsuwa sosai wallahi beside kuma ni din ina kaunarka har cikin
raina don haka tunda you are pure baka harkan banza kai nake son friendship din mu
ya zamo zumunci a yanzu dakai.
Ina mai baka shawara akwai alheri sosai da zaka samu a cikin harkan nan har
idan ka rike gaskiya a yadda kake din nan baka sauya zuciyar ka daga baya ba.
Don mutane da yawa a yanzu kudi na canza masu akida saidai idan kayi tunane
tunda kana da contact dina zaka iya kirana naji shawaran daka yanke akai .
Takai hannu ta kamo nasa hannun tana fadin kada ka damu Allah ne ya hadani dakai
abar zancen so yanzu a tsakanin ka daukeni yar uwa a wajen ka.
Zanso ace kaima ka shigo cikin system duniya tanayi dakai kamar kowa amma ta
hanya mai kyau bata banza ba.
Hannun nasu data rike ya kalla tayi saurin saki tana fadin sorry na manta dakai
malam ne ai addinin ku bai yarda da hakan bako iam sorry for this.
Ta sake ta gyara tsayuwa tana fadin ni zan tafi saina jiki nasan ba zakace a,a
by god gra grace don abune maikyau da zai tamakawa rayuwanka.
Nagode yace da ita zanyi tunane akai idan babu matsala zakiji itama godiya tayi
mai suka rabu ta nufi tsadadden motanta dake fake a gefe fara sol mai shegen tsada
da sai wa yanda suka kafu suke shiga irinsa.
Juyawa yayi zuwa cikin gidanjen nasu da ake kira da one milleum quaters anan ne
kuma suka hadu da Meabe din wace ta taba fada mai zamanta a nan na dan lokacine ta
kusa kammala ginanta da zata koma cikinsa very son.
Dutse biyu a lokaci daya zancen wanan kafiran zai tsaya nazari ko zancen da
Saiba ta kirashi dashi zai tsaya duba fadawa yayi kan kujera tare da tallabo kanshi
yana lumshe ido.
Dolene yaje gida ba zai kira kowa ba don ba zai fahinci gaskiyan meya faru ba
gara yaje da kansa ya ganowa idonsa haka kuma duk wace ya kama da laifi akan
mahaifiyarsa zaiyi mumunan sabawa maishi don ya fada masu wanan duk sun sani kuma.
Ba mama Dubu ba har iya da kawu dauda suna da kwakwaran kashedi ga duk iyayyen
nasa daya kafa masu don bai yuyu a garesa su wullakanta mashi iyayyensa shi bai
wullakanta nasu ba.
Haka yake murzan goshinsa da hannuwanshi yana jin wani iri kasan zuciyarshi
zancensu da Meambe na dawo mai akai sam ba zai taba yarda ya jefa kansa cikin
halaka ba.
Mafi yawan masu kudinnan na kabilu kudinsu kudin tsafine don haka shikan ba zaiso
abinda zai tabfba martaban gidansu ba.
Gara ya dogara da dan juya kudinsu da yakeyi tunda ko wanan akwai daukaka a
cikinsa yana tsoro matuka da wanan shawaran da Meambe ta kawomashi.
Da haka washegari ya dauki hanyar gida tunda safe yabar lagos din don baijin zai
iya daukan lokaci baije gida yasan abindake faruwa ba.
Karon farko ke nan daya tsani halaiyar matan nasa da irin fitinansu da suka
kasa kwantar da hankalisu su zauna lafiya a tsakaninsu.
Tsuki yaja yana mai ganin laifinsu duk kansu amma na Asmau yafi don me zata
canza halinta daya santa dashi akanshi.
Yasan Nusaiba zata iya jan fitinan da sai Asmau din takai ga tankawa amma meye a
ciki idan ta shareta tayi haukanta tagama yarasa Saiba wace irin yarinyace mara jin
magana haka wai ?
Hanya ya tsaya ya sai doya manja jan garin kwaki domin iya dake sonshi sosai
saura a can gida yake saya idan yaje wanan ne kawai yake saya a hanya don yafi
sauki da kyau a nan yake tsayawa ya saya.
Baiga Zaria ba duk uban sammakon daya buga sai wajajen karfe tara na dare ya
shigo garin zaria kai tsaye gida ya dosa don dare yayi baijin kuma mama tana tudun
wanda a lokacin yafi kyautata zaton dai tana gidansu yanzu haka .
Haka shima Abubakar sunyi waya da mama take shadai mashi cewa tana unguwarsu
wajen iya don haka shima kai tsaye a can motarshi ya saukeshi da kayanshi ga baki
daya daya sayo Sahabi yana ta mashi sheri akan kayan bai kulashi ba.
Saibace ya sama wajen part dinsu tana waya kala batace dashi ba shima kuma bai
kula da ita ba haka yayi ta jidan kayashi yana kaiwa kofan iya da sukr ciki part
din da yarta mama basu sanda isowarshi ba har yagama jido kayan daga waje cikin
wahala ya shigo dasu lokacin ya koma ya kwankwasa kofan iya din .
Mama Dubu ce ta bude kofan tana ganin danta ta dan murmusa tana fadin ikon Allah
kun karaso ke nan sannuku da hanya.
Daga ciki iya ke tambayan waye tace habu be Allah ya dawo dashi lafiya tasowa
iya tayi tana fadin da daren nan kuke tafe haka Bukar sannunku da hanya .
Karasa fitowa mama dubu tayi tana fadin a,a kaya haka ka zo dasu haka Habu kuma
duk bamuji shigowanka ba sannu da zuwa ta duka ta fara tayashi kwasan kayan zuwa
cikin falonsu iya din.
Saida aka gama kwasan kayan kaf mama ta nufi wajen dan karamin fridge tana
daukowa dan nata ruwan leda karba yayi yana fadin bari naje nayi wanka mama indawo.
Ya fada tare da juyawa bai tsaya sauraren iya dake fadin ka zauna kaci abinci
kafin kaje wanka mutum sai kace agwagwa da son wanka dai juyowa yayi ya dubeta ba
tare daya tsaya magana ba ya fice.
Yana jin yadda Saiba ta kure kida a gefen part dinta zakice wani sha,anin buki
ake a wajanta alkawari yayiwa kansa zai kawar da ido daga duk wani abinda matan
yayan nasa zasuyi a gidan.
Don haka bai tsaya kulata ba ya bude part dinsu dashi da kaninsu dake boarding
school anan suke da dakunoninsu don sunbar can cikin gidan nasu yanzu tun bayan da
yayan nasu yai aure.
Yafito dogon rigan jallabiyansa ya zura a jikinsa ya shimfida sallayan sa ya
tada sallah saida ya idarne ya kula da gyaran dakin da akayi wanda yasan ba aikin
kowa bane sai mama Allah sarki mama ya fada yana lumshe ido.
Can yaji sautin buga kofa hakan yasa ya saurara da kyau ba karya kunnuwansa ke
masa ba don ko nan din ake duka hakan yasa ya mike yana duban wayansa dake
hannunsa.
Karfe goma saura na dare a lokacin don haka ya nufi get din kai tsaye daga ciki
yake tambayan waye .
Aka bashi amsa da Jafar bude min get hakan yasa ya leka yana mamakin yadda akayi
yayan nasa yayi tafiyan dare haka tun daga lagos.
Saida ya tabbatar daya shiga da motan ya mayar da kofan ya rufo ya saka kwado
dan basu da maigadi a lokacin karasawa yayi wajen motan yayan nasa yana mashi sannu
da zuwa.
Motar ya bude ya fito yana amsawa kafin ya daga kai ya kalli part din nasa da
kida ke faman tashi yana fadin wanan kuma me suka samu haka yau ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f


MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
6️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,



HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Kai Abubakar ya kawar gefe daya alaman baima saureshi ba alokacin nufar part din
yayi ya fara dukan kofan cikin hasala nocking ukku yayi masu kyau cikin hasala
hakan yasa Asmau ta daure ta fito tana fadin ana zuwa kafin ta tsaya tana tambayan
waye ?
Ke bude min kofa nine jin muryanshi yasa ta bude kofan da sauri gami dayi masa
sannu da zuwa dan kallon second ya jefa mata ya gane daga barci ta shi a lokacin ke
nan har sun shiga barci.
Ciki ya shiga yana fadin wanan kidan haka fa kamar gidan yan kwaya batayi magana
ba don haushin da taji da dan cikinta an hanata shakat yazo kuma zai tsareta da
tambaya ?
Wurin fridge ta nufa ta dauko mai goran ruwa ta nufoshi dashi bai tsaya karba ba
kai tsaye dakin Nusaiba ya nufa ya tsaya daga kofa yana daga labule.
Kwance ya hangota tayi rub da ciki tana barci sai kanta gwigwiyye da hula ya zame
suman kai yayi wani tsatsaye tsirma,tsirma dashi yaja tsuki cikin takaici.
Takawa yayi zuwa wajen da kidan ke tashi yakai hannu ya kashe kidan duk da hakan
bata motsa ba hakan yasa ya kai mata mugun maka a tsakiyan bayanta ta tashi firgice
tana fadin wani dan ,,,,,,,,
Ganinsa yasa ta soma kame kame tana fadin umm,umm sweet J dama kana hanya ashe
shine baka sanar muna ba ?
Fuska a murtuke yake fadin wanan kidan na meye haka ke wata irin yarinyace
Nusaiba baki ganin kina daukan alhakin sauran jama,an gida ?
Ke shadaniyar inace wai kina yar musulmai da daren nan zaki kwanta min da kida
haka a cikin gida kamar gidan disco don rashin tauhidi a zuciyarki ?
Aiko kira,a kika saka ba zaki kure volume dinsa haka ba don gudun shiga hakkin
wani saidai ki kunna iyake.
Daga hakan ya juya ya fita inda ya hango Asmau a tsaye inda ya barta da ruwa
tana jiran fitowarsa daga dakin abokiyar zaman nata.
Karba yayi kafin yayi niyar zama saman kujeran dake tab da kayan wankin Asmau
data nado waje kwanan su sunkai biyar a wajen bata kwashe ba tana kuma kallon kayan
a wajen.
Tsuki yayi ya fasa zama yana maijin wani irin zafi a zuciyar shi ya nufi hanyar
fita part din saidai yana fitane yaga alaman part din duk an kashe wuta ke nan masu
part din sun kwanta haka ke nufi hakan yasa ya juya zuwa wajen motarshi daya bari
bude bai dauko komai ba sai rufe ko ina da yayi har gidan ya duba yana da tabbacin
Abubakar ya rufe ko ina a lokacin yasa ya koma part dinshi kai tsaye wurin
iyalinshi.
Kallon takaici ya tsaya yana karewa falon dake hargitse zakice ba mata biyune ke
rayuwa a part din ba babu inda baida miskila don da gani falon nan bai samu shara
ba na tsawon kwanaki .
Dama sai ya sanar dasu ranan zuwanshi maigirki takan garje tayi dan kwaskwarima
gyaran sama sama don sunsan sam baya son kazanta yanzune da ya iso zai soma fada
balle wanan zuwan dayayi masu na bazata babu sanarwa.
Don haka babu zancen gyara a wajensu koda ya shigo rasa mai zaiyi a falon yayi
ita Asmau itace ta mike zuwa part dinta ta shiga gyara gado tana kawar da kayan
data tula a ko ina dakin.
Don ta dara Saiba kazanta gaskiya ita dai saiba tana da garjewa ta gyara jikinta
da inda zata kwanta amma wanki da sauran aikin gida sune aiki a wajenta.
Baicewa Saiba komai data hakkince saman gujera tana jiran taji me zaice dasu ko
kuma taga inda zai shiga ya kwana duk da tasan in zancen gaskiya za abi wurin
Asmauce zai shiga ya kwana tunda itace tayi girki a ranan sukaci.
Dama ance mai mata fiye da daya kullum a cikin lissafi yake don gudun fadawa ga
halaka saidai wanda baida tsoron Allah zai iya dulmuye gaskiya yayi son ransa.
Donshine Jafar kai tsaye don yabi lissafi tun a hanya ya gano dakin da zai
sauka kai tsaye ya nufi bangaren uwargida Asmau wace ya samu tana shimfida zanin
gado don shi.
Sam Saiba bata ji dadin hakan ba yana shiga ganin ko dan zama baiyi sunyi yaya
hanya ba bai bata lokaci ko kadan ba sai taji ba dadi sam a ranta ta mike a cikin
fushi zuwa dakin ta.
Yana shiga ya tsaya a kofa ya harde kafan shi a waje daya yana bin Asmau din da
take aikin gyaran gadon a gurguje da kallo a cikin mamaki.
Ta jawo room freshener ta fesa ko ina har zuwa bayi kafin ta juyo gareshi tana
dan sakin murmushi tace dashi bissimillah .
Ajiyan zuciya ya sauke kafin ya motsa a yadda yake ya tako yana balle aninaiyar
rigansa cikin daure fuska tunawa tayi da tabar towels din da yake amfani dashi a
wajenta waje hakan yasa da sauri ta nufi falon da bakowa sai hasken wuta da aka a
kunni ta nemo tawul din ta kashe ta dawo daki tsaye ta sameshi a bakin bayin tawul
din ta mika mashi bai karba sai sunan ta daya kira.
Da Asmau ta yaya zanyi amfani da bayin nan don Allah komai a kazance ke wata
irice saboda Allah ace mace ba tsabta ko kadan kedai baki kaunar ki tsaya ki gyara
koda muhalinkine saboda Allah ?
Ai bansan zaka dawo ba shiyasa ban gyara ba ta fada a sanyayye kallon takaici
yai mata kafin yace au sai zan dawo ke nan zaki gyara ashe ?
Bata daiyi magana ba don tasan jafar yana da bala,in hakkuri da halayensu don
da wanine yadda yake dan gayun nan dashi daya anji kansu a kullum amma haka yake
shanye takaicin su a zuciyarshi.
Abubakar a bangareshi haushi da takaicin yayan nasa ya juya zuwa dakinsa dashi
ya rufo duban lokaci yayi a jikon wayasa shadaya bai rufe ba a lokacin haka kawai
yaji yana son kiran layin Yanda ya gwada ya gani ko zai shiga.
Saidai ya tsaya yana wasi wasin kasan zuciyashi ya kirane ko yabari da safe
baijin zai iya hakan yasa ya danna kiran Allah da ikonsa kuwa yaji layin ya shiga
kai tsaye ta soma kira.
Har ya debe rai da daukanta sai gashi ta daga ta dauka da sallama muryanshi
taji yana fadin baki barci ba ke nan ko kuma nina tayar dake daga barcin yanzu.
Sautin murmushinta yaji tana fadin amincin Allah ya tabba bata a gareka kun
sauka lafiya ko kuna hanya ban zata akwai layinka cikin waya ba ai sai yanzu daka
kirani.
Ke nan baki duba wayan taki ba ko gaskiya ban duba ba kasan mun wuni aikin
gyaran kaya yau da kula da dabbobin baffa da suka wahala a wajen tatsansu da mukai
tayi a yan kwanakin nan.
Au ashe dabban kayi wahala itama sai yaji tayi murmushi tace halan ba rayuwace
da ita ba yadda mu yan adam muke wahala ai itama rai gareta don haka sai mun kula
dasu sosai don ba karamin alheri suka kawo muna ba a rayuwa.
Sanadin kayan da kuka saye muna na samu baffan mu yau har girki yasa mukayi
akaci aka koshi a gidan ko sallah albarka a yau din nan.
Yadda take maganan yasa bai katseta ba don yana fahintar wasu abu daga cikin
zancen datake ta zubawa din a lokacin duk shi bamai yawan son surutu bane amma sai
ya biye mata.
Ya fahinci rayuwan yaran a can yana cikin wahala a hannun yan uwan mahaifinsu da
zaman su ya koma hannunsu.
Suna a cikin matsi da tsangwama babu freedon sam a tare dasu kamar sauran yara
karatunsu da sukayi ya tashi a banza yanzu wace takai matakin karatun Nurse a yanzu
ta koma tana tatsan nono a rugga saboda rashin gata.
Da wanan tunanen ya kwana a ransa har gari ya waye duk da ya dan samu runtsawa
kadan saboda gajiyan dake jikinshi a lokacin na bin dogon hanyan da sukayi tafiyan
zuwa da dawowa haka.
Don shine bai fito ba da safe da wuri saboda bayan sun dawo daga sallah ya koma
ya kwanta barci sai zuwa shadaya saura ya mike ya shiga bandaki ya watsa ruwa tare
da brush din bakinsa ya fito.
Washe gari mama Dubu tana kitchen tana hada masu breakfast sai jin sallaman
Jafar din tayi a kofan kitchen din amsawa tayi tana mashi kallon mamaki da yaushe
ya dawo.
Ya fahinci kallon da uwar ke masa yasa yace na dawo tun jiya da dare ai mama kun
kwanta a lokacin Abubakar na samu ya bude min gida na shigo.
Malam meyasa baku tsoron tafiyan darene wai don haka take kiransa da malam Jafar
kamar yadda uwaye da dama sanadin marigayi malam jafar suna kyautata zaton diyansu
su samu irin albarkansa suke kiran yayansu da malam jafar.
Ai ba da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login