Showing 294001 words to 297000 words out of 328222 words

Chapter 99 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Banda niyar zuwa ko wani event a cikin sha,anin bukin donshi ko gyaran jiki ban
tsaya nayi ba amma da nayi tunanen kada ai min girshi naje amin kumshi da kitso da
gyaran jiki don haka a wahalce na wuni a ranan.
Yana can gidan da ake jiransa bayan yayi min kwana biyuna da zaiyi gidan sannan
ya koma can gidan don haka an fara sha,anin bukin yana gidan nasu a karshene zai
dawo gidana har a daura aure yana gidan.
Duk da iya ta dawo gida daga asibiti amma bamu daina saka mata abinci daga nan
ana kai mata ba don surfan tsufa tace abincina kawai take iya ci hakan yasa na dage
ina girkawa da ita ko yaushe.
Kwance nake ina barcin gajiya lokacin da maman tudu ta bugo min waya da basu
ganni gidan wajen taro ba na rasa abinda zance mata karshe dai na fito fili na fada
mata gaskiya cewa ina gudun fitina yasa na zauna gida.
Kada ki hakan yar uwar mijinkice fa ko meye ki shiga koda ba duka ba ki daije a
ganki yafi kice kin zauna gida baki tafi ba ba zaiji dadin hakan da kike nufin yi
ba gaskiya.
Nayi mata godiya barcin da ban koma ba ke nan a lokacin tunda ranan kamune don
haka zanje da yamma ayi kamun dani ke nan sunsa a kofan gidansu na cikin gari za a
hadu zuwa dan wani wajen event a unguwar.
A makare naje wajen don ban fita ba saida na gama har abincin dare don gudun
yamma na fito shiya turo da motarshi aka daukemu na samu a cika wajen sosai amma
ana ganin zuwan duk wanda yazo taron a yadda tsarin wajen yake.
Aminu ne ya jawoni zuwa wajen don haka ya shiga dani sosai inda za a ga
fitowana daga motan ya tsaya kafin na saka kafa na fito a hankali.
Tankar ba ciki a jikina irin kwaliyan dana caba duk da nauyin cikin da nake ji
yana hanani sukuni wanan ban yarda na biyewa hakan ba na lalace don ban bari an
barni baya ba gaskiya.
Yar uwar Asmauce ta fara tabata tana nuna matani kafin saiba ta farga da abinda
suke kallo a wajen.
Nida Biba munsha kwaliyan mu muna fita ya juya ya nemi waje yayi packing a can
nisa kadan da wajen nan gulma ya dan fara tashi ga matan dake wajen wasu na magana
da nice amaryan jafar ai.
Wasu kuma suna zance akan cikin jikina yadda na sameshi a cikin jinya yayin da
wasu ke fadin yanzu ya fisheni daban a cikin matansa nice ke yadda naga dama a
gidan.
Kamar Aminu ya sani yana fitowa ya kawo min key din motan ya mika min don yaron
akwaishi da gudun zuciya sosai bai yarda ace yayi laifi ta bangaren kawun nasa yana
da taka tsantsan sosai wallahi.
Sai a wanan wajen muka hadu da mahaifiyarshi ya fada min tazo kwana ukku ke nan
a lokacin don haka ta taso daga inda take zaune muka gaisa a cikin mutunci da ita.
Wanda nasan ba komai bane yaron nata ya fada mata yadda muke zaune dasu a gidan
ya kawo hakan a yanzu.
Salimace ta taso ta kamani tana min sheri wai ciki ya boyeni ya hanani shiga
mutane koda yake ita ai kyau taga cikin ya kara min na dan harareta ina murmushi.
Wajen zama ta sama min daga inda yan gidan suke ban zauna ba saida nabi matan
yayyunshi su yaya Auwal na gaidasu na dawo na zauna.
Nida biba muna kallon abinda akeyi a wajen hango yar uwata da nayine yasa na
kara mikewa zuwa wajenta muka gaisa take fadin yanzu take cewa idan bata ganni ba
saita biya ta gidan mu ta dubani.
Share zancen nayi na basar ina fadin ina yaran tace suna gidan makwaciyarta ta
barsu duk a cikin filanci muke maganan da ita lokacin.
Na hango Saiba a cikin wani dogon riga tana kai kawo a wajen taron kafin can na
hango tana magana da Aminu sai naga ya nuna matani tana magana kamar da tsawa
dashi.
Wai ashe cewa tayi ya bata key din mota zasuje wani waje su dauko abu yace
makullin yana hannuna kuma uncle yace kada abawa kowa motanshi bayan ni.
Shine take fada kamar ya yace kada a bawa kowa motarshi ita din tafimune data
shiga sai gashi yazo yace in bashi key inji saiba yake mayar min dame tace nace ta
kira mai motan ta fada mashi sannan na bata key din.
A shirye nake dasu nasan hakan plan ne yasa ban bata key din kai tsaye ba da ace
akwai girma da arziki a tsakanin mu sai in bata key din ai kayan mijintane itama .
Amma dana fahincesu saina hana key din yaron ya juya ya koma yana fada mata
abinda nace game da amsan key din a wajena.
Fisge fisge ta soma tana nunani ana riketa daga wajen muna tsaye maria na fadin
kai Rahama ki mike mata mana kafin ta tara maki mutane a nan.
Ba zan bata ba don ba ita ta ban ba wasa wasa sai gashi an taru a kanta tana ta
zage zage wayana dake vibration na dauko a jakkata shine akan layi na dauka a
fusace sai naji yana fadin.
Kina inane ke nace wajen buki mana yace ance saiba na fada dake a wajen don kin
hanata key din mota ?
Au dani take nidai naga tana fisge fisge na zata iska ta hau ai look kada ki
yarda kibawa kowa key din nan idan abin baiyi ku dawo gida kawai don Allah ?
Na zata kin biye mata don ba hankaline da itaba bata duba condition dinki saboda
hauka na cika masu motan da suke amfani dashi tun shekaran jiya yau kuma na basu
kudi su kara mai a cikin motar.
Don tana mara mutunci hakan bai mata ba saita karbi key a hannunki don kishin
tsiya zata gamu dani wallahi dif na kashe wayan ina fadin banjin ka yaya.
Munafuncin maza kawai ai baka fada min kayi masu hakan ba sai yanzu nuna min
yayi naje da motarshi kada in hau motar haya zuwa wajen kawai kuma mu kula mai da
mota kada in yarda inbayar mashi da motanshi ga kowa.
Sai kawai mukaga fada ya koma da salima ga saiba can da nata nan kuma ana fada
da salima abin ya bamu mamaki matan yayyunsu suka shiga fadan salima din ana ta
cacam baki a wajen.
Bamu san meke gudana ba acan din don muna da dan nusa dasu matar yazid da aka
fara fitinan tazo ta samemu muna tare harda ita.
Saida wata kanwarsu yaya matar aurece ita tazo tana fadin bafulata kin yamutsa
wajefa da fitina ga amarya can na fada dake wai zuwanki taron nan bai mata rana ba
ya bata mata buki.
Kishiyarki na fada a dake a barta tazo ta dukeki ana riketa can, nan kuma suna
zaginki da mijinku ashe salima tana wajen ta basu amsa shine shine abinya zama
fitina ya barke a tsakaninsu har ana batun bawa hammta iska a tsakaninsu.
Muryan maria naji a hasale tana fadin Au haka tace ashe, bamu ko sani ba ai ba
zata kara ganin mu ba ai kuwa, koda Rahama tazo wajen nan ba wanda yaji bakinta da
wata,
Ta daiyi da wace ta tayar mata da fitina don itace ta bata mata bukinta ba Rahama
ba watau Rahama itace marainiyar tako ?
Mariyace ke fadin haka a hasale taci gaba da fadin tun zuwana naga saratu na
harare harare a wajen nan, sai sun san dai wanda ya bata masu sha,anin bukinsu don
ba Rahama ba dai kam.
Dani da mariya din da matar yazid muka bar wajen bukin a ranan ne kuma rana ta
farko dana fara jan mota a garin zaria don ko biba ban tsaya nema ba tunda tana
tare da yan gidansu Aminu kuma ya bace a wajen taron.
Saida na saukesu gida na nufo nawa gidan kai tsaye yayi kiran wayana ban daga ba
saboda hayaniya banko ji kiran ba a lokacin yasa ya nemi Aminu .
Aminu din ya kirashi yana sheda mashi na bar wajen bukin da dadewa kodaya dawo
gida ni ya sameni gidan abinda ya fara tambaya shine waya jawoki zuwa gida ?
Nina jawo kaina mana na bashi amsa ya tsaya yana min kallon mamaki baiyi magana
ba ya nufi dakinshi kai tsaye don a gidan yake sai daya gama ya fito ya fita zuwa
massalaci sallah magariba da isha,i.
Ya dawo ina dakina jin shigowanshi gidan yasa na fito daga dakin ina gaidashi
abinci na dauko na kawo mashi falo inda yake zaune yana waya.
Ya harde kafafuwansa a waje daya a mike yana dan jujuyasu yake wayan yana fadin
shi gaskiya yasan dama za ai haka ai wallahi ya fada mata tabar mashi gidansa tunda
bataji meyace da ita kafin ta dawo ba.
Ai ya fada mata datayi kuskuren akan yarinyat nan tace zatayi mata rashin mutunci
ba zai kyaleta ba saurare naji ya tsayayi kafin yace shin mama ana aure dolene ?
Ni dai na kawo yarinyar nan gidan nan yanzu kuma nace ta tafi gidansu tunda basu
da mutunci itafa ta rokeni motan nan banyi mussu ba nax bata key harda kudin mai da
zasuyi jigila dashi.
Don naba Rahama tawa motan Aminu ya kaisu abinda zatajeyi shine kuma zai zama
jidali a wajenta yanzu a bainan jama,a har ana kamata tana barin a bari taje ta
duketa.
Watau bata damu da halin da zara iya shiga ba ko ba ruwanta da cikin jikinta ke
nan ita idan an barta da Rahaman badon ciki ba me zata diba a wajenta ?
Saurare ya somayi na dan lokaci kafin naji yana fadin dole inyi fada mama
cikine jikin yarinyar nan fa mama idan tayi mata illa fa hajan bai shafeni ba ke
nan ?
Sai in tsaya tayiwa yarinyar mutane illa tunda ta kudurta hakan a ranta Rahama
bata taba damuwa dame nake masu ba ita dion banyi mata ba itayi fushi
Kuma ta sani tasan ina masu ai ko ita ba mutum bace koba aurenta nakeyi bane
itama akwai wanda yakai nusaiba wahal dani a cikinsune mama ?
To wallahi ki fada mata duk ta kuskura takai hannu a kan wanan yarinyar again
na barta har abada ke nan a rayuwana tunda ita mutumiyar banzane na fahinci hakan
sosai yanzu.
Tana magana bai tsaya saurara mata ba yacigaba da fada karshema ya kashe
wayanshi yana huci ya ja plate din abinci zuwa gabanshi.
Yau da ace ina yawan korafi akan abubuwan da nake gani kansu ashe da ban samu
wanan shedan ba daga bakinsa a yanzu ?
Ashe yasan nasam komai nunawane banyi a gabanshi sai in nuna komai banji ba akan
harkanshi da matanshi koda sun bugo mashi waya a yana gidana ban yarda na taba nuna
mashi kishin da nake ji kan hakan ba a fili.
Saida yayi cibi kamar biyu zuwa ukku naji muryanshi yana fadin yaushe kika iya
motane ke ban sani ba ?
Ajiyan zuciya na sauke kafin nace dashi ya jima mana tun ban aureka ba na iya
mota lokacin da nake zuwa Abuja hutu anty salma tasa aka koya min driving.
Lalai kin kai bafulatanan asali Rahama amma baki taba nuna min kin iya ba har
nake zancen a dinga koya maki keda wa yancan kafin Allah ya hore min in sayawa kowa
nata ?
To idan na nuna meye faninshi yanzu ai gashi daya kama ka sani kasani din ai,
kuma don Allah kabar sa kanka a cikin zancen mu da matanka don hakan yana kara min
bakin jini a wajen yan uwanka na saya zancen bance mama ba nace yan uwanshi.
Rahama kada in magana ta illantaki don ana tsoronta ita din me har waye Nusaiba
yar iskan banza kawai dama haka mama ke son gani yasa ta takura min sai in dawo da
ita.
A zatonsu idan ta dawo zata kwatar masu wani abu dayafi wanda nayi masu a yanzu a
wajena kyalesu nayi naga plan din nasu basu san waye Nusaiba ba har suke tunanen
hakan a wajenta.
Yarinyar da bata son taga duniya naiwa wani alheri koda kuwa ita mamane da kanta
har inta sani sai mun samu matsala da ita ta nuna nata iyayyen fa don wauta ?
Wai ita suke sa ran tayi masu abinda ban tashi yi akansu ba yanzu kyalesu daga
su har ita jira nake ya fito a tsakaninsu ai wanan kan dole inyi mata kashedi a
kansa tunda bake kadai bace.
Nasan aiba zata iyaki ba tunda sun gwada syn gani yanzu so take tayiwa cikin
jikinki rauni a fahintana shiysa take nemam jidali dake.
Tayi da wani ai nibama zan koma zuwa wajen bukin ba balle ace ga kuma laifina
wanda naje din nan ya isa hakana kuma.
Abinda nayi niya bayarwa zanbawa Aminu yakai masu shike nan a zauna lafiya tunda
basu son ganina a sha,aninsu.
Saboda me ba zaki ba gidantane ko bukin yar uwarta akeyi da zakice ba zaki ba
zaki tafi in takai yar iska ta kara tankawa a kanki kuma ?
Ai baki san Nusaiba bace tayi hakane kawai ta baki tsoro amma komai bata iyawa
na gaya maki ita Asmauce har yanzu bata fahinceta ba.
A,a mai bukin tace munzo da yar uwata zamu bata masu sha,aninsu suna bukinsu a
cikin dadin rai zuwan mu yasa muna son bata mata buki ?
Ita Saratun tace hakana har wani buki bukin da suka sawa kansu karya a kanshi
daga ita har mijin bar yar iska karya yazo ya shimfida masu suka hau suna hauka.
Daga ita har mama kallonsu nakeyi itace fa a matsayin ta hudu matansa ukku itace
yanzu ta hudunshi sai taje ido ya raina fata irin gidan nan ne kuma family house
zai kaita.
Musu kai kaya ai suna can yaya Ai ta kirani dazun nan tana sheda min sunje sunga
abu na daban ba abinda aka fada masu bane ko kayan basu shiga dakin da aka nuna
masu ba a matsayin nata yanzu suna can dai ai na kirasho yace wai bai gama ginansa
bane kiji makaryaci hakan ne daidai da ita yar iska dama sai mai karya irinsa zai
iya kwasanta ai suje can su karata dashi tunda mutumiyar banzace ita.
Wai yaya tana cewa ko za a kama mata haya ni zan kama masu haya ya zauna da
matarshi ke nan duk shekara inbiya ko ?
Shi habibin ashe makaryacine don haka take kiransa da habibi kowa dashi ya
sanshi a fanninta.
Ya amsa yace babba kuwa aini da ganinsa nasan mutumin banzane yanayinsa kadai ya
nuna min hakan a kanshi makaryacine yace shine manager a bankin ashe karyane.
Haka akace mana manager ne na bankin manoma ta kasa karya yakeyi ya fada yana
mikewa yace tadaiyi auren shine burin mu a yanzu.
Sai banji dadin hakan ba don za ayi a dawo ana da an sanine a karshe naja bakina
nayi shiru ban sake uffan ba akan zancen shima kuma ya fada min ne don yasan ba za
a taba jin zancen a bakina ba indai nice.
Can gidan kuma ashe labari yazo masu daga yan jere irin abinda sukaje suka sama
a gidan hakan yasa hankulansu ya tashi ita kuma wawiya bata yarda ba wai ai yace
dama bai gama gina inda zasu zauna ba.
Shiyasa yaso a daga auren amma su yaya Auwal sukaki yarda da hakan sukace ayi
haka dai a wuce wajen.
Karshe dai dole kowa yayi shiru amma mama hankalinta bai kwanta da irin yadda
ina hafsatu ta labarta mata komai ba har matanshi da yaransa da suka gani.
Hakan yasa ta kirashi take kara fada mata ina shiga dakin naji yana fadin to
yanzu mama ko hakan gaskiyane yaya zamuyi tunda ita tace tana sonshi .
Hakkuri za ayi da fatan zaman lafiya su sauran matan da suke zaune dashi ai basu
mutu ba ka saurareni malam wanan zance abin a dubane tun yanzu.
Mama ba rawan kanta ya kaita ba koma yaya abin yake ai dole dai hakkuri za ayi
yanzu tunda ba za a fasa auren ba.
Ya kashe waya don tunda na shigo na fahinci da ita yake waya na juya zan fice
daga dakin yayi min hannu dana dakata kar in tafi na dawo na zauna don banda
jimirin tsayi a lokacin.
Mama ke nan ta fahinci inda saratu takai kanta hankalinta ya daga a yanzu shine
suke ganin laifin mutane kan anki kara kudi ayi karya niko ko a jikina don ita ta
kanta ta nace sai shi a barta taje ta gani ai yanzu.
Nima wallahi na damu irin hakan babu dadi ai maka karya sai kaje ka samu ba haka
abin yake ba kuma babu yadda zakayi an riga da anyi din.
Sherintane yake shirin cita shiyasa ake son bawa da tsarkake zuciyarsa akan kowa
nan tace dake ai tana yarinya karama ba kwadayin da zai jata ya kaita auren mai
mata koda gudane ?
To, gashi yanzu ita bako mai mata daya ta aura ba mai mata har ukku itace ta hudu
kinga Allah ya ceceta da irin rayuwan abokan zamanki na kazanta kuma.
Ai, Ba,a kula irinsu anty saratu yaya ni harga Allah ta ban tausayi wallahi don
babu walwala ko jin dadi dai a gareta yanzu gidan yawa ai fitinane babba ya
tunkaro ta.
Aita iya makirci sai su saje dasu suyi tayi niko a jikina na jima da sallama
lamarin yarinyar nan a rayuwana tun lokacin da tace da kudin gadon mu nake aure na
sallama lamarinta.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login