Showing 201001 words to 204000 words out of 328222 words
Chapter 68 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
shi bai zama ya fadama damuwarsa
ko wani abin rayuwansa saidai yayi tayin abu noku noku a zuciyarsa.
Ya habu din ne yazo ya wuce mu a fusace ya shiga dakin bai jima da shiga ba
likitocinsa sukazo hakan yasa aka fito daga dakin.
Sun jima a ciki sosai kafin ya habu din ya leko yana kirana hakan yasa na mike
zuwa dakin na samesu tsaye a kanshi na gaidasu.
A cikin harshen turanci likitan ke fadin itace wanan ko ya amsa da eeh ya
kalloni yana fadin madam sannu ko ya kuma mukaji da jimame don Allah wani aiki zaki
danyi muna a yanzu.
Muna son kiyi magana da maigida ko zamuga responding din hakan a garesa kinga in
akwai improvement zamu dan gane musan abinda zamuyi mashi.
Kin gane Rahama ana son kije kusa dashi yanzu ki danyi mai wani abinda zaisa ko
ya dan motsa koya bada amsa ya habu ke fadin hakan a cikin damuwa.
A hankali na motsa zuwa bakin gadon gabana sai faduwa yakeyi suko duk sun motso
kusa sun zuba min idanu sai addua nakeyi a zuciyana.
Hannunsa na koma a hankali na hada da nawa nakai zaune bakin gadon ina fadin
sannu yaya Allah ya baka lafiya na shafo fuskansa sai yayi kamar ya lumshe idanunsa
yana ajiyan zuciya.
Great naji wani likitan ya fada a gefe ki kara yin wani abin madam wanan
bahaushen ya fada gareni na lumshe ido nace dan gyara zama ina fadin.
Yaya zaka kara shan koko ko abinci zakaci suna tsaye kamar sojoji sun kurawa ko
wani part din jikinsa ido wanan karon da hannunsa yayi min alaman don hannun ya dan
motsa yasa na kalli wajen hannun nasa da sauri danaji ya motsa din don hannaye mu
suna harde lokacin.
Sosai suke fadin akwai cigaba insha Allahu in bashi kunu din su gani hakan yasa
na hada dan kunun koko din na fara bashi saidai wanan karon baisha sosai ba kamar
farko.
Suka daiyi dan bayanan su kafinsu fita zuwa inda suka fito aka barni da yaya
Habu sakin dake cewa dani kada ki yarda kina matsawa kusa dashi Rahama ko yaushe ya
kasance kina gurinsa .
Ni zamu tafi wani waje dasu mama kila zamu kai dare bamu dawo ba don Allah ki
kula kada ki yarda da zancen cewa ki matsa a nan din.
Kin dai gane me nake nufi duk wanda ya kawo abinci ko wani abu kada ku bashi
idan bakece kika hado mashi ba a daidai lokacin Saiba ta banko kofa tana fadin.
Ai batafimu ba da za,ce sai ita kadai zata dinga shiga don ana son a nuna mu
bakowa bane za ai muna haka tayi shiru don kallon da yaya Habu din ya banka mata
yana fadin.
Ke kin gane ba ko wani lokacine zaku dinga shigowa daki nan ba haka kuma ba ason
hayaniya a wajensa donshine Rahama kawai sai yaya isah da yaya auwal aka amimce
yanzu su dinga shigowa.
Rahama din tafimune kome ta fada cikin kafeshi da idanu idan ma tafikune ke
zakibawa kanki amsa mu yanzu lafiyansa muka jawa kawai ba wani abin kishin ki ba
can don haka ki kiyayye a zauna lafiya yadda likitoci suka fada din.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join
my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ
[3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
6️⃣5️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Wani kallo tayi mai ta juya ta fita daga dakin bata tsaya ba ta nufi hanyar fita
daga asibitin kai tsaye Saarece ta hangonta ta nufeta tana kiran sunanta.
Ta juyo a hasale tana fadin akan me za ace bamu shiga wajen miji mu ko Rahama
ta fimu ne don kawai tana kanwar matarsa zai dinga nuna muna bambamci da ita ko
me ?
Haba dai kinga haka yana yuyuwa ita kadaine halan da za ai hakan wananma ai
maganam bamzane watafi a cikin halan da zaice hakan ?
Idan bata fimu ba aiba zai fadi hakan ba zaman me zan zauna nayi tunda ba rako
mata nayi duniya ba zo muje ga mama can kada ki tafi idan kin tafi ai taci bulus ke
nan a kanku ?
Jin hakan yasa ta biyo saare din zuwa wajensu mama din inda suke zaune saman
tabarma da abokan zamanta suna tattaunawa kan jikin jafar din.
Mama kinji wai ya Habu kada su saiba su shiga dakin da ya J yake sai Rahama
kadai aka yarda ta shiga wajensa amma banda su ?
Wai meke damun habune haka mama dubu ta fada kafin ta rufe baki mama tace haba
dai dubu tunda kikaji yace hakan ai dole akwai dalili tunda ciwon yaron nan baison
damuwa ko dogon motsi a kusa dashi.
Amma sai ace matansa ba a yarda suje kusa dashi ba sai wace aka so taje din
zata tafi wanan wani irin danyen hukuncine haka yaya ?
Habu din ne ya fito daga dakin da saurinsa hankalinsu ya koma kanshi ya karaso
yana fadin ya isah fa lafiya dai suka tambaya don yadda suka ganshi a hargitse.
Baba Tanimu ne yayi waya akan wani yaje ya karobo wani abu azo dashi banda
lokacin zuwa yanzuni don tafiya zamuyi dasu mama zuwa wajen wani mai magani kuma.
Aiga Auwal can ya dawo ina ganin gida suka danje zai tafi mama ke fadin kai habu
meye hujjanka nacewa yaran nan kada suje kusa da mijinsu sai wace zuciyar ka ya
yarda da ita ?
Ni kuma mama yaushe nace hakan aina fada dole akwai dalili yanzun nan saratu
tazo da wanan tana nuna Nusaiba tace wai kace kada su shiga mama uwargidan su mama
dubu ke fadan hakan.
Mama yaya za a bari suna shiga haka barkatai wajen mutumin dake son natsuwa a
yanzu tashigo tana fada wai ko don me zansa likita su kira Rahama ?
Nace don itace kadai ke zuwa kusa dashi ya gane tazo hakan laifine ko tsoronta
akeji da zata dinga zuwa tana tayarwa mutane da hankali bayan wanda muke ciki
saboda bakin kishi irin nata ?
Bako za a bari ba tunda haka dama jinya ya gada ba kowa bane zai shiga haka kai
tsaye aiko lokacin da Alh ke jinya ke dubu daga ke sai nice muke bayayyan shiga
gurinsa a lokacin.
Jinya abune fa da yake son natsuwa da maida hankali illa iyaka a bishi da addua
Allah ya bashi lafiya ya mike shine abinda yake bukata garemu yanzu.
Ke kenan da kika san hakan ai kin fada iya ta tsoma baki daga gefen da suke
zaune suna saurarensu .
To umma tsoronta za aji tunda ga gaskiya aki fada saboda ana gudun kada zuciyarta
ya baci ita idan tana da tunane ai wanan abin yanzu na kowane bana mutum daya ba.
Ke Nusaiba ki natsu kada ki tayarwa mutane da hankula a nan muna fama da kan mu
da abinda ya damemu ke inkina da kunya ya kama aji hakan a wajen ki yanzu ?
Ina wanda kike fadan kansa shine a kwance rai a hannun Allah idan kina da tunane
har aji wani zance haka a bakinki yanzu kuma ?
Meke faruwane mama ya Auwal yake tambaya bar yariyar nan tana son dagawa
mutane hankali bayan wanda muke cikinsa a yanzu don ance su fito aba majiyanci waje
ya huta take fada da Habu.
Dama naso cewa a rage wanan shigowan da akeyi abar wa yanda zasu tsaya kawai
tunda ba ganinsa akeyi ba zama kawai ake zuwa ayi ta hira a zauna gida abishi da
addua zaifi.
Wanan yarinyar amaryan shi ita damu zamu iya kulawa dashi tunda zuwanta yana da
ma,ana a wajen nan ko dazun ya gane tazo don ya amsa mata adduanta da take mashi .
Kunga gara din tana zama a kusa dashi ko yaushe zaifi mama ta katseshi da fadin
abinda likitocin da habu suka fada ke nan ya zama matsala a gareta.
Ai ba ance kada ku shiga bane hayaniyace ba a so a wajensa yasa aka fadi hakan
amma ku da mijin ku a hana ku shiga ku ganshi.
Dole dai me jinyar tasa idan tana da tunane ai ta bada wuri kuma ku zauna dashi
din tunda jinya shina kowane bana mutum daya ba .
Saiba tana gefe tsaye tana sauraren mama din don a gaskiya zatace wanan matar
tana yawan shige ma lamarinta ko wani lokaci ta gaji da irin halin da mama ke nuna
mata ko yaushe idan magana irin haka ya taso zata nuna itace mara gaskiya a cikin
zancen.
Wani bangare na zuciyarta ya gargade da kada ta yarda ta soma yiwa mama rasgin
kunya duba ga yadda gaba daya family din suke ba mama girma.
Yin hakan zai iya haifar mata da wani matsalan da zai jawo barin ta gidan kai
tsaye donshi tayi shiru kamar tana daukan nasihan da mama din ke mata a lokacin.
Saiga mama din ta koma magana kamar na lalashi a gareta tana fadin kuyi hakkuri
wanan aiba komai bane idan anyi hakkuri duk hakan mai wucewane fatan mu dai Allah
ya tayar da kafadan yaron nan ya samu lafiya ku koma zaman ku yadda kuke shine
fatan mu kinji a dinga hakkuri da kuma saka basira cikin lamari.
Hakan yasa ta danji sanyi a zuciyarta har ta nemi waje ta zauna daga gefe tana
sauraren kowa a wajen .
Har zuwa lokacin dasu mama har iya suka mike suka bar cikin asibitin tare da habu
suka tafi inda ba wanda yasan inda zasu din sai su kadai.
A cikin rashin sanin hakan na fito da wanan kayan nasa da aka cire mashi da
niyar zuwa in wanke su a bakin famfo saidai kada in barshi shi kadai yasa dana fito
na nufo inda suke zaune na dan duka a tsakaninsu ina fadin.
Zanje in wanke kayan nan daya bata ko wata a cikinku zata shiga ta zauna dashi
mama din ke fadin ke nusaiba ki shiga tunda yar uwarki nada goyo.
Kamar ba zata mike ba ni dai na bar wajen na nufi wajen famfo don wanke kayan a
can Maria da salima suka sameni mun jima tare dasu a wajen don dana gama zama
mukayi muna hira dasu duk akan ciwon yaya din.
Maman tudun wadace ta mike ta shiga dakin inda ita da umma inda suka sami saiban
zaune tana waya sundan jima tsaye a kansa suna kare mashi kallo kafin mama din ta
fara magana tana fadin.
Gyara mashi hannun can daya taushe ta dakatar da wayan tana kallon hannun nasa
tace haka na sameshi na zata ko hakan yake jin dadin kwanciya din suka barshi.
Suwa ke nan fa ke yar nan ki iya kanki don Allah abinda ake fadi ke nan kuke
ganin kamar an barku baya shi jinya kula yake so kaba maishi kinga ko wayan nan
bai dace ace kina daga murya haka ba gabanshi.
Wani irin kallon rashin kunya ta jefawa mama din kafin ta mike tsaye ta nufi
wajen hannun da suke magana din tana kokarin dagawa a cikin karfi.
Haba dai yi mashi a hankali mana kinsan jikin ba karfi sai a sannu dole za ai
mashi komai yanzu umma ke fadin hakan a gefen mama din.
Ganin ta kasa dabaran yadda zata dagoshi yasa ita umma din mikewa suka kama mashi
daga shin da zasuyine suka gane yayi lalura a lokacin .
Umma din ke magana tace yanzu yaya za ayi don sai an dagashi gaskiya daga inda
mama take zaune take fadin sai takira yar uwata su dagashi a sauya mashi kayan
tunda ya bata wa yan nan.
Gabatane ya fadi ta yaya zata iya hakan amma bari ta nemo Asmau tagani suma su
nuna tasu bajintan da ake ganin basu iya din.
Fita tayi ta nemo Asmau din ta shigo take fada mata abinda zasuyi abinda Asmau
ta fada shine ta yaya zamu iya daga shi har mu cire mashi wanan kayan Saiba ?
To ya zamuyi su mama sunce mu canza mashi in bamuce haka za a barshi cikin
lalura tunda mazan basu kusa a yanzu kune dai dole a yanzu zaku sauya mashi ai.
Kayan da ya habu din yasa nazo dashi suka dauko sai nan suka tsaya dabara fita
su mama sukayi suka barsu dashi a dakin saidai sun rasa yadda zasu fara tsarkakeshi
balle su sauya mashi kayan jikinsa din.
Ita saiban ce ta fito nemana dole nice nazo a cikin karfin hali na tare da
taimakonsu muka samu aka sauya kayan na goge mashi jiki muka saka mai wasu tufafin
a ranan na kara sheda cewa dan Adam ba a bakin komai yake ba a wajen Allah.
Iya kar dan adam a lokacin da yake a raye shine yake cikin koshin lafiyansa yake
jin kansa dashi wanine ashe da zaran ka rasa lafiyan ka ka rasa komai ke nan a
rayuwanka.
Yau yayane haka ake dagashi kamar dan jaririn da bai taba sanin duniya ba balle
abinda ke cikinsa shine yau yake lalura a kwance har ake kyamar tabashi haka ?
Komawa nayi still na wanke kayan daya bata din na nado wa yan nan din dana
wanke da farko saidana dawo na zauna mama ke fadin waiko kinci abinci yar nan ?
Maria ta kalleni take fadin bansa taci komai ba mama don tunda safe tazo wajen
nan gara dai kici wani abin a cikinki kada ke ma ki kwanta ciwo .
Shi jinya saika daure kana kula da kanka kaima in ba haka ba sai anyi haihuwar
guzuma da kwance uwa kwance.
Ki duba ko zuwan nan yan uwanki naga sunsha su lemo da kayan sanyi kada ki yarda
ki bari ciwo ya kasheki hakan ba damuwansu bane su .
Kece dai din a tsaya don sauya masa tufafi ita mai fadan gashi ta kasa mashi
komai amma don daurin gindin iskanci nan tazo tana muna sababi dazun .
Yanzun gashi don bata da kunya ta kasa daukan kayan ta wanko ina nan iskancin
nan ba zan lamunceshi ba idan ta samu dubune tana juyata yadda take so niba zata
sameni hakan ba .
Yaya da dai kin saka masu ido don koda kikace su sauya mai kaya ta kuma daina
daga murya bakiga irin kallon da taimaki ba ?
Amina na sani sarai shiyasa nake son nayi maganin rashin kunyar yarinyar nan a
wajen nan tea maria ta hado min mai zafi ta ban nasha don haka mama idonta yana a
kaina.
Su ummah da mijinta da maria ta kira a waya ta sheda masu halin da yaya J din
take ciki suka taso daga kaduna da yaransa maza biyu suka zo ganinsa.
Mun jima dasu a cikin dakin yayin da saiba din tazo ta zauna ta kafemu da idanuwa
saikice taji labarin zamu bashi wani mugun abinne da bata yarda da hakan ba.
Koda suka fito donsu wuce mun jima da ummah tana bab magana banda kuka ba
abinda nakeyi shima mijinta haka ya ban baki danayi hakuri hakan jerabawane a
gareni.
In dage da addua da rokon Allah ina nema mashi saukin hakan a wajen Allah inda
ummah take fadin sunyi magana da Hardo yace akwai abinda zai turo muna zuwa gobe.
Sun tafi ina jin kamar kada su tafi su barni a cikin wanan halin dana tsunci
kaina a cikinsa don gashi ina kallo farin cikina a cikin wanan halin .
Haka anty Barakha ta iso zuwa yamma itama inda tasha kukanta tare da nuna
alhininta ga halinda dan uwan nata keciki nice na debo mata abinci ta samu tayi
sallah ta zauna taci suna zancen da yan uwanta mata su salima da saare.
Gudu kawai ya habu ke shegawa tun suna dan hira a motan tsakanin iya da yayanta
har yakai duk sunyi shiru saboda tafiya da nisan wajen da suka dosa din.
Sai iyace da tayi barci ta tashi take fadin kai Dauda a ina kasan wanan wajen da
har kazo a lokacin ?
Iya me nema ai baya ganin nisan waje idan yana da bukata nima wata yar uwar
Hafsatuce ta nuna min wajen don ita wajen zuwantane a lokacin.
Hafsatu ke mata hiran ita halima shine tace da za aje wajen za a dace don ba
wanda yajen bai dace ba .
Kinji dalilin dayasa na shawarci ita halimatu din da mijinta a lokacin don da a
tare zamuzo dasu sai bai bada goyon bayan hakan ba yasa nazo ni kadai a lokacin.
Saidai bayan nazo dinne na fahinci irin aikin mutanen da garama da banzo dashi
ba ashe don ba zai yarda muyi irin abinda akace ayi ba lokacin.
Kinsan halinsa zaice shirkane ko wani abin kaucewa hakan yasa na karbo mata
baki alaikum nakai mata tayi amfani dashi Allah kuma ya kawo rabon.
Kaiya rabon wahala ko tunda lokaci yayi idan akai hakuri ai samu za ayi tunda
komai dan lokacine Allah ya riga yayi tana da rabo don haka ba mahalukin daya isa
ya hana yaran nan zuwa duniya nan.
Don ni tun a lokacin ban so irin wanan abinba dauda kaida matarka kuka kafe akan
hakan har kukafi yar uwar taku damuwa hakan a lokacin
Yanzu ina dadin hakan don Allah abinda a karshe ake wanan irin wahalan yaron
nan Allah kadai yasan irin halin rayuwan da yake tsintar kansa a cikin sa.
Yau har abin yakaishi ga