Showing 123001 words to 126000 words out of 328222 words

Chapter 42 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

mai yawan gaske da abinsha na kwalaye.
Daga dakin da muke muna jin su hjy yabi suna guda ganin irin gadan da ake baje
masu a cikin bajinta don duk basu zaci hakan ba.
Daga falo ina jin hjy yabi na kwalawa anty salma kira tana fitowa tace yoo
Salma kinga abin arziki haka yaki karewa a gidan kanwarki ?
Ai nace munga wajen zama mukam kila sai angon ya dawo ya tasamu gaba ya maida mu
gida irin wanan gada haka aiba zamuso komawa gidaba mukan ana kawo muna wanan
arziki haka.
Fadawa yarinyar nan ta kara zage damtse taci arziki tabar arziki a inda ta
ganshi don wanan wajen sakata da walawane ba irin na zubarwa ba.
Ta fita zancen wayan nan matasa nata ta kama mijinta duk macen da take gidanta
ita kadai sai taso saka kishi a kanta kan kishiya tasaka batama da wata kishiya a
duniyan nan.
Yo mai zai dameki yar nan tunda ba unguwa daya kuke dasu ba iyaka kiyi hakkuri
tare da matanshi kika sameshi don haka kada ki yarda kiyi dakon kishinsu a
zuciyarki ki wahala .
Idan yazo miji ya tafi sai an dawo sai kiga an zauna lafiya duk abinda zai masu
ko zaiyi da wata a cikinsu kada ki yarda wai ranki ya baci .
Don haka wasu mata suke wanan yasa ake wahalan aure a yanzu ka samu mutum da
iyalinsa kace saika rabasu da karfi da yaji.
Wanan yasa matan yanzu da yawa basu son kishiya don basu san ko da wace ka shigo
masu ba munji ta soma hauka kada ki yarda saboda da kishiya Allah ya konaki gobe
kiyama ki barta ita tayi tayi duk abinda zatayi ke dai rike Allah da Annabinsa
makami a gareki.
Komai tsiya dai bata tasowa tazo nan sai ranan da kuka hadu in har wani abu ya
haduku nuna mata kawai ke baki da lokacin shirmensu.
Shiko miji da ance yau yana gidan ki ko baya gidan ki kyautatawa a tsakanun ku
kada ki yarda kiyi sanya wajen ganin farin cikin maigidan ki.
Sunyi maganganu masu inganci da in mutum nada hankali zai dauka don babu shege
a cikin zancensu da farko inda daga baya kuma suka koma barkwanci anty salma na
zolayansu da ko a koro masu naman ne ?
Washegari tunda naga suna shiri na shiga damuwa don sammako zasuyi har matan
kaduna su hudu da ummah ta hadomu dasu lokaci daya suka juya tare da tukwaicinsu na
kawo amarya da anty su babba ta mika masu daga ango.

SOUTH AFRICA

Shi kanshi ya kadu iya kaduwa da ganin irin riban daya samu a wanan harkan ta
ma,adanai daya soma tare da Maibei .
Da farko yaki shawaran nata kamar dole tayi mai kan wanan halakan bayan dogon
bayanin yadda abin zai kasace a tsakaninsu.
Maibei tasoshi da arziki a rayuwansu ta kawo mai boyayyen sana,a damu yan arewa
bamu faye daukanshi da muhinmanci ba a nan.
Sai gashi shiga farko da kayansu yayi yaga ya samu abinda lissafin kan mutum ba
zai iya kwatantawa ba wai duk a sunan riba.
Ranan daya kira Meirbe yana sanar da ita irin yadda kayan suka samu karbuwa cewa
tayi dashi ai dama na fada ma saidai ka zama boss ba zaka kara zama a karkashin
wani ba idan har ka gane wanan sana,an.
Ta fita da ma,adaine akwai wuya akwai hadari a ciki saidai amfaninsa yafi ga
mutum yayi mata godiya suka kashe waya.
Bayan satine ya kirata kuma again bayan sun gaisa yake fada mata ya gama komai
yana son ya dan dawo Nageria saboda family dinshi.
Take fadin haba dai family ai donsu ake neman kudin nan sunsan kana wajen neman
kudi me zaisa ka damu ?
Kinsan ina da mama kuma ina da yan uwa meaibe haka kuma matana a ysnzu ukku
nayi sabon aure ina gab da tafiyan nan yanzu haka amaryan nawa ta tare a gidana ban
gari.
What kai at your age kamarka ke da mata ukku gentle man haba haba ina zaka kai
mata ukku a rayuwan ka me kake so ga mata hakane ?
Dariya ya kwashe dashi tace wait woo are you kidding me in wasa kakeyi ka bari
please ina aure dai mutum ya samu mace daya is ok for him sai su haihu tare su dubi
yaransu ?
You know iam muslim my religion accept this for me our prophet comand us to
marry four wives if posible for a man and there is special reward for doing that in
islam .
If you can feed them give them a shelter and cloth them and all there needs
katseshi tayi da fadin is that all you can give a woman my friend stop telling me
this ?
Wai har kana fadin kayi sabon aure for where my friend wace mace zata yarda ka
aureta kana wani duniyan ka barta a gida ?
Iam telling you wallahi ni angone nayi aure kafin na bar Nageria kalman wallahin
da taji ya ambata da suka san musulmin kwarai bai wasa dashi yasata fadin .
Eeee way are you serious my friend ya kara furta wallahi i marry a young fulani
girl but she is schooling now in A B U zaria ,,,,,,
Ta sake katseshi da fadin so you are serious friend who is dis lucky girl that
charm you heart ?
Tayi sa,a data sameka a matsayin miji a rayuwanta duk da ka bata mata tsari don
nasan ba zataso ta zauna a cikin mata haka da yawa ba tana educated ?
Dariya yayi yana fadin mu a wajen mu musulmai wanan ba matsala bane don haka
muka taso muka gani ga iyayyen mu.
Sun dan jima suna hira kafin suyi sallama da juna akan zai kara kiranta idan
tafiyan nasa zai yuyu a lokacin kamar yadda yake so.
Bayan sun gama waya ya zauna yana tunanen zantutukan da sukayi da ita din haka
dinne gaskiya akwai tauyewa a cikin lamarin wani lokaci amma zai iya kokarinsa
wajen ganin bai tauyewa kowa hakkinsa ba.
Yau da ace baida zarahin hakan ya kumayi hakan yasan akwai tauyewa sosai a cikin
lamarin yadda zai daukota ya jefa cikin matansa da kansu har yanzu basu bari ba
balle a dauko wata a hadusu zama a waje daya.
Matan dakowa nasa baida mutunci a idonsu kowa suna masa kallon bai isa ba har
dai Saiba daya dauko wace bai gama sanin halinta ba ta yaudareshi ta hanyar
abokinsa.
Wai kuma yanzu itace mama take nunawa goyon baya don saboda Saratu kome shiya
rasa abinda ya rufewa mama ido har take masa wanan mumunan fahintar ayanzu.
A iya saninsa ya taso cikin yiwa mahaifansa biyayya tun mahaifinsu yana raye har
zuwa kawu da suka dauka mutum na uku mafi daraja a idanusu.
Amma yau sai gashi an wayi gari duk hakan na kokarin ya tafi a banza wajen mama
tunda har take iya zarginsa akan kudin da bai taka kara ya karye ba.
Ya dan murmusa ya gyara zama don tuno ko dai saboda Rahamane har kiyayyanta da
mama ya shafeshi haka amma a iya saninsa ai mama bata taba nuna bata kaunar
yarinyar nan ba a gabansa.
Don ko dan zaman jinyasa da sukayi ya fahinci kamar akwai kyakyawan halaka sosai
tsakanin yarinyar da mama don yadda take yabonta a gabanshi yana daya daga cikin
abinda ya kwadaita mashi yarinyar ta kasance daya daga cikin iyalinsa don ita mama
din data nuna hakan .
Sai gashi kuma abinda bai taba zato bane ko tsamani yake fitowa daga mama din
yasan sun taso mahaifiyarsu na matukar sonsu a rayuwansu.
Mama irin mahaifan nan ne da keda rayuwan da ran yaronsu ya baci gara nasu ya
baci sau dubu a wuni.
Haka kuma akan danta zata iya yin komai yasan da wanan don haka dole akwai wani
abinda ya faru da baisan dashi ba game da mama din.
Koma meye tunda har ba laifi yayi ba kawai don ya auri Rahama zaisa mama ta nemi
tozartashi haka a idon duniya ?
Zaije gidan zai yi kokarin ganin ba a kai ga samun matsala ba tsakanin shi da
mama din ko yan uwan nasa in sha Allahu yasan wajen matsala gudane sai yayi da
gaske akan matanshi don ko bai samu matsala da Asmau ba dolene zai samu da
Nusaiba.
Sau daya ya daga wayanta kafin ya baro Nageria irin ashar din data dinga mai
tace zatayi a gabanshi yasan ba zai lamunci hakan ba gaskiya.
Koma meye yana rokon Allah ubangiji ya kawo mai sauki akan komai ko wani
bangare magana dayace a yanzu itace dole ya jajirce ya kara zama namijin gaske ako
wani fanni.
Yajima zaune yana zancen zuci har tsawon wani lokaci kafin ya mike zuwa ciki
don ya watsa ruwa a jikinshi yana son fita da yamman zuwa wani waje.
ZARIA
Tun bayan tafiyan su anty salma gidan yai shiru duk da Nafisa da Salma suna gidan
amma suna daki suna barci kasa kwanciya nayi na fito na gyara ko ina na gidan sai
kusan azahar suka tashi banga laifinsu ba tunda akwai gajiya a lokacin koni ban
samun sukuni idan ba naga waje da tsabta ba haka yasa na kasa kwanciya na gyaro ko
ina .
Wanka nayi tare da sallah na saka wani atamfa saiki rantse abayane rede made
dinkin ya hadu sosai gashi kayan sun matukar karban jikina.
Kalansu yayi min kyau sosai dama tasan hakan yasa komai ta zabo min abinda
nafiso don sai incema na zabo a cikin rashin sanin cewa nice mai kayan a lokacin.
Ban fito daga daki ba duk da ina jin muryoyinsu a falon sun kuna tv kuma suna
hira saida nayi sallah la,asar Nafisace ta lekoni taga ina sallah take fadin har
la,asar yayi ashe muna nan zaune.
Bayan mun fitone na gabatar masu da dan dabaran da nayi muna don kada mu zauna
da yunwa duk da ban tsamanin hakan akwai abubuwan da zamu iya ci a lokacin.
Tunda ns fito naji salima tana fadin wai kan uban nan wai Ramaah ko dama course
aka kaiki yine Abuja ?
Nifa gaba daya wallahi kin sauya min sai nake kallonki kamar bake ba Allah tun
jiya duk kin sauya min ga sanin da nayi maki ga baki daya kin juye kin zamo min
wata ta daban.
Dan murmushi nayi ina fadin kai anty salima wani irin sauyawa kuma don Allah ni
din daice Rahaman da kika sani a idonki.
Gaskiya akwai drama wallahi na yarda da ake fasin akwai wani rahama a cikin aure
da sai wanda yayi yake fahintar hakan.
Na duka na bude abincin dana aje a gabansu suka dago suna fadin meye wanan
abincine na basu amsa.
Salima dake kishingide ta kalleni tana fadin yaushe kikai wanan aikin Ramaah
nace kuna barci tace wai yadda na gajin nan nima nasan nayi barci sosai wallahi.
Tun shekaran jiya da ya Habu ya kiramu wallahi bamu huta ba muna tsaye ai dole
mutum ya gaji don ma gidan anty Ai muke akwai yan mata a gidan da suka tayamu aikin
.
Wallahi naji dadin kai aikin nan da akayi gidan anty Ai ai kinga yadda take
farin ciki kuwa sai kiran abokan arzikinta takeyi tana sheda masu abin arziki ya
sameta.
Da kikace ta bar komai daya rage a wajenta idonta kamar zatayi kuka a lokacin
tama rasa me zatace a lokacin don mamaki Nafisa ke fadan hakan.
Nafisa anty Ai mutum ce fa tafi mun su anty yar malam sau dubu wallahi baki taba
jin zance ya tashi ace da anty Ai a cikin zance.
Nima ai hakan yasa naji dadi da kika fada a cikin gida cewa yaya yace gidan anty
Ai za ai komai har baki su wuce.
Wai baki ji sakaran nan Saiba ba da nake fadawa iya tana tsaye sai cewa tayi wai
dama ita ya dace aje can tunda taronna yan kauyene ai.
Kuci abincin mana na fada ganin sun bar abincin a bude yana sanyi a lokacin
saidai hakan bai hannusu hiran ba sukaci gaba da hiran yadda Saiba tayi ta iya
shege tana cika baki.
Salima ta kare da fadin saiga shegiya tayi lakwas dataga karyan bariki baki ya
mutu ance bayan zuwan mu nan ai bala,i tasa don wallahi yaya yayiwa kowa bazata ga
auren nan.
Gaba daya ya nunke kowa a baibai don bai bari kowa ya fahinci komai ba su matar
kawu ba a samu kafan iya shege ba wanan karon da bukin maria yaya habu matar nan
tayi iskanci sosai wallahi.
Ta hana komai karshe ta kwashe takai gidanta sukai ta amfani dashi muguwa kawai
ni wallahi nasan itace ke kara yiwa mama fanfo akan komai.
Itama mama ni har mamakin yadda ta sauya nakeyi ni yanzu har tsoro nake ji idan
mun koma gida nasan ana jirace damu mu koma a zazagemu.
Ina gefe daya na takure a waje daya ina sauraren hiransu wanda nake ta auna
abin a zuciya da nice mama bataso komai me nayi mata haka ta tsaneni lokaci guda ?
Sallah magaribane ya tayar damu a wajen nashige daki suna falo nan sukai sallah
ina zaune na kunnu wayata naji karan budan get din gidan muryan maigadin gidan yana
tashi.
Wai ashe maigidan ne ya dawo a lokacin yake mashi sannu da zuwa salimace ta
leko tana fadin ke ga yaya nan wallahi dama ya habu yace kila yau din nan ya iso
ai.
Mukan zamu tafi gida ke ban yau ashe sai lokacin na dago ina fadin haba anty
salima ku tafi gida kamar ya ?
In kun wuce dawa zan zauna kuma a wanan gidan kaji munafuka angonki ya dawo kice
wai dawa zaki zauna inba kina son sai dare yaya ya gargadamu mubi hanyan tudun wada
da kafa ba.
Don wanan kwaliyan haka muddin yaya ya gansa yau wallahi idonsa rufewa zaiyi
yace me kuma ya tsayar damu ?
Na girgiza kai ina fadin anty Salima bamu haka dake fa keda kuma nake samun sauki
a wajen ki kin maye min gurbin mariata yau.
Tayi waje tana dariya na soma jin muryansu suna mashi sannu da zuwa yana amsawa
a cikin muryan nan nasa da dan maganan shi da sauri da sauri yana fadin a,a Nafisa
kuna nan ashe sannuku da kokari fa salima ya akayi kunsha hidima fa.
Can dai na daina jinshi a falon suma hakan saidai baifi ko minti biyar ba kuma
naji yana fadin ya haka kuma ina kuma zaku da daren nan .
Muryan Nafisa naji tana fadin gida yaya wai kada dare yayi muna a nan mu rasa
abin hawa yace gida yin me kuma don Allah ku mayar da kayan nan ba inda zaku yanzu
kamar wa yanda ake kora kuma ina ita Rahama din ?.
Muna ga rasulu na fada karda kirana zaiyi haka gabansu shifa haka yake ashe da
kowa tsatsaye ba ruwansa.
Ina zaune a inda nake na maida hankalina a wayata naji an ruro kofan da sallama
ta dan dago mukai arba dashi naji gabana ya soma faduwa .
Shima hakan yaji gabansa ya fadi a yadda ya hangoni din zaune saman kujeran dakin
na dan dogara jikina ga hannun kujera din da wayata a hannuna.
Ga wani irin ni,inttacen kamshi mai kashe jiki dake masa barazana da zuciyarsa ya
tako har zuwa gabana na dago cikin sanyin murya ina mashi sannu da dawowa .
Ya lumshe ido yana amsawa da yauwa amarya kinsha kamshi ya kika zauna ke kadai a
nan gasu can a falo su ko duk bakuntace har yanzu ?
Kamar yadda ya dake ya nuna ba komai nima hakan na dake na fara bashi mamaki nace
a,a sallah nashigo inyi sai ban fita ba.
Taso kije wai gida zasu yanzu amma nace a,a saboda me zasu gida yanzu daga
dawowata muje falon mu samesu .
Jin hakan yasa na mike tare da daukan dan yalolon gyalena dake gefe daya daga
dagashi sai wani kamshi ke fita na daban a dakin hakan yasa ya lumshe idonshi.
Ina mikewa naji ya cabki hannuna lokaci guda gaba dayan mu saida kowa jikinmu ya
amsa yayi wani yarrr tundai ni da tunda nake babu namijin daya tana ko gwada rike
min hannu a rayuwata.
Inda shi kuma tsaban taushin da yaji a hannun nawane ya dimautar dashi haka muka
fito falon suna zaune tsit a falon sun kurawa tv ido sukaji muryanshi yana fadin.
Ga dai matar gidan na kawo muku tunda kuna son yi mata tawaye ku gudu zuwa gida
Nafisa tace Allah yaya daka barmu mun tafi tunda ka dawo me zamu zauna yi kuma a
nan ?
To ke Rahama kinji sai ki basu hakkuri ni dai ban korar maki suba kada kice don
ni suka tafi na dan kallesu nayi murmushin da nasan zai dagulashi aiko saida
tsikar jikinsa ya tashi nace aiba zasu tafi ba su barni ni kadai.
Bari na kawo maka ruwa yaya nan na zare hannuna daga rikon da yayi min a cikin
dabara na nufi kitchen a cikin wani tako da ban ma san ina yinsa ba lokacin.
Inda ya shagala da kallon bayana ga rigar ta daneni ta baya mazauna da nakan
juyawa anty maria don taji haushi suna boucing a ciki.
Ya zauna yana lumshe ido a cikin gajiya ga wani bakon kasala da yaji lokaci guda
yana sauka mashi tunda yai arba dani ya koma daya sani hakan zai samu taro da
yabar yaran nan sunyi tafiyansu amma yanzu ya riga daya kwafsawa kansa kuma ai.
Ruwa na dauko


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login