Showing 165001 words to 168000 words out of 328222 words
Chapter 56 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
bari yaje massalaci yayi sallah
ya mike ashe yana da alwalanshi ya fita.
Bayan ya fita na kwashe kayan naga lemukan sha masu sanyi a ciki har naman kaji
da dai yan abin makulashe su yughut nakai kitchen na adana na tafi sallah.
Bayan isha,i ya dawo gidan abinci nayi mai tayi baiki ba don ya samu biba tana
cin nata a falon ya zauna ya soma ci yakai rabi wayanshi yai kara ina aje mashi
ruwan sha a lokacin ya dauka naji yace gani tafe ya karasa cin abincin nasa ya
mike.
Yake fadin zan je gida wai Asmau ce ke jin jiki nace Allah sarki agaida ita dasu
mama zasuji yace ya kara min saida safe ya fita.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
5️⃣5️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
A cikin dare muna barci ya bugo min waya saidai wayan tana a silent ban samu dagawa
ba lokacin sai washegari ya sake kira har na shirya lokacin naga kiranshi na dauka
a zatona zai tambaya ko mun tashi ko kuma yai min ina kwana ?
Sai gashi bayan mun gaisa yake min albishir din haihuwar matarshi Asmau data
haifi da namiji a cikin dare .
Da murnata nake fadin cikin farin ciki lah anty Asmau ta haihu Allah ya raya
Allah yasa albarka ga yaron yasa mai akidar addini a zuciyar shi ita kuma uwa Allah
ya bata lafiyan shayar dashi sai faman fadin amin amin nagode Rahama yakeyi.
Nace a shafa min kan baby kafin nazo ganinsa yace zan shafo maki baki ganshi ba
bouncing baby dashi kamana wallahi .
Na kwashe da dariyan yake zakice yana gabana a lokacin sai bayan mun gama wayan
nake fadawa Habiba zancen haihuwa tayi wani dunkunkun tana fadin Allah ya raya.
Abinda su a kullum sukaga mutane sai su nuna basu sanka ba sai ka tsaya kana ta
masu dogon kwantance karshe suce owooo ba zasu ba mutum ko ruwan sha ba.
Kai habiba kowa da irin halinsa haka suke su halinsune hakana ai tace Allah anty
shiyasa muka bar zuwa gidan gaidasu amma da ko wani sallah muna zuwa ai mu gaishesu
muka daina.
Shiyasa da akace zan zauna a wajenki na zata halinku daya dasu ai nayi ta kuka
ina fadin ban zuwa maman mu tace in taimaka inzo kada ran uncle ya baci saida nazo
naga ba haka kike ba ashe anty ?
Da farko nazone in kwana biyu in koma sai naga ke kina son mutane kina kallon
kowa da mutunci kai biba watau daba ba zama kikazo yi ba ashe tayi dariya tana
fadin zan zauna ai anty ba inda zanje yanzu.
Shigowan ya Ibrahim yasa muka mike gaba dayan mu muka fita ya sauke kowan mu ya
juyo kamar yadda ya saba muna a kullum.
Yar uwa na taushi zuciyana sosai akan yaya J da matansa ina kuma rokon Allah
daya sassauta min zafin kishi irin namu na mata game da zaman takewan mu.
Alhamdullahi kuma don ance Allah maji rokon bawane duk da abin dai sai a
hankali idan ya kwanto zuciyana ina danjin wani abin lokacin da sauri kuma Allah
zai tamakeni abin ya gushe min a kasan raina.
Don haka tunane na farayi da me zanje idan zani barka don dole dai inje mata
barka kuma zai kasance zuwana na farko tunda na auri ya J wanan zuwan zanga irin
tarbon da zan samu daga kowa dake gidan.
Bayan mun dawo gida na bude akwatin turamena na dauko wani zani daya dan burgini
a ciki na aje saman gado niyata na kara bude na kayan kamshi in hada mata dashi
inkai masu .
Muna kitchen nida biba ne ya shigo har kitchen da ya same mu muka shiga
gaidashi da wuni yana amsawa nake tambayashi maijego yace suna lafiya.
Na karayi mashi barka da arziki yayi godiya ya juya zuwa falo ya zauna a nan na
sameshi nakai zaune a kusa dashi yace a gajiye nake sosai yau banjin zan kara fita
a yau da sauri na juya na kalloshi don nasan ba gidana yake ba da zaice hakan ?
Ban gama mamaki ba ya kara fadin hada min ruwan wanka masu zafi in gasa jikina
dana dawo sallah naci abinci inbdan kwanta in huta.
Sam jiya bam samu barci ba muna asibiti saida ta haihune kusan asuba na samu na
dawo gida ban kuma yi barci ba aka kira sallah na fito haka mutane ke shigowa suna
muna barka da arziki.
Tsam na mike zuwa hada mashi ruwan wankan dayace sai dai zuciyata a cunkushe don
na kasa fahintar manufan hakan.
Saidai ban sani ba ko zai kintsa daga nan gidanne ya wuce can din zuwa anjima
kada in mai mumunan zato yasa na kawar da zancen kasan zuciyata.
Har yaje yayi wanka bai kara magana ba nikan na fito naje maci gaba da aiyu kana
naji lokacin dayake fadin shiya fita massalaci.
Sai bayan isha,i yashigo gidan ina daki zaune a inda nayi sallah ina duba
sakonnin wayata ya shigo ya sameni da sallama dauke a bakinsa.
Na amsa tare da dago kai ina gaidashi yake fadin abinci zaki ban na dan kwanta
kada in fadi a gajiye nake sosai yau wallahi.
Na dai mike tare da taimakonshi daya miko min hannu muka nufi falon Biba nasawa
kira ta fito daga dakin da take ta sameni a kitchen ina hada abincin abincin ta na
bata don yarinyar nada wata dabi,a idan ban bata abinci ba komai yunwar da take ji
bata taba diba taci sai lokacin dana bata din.
Na fito na jera mashi lokacin har yakai kishingide a wajen yana waya saida na
hada komai nayi mai nuni daya fara ci din yaja ruwa ya dauraye hannunsa ya soma ci
ina gefe zaune ya kalloni da alaman tambaya inci mana na kada mai kai alaman a,a
don na fahinci wayan da yakeyi yana da muhin manci a gareshi lokacin .
Zance na miliyoyin kudi yakeyi don haka nayi gudun nayi interrupts dinsa a
lokacin har ya kusa gamawa yana kan wayab ina jin maishi na tambayanshi abinci yake
cine halan naji yace ehh new wife dina ta hada min delicious nake ci yana dariya
yake fadin ko mai nata na bam mamakine ita kamar yadda take ai.
Banyi aune ba naga ya haskowa wace yake wayan da itani yana fadin kinganta nan
yana nuna mata fuskana nayi kasa da kaina cikin kunya.
Yake fadin ku gaisa mana amma bata jin hausa fa turanci zaki mata zance ranan ya
fara jin kalman turanci a bakina da abin ya bashi mamaki matuka.
Har yake tunane wai ko da gaskene munyi zaman rugga da ake fadin munyi kuwa
shifa al,amarin mu yana matukar daure mashi kai sosai wallahi.
Kafirace na gane hakan ta yanayin shigarta da nagani suman dokin dake kanta daya
zubo sai yanayin rigan jikinta kuma dana kara fahintan ba musilunci a tare da ita.
Muka gaisa da ita take fadin gaskiya ina da kyau matuka dole handsome ya rude a
kaina ashe a yanzu baida zance sai nawa a bakinsa meye sirin abin ne wai ?
Koda yake ga sirin ta gani da idonta ai kurciyata yake diba da yake kara mai
karfi take fadin in kara kula da shi sosai don Allah nayi dariya ina mata godiya ya
juya da wayan yana cin nama sukaci gaba da magana dashi duk a kaina daine har
sukayi sallama suka kashe wayan tasu.
Ni kan harna mike ina tattara kayan abincin zuwa kitchen na dawo ya mike yana
fadin a ina yarinyar nan take kwancine da cewa habiba yake tambaya ?
Tare muke kwana da ita a dakina na bashi amsa yace to a dakina ke nan zamu
kwanta ko mu bar mata waje ?
Anan zaka kwana ke nan ya kalloni cikin mamakin da ni yakamata ace nayi mashi
tunda nasan bai gama kwanakin da zaiwa matanshi a can ba tunda na fahinci two two
days ne kwanan namu kamar yadda akasarin musulman hausawa sukeyi a gidajensu wajen
raba kwana a tsakanin matayesu.
Shi da kansa ya koma ban amsa da anan zan kwana tunda kikaji na fada ai ko
akwai matsala da hakan ne ?
Nayi lau da idanu ina rausaya kai nace gani nayi dai baka idda kwanakin ka bane
a can ai tunda kwana biyu kawai kayi a wajensu ?
To anan din da baki son in kwana zan kwana din ya mike ya nufi dakinshi kai
tsaye yana barina wajen dana bishi da kallo marata dake dan yankawa ya kara yankawa
alaman dai period yana gab da zubo min don haka yake min idan na kusa period
akarshen wata.
Daki na koma na kimtsa duk da dare baiyi ba sosai a lokacin saida na gama na
nufi wajen biba dake takure daki kasancewar shi a gidan na samu har ta soma barci
da littafi a hannunta.
Dan bugun ta nayi ta tashi nake fadin tashi kije dakina ki kwanta uncle fa ya
tafine anty naji ta tambayeni ?
Sai nayi dan murmushi nace ba a nan zai kwanta ba yana dakinsa jin hakan yasa
ta mike sai kuma tace da dai kin barni nan din in kwana anty ?
Bazaki kwana a can din ba shiya kwanta tun dazun ai yana dakinsa hakan yasa muka
fito tare zuwa dakin nawa da ban fita ba saida naga ta kwanta na rufo mata kofan
bayan na kashe wuta.
Dakinsa kodana shiga har ya kwanta kamar yadda yace barci ya soma dibansa na
kashe wuta na rufo dakin na kwanta a gefen shi .
Na zata barcin nasa yayi nisa sosai yasa nake komai a hankali don kada in
tasheshi amma me banfi minti biyu da kwanciya ba naji ya mirgino guna yana rugumana
tare da ajiyan zuciya.
Saida ya shaki suman kaina dake a daure don ko kitso ban samu yi ba niyata sai
zai dawo gidana zanyi kitso din da dan gyare gyare sai gashi abin ya zamo min
bambarakwai ban fahinci meke gudana ba a yanzu gidansa.
A yadda daina fahinta shine dole akwai matsala tsakaninshi da saiba har ya kawo
haka kuma dole wanan matsalan babbane duk da ko suna hakan a da can ba fahinta
zanyi ba irin yanzu dana shigo cikinsu dole a yanzu in fahinci hakan a tsakaninsu
duk daba hiransu mukeyi dasu ba dashi.
Kiss yakaiwa wuyana yana fadin I love you Rahama ina son kamshin nan naki sosai
yana min dadi a raina nakan ji kamar bani bane idan na kasance dake haka a yanzu ?
Cabdi jam watau gaskiyane anty salma da malam mu na vocatinal center da sukace
wasu mazajen kamshi tsabta da iya girki ko iya magana yana sa su kasance da mace
har a dauka kamar asiri macen take masu suke rikicewa haka akansu.
Anty Salima da saratu sun taba hira mai kama da gulmanshi a gabana ita saratu
take fadin takan rasa yaya yake kasancewa da matansa yadda yake dan gaye din nan su
kuma san gasu kazamai tun dai Asmau dako wanka yake zama mata aiki koda yana gari
zata iya maimaita kaya guda a kwanaki acewanta wai wankin ne yake mata wuya yasa
bata saka kaya lokaci lokaci.
Sai salima tace ni banga gara ba a dukkansu duk halinsu daya shiyasa sukai abota
a school lokacin don kazantarsu iri dayane wallahi.
Nayi dan murmushi ina juyowa gareshi nace a cikin muryata dake kara rikitashi
love you too yaya J.
Naji ya kara kameni yana fadin really ?
Uhumm na iya fada don sallon daya saukowa jikina a lokacin haka muka samu raya
daren dashi duk da nasan hakkin wata ya dauko ya kawo min amma sanin halinsa nasan
yana da dalilinsa nayin hakan a lokacin.
Washegari daga school naje gyaran jiki don nasan dole koda yamma ko washegari
zanje gidan don haka dole in gyara jikina yadda zan fuskancesu don ba zan yarda
inje masu a yakuce ba su samu abin kushewa a jikina duk da kishiya komai haduwan ki
saita hango muni a jikin ko cikin shigarki.
Kishiya bata taba hango abinda miji ya gani ya auro ki saidai akasin hakan
agareki da zata rike a kamin yakarki wajen miji.
Ni kaina nasan gyaran yayi ba laifi a shagon yazo ya daukeni zuwa gida sai
sambatu yake duk da da farko na hango damuwa a fuskanshi amma muna hada ido dashi
duk bacin ran dayayi dakon ya gushe a fuskansa din lokaci guda.
Ina zama yake fadin nawa kika biya matan nan Rahama ?
Saida na kalloshi nace dubu biyar suke karba sai naga ya bude mota yana fadin ina
zuwa ya fita kai tsaye shagon ya shiga na bishi da kallon mamaki ko me zai masu
kuma ?
Sai gashi tare da matar tana gyara lafayanta zuwa kai tana gyara rufe jikinta
tazo gabana tana dariya tace amarya oga ya kara muna kudin gyara fa.
Kinga sako yakai ke nan shine na fito inyi godiya a gabanki don gobe ki dawo mu
kara cancara mashi ke dakyau fiye da hakan ya shigo motan yana murmushi tare da
gyada kai.
Har da musayan lamba mukayi da ita a gabanshi yaja mota ya tafi sai wani kallo
yake jefo min can yake fadin gaskiya matar nan ta iya gyara sosai Rahama kinga
yadda kika kara fitowa fresh dake don Allah meye sirin da suke maku ne anan wai ?
Kin ganki kuwa kin koma min yar filonki sak dake haka har yafi irin ganin dana
fara maki Allah a ranan dana fara ganin ki haka kawai naji gabana ya fadi duk da a
lulube jikin ki yake da wanan katon hijab din da kike sakawa lokacin ?
Amma saida naji gabana ya fadi sak ke din na dade ina nema a rayuwata saidai a
lokacin wallahi ban kawo komai game dake ba a raina tunda naga kamar Habu yai muna
shinge a tsakanin mu ba yadda zai kasance in sameki ?
Sannan kisan me wallahi duk lokacin da zan ganki sai dabi,un ki sun burgeni a
lokacin don haka nidai kawai kina burgeni duk lokacin dana ganki amma saboda Habu
mijin yarkice bantaba kawo komai a tsakanin mu ba dake irin haka ?
Ashe ke dinma rabotace kedin daice mafalkin rayuwata Rahama sak yanayin ki da
komai naki kalan dana dade ina mafalkine Rahama macen dana mallaka ta kasance a
hakan cikin tsabta da sanin darajan kowa na tare dani ta kasance mai biyayya da
dokokina Rahama .
Sai gashi Allah ubangiji ya kawo min ke a saukake ba tare da wani shan wahalan
komai ba Allah ya duba min kuncin da nake kwana dashi nake wuni dashi yaban ke a
cikin ruwan sanyi.
Wai ace mace don ta haihu ai irin gyaran nan da miji zai shigo yaji dadi amma
ina babu shi Rahama yau saida nayiwa Asmau kaca kaca a gaban mutane.
Wanan ai sai a zageni wallahi sai ace kaina kawai nake gyara na barsu a
wullakance haka idan kai magana kuma ace mutum ya faye fitana.
Zasu gyara ka barsu kawai ka daina fadan dan nan da kake masu a gaban mutane don
Allah yayi tsuki kawai ya maida hankalinshi ga tukin da yakeyi din saida muka shiga
get din gidan nake tambayanshi ?
Yaushe zaka kaini inyi barkane yaya kada ace banje ba ko ina bakin ciki da
haihuwan yasa ban damu ba ?
Saida ya parker mota naji yace gobe baku fita gobe sai ki shirya in kaiku ku wuni
can keda habiba ko daga can idan kun gama zaku dawo in biya daku gidan mu ku
gaidasu mama can din.
Naji dadin hakan yasa nace har gidan yaya Ai sai muje da anty Rukkaiya yace duk
a goben Allah ya kaimu lafiya idan da lokaci sai mu biya ai ku gaishesu.
Wanan yarinyar ma ai taso taje taga mahaifiyar ta don ban tsamani ai ta tafi
tunda tazo gidan nan ko ?
Gaskiya bataje ba tunda tace min ta zata ba haka halina yake ba da tazo da niyar
komawa gidane sai taga ashe ba haka abin yake ba ?
Aina sani ya fada yana bude mota ya fitar da kafansa daya waje yana fadin koda
naje daukanta ai da kuka tafito bata so zuwa nan din ba.
Sai gata ta fito daga cikin gidan da dan murnanta tana dariyan ganin dawowan mu
tana gaidashi ya amsa yana fadin Habiba dagani dai ba zancen komawa gida yanzu ko
anty ta karbewa yaya ke ke nan ?
Tayi murmushi tana boye fuskanta nace tazo ta dauki kaya a bayan mota lokacin ta
juya da sauri zuwa wajen bayab motan ya bude ta kwaso kayan da nake gani kamar na
baby ne yaso lokacin.
Saida tayi gaba yake fadin abokina ya aiko minsu daga kaduna yau saidana biya na
karbo naje daukoki ai nace dama bai wahal da kansa ba tunda ba amfani zasuyi dashi
ba sai dai a jibgesu don basu gyara kansu ba balle yaransu.
Ni dai nace rabon sune don haka abar zancen nan ai saida naje dakina na rage
kayan jikina na fito na hada mashi abincin da muka girka don rana wanda har lokacin
yana da zafinsa saboda kyau warmers din nake amfanin dasu.
Banyi wani girkin dare ba fruit salad da nama shi muka sha muka hada da naman
muka kwanta ni dai ido na kawo na saka kawai ban kara magana ba tunda na fahinci
bai son maganan a lokaci amna