Showing 168001 words to 171000 words out of 328222 words

Chapter 57 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

dole nasan akwai masa dayasa hakan .
Washegari ko tunda safe mukayi aiyukan mu don fitan da nasan zamuyi din yana
daki yana barcinsa shigowan kawu gidan yasa naje tmna tayar dashi daga kwana.
Hakan baisa mun zauna ba shirin mu mukaci gaba dayayi bayan na gabatarwa kawu
da komai na koma kitchen don mu rage aiki tunda nasan sai yamma lis zamu dawo gidan
kila ranan .
Daga kitchen din na ke dan fahintar abindake faruwa zuwan kawo kan matsalansa
da Nusaibane don naji yana fadin ai na fada mata saita gane kureta kawu.
Ta dauka da wasa nakeyi ko wanan karon ba zanji ta kowa ba tunda ni ba mai
tausayina akan matsaloni dasu sai zance ya tashi ace nayi hakkuri don haka in zata
zauna ta zauna tunda zaman mama takeyi ni ba zan koreta amma ba ruwana da ita kowa
ya sani.
Banyi wani abin asha ba don na tare a nan gidan Asmau ce ta haihu don haka ina da
inda zanje in huta a yanzu babu takura a gareni kuma kun gani.
Kawu din ya tausa murya yana fadin abinda nake son ka gane tunda har mahaifiyar
ka ta nuna hakan bai mata ba kayi hakkuri kai Jafar ka shirya da matar ka kada ka
shafawa wanan din laifin daba itace ta sakaka yin hakan ba.
Sai naji yace kawu ina yarinyar nan dai nine ke auren ta ba wani ba kuma zamana
takeyi a gidan nan don haka ina rokon kowan ku daya saka min ido da ita don Allah ?
Nidai har kawu ya tafi banji sunyi maslaha akan zancen ba tsakaninsu saidana gama
na fito kitchen din nasawa Biba kira daga dakina.
Ta shigo ta sameni kayan dana dinka mata don gudun kada a girshemu haka na fitar
mata da kala daya komai set da gyalensa da takalma har yan kunne na mika mata ina
fadin taje tayi maza ta shirya nasan yanzu yaya zai fito mu tafi.
Ta karba da murnanta tana min godiya murmushi kawai nayi ta juya zuwa dakinta don
ta shirya din .


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

5️⃣6️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Wasu jajayen atamfan super wax mai dan surkin flower yellow a jikinsu da akai min
wani dogon riga yaji kwaliya har yagaji don kyau zakice jallabiyace rigan don yadda
aka fitar da shi.
Takalman kafata kuma half cover ce ta mata mai duwatsu new design sai gyale
yellow mai duwatsu dana yafa hakama kunnena fashion na saka dayai shige da kayan
sai agogo a hannuna da yar karamar jakkata yello.
Ki firhita kishiya ga shiganki ko ta yaya yafi ace sai mace tagani ga kishiya
taji haushi inji anty salma take fada min hakan ko yaushe.
Donshi na tsaya na gyara yadda ya kamata ga wani kamshi da nakeyi na ban mamaki
a haka na fito na rufe dakina kamar kullum idan zan fita daga gidan duk da muna
rufe falon da ko ina amma ban yarda saina kulle dakin nawa kuma hankalina yake
kwanci.
Ya fito yana waya mukai arba dashi ya sake wayan yana fadin dankari wanan
kwaliya haka Rahama ai sai ace yau din ne sunan ma ga baki daya.
Yau ba suna bane yaya amma yau din ya kasance rana mai muhinmanci ce a gareni na
juya wajen Biba ina fadin dauko basket din da muka shirya ki fita min dashi waje
sai ki dawo ki dauki sauran ledojin nan kuma.
Ta juya zuwa kitchen din ta fito da basket din dana shirya din da zamu jewasu
iya da mama dashi na tsaraba ba komai bane yasa hakan don basu taba zuwa gidana
sunci girkina ba yasa nayi wanan dabaran hada masu abincin muje masu dashi.
A kofan gidan ma saida ya tsaya yana tambaya meye wanan kuka dauko hakane wai
yana nuna basket din da nake gyarawa biba zananshi a bayan mota da take zaune.
Na juyo ina fadin iya da mama zan kaiwa girkina suci sai yayi murmushi ya bude
mota muka shiga maigadi yana tsaye har muka fita yana muna a dawo lafiya .
A hankali yake jan motan har muka kai wani shago ya tsaya yace mu jirashi ya
fita sai gashi da drinks na kwalaye masu sanyi saida ya zauna yake fadin ki hada
masu da wanan din idan kuje nayi mai godiya a fili.
A raina kuma nace Allah na godema da dabaran hakan yazo min nayi wanan abincin
don iyayyensa din.
Tunda muka doshi gidan na fara jan addu,a a bakina na neman tsari gako wani irin
fitina daka iya tasowa ga zuwan namu har ya dosa kan motan zuwa cikin gidan muka
shiga.
Da Saiba muka fara ar,ba tsaye da wasu matan abokanshi da sukazo barkan haihuwan
da farko inaganin bata san tare muke ba saida dayan take fada mata haka yasa ta
dago tana bin mu da kallo.
Da alama tayi matukar razana da ganina don ba karamin tsoro shigana ya bata ba
tagama fada masu akan yar kauye yake son ya wofintar da ita itako zata nuna mashi
ko wa take.
Sai ga matar Nura na fadin kai Nusaiba kardai ince wanan kike kira da yar kauye
ina itace amaryan taku ai ko ?
Jin hakan data fada yasa ta dago da sauri ta kallomu tabbas din kuwa nice nake
fitowa daga motar ina dariya don cewa da yayi bai ban bakin shiga wurin yanda ba
sai wani lokacin nake fadin haba yaya kaima kasan aiko don Abba da akace baida
lafiya zan shiga ai yace don kinsan ban iya hanaki zuwa duba babana ko kikace
haka ?
Part din su iya muka nufa da kayan dana dauko din muka bar saurab a cikin mota
don ba anan zanyi amfani dasu ba na abokan zaman mamace da yace zamu je gaidasu
daga nan.
Shine agaba muna biye dashi mukai sallama muka shiga iya na zaune da tasbaha a
hannunta mama na kasa zaune tana waya saidai shigowan mu yasa ta katse wayan da
takeyi din cikin bacin rai ta amsa gaisuwan da muke mata din.
Don tun kan na zauna na rusuna ina gaida ita kana na juya wajen iya dake fadin
kai kakai amaryace yau a gidan namu haka ?
Lalai marhabin da amarsu ta ango bakya laifi ko kin kashe yar masu gida kuwa
laifinki kadanne a wajen ango nayi murmushi ina fadin iya mun sameku lafiya ya
bayan rabo ?
Yaki nan ki zauna ta fada tana nuna min kusa da ita a gefen kafan mama dake zaune
a kasa din nace a,a iya nan ma yayi min barkan mu da arzikin saukan anty Asmau
Allah ya raya muna.
Tace amin yar nan haka akeson Allah ya sauke sauran al,umman Annabi baki daya na
amsa da amin iya na sake juyawa wajen mama din nace mama barka da arziki ?
Ta amsa da barka dai Rahama tare kuke tafe ashe ban amsa mata wanan ba din take
fadin barakace ta bugo waya tun dazun suna rikici da mijinta akan kudin ta wai dake
wajenshi.
Ta fada tana kallon dan nata dake kokarin zama a gefen iya inda tace in zauna
da farko din naki.
Naji yace jam rikici kuma akan me ba ita tabashi kudin ba son me kuma zatace
suna rikicii kan hakan ai dole suyi rikici ya karbe mata dan kudin ya cinye yanzu
kuma ya dauko mata kishiya.
To meye laifinshi a nan Dubu yayan kima ai kusan haka dinne shima ba aure ya
kara yanzu ba da kudin ku ya shiga hannunsa abinda duk nakewa gudu ke nan ai tun
farko gashi ko ya faru.
Shima kawu aure yayi kome yana tambayan iya din cikin mamaki tace au bai fada
maka ba ke nan to ina zai fada tunda yasan bai da gaskiya koshi ?
Na juya wajen anty Saratu da fuskanta ke hade kila don zancen anty baraka dinne
ko wani abu ke damunta nace anty saratu mun sameku lafiya ?
Ta sauke ajiyan zuciya tana fadin ke dai Rahama lafiya kalau yaya gida ya amarci
kuma ta fada tana kokarin gyara yanayinta din na farko.
Ta dora da fasin wai wanan yar kamar yar wajen yaya Ai ko da cewa biba data aje
basket din nace tazo gefena ta zauna itama a kasan da nake zaune din.
Itace habiba na fada don ban tsaya wani sanyin da zataga hanyar sakar min wani
zance ba don nasan zata iya indai anty saratuce shiyasa na sake ina magana ta bajin
nauyin su kamar yadda suke zato da farko idan mun hadu.
Wanan yasa na zake na shanye duk wani kawaici a idona ina bata amsa a lokacin
saidai bana wuce gona da iri ba irin hakan .
Iya zancen yaya daban da wanan fa don yaya ko yayi aure bai farawa ya taba muna
kudin mu dake hannunsa ai wanan kuma fa duka kidin ta dauka ta mika mai don
sakarci.
Akwao kudinku ke nan a hannun kawu ya tambaya sai tasha kunu a fuska tana fadin
akwai mana zai fara ya taba min sune tunda yasan yadda kudin suke?
Mama meye rashin zama dayansu ai gaskiya iya ta fada gashi ya ban kudi daga
cikin kudina ya hana kusan wata daya ke nan fa ana binsa ya bani sai yace wai suna
hannun wanda ya dankawa.
Saratu nikan wai meyasa baki da hankaline wai don Allah haba kinyi maganan kudin
nan yace ga uzirinsa ba sai a jira kayan su zama kudi a kawo maki ba ?
Hakafa kike abinki wani lokaci baki tunane idan abinki ya motsa saiki koma kamar
da yaso fitowa ciki ranan ni banson irin haka wallahi yanzu da zancen yar uwarki
zamuji data dameni da koke koke ko naki da kike son dagawa mutane hankali dashi.
A,a mama ni bance zan dagawa ko hankali ba ai adai bani abin dana tambaya ko
aban kudina duka tunda abin ya fara zama haka ?
Ke tashi muje ki gyadasu ya fada ya mike tsaye ba tare daya tofa komai a cikin
zancen ba sai na mike da sauri kamar yadda ya umurceni din na juya ina fadin iya ga
abinci nan na girko maki tunda baki zo kin ci a can ba ?
Kai kai kai kice girki amarya yau zanci gidan nan ke nan bari na kurkure baki
nazo na dandana ko kin iya girkin muka fita muna dariya.
Bayan fitan mu takecewa yar kin gani ai abinda kike nema ke nan dama har dan
uwanki yasan abindake gudana yai muna dariya ana zancen yadda za a kwantarwa yar
uwarki da hankalinta a samu kudinta ya fito kin dauko wani zance kina son tayarwa
mutane da hankali.
Mama nifa bance komai ba kudin nan tunda kikace kawu za aba nace maki a,a kika
hakeni na yarda yanzu kuma kinsan abinda nake sonyi da kudin nan kuma za a ga
laifina ?
Don ganin iya ta mike zuwa baya yasa mama din tausa murya tanawa Saratu fadan
abinda take kokarin yi din akan kawu gaban yayan nasu duk daya nuna bai damu ba
amma sai bataso hakan ba a lokacin.
Tare dashi muka shiga part din akwai mata sosai a wajen nasu yan barka wanda na
sheda wasu don harda salima da Nafisa suna part din tare da yan gidansu Asmau don a
unguwa daya suke don haka ansan juna.
Ihu suka saka min ita da Nafisa kafin su shiga gaida yayan nasu na dan dara
muka rugume juna aka gaisa su suka kaini dakin mai haihuwa dake zaune kanta babu ko
dan kwali balle hulla kan ya dankare da kitson da akai mata din zanen yawo.
Muka gaisa yar uwarta na fasin ga waje in zauna a gefen gado da aka shiga
tattara kayan wajen saidana zauna nida habiba aka miko muna yaron muka dauka.
Nayi mashi addu,an Allah raya mun dan kai kamar minti ashirin a zaune shiru na
mike na karbi ledan dake hannun biba na mika ina fadin ga zanin daukan yarona.
Yan uwan nata suka shiga godiya muka fito daga dakin dake wani irin bashi duk da
kanshin turarena ya bi dakin lokaci guda amma haka bai hanani jin wanan bashin ba
kona meye oho ?
Falon muka fito muka kara zama banjin ya fita lokacin nafi zaton yana dakinsa
don can ya nufa tunda ya gama gaisawa da mutanen falon.
Ina anty Saiba tana ciki kije ku gaisa kizo muje wajen yandan ki Anty Salima ta
fada na dan kalleta ta mike tsaye tana fadin muje ai yanzu tabar wajan nan itama
duk muna nan zaune.
Bata dakin da alama tashiga bandakine dataji shigowan mu muka fito bamu tsaya
jiranta part din muka fice zuwana yar uwata dana matsu muyi arba da ita a lokacin
don a yanzu nasan tasan munshigo gidan tunda munyi waya kafin na fito gida.
Wanda a yanzu zaune take kawai gidan bata wani dogon hurda da kowa sai salima da
iya dama dai kusan hakan ake zaune saidai na yanzu din yafi worse ne kawai saidai
haihuwan nan na Asmau tace dani ta danga canji ga Asmau don data shiga barka Asmau
ta mata bazata don ta mika mata yaron wai ta shafa mai man zaitun donta samu an
mashi wanka lokacin.
Iyace dai mai wankan yaran idan sun haihu dama ba wata ake daukowa ba tunda da
dan karfin ta har yanxzu shine tana shiga iyan ta gamawa yaro wanka tace a ba Yanda
din tayiwa yaron shiri ita kuma tashiga nata wankan.
Wanda bata zaci hakan ba tunda da farko duk sun dauki zafi a kanta kan zancen
aure masu miji dani yar uwarta nayi a cewansu asirine mukai mashi muka sameshi haka
a bagas din.
Koda muka shiga ashe Saiban na tsaye ta windon dakinta don shike facing din part
din yanda din tana kallon mu zaune takai saman gado ta jawo waya ta dannawa yar
uwarta ikilima kira.
Tana dagawa tace Saiba ya akayi yazo din anyi magana tace anty ikilima inafa ya
dai zo da wanan yar iskan yarinyar tayi barka.
Anty Iklima kinga yadda yarinyar nan ta koma kuwa cikin dan kwana biyun nan
wallahi koke kika ganta sai kince ba ita bace Ramaah da kika sani a baya.
Takoma sak irin manyan matan nan da yake korafin son yaga mun koma da kullum
yake fada yana son ganin hakan a kan mu.
Mena fada maki Saiba ai dama nace kibar biyewa Asmau kuna wanan rayuwan
kidadancin kamar wasu jakuna kinki ji ?
Yanzu gashi dan hakin da kuka raina na nema ta tsone maku ido keda bakinki kin
fada ko wanan baisa ya fita batunku ya baku baya tunda abinda yake so ke nan dama ?
Tundai ke kice baki da aiki sai cusa mai bakin ciki ance ga yadda zakiyi ki
tsaya kina takama da kin gama dashi bai iya komai sai abinda kikace dashi ?
To yanzu kin gani masu iya magana sunce ko kana da kyau ka kara da wanka kin dai
san Jafar yayi kokarin zama daku haka Nusaiba ku zauna yayi takashe maku kudi amma
a banza baki amfani dashi saidai ki sayar ko ki kimshesu cikin akwati tun farko
abinda inna take maki gudu ke nan amma baki ji Nusaiba ai yanzu kin gani.
Anty Ikilima nagaji da zuwa gidan malam nan wallahi bani ganin biyan bukata gaba
daya yanzu abubuwan sun juye min yadda ban tsamani ba sam inayi kamar banayi
wallahi don banko gabanshi balle na samu aiwatar da abubuwan dana karbo din.
Ki bari ai zan shigo ana gobe suna kuma naji inna tace zasu zo barka kinga
nasan zata zauna dashi ai donshine ma bazan biyosu ba don ina son inzo in kwana din
idan nazo sai musan yadda zamu bullowa zancen nasa.
Sun dauki lokaci suna waya kafin dai ta taushi yar uwar nata ta bata shawaran da
ita saiban take ganin yana da wuya ta iya hakan ga jafar din da take gani idan ta
sameshi yanzu saita hukuntashi fiye da tsamaninta.
Zai gane shayi ruwane idan ya shiga hannunta saita bashi mamaki sosai ta rama
duk wani takaicinshi dake zuciyarta abugeka a hanaka kuka shine abinda jafar yai
mata a yanzu kan Rahama.
Muna shiga maria na zaune tana ba Abba abinci tun daga kofa nace da yaron baby
na ya juyo da sauri yana kallona sai yai kamar zai dago zuwa gareni sai kuma ya
noke zuwa jikin mamanshi yaki zuwa wajena din.
Wai Ramaah kece haka abinda Maria din ta fada ke nan tana min kallon mamaki na
dan bata rai ina fadin kinga duk na lalace ko ?
Ta watsa min harara tana fadin wani lalacewa kuma gaba daya kin sauya kamar bake
ba ummah nacan tana damuwa akanki kullum sai tayi min magana a kanki wai naki zuwa
in duba matake .
Ni kuma ya Habu ya hanani zuwa gidan duk sun sakani a gaba kan maganan ki na
karasa ina fadin to ai gani nazo yau muka fara gaisawa da ita lokacin Nafisa ta
shigo part din tana dariya tace.
Wai ashe bakuga saiba ba da kuka shiga yanzu ta fito tana fada dake Salima wai
zakuyi tsiya idan kina shiga huruminta dolene saita gaisa da yarinyar nan da zaki
kwasheta zuwa dakinta ?
Allah sarki shi gaisuwan ma wani fitinane ashe banzata haka bane da bance muje a
gaisa ba ai ?
Mun bar zancenta aka dauko hiran anty baraka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login