Showing 147001 words to 150000 words out of 328222 words

Chapter 50 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

ta kafa kai tana zuka gyatsan da
yazo matane yasa ta sauke kwalban a bakinta.
Ta saki wani uban gyatsa tana hamdallah ta ture abincin gefe daya Aliyu dake
gefe zaune ya zubawa uwar ido tun bayan shigowanta gidan yake nazarin abubuwa da
dama game da mahaifiyar nasu.
Daki ya shiga yasa mata kira take amsawa tare da juyowa ta hangoshi zaune saman
kujera yana dakon shigowanta dakin.
Saidai bata da niyar tashi daga inda take zaune din don sai hiranta take zubawa
tana bada labarin abinda ta gano da wanda akayi saidai ba zancen rabon gadonsu da
sukayi da yan uwanta a cikin hiran nata.
Daga daki yaron ya kara fadin mama fa sai kanwarsa ke fadin mama yayana magana
dake a dakifa tundazun kallon yar tayi tana fadin ina jinsa me zanshigo daki in
mashi ?
Muna nan zai shige daki yace inzo idan bai iya fadan abinda zai fadi a nan ya
bari har lokacin dana taso yaron yana jin hakan ya mike tsaye ya fito daga dakin
daidai lokacin mahaifinsu ya shigo gidan shima cikin murna da ganinta yana fadin
wai baya batada kada ?
Yanzun nan na fita fa ashe har kun iso mun iso malam mun mun sameku lafiya yaya
gida da al,amura kuma ?
Yana washe baki ya samu waje ya zauna a gefenta yana fadin kunsha zaria dai kam
daga tafiyan kwana ukku gaku sai yau din nan muka ganku ?
Tafiyane ya kama haka mun tsaya saida akai komai a gaban mu na samu na taso
Aliyu dake tsaye dan nisa kadan da bayan mahaifinsu yana mata alama da ido sau daya
ta kalloshi ta dukar da kai ta cigaba da magana da mahaifin nasu.
Ganin bata kula dashi ba yasa ya fice daga gidan kofan gida ya koma ya zauna yana
dakon fitowan mahaifin nasa .
Saidai mahaifin nasa yakubu kamar yasan da hakan a lokacin yaki fitowa daga
gidan suna can matarsa baraka na mashi hiran yadda zama nasu ya kaya a lokacin.
Ya gyada kai yana fadin mena fada maki a baya malamin da naje wajen kafin ki
wuce aiya fada muna zai bayar da kudin ba tare da yayi gardama ba.
Yanzu dai aikin gane gaskiyan da nake fada maki cewa kune mata aka tauye su suna
amfana da kudin ku sun gina kansu sun bunkasa sun barku a cikin wahala.
Idan ba yasan ya samu ba wanan kudin za ace an tarawa wanan uban riban haka mai
yawa ya dade yana moriyan abinsa shi kadai ba tare da kowan ku ba.
Hakane ai kafin naje na samu saratu ta zuga mama sosai har mama ta yarda da
zancenta cewa da dukiyan mu yake wanan abubuwan tunda ba binkcike akeyi kansu ba.
Shima kawu daya zo haka yace da mama din shiya bada karfin gwiwan da har aka
samu aka zauna komai kudin kowa ya fito a cikin mu.
Yanzu kuma ai sai ya samu wanda zaiyi facaka dashi da yake dauka yafi kowa yaron
nan baida kirki ina fada maki baki yarda yanzu ai gashi kin gani dama kyautan rufe
baki yake maku don kada a tambayeshi kudin nan.
Jafaru fa kafansa ya dafa kasa malam har kyautan gidaje naji yayiwa Habu da
Yazid a wajen kufa ya tambaya da sauri tace mu ai matane ba zai bamu gida haka
bakatan ba.
A,a lalai dole ya kawo maku kudi haka masu yawa ya toshewa kowa baki amma ki
rubuta ki aje zai dawo daga baya yana maku dadin baki ku hada kai a bashi yacigaba
da juyawa .
Cabdi yana da wuya hakan don yadda akayi din nan banjin zai karbi kudi a hannun
wani kuma nasa kason ma jiya muke ji da dare wai yace a buge massalacim kofan gidan
mu din nan a tayar da wani Allah ya kai ladan hakan ga baba.
Kaji dan duniya ya fada yana mikewa yau kuma ina mota saratu ta kirani take fada
min cewa wai yayiwa matansa akwatuna da mama dasu har iya na tausan gaba din nan da
maza keyi.
To shi sana,an me yake hakane wai indai ba smogal ko safara yajefa kansa a ciki
ba yake wandaka da kudi haka ya kamata a buncikeshi dai gaskiya.
Ance sana,an mai sukeyi yanzu kuma naji yana fadawa iya cewa yana kai kayan
ma,adaine kasan waje akwai samu sosai ga hakan .
Ni yamace yana son ganina kafin na wuce ban tsaya jiranshi ba na taho abina to me
zai min yanzu tunda hakkina ya fito a hannusa ba abinda ya rage kuma ai ?
Mena fada maki dama kudin nan yake son ya biyoki ya karbe yace ki bashi tunda
yaga kamar kece mai taushi a cikin ku.
Kofa ya nufa yana fadin ni zan fita me za a zo maki dashi a daidai lokacin
wayanta ke haske bata dauka ba take bashi amsa da ba komai saidai dan abu mai maiko
haka dai ?
Tana duba wayan take fadin ikon Allah jafar dinne fa ke kirana yace aina fada
maki zai saka rai ga taki dukiyan ta dauka da sallama tana fadin bari muji me zaice
ai.
Jafar ta ambaci sunanshi yake fadi a bangarenshi Anty baraka kin tafine ban sani
ba ashe saida nazo ake fada min ai kin wuce naso muyi wata magana dake wallahi.
Cabdi nikan gani Gusau ai jafaru da yake tunda safe na taso kasan malam bai son
inyi tafiyan dare yace hakane to an isa lafiya yaya su malam iliya din suke ?
Ta amsa da lafiya yanzu yaya akayi jafaru yace leter on zamuyi magana ai dama
zancen Aliyu naso muyi jin hakan mijin nata yayi murmushi yasa kai ya fice Aliyu
dake kofa ya fado dakin yana fadin uncle Jafar ne mama abani shi don Allah ?
Ya mika hannu ya karbi wayan yana fadin Uncle ina wuni fita yayi da wayan a
hannunsa sukai magana ya gamsu da maganan kawun nasa a lokaci.
Ya dawo da wayan ya mikawa maman nasa yana fadin yace zakuyi magana dashi ya
samu waje ya zauna a gefenta yana fadin.
Mama ina ta maki kwantance da kada ki yarda da duk wani dadin bakin da baba zai
maki kada ki yarda da baba don Allah .
Yana fadin hakan tace babangida banson rainin wayau banson rashin kunya kaine
zaka fada min zancen mahaifinka dana zauna dashi.
Dana zauna dashi da farko har na haifeku kaine kake zuwa ka koya min dabarun
zama dashi din ?
Babangida ka fita min a ido tun ban saba maka rai a wajen nan ba wallahi ina
ruwanka da sha,anina da mahaifinka ?
Kallon mamaki ya bita dashi kafin ya mike baki a laikum ya fice daga dakin har
ya nufi wajen fridge dinsu sai kuma ya fasa ya fice daga gidan baki daya
Alkawari ya daukarwa kanshi ba zai karawa uwar tasa maganan komai ba dangene da
abinda ya hango yana tunkarota kan mahaifin nasu.
Yasan tabbas mahaifinsu dabara irin ta miji da mata yake sonyiwa mahaifiyarsu
gashi kuma maman nasu ta kasa saurareb shi .
Idan ya mata hankaline zai tashi a banza don ba fahinta zatayi ba lokacin saboda
dadin bakon mahaifin nasu daya inma bakinshi wajen tsara mutum don haka yin shiru
da bakinsa yana kallon irin bidirin da suke zubawa a gidan
Tun dawowan mahaifiyan nasu aka tsiro cin dadi a gidan nasu inda baraka sai
barin kudi takeyi shiko malam yana manne da ita yana mata dadin baki.
Alkawari iri iri da labarai sai fitowa sukeyi a bakin mahaifinsu donshi yanzu
Aliyu ya zama kamar makiyinsune a gidan don tun ranan da mahaifinsu yai mashi tas
yana fadin ya facin Aliyu din yana bakin ciki da lamarinsa a gidan don haka zai
dauki mataki mai karfi akansa yaja bakinsa yai shiru tare da saka masu ido ga duk
abinda sukeyi.
Babu zancen za a bashi kudin jari ko wanda akai mai alkawarin in an samu za a
sai mashi offer wajen aiki da mata garin ma,aikantan gwaunati ke sayarwa.
Hakan yasa ya nemi laban kawunsa Jafar ya kirashi yace yazo Zaria ya samu habu
sun riga da sunyi magana a kanshi don haka daya taso daga gidan bai fadawa kowa ba
sai kanwarsu da yace da ita zai tafi ya nemo kudi ya bar garin.
Zarian ya nufo amma kuma ya samu ance Habu don yayi tafiya dole ya juya ya dawo
gida ba tare da bukata ya biya ba.
Inda Habu yana sane yaki bari ya gana da yaron a lokacin cewan Habu idan anyiwa
yaron ai kamar ita Baraka akaiwa don haka taje taci barnan ta a yanzu tunda tace su
diya mazan dakin su basu da taimako ko amfani a garesu.
Don har matayesu sun fisu dara don akan matansu suke mutuwa ya dawo ya samu
mahaifiyar nasu baraka ta dauki kudin daya rage taba mijin nata don ya juya
matasu .



ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/17, 08:36] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

5️⃣0️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Da dare bayan sallah sallah isha,i ina zaune dakina naji dawowan yaya J hakan yasa
dana tabbatar da yashigo na mike na nufo fallo in mashi sannu da zuwa.
Ashe sai lokacin yake shigowa gidan da wata yarinya a bayanshi bayan nagaidashi
na kurwa yarinyar ido ina mamakin in ya fito da ita ?
Shiko ya juya yana fadin shigo mana daga ciki habiba ga maman takima ta fito ai a
sanyayye na furta mai sannu da dawowa yaya ?
Yauwa Rahama an wuni lafiya ya gida wanan yar yaya Ai ce Habiba na dauko maki
rikonta zaku zauna tare a gidan nan.
Na daga kai na kara ksllon yarinyar ina fadin Allah sarki sannu da zuwa biba ko
don ina jin sunnanta a bakin su anty Nafisa.
Ta gyada min kai nace karaso ki zauna mana ina zuwa na mike ruwan sha na dauko
mashi nata a babban gora sai ita dana daukowa karamin gora na hado masu da cups na
kawo masu.
Saidana zuba mai na mika mashi ya amsa yana godiya na mika mata karamin gora da
cup itama tayi godiya ya kurbe ruwan yana lumshe ido.
Zama nayi daga gefenshi ya kallo Habiba din yana fadin to Rahama ga habiba nan
na karbo rikonta a hannun yaya Ai daga yau din nan zamanta ya dawo a karkashina
dake zata zauna nan gidan tare dake da fatan zaki tayani rikonta cikin aminci.
Ya kara maida hankalinshi a kaina kasa nayi da kaina ina fadin Allah ya tayamu
riko yace amin ke kuma habiba ina son ki zauna damu a cikin amana banda wuce gona
da iri banson ko kadan inji wani abu ya fito daga gareki don Allah.
Idan kina da damuwa ki fadawa Rahama ko menene zata sanar dani ba sai kin fada a
gida ba tun yanzu idan kinsan ba zaki zauna damu ki fada in mayar dake in samo mata
wata da zasu zauna anan tare din don banson abinda zai taba min zumuncina da yar
uwata.
Tayi kasa da kai tana fadin zan zauna Uncle yace to madallah sai ki nuna mata
inda zata zauna ya kasance shine dakinta a cikin daku nan can biyu.
Ya mike ya nufi dakinsa na sauke ajiyan zuciya tare da kallon yarinyar nace taso
muje dai kiga dakin duk biyu na bude mata donta zaba ta zabi daya ta dauko kayanta
dake falo zuwa dakin.
Wajenshi na koma yana tsaye yaba kofa baya yana waje na karaso a hankali sai na
fahinci da daya daga cikin matansa yake waya a lokacin.
Ban tsaya ba na nufi bandakinsa na hada mashi ruwan wanka da kara tsabtace wajen
na fito a zaune yake yayi shiru ya kurawa kasa ido.
Ya dago kai ya kalleni nake fadin ga ruwan wanka can na hada maka yake fadin
yana kaiwa kwance yace kina shagwabani da yawa fa Rahama ?
Zan ji daban daga gobe idan ban kusa dake kwana biyun nan kin shagawabani ina
jin nima namijine a yanzu gidansa.
Ko ruwan wanka da nasha sai an bani har kinsa na fara zullumin tafiyan nan da
zanyi in barki duk daga yarinyar nan dana kawo maki amma nasan hakan ba zai tare
komai ba.
Daga inda nake tsaye din na danyi murmushi ina fadin ai gara dai a tafi din a
nemawa iyali abinci yafi zama a gida ko yaushe.
Wallahi har kin tuna min da mahaifin yarinyar nan Habiba ban yake ban labarin
su da taimaka masu da yake sonyi ya kara da fadin yana daga cikin dalilin dana
dauko yar nan don a rage mata wahala.
Idan Allah ya dawo dani lafiya don Allah Rahama ki tuna min a san abinda za a
taimaka masu dashi da zai tallafawa rayuwansu na amsa da insha Allah.
Ya dan yun kura kamar zai mike sai kuma ya koma ya zauna yana fadin ina ganin
dai yanzu ansai duk wani abinda zaki bukata a gidan nan can ma na gama dasu saidai
sun bugo waya yanzu suna min korafi wai ban sayo masu gas ba nace Nura zai zo ya
dauka yakai masu refilling .
Ko har da naku zai dauka din yayo nace nan kan ina ganin ba yanzu ba dan banyi
komai dashi ba idan dai ya kusa karewa ayi min magana yazo ya kai maku koda yake
bari kawai ya sayo exctra ya kawo maku in case .
A take ya bugawa Nura din daya karo mashi exctra a aje ako wani gida har wajensu
mama ya mike yana cire tufafin jikinshi na dukar da kaina kasa cikin kunya ina
mamakin yadda sam bai kunyana shi sai kice mun jima dashi da aure ko mun jima da
sabawa.
Ganin ya shiga yasa na tsunce kayan daya cire na adana a gurguje na gyaro dakin
na fito falo abinci na jera mashi nakaiwa Habiba nata a dakin.
Itama na samu harta sauya tufafin jikinta ta saka wani kodaden rigan barci haka a
jikinta sai hula tana zaune tayi shiru nashigo dakin ina fadin har kinyi shirin
kwanciya ashe ?
Toga abinci nan kici kada ki kwana da yunwa na fito na koma dakina inda na dan
zauna in huta yakai kamar awa daya sai gashi ya shigo dakin.
Yana fadin badai har kin kwanta ke nan ba Rahama ?
Na dan mike ina fadin a,a ina jiran kafito kaci abincine kai nake jiran ka gama
sai in kwanta din yace kinci abincin ke nan ke kai na girgiza alaman a,a.
Ki tashi muje muci abincin ya fada yana miko min hannun shi dolena na kama muka
fito falo duk a tsarge nake kada habiba ta fito ta samemu taga abinda yakeyi din.
Wayarshi daya zamo mai kamar rabin rayuce ta shiga ruri ya dauka yana tsoki yake
fadin ibrahim ya akayine naji wanda ya kira da ibrahim din yana mashi bayani.
Lokacin na samu daman mikewa zuwa kitchen da kayan dana kwashe na abincin da
mukaci din dashi .
Don dole yake sani gaba sai naci abinci kusan rabin ledan da nake sakawa don
shine a yanzu nayi dabaran rage hannu wajen saka abincin.
Har ns fito yana kan wayan a cikin dan fada fada yake bayani inda naji yana
fadin wai me isa yake nufine haka lokacin na fito ya ya futoni da hannu alaman inzo
gareshi.
Dole na nufishi hannuna ya kama ya zaunar dani tsakankaninsa yaci gaba da
wayansa yana wasa da sumar kaina wanda ni kaina kitson ya fara isata lokacin.
Amma shi kuma hakan naga bai dameshi ba illa dadin hakan yake masa gaskiya gyara
wani abune dake karawa ma,arauta daraja a idanun junansu wanda sai a yanzu na
fahinci hakan.
Don yana gama wayan ya kara kai kanshi saman wuyana yana shakan kamshin jikina da
ko yaushe ban rabuwa da hakan yake fadin zanyi missing din kamshin nan naki Rahama.
Jin hakan yasa na kara narkewa a jikinshi ina murmushi don nidai din na kasa
sakewa dashi irin yadda yake min Allah yagani ban san ya zan iya daga ido nace nayi
mai hakan ba a lokacin.
Monday zaki fara fita school nayi magana da Auwal namu kanin Nafisa shine zai
dinga zuwa ya dauke ku har yarinyar nan yana sauke ku a school idan an tashi ya
dauko ku ya dawo daku gida saiki karbi key a hannunsa sai kuma washegari ya dawo ya
daukeku din.
Nagode na fada ya dan yunkura yana fadin ban accout number dinki zan tura maki
kudin komai har na man mota da zaki rike a wajen ki.
Tafiyan safiya sukayi inda yaya Habune yazo ya daukeshi na fito ganinsu zaune
tare suna cika wani takarda yasa na dan koma da baya na lebe a cikin labule ina
gaidashi da kwana.
Lokacin ya dago yana fadin a,a Rahama antashi lafiya ya gida na amsa a kunyace da
lafiya ina su anty Yanda ?
Baki barin kira min mata da yanda ko aikece yanda din yanzu ba Maria ba look
Habu kabar min matana da surutu taji da rashina da zatayi a yanzu kusa da ita zo
Rahama ya fada saidai na kasa zuwan dole saida ya mike ya biyoni har dakin mun dade
a rugume yana lalashina kafin ya Habu yasa mashi kira yana fadin zakabi ta Rahama
wallahi ka rasa jirginka ka fito mu wuce kawai malam.
Dole ya sakeni


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login