Showing 291001 words to 294000 words out of 328222 words

Chapter 98 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Zance ya tabbata kuwa don Nusaiba dai Aminu ya fara fada min yana ganin kamar wanan
dayan matar uncle fa ta dawo.
Don yaga motoci da mata sun shigo sunata guda zuwa part dinsu a hakan kuma
salima ta kiran ita da Asmau da yanzu tun bayan kiran da Asmau din tayi min muke
dan gaisawa da ita sama sama don data kira cewa tayi dani.
A Amarya Rahama dai kin sharemu gaba daya ko kizo gidan nan ki duba yaranki inmu
ba dubamu ?
Nace ban shareku ba anty gani nayi dai ya kamata naje gida na dawo kece
yakamata ace kinzo kin duba jikina ai sai naga ba haka ba.
Lalai kuwa anyi haka to amma ai kinsan halin gidan mu Rahama yanzu da anji nazo
gidanki sai a fassara min abin da wani manufa ta daban shiya ban zo ba.
Anty in baki zo ba saiki turo min yaran ba tayi dariya kafin tace to kinji dai
mutumiyar mu zata dawo ko mama ta matsa wai ta dawo tunda dukkan mu bamu da amfani
kanmu kawai muka sani mu sai yan uwan mu.
Ikon Allah mudin to da wa zamu sani banyan kanmu da yan uwan mu dake kulamu
wanda bai kaunanka ai kaima kayi nisa dashi ni ban damu wani yasoni ba bayan Allah.
Son Allah kadai da Annabinsa nake nema sai mijina ban damu da son wani ko wata ba
can don basu a gabana don Allah anty ki sa masu ido ki daina kula kowa da shirmensu
neman bakinki sukeyi dama aji dadin bata labarin idan ta dawo.
Ta dawo mana ba daina halinta zatayi ba ai saima abinda zai karu a yanzu don
hakani dawowanta bai taba damuna ba anty ni kawai abinda nake so dake anty shine
kiyi hakkuri don Allah.
Ban dai daukeki makiyana ba don zama tare ya hadamu a yayata nake kallon ki har
yanzu naji tana fadin wallahi nasani Rahama.
To kiyi hakkuri abinda kika san baiso ki daina don Allah kema ki zage yadda kowa
keyi a zama daidai ki fita batunsu kada ki biye mata yaran nan sunyi wayau a yanzu
sun fara fahintar komai fa.
Mun jima da ita muna magana har ina mamakin ko nawa ta saka a wayanta lokacin
data dade haka tana magana dani din.
Tun bayan haka muke gaisawa shine a ranan ta kirani take fada min zancen
dawowan Saiba din ita ma na fahinci nufinta so take ta hada kai dani a yanzu ni
kuma ba zan yarda da hakan ba hadin kai da kishiya cutane adaiyi zaman lafiya kawai
kowa ya mutunta juna shike nan a zauna lafiya.
Munyi hakan na kashe wayan tare da dimbin tunane a zuciyana a ranan yaya bai
gari yayi tafiya amma ya kirani tunda safe yana sheda min cewa zai dawo a ranan .
Don yanzu tafiyanshi ba irin na dadewan nan bane da yakeyi a baya iyankashi yayi
kwana biyu ko ukku ya dawo gida.
Duk da nasan tunda Nusaiba ta dawo bai garin don haka idan ya dawo a can zai
sauka donshine ban matsawa kaina da mashi girki ba duk da nice da girki idan ya
dawo din.
Ashe wai hakan plan din Saratu ce na saiban ta tare a lokacin don su bata muna
plan su hadani fada da yaya don dole sun san in anyi hakan zamu samu matsala a
tsakanin mu dani dashi.
Tun yana can ya samu labarin dawowanta din don suna waya yake jin hayaniya yake
tambayan tana ina tace zaria dakinta don ta dawo tun jiya daga haka baice komai ba.
Koda ya dawo din kuma gidana yayo direct ana ruwan sama a lokacin muna daki
nida Biba dake zaune tana assignment ya shigo ita naji tana fadin uncle ya dawo.
Jin hakan yasa nace ina take fadin taji muryanshi a falo kafin nayi wani magana
sai gashi a dakin nawa yana fadin nakan fada maku idan kun shiga ku dinga kula da
rufe gida.
Kasan nan yanzu ba wani sequrity kwarai a yanzu Aminu muke jira ya shigo ya dauki
abincinsa na bashi amsa.
Idan yazo ya kwankwasa mana ko a aje mashi daga waje ana ruwan nan sai mugu yayi
amfani da daman yazo ya cuta maku a raina nace cuta yafi naku kuma ?
Na dan dago nayi mai sannu da zuwa ya amsa yana fadin ya kuke Alhamdullahi na
fada a cikin basarwa ya juya ya fita mai karatu har zuwa lokacin ba wani sakewa a
tsakanina dashi irin baya qda muka dan shaki yanzu duk na daina hakan duk da
shawaran da mutane ke ban wai yana sona don haka kada in nuna abin ya dameni a
bamgarena.
Dole in nuna don yiwa dan cikina gata baka sanin halin mutum ka zauna ya
shanmaceka nasan waye Saiba da Saratu hakama mama da danta.
Don haka ban sanyaya a wanan zance ba gaba daya na kara dagula mashi lissafi
idan ya dauka ni ruwan sanyice zan nuna mashi kalan tafasana a yanzu.
Bafulatana fa nake ta asali ba muna fulani ba zuciya gadan shi mukayi a jinin mu
yake ba ara min akayi ba idan kayi min sai nayima don bamu yafiya kona kara balle
na fili.
Ki tashi idan ya fita saiki rufe kofan nacewa Biba daga inda nake kwance jin
hakan yasa ya dan juyo yana fadin idan na fita ina ?
Nina rufe kofan aidana shigo ko Aminu din bai dauki abincinsa bane baya gidanne
har wanan lokacin biba data mike don barin dakin take fadin ina ganin yana nan don
da aka fara yayyafi yana falo yana cin abincinsa.
Tana fita shima ya fita hakan yasa na mike zuwa kitchen na shirya mai abinci na
kawo falo na dauko ruwa na samu ya fito yana waya naji yana fadin na dawo mana tun
dazun ina nan gidan wajen Rahama.
Yadda ya tsaya sauraren wayar yasa nasan maishi na koro mashi zancene a ciki na
juya naji yana fadin mama wanan kuma ra,ayinane fa bansan da dawowanta a jiya
bani ?
Kai kai kai su mama dubu dai anga lagwai da tsohuwar nan nada ikon kasheni na
tabbatar data halakani ta gama a duniyan nan.
Yanzu uwace ke fada da danta haka akan matarsa a fahintana sunyi mai bazata shima
ya mayar masu da hakan idan Saiba ta dawo a ranan girkina don su nuna min isa to
Allah ya hau dani kansu ga baki daya yanzu.
Da wayan yayi yawa bayan ya kashe aka kara kira naga ya dauka yana fadin na
dawo ina gidan Rahama.
Karshema yaja tsuki ya kashe wayan tashi baki daya ya aje gefe daya yacigaba da
cin abincinsa ba dai wani hiran da mukeyi na zauna ya gama in kwashe kayan a wajen.
Ina zaune kamar ban fahinci meke faruwa ba a lokacin har ya gama na kwashe kayan
bance dashi uffan ba shima haka baiyi magana ba.
Na fito kitchen yake fadin maganina fa da ruwan addu,an da kike ban ban hada ba
na bashi amsa na shige daki na barshi a falon zaune .
Kayan kwanciya na sauya a jikina na kwanta can dare wajajen sha biyu da rabi
barci ya soma daukana sai gashi a dakin yana tayar dani.
A cikin idon barci na bude ido na sauke a kanshi yana tsaye kaina saye da farar
jallabiyansa mai dan hannu yake fadin wai meye haka Rahama kinfa san ina jiran ki
kinzo nan kin kwanta kuma ?
Ido na mayar na lumshe kamar ban san yana tsaye a wajen ba sai jinsa nayi ya
fita daga dakin na soma barci ya dawo ya kwanta a bayana don jaraban maza daya
motsa mai ya kasa rike fushinsa da yakeyi dani ko dai wani abu.
Washegari da safe har muka zauna karyawa bai kunna wayansa ba saida ya fito ya
zauna naga yana kunna wayan kamar ana jiransa a lokacin kira ya shigo.
Tarr naji me take fada lokacin don kusa dashi nake zaune lokacin saibace take
fadin ba sai ka nuna min kafi jin dadin abu kazan yar fulani ba zakai min haka.
Yace ashe kin sani to tunda kin sani kisan matsayinki yanzu kada ki hada kanki
da ita don ita din ba tsaran yinki bace look Saiba mena fada maki game da yarinyar
nan kafin in yarda ki dawo ?
To udan bakiji ba kada kiyi mamaki yau din nan ki kwana gidanku na har abada ba
dai kinga na kyaleku ba kada ki dauka bokan da kike bine aikinsa yaci a kaina karr
nake kallon ku wallahi.
To in kwana mana sai me dama ban saba kwana bane a gidan namu wallahi akan
wanan yar dajin matar taka ba zakai min wullakanci in kyaleka ba Jafar.
Tunda banga abinda tafini dashi ba da zan dawo ka dauki kwanana kakai mata don
ita tafi ko wace mace a idonka yanzu kome ?.
Kwanafa kikace gashi kin ba kanki amsa tafiki komai ke nan ashe kin gane hakan
keda kukace zaki dawo ki zauna zaman yarki ina ruwanki da kwanan da nakeyi da
matana yanzu kuma ?
Zaka dawo gidan ai ta fada a hasale kamar wace idan ya koma zata dukeshi a ranan
ta kashe waya yaja tsuki ya dauki plate din abincin dake gabanshi yana fadin
mahaukaciya kawai wanan ba zata taba canzawa ba tayi hankali ba wallahi.
Wacece na samu kaina da tambayar karya tankar banji me sukeyi a wayan ba da ita
ya dan kawar da kai kafin ya ban amsa da Nusaibace mana mahaukaciyar banza da wofi.
Naja bakina nayi shiru don ba abinda ya shafeni bane zancen har ya gama kamar
kurame haka muka zaune a wajen ba wanda ya kara magana a cikon mu.
Saida ya dan jima ya mike yana fadin bari na leka gidan in dawo ina yaron ki
yakene nace ya fita school tunda safe ok yana da lectures ke nan ko ?
Ban tsaya bashi amsa ba don zuciyana dake famam sake sake a lokacin ko don wanan
mahaukaciyar zan daure in biye masa mu kara haukatata kafin nasan abinyi.
Lokacin kuma na fahinci dole akwai wata a kasa cikin zancen dawowanta gidan dole
a kaina ta dawo ko wani abu amma yadda naji magananta haka a tsaye bawai irin na
wacce tayi nadama bace gaskiya.
Koda ya isa gidan ya samu mama ta hau ta cika don me yayiwa matarshi haka da
wanan zancen ta tareshi da fada ga matarshi ta dawo don ya nuna masu iyakarsu yaje
gidan wata ya kwana ya barta nan ?
Amma dai mama gidan matana na kwana ko da zata dawo wa kuka fadawa dawowanta ga
shekaran jiya din ?
So tunda banda amfani ga da zata sanar min zata dawo ai gara inje inda akasan
darajana ko kai ji nan malam naga yarinyar nan gaba daya ta juyema kai to ka natsu
kasan abinda kakeyi yanzu.
Rahamace zata juye min kai kuma mama ya tambaya fuskanshi dauke da murmushin
mamaki ga maganan mahaifiyar nasa.
Inda mama din tace ba dole ince haka ba tunda kai baka san me kakeyi ba ta ina
ka taba jin anyi hakan itama inba makira bace ai tana da labarin matarka ta dawo
data karbe ka .
Ina ruwanta da zancen dawowan Nusaiba mama tunda ba a unguwar nan take ba ina
zata sani koma dai ta sani ko bata sani ba dai tunda tasa kayiwa wata wullakanci
itama ta saurarinata ai yana tafe.
Mama wai meyasa kike saka kanki cikin irin shirmen nan bafa dake ake zancen nan
ba banga abinda zaisa kina saka kanki irin wanan maganan ba girman ki na zubewa ?
Ooh yanzu don na tsaya gyaran gidanka shine girmana ke zubewa malam to ya tude
karshen zubewa ke nan badai ga yar gwal din matarka zai zube ba kawai to aida sauki
tunda iya nan zai zube din.
Mikewa yayi yana tambaya iya tana can bangaren ne har yanzu salima ya samu ta
amsa mai da tana can yau ta tashi bata jin dadin jikinta tun jiya.
Subbahanallahi ya fada ya dakata yana tambayan ta meke damun iya din take fadin
gudawa tayi sai jikinta ya mutu .
Shine baku kaita asibiti ba mama kuka barta a gida haka amma haka baiyi ba
wallahi ya fada ya fita da sauri zuwa part din da iyan ke ciki.
A kwance ya samu tsohuwar cikin wani hali na ban tausayi da sauri ya kamota
zuwa asibiti shida salima da mama din akaje asibitin dole aka kwantar da ita aka
saka mata ruwa.
Lokacin ya kira yazid a waya ya haushi da fada kan rashin kula tsohuwar da
baiyi ba kuma yana gari fada sosai yayi da kanin nasa yana bashi hakkuri.
Sai lokacin jikin mama yayi sanyi ta shiga kame kame tana fadin wallahi na dauka
irin yadda yakan dan bugeta ta mikene kawai.
Mama bidon Allah yayi iya da tsawon rai mai lafiya ba jikin iya a yanzu ba
komai zaku bata taci ba ya kamata ace ana duba irin abincin da zataci tunda tana da
gatan hakan a yanzu.
Ya bugo min waya a gabansu yana fadin in shirya abinci gasu nan asibiti da iya
an basu gado hankalina ya daga anyi dace nagama abincin rana ke nan na kwashe na
cika kula Aminu yakai masu.
Wanan ciwon na iya ya kwantar da fitinan da akaso tayar mashi wanda shima a
hake yake dasu ashe kan hakan da dare tare mukaje dashi duba jikin iya din don
yazid ya kawo wa yancan da zaizo da matarshi sun duba iya din.
Akwai haske tar a lokacin duk da shigana ba wani shiga nayi ba a lokacin amma
hakan ya tsonewa mama da iyalinta idanu .
Duk dago kai zanyi zan samu dayansu yana satan kallona a cikinsu bamu jima ba ya
soma fadin wa zai kwana a nan din nida Dubu zamu kwana Hafsatun kawu ta fada.
A,a mama ki koma gida abar mama ta kwana don ko maman tudu taso tazo ta kwana
sukace basu son mutane da yawa a nan din.
Da dai ka barmu mun kwana mu biyu din tunda ba a san me dare zaiyi ba a hankali
na fara takawa don barin dakin cike da mamakin hali irin na mama din .
Ke nan tana nufin jinyar mahaifiyarta sai wani ya saka mata hannu a cikinsa
bayan tasan ba shiri bane a tsakaninsu ko banza.
Ya jima a tsaye kan iya ya dago yana fadin bari nakai yarinyar can gida indawo
bai tsaya ba ya fito zuwa wajena ina tsaye na dafa mota ya iso yana fadin muje ko ?
Saida muka soma hanya nake tambaya yaushe iya ta soma ciwo duk ta rame haka yace
waya sani ko yanzu ai salimace dana shiga take fada min da haka zata halaka a daki
ita kadai.
Daga asibiti idan an sallamota nan gidan zan kawo maki ita don ta samu kula mai
kyau don Allah ace abar tsoho da yunwa ga tsufa ga ciwo sai lokacin da akaga dama
za a bata abin karyawa taci ?
Ni dai banyi magana ba har muka isa gida duk abinda zan fada idan ba zagin
mahaifiyarsa zanyi a gabansa ba me zance don laifin duk natane game da hakan
gaskiyaa.
Tunda ya dawo bai koma ba kamar yadda yace don har mama ta bugo waya wai in zai
dawo yazo masu da ruwan zafi a flask.
Yace gaskiya ba zai samu dawo ba don har ya kwanta saboda yana jin rashi dadin
jikinsa.
Hakan yasa tayi fushi ta fara zage zage tana fadin Jafaru baida ta ido akan
wanan yarinyar don in yana gabanta tankar yana gaban Allahnshi ne
Haba dai dubu kada kice hakan kawai dai zuciyace take kaunan mai kyautata mata
duba ga irin kokarin yarinyar nan gareshi ba tsoro bane hakan kyautatawace kawai a
tsakaninsu.
Kin dai tsani yarce har baki ganin kirkinta a yanzu amma ai tayi kokarin da ba
kowa zai daure yayisa ba kinga ko dole yaso abarshi a yanzu yadda tayi fama din nan
a baya kanshi
Na kula kema hafsatu a yanzu kamar kin fara shakku da tsoron yar nan koda yake ba
laifinki bane koda kinyi hakan don kanki kikewa yaki hakana din.
Kwanan iya biyu ta samu lafiya kamar yadda yace yaso ya wuto da ita gidan mu sai
iyan tace dashi a bari agama bukin Saratu in muna raye sai tazo ta zauna dani har
in haihu shiyasa yayi na,am da hakan ya barta.
Sun fara shirin buki gadan gadan har lokacin ana neman abinda ake nema din na
wasu abubuwa ga yan uwan duk kowa yaja bakin aljihunsa ya tsuke yana kallo.
Shine mai saukin da suke saka ran zai fitar dasu kunya shi kuma din ya nuna
yanzu Habu ma ya fishi karfi don dukiyanshi da aka wawashe yana kwance bai gane
komai ba.
Ga karyan da take sonyi ta burge mutane a wajen bukin nata ba abinda ya kamkama
daga wajenta shima angon ta rasa gane kanshi a yanzu datayi magana zaice ba kudi
bai son karya a sha,ani.
Tana sonshi kamar me don haka saita kyale ta kasa tambayansa komai abu yayi yawa
ya taru masu lokaci guda.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/1, 21:12] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

9️⃣1️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login