Showing 135001 words to 138000 words out of 328222 words
Chapter 46 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
yaya Habu yazo muna dashi tun safe.
Har yazo suka dan zauna kan zancensu da mama ban samu ganawa dashi ba a lokacin
yaso ya ganni mu gaisa koda yaya ya duba mashini har lokacin ina kwance jikina yai
zafi kuma ban falkaba balle insha magani.
Har yaya Habu din ya tafi shima ya mike zuwa dakinshi yayi wanka ya dawo nawa
dakin still ina kwance a takure ina barcin .
Ya tsaya ya kura min ido na dan lokaci kafin ya kai hannusa a saman jikina yana
taba temperature dina yaji jikin ya gashe sosai a lokacin.
A dimauce ya fara kiran sunana a hankali hakan yasa na bude idanuwana a cikon
nauyin barci na sauke a kansa yana zaune gab dani ya dan rankwafo jikinsa zuwa nawa
yake fadin.
Rahama baki da lafiyane haka har sosai shine baki fada min ba muje asibiti ?
Idona dake lumshe na kara dan budewa ina fadin idan nasha Panadol zan warke
basai naje asibiti ba..
No tashi dai muje kiga doctor zaifi ga jikinki yayi zafi haka kice in barki a
gida ?
Bari nasha magani idan bai bari ba sai muje asibitin na fada ina kokarin mikewa
cikin karfin hali.
Ina zakijene wai na bashi amsa da magani zan dauko a jakkata ina jakar take ya
tambaya yana kallona don duk maganan da mukeyi dashi tun shigowan shi idona a
runtse yake na kasa hada ido dashi.
Gaban mirro yaje inda na nuna ya dauko maganin da goran ruwa ya dawo yana mika
min dakyat na dago kai zan karba a cikin kunya.
Yake fadin toki bude ido mana ki karba ya zauna gab dani jikin mu yana gugan na
juna dashi na sakeyin kasa da kaina.
Murmushi naji yayi yana fadin Ok har yanzu kunyane to bari na sake fitar da
kunyan taki donki daina jin nauyina gaba daya don naga kamar da sauran ki har
yanzu.
Da sauri na kalloshi wanan karon ina fadin wallahi ba haka bane kawai ba zan iya
bane nayi kokarin komawa saman gado don yanayin jikina.
Yayi murmushi yana dafa goshina ya bare maganin ya bani nasha ya mike yana fadin
ina zuwa falo ya fita ya hado min tea mai kauri ya kawo min saida ya tsureni nasha
ya fita da kofin na koma na kwanta.
Barci na koma ban falkaba sai wajajen sha biyu da rabi har lokacin yana gida
ranan bai fita ba shima barci yayi ya rufe gidan don duk wanda yazo ya koma ya
umurci maigadin daya rufe gidan kada ya budewa kowa.
Jin motsin falkawana na shiga bandaki yasashi bude idonshi daga kwancen da yake
yana barci a gefena kafin na fito na samu ya kunna wayanshi daya kashe.
Don tunda zai kwanta ya kashe wayan don kada a dameshi barin maganan da yakeyi da
wanda yake wayan yayi ya dago yana fadin to ya jikin naji zazzabin naki ya sauka
tun dazun ?
Da sauki na bashi amsa ina zama bakin mirro na don shafa mai saboda na tsaya nayi
wanka a bayin kafin in fito.
Ya mike zaune da wayan saidaya gama ya tako zuwa inda nake ya karbi man ya fara
shafa min a hankali na lumshe idona a cikin kunyarsa.
Saida yazo daidai kirjina sallpn da yake murza min man yasa na bude idona na
kalleshi ta cikin mirro ido ya kashe min ta cikin mirro yana fadin in daina
aikinane fa ?
Dariya ya bani da yasa na danyi murmushi a fili nace nagode yayi hakana ai shafa
man ya isa malam.
Aikinane wanan don haka babu godiya abarni nayi da kyau nayi kasa da kaina kawai
saida ya gama don kanshi yakai min kiss a goshi yana fadin bari na dan watsa ruwa
nima tunda naga kinji sauki ya fita daga dakin zuwa nasa.
Saiba dake zaune tana cika tana batsewa don haka ta kwanta takuma tashi a hakan ga
kuma wani bakin cikin daya kara izo mata .
Don tun safe bai shigo gidan ba har wanan lokacin haka yasa ta mike zuwa falo a
cikon fushi ta samu Asmau da yaran suna cin indomie a plate daya.
Ta zauna tana jan tsuki Asmau ta dago kai tana fadin kin tashi ke nan ta wani
kallota tana fadin aiba barci nakeyi ba dama.
Wai kinga dan iskan mutumin nan har yanzu bai leko gidan nan ba tunda ya aje
dabbobi a gida yoko dabbobi ma muke ai ya bamu kulawa gari ya waye haka har daya da
wani abu ?
Asmau tace wa,kenan fa ?
Ta yo mata kallo mai kama da harara tana fadin J mana don ranan bai samu sweet J
din ba a bakinta sai J data kirashi dashi cikin hasala.
Keko dai amaryace fa dashi Nusaiba yana can yana soyayyewa tukun ai dolesa dai
ya lekomu dama don ya huta ya ki kawota nan cikin mu ya kebeta daban ai.
Wata amarya har ina amaryan take abu haka kamar kara shi yaga mutum har yaje
zubar da mutuncinsa akan wanan yarinyar.
Ni wallahi ba zan dauki hakan ba shima ya sani akan wanan yarinyar ya dinga nuna
mu bakomai bane itace mutum mu tashi tun safe yaki ko bugo waya ya tambayi lafiyan
mu dana yaran nan ?
Ruwa Asmau ta dauka tana bawa yar wajen Nusaiban ba tare data kula da abinda
saiba ke fadi ba sai abincinsu sukeci da yaran.
Taja tsuki ta rarumi wayarta dake gefe tana fadin wai don iskanci harda kashe
wayoyinsa tun safe nake gwada kiransa ana cewa wayan yana kashe.
To aina fada maki baki yardaba ke nan da zancena amarcifa yake sha ai dole ya
kashe wayansa bakiji ance amarya kona kara bace amaryace balle wanan yar filoce fa.
Koba hura sai asha nono don dara dara surbajo ce yana can ana gigitashi da abin
na amare.
Kiran ya shiga yayinda take watsawa asmau wani harara da take dauka sakarai bata
san ciwon kanta ba ita kan taji ya dauki wayan ba bata lokaci tace dashi.
Malam dabbobin daka aje a gida ba kulawa suna bukatan ka anan kan wanan sakaran
yarinyar har zaka nemi ka wullakantamu kaki shigowa tun safe wajen mu ?
Ohh Saiba Allah ko gari ya waye ashe shaf na shagala an rudani bansan har gari
ya waye hakaba ai wallahi ashe kuna son ganina ?
Na dauka baku da bukatana ai yasa na shagala a inda akasan muhinmancina namji
mutumin dake gudun ka yake kyamarka kada ka shafa mai ciwo ya naka a yanzu ya samu
wanda bai kyamarshi me kike gani ke nan zaiyi a yanzu ?
Yar iska sallon yaudaran datazo ma dashi ke nan dama yasa akai munafuci aka
koramu gida don a samu shige maka wallahi mu zubo dani da itace a gidan nan.
Zakizo nan ke nan inda muke Ok fine sai kinzo din ai gara kizo kiga inda aka san
zafina da darajana zaifi ta kashe wayan a cikin takaici da kunnan rai.
Kinji ko meyana fada maki a yanzu yana cikin gigin amarci komai yana iya fadawa
mutum idan yai magana dama kyaleshi kikayi .
Tunda duk tsiyarsa dai baikai dare bai lekomu ba nan don haka meye zai damu mutum
akansu yanzu.
Taja tsuki ta mike tsaya zuwa dakinta har ta zauna kuma ta fito saigani Asmau
tayi ta fita ta girgiza kai tana murmushi tana fadi a fili wahalala kawai ba dadi
ashe ?
Tasan dai ba fita zatayi ba a yadda ta fita don ko mayafi bata dauka ba don haka
kila cikin gida zata tace ai cin tuwon kishiya rankone.
Nusaiba kuma part din iya ta shiga ta samesu zaune dasu anty baraka suna hira
iya ina mama take keya baraka ta bata amsa taja ta tsaya saiga habu ya shigo yana
fadin.
Ina mama karfe hudu mutanen nan zasu shigo a zauna na kira J yace dani zai shigo
kafin lokacin yau hutu yakeyi yasa bai shigo ba.
Ai dole ya huta yau angone fa balle jafaru da bai samun hutu kullum a uzurce
yake da tsabga baida lokacin kansa balle na wani.
Yanzu ko dole yabawa amarya hakkinta ai ya zauna tare da ita na dan lokaci su
huta tare itama akwai gajiyan buki a tare da ita iya ke fadan hakan cikin rashin
damuwa da saiba na wajen lokacin.
Balle yau Rahaman bata jin dadi tun safe ya kirani na kawo masu abin kari daga
nan nakai masu har na fito bata san nashiga ba tana kwance.
Kai masha Allah kace abu yayi kyau haka yar albarka kenan haka muke son ji ko
yaushe Allah ya shirya muna yayan mu a tafarkin addinin musulunci ga baki daya abu
yayi kyau wallahi sosai.
Ba a kawo amarya washe gari ka ganta kwashi kwashi da idanu ba kunya ba tsoron
Allah tana rawan kai da guloto sakarai bata san mutane na mata kallon banza bane
sun dauka hakan wayewane yanzu banda sakarci.
Dariya habu yayi ya juya zai fita mama ta fito tana fadin Habu naji muryanka ina
bandaki ya juyo yana fadin ehh mama dama zancen malaman nan da zasuzone nazo fada
maku da karfe hudu sukace zasuzo yau.
Don tsabga garesu saida J ya kirasu dazun da naje wajensa shine sukace zasu shigo
da karfe hudu din in sha Allah.
Yanzu fa nake tunanesa na dauka yayi tafiyane ai banga ya shigo gidan nan ba yau
yana nan mama yana hutawane kawai zai shigo anjima.
Yana dai jinya zakace anty baraka ta fada tana dariya mama dubu tace jinya kuma
jinyarwa shidai habu ya fita yana dariya sai anty baraka ke fadin amaryansa mana.
Itace wai yau ba lafiya saida shi habu yakai masu abinci dazun toooow Allah ya
sauwaka tun yanzu an fara ciwo kuma haka ?
Kaiya banda abinki dubu kaji ance amarya ba lafiya a daren farko ai kasan meya
gudana kuma haba dai kina magana haka ba lissafi kuma dai ?
To iya me kuma nace Allah ya sauwaka yakai yan baya ga danshinta mama dubu ta
fada tana zama saiba ta juya kawai ta fita daga part din ba tare dayi maganan daya
kawota ba.
Munafuncin banza da wofi Allah iya nan idan batayi hankali dani ba wata rana
saina faceta a gidan nan .
Iya din Asmau dake kishingide ta dago tana fadi tace kada ki soma gangancin
hakan ga iya don wallahi ba zakiji dadinsu ba kaf dinsu idan kika taba iya ko mama
gidan nan.
Kansu fa a hade yake jallone da mufinsa idan kin kula da tafiyan mutanen gidan
nan daya bayayi saida dan uwansa .
Kaf dinsu yaya J shike juyasu gidan nan kin taba iya donshi zasu kyaleki kike
zato ki dai tsaya akansa shidaya munanana maki a yanzu.
Tsuki taja ta mike zuwa daki a cikin wani irin jin haushin kowa a gidan don ba
wanda ya damu da halin da J din keson nunawa akansu yanzu itako ba zata yarda da
hakan ba.
Don wanan yar fillon me zubin mayu daya dauko zai nuna su ba matane ko me
gaskiya hakan ma ba zai sabu ba wallahi.
Sai karfe biyu da rabi ya shigo gidan duk da sunga anshigo da wasu kaya sun san
shine ya shigo gidan amma bai zo part din ba tukun.
Asmau dake falo kwance tana wayane ita kuma saiba na kitchen tana hada abinda
zasuci maigadi ya shigo da kayan ko kallon kayan batayi ba inda ya aje ya fita a
kofan kitchen din.
Saida Asmau ta shiga kitchen din take fadin au baki dauke kayan nan ba ina ganin
yaya yazo dasu fa kayan miyane nasan aka sayo ta duka tana bude buhun kayan.
Su kayan gwarine da nama mai yawa sai mai gallon biyu a gefe aje da kwalin
taliya dana indomie zasukai shida duk a kofan kitchen maigadin ya zubesu wajen.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
4️⃣6️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Saida ya gaisa dasu iya tagama sakamai albarka ya juya wajen mama yana tambaya
suna dai lafiya ko ?
Ido ta zuba mai tana hango annuri da annashuwa a tare da dan nata da hakan ke
nuna yana cikin walwala sosai a lokacin saidai har yanzu tana jin zafinsa a ranta
wanda ba zatace ga dalili ba.
Ita dai abinda tafi dauka shine yayi aure bada izininta ba ya nuna bata da
tacewa gareshi ya isa yanzu bai bukatan shawaranta a yanzu.
Inkin debe wanan ba zatace ga abinda da dan nata yayi mata ba da zata fada don
Jafar shine na daya a kaf iyalinta dake mata biyayya.
Zata iya fassara wanan abin da jin zafin abinda yaiwa matanshi na cin fuska don
zata kira wanan auren da sunan cin fuska a wajensu yayi aure ba tare da sanin kowa
a cikinsu ba inbada kawu da yaiwa dole ya daukeshi zuwa neman aure kamar yadda kawu
ya fada mata.
Jin tambayan da yake mata yasa ta nisa daga dogon tunanen da takeyi nasa a
lokacin tace lafiya lau muke Jafar ya wajen ita Rahama din naji Habu na fadin bata
jin dadi kuma ?
Da sauki tasha magani kafin in fito ta samu sauki don taki yarda muje asibiti ai
dama Rahama bata son ko magani balle zancen asibiti Salima ke fada.
Ai naga alama ta daiji sauki da ranan nan don saida naga taci abinci nafito na
barta zaune a falo tana gaishekuma.
Iyace ta kara fadin amaryace mai batun hankali injin dai kazo min da tawa sauran
kazan amarcin naku ya mike tsaye yana dariya yake fadin iya ke aiba saura za a baki
ba taki dakwalwan za a kawo maki dai kema.
Daga part din iya nasa part din ya nufa inda ya samesu a kitchen tsaye suna
sa,insa a tsakaninsu kan kayan da aka shigo dashi din.
Daga kofa ya tsaya rike da hannun yar wajen saiba yana fadin wai ya hakane kuma
ku dai baku zama bakuyi fitina a tsakanin ku ba ?
Wai cewa nayi a dauko wanan naman daya saura sai a soya kada a hada da wanan
shine wai ban isa ba a hada waje daya duka Asmau ta fada.
Don me zakice haka ba ita bace babba ita tasan yadda za a adana kayan ke meye
naki a ciki tunda tace haka za ayi jafar ya fada.
Au Allah ko ashe an fara babba a gidan nan yanzu to maji magani ashe ta fada tana
mashi wani irin kallo na yatsune.
Kedai baki zama a waje ba ai fitina ba saiba ni bansan abinda yasa kike wanan
rayuwa haka ba juyawa tayi ta bashi baya tana juye abincin data gama dafawa a plate
ya bita da kallo kafin ya koma fadin.
Wait naga kin juye abincin duka sufa ba zasuci bane tace ka tambayeta mana ai
dazun ta dafa itama taci da yaran ?
Asmau yaushe kuka fara girki daban dabab a gidan nan gashi nan a cooler na zuba
mata kuma ta gani ta dafa wani ai.
Abincin da yayi sanyi kuke son inci ta juyo tana fada yace ke ba bawan gidan ku
nake ba da zaki dinga min barnan abinci haka in saka maki ido.
Gidan mu kan ai kaima kasan yafi karfin ka balle daga magana ka jefo gidan mu a
ciki haka kawai daga zance ka nemi ka zageni tunda dama kana hasale dani ?
Na dai fada maki kada na sake gani ko jin an raba min girki a gidan nan idan ba
haka ba rai zai baci wallahi ya fada a hasale ya juya zuwa dakinsa.
Asmau da saida ta gama gyara kayan ta fito tabar kitchen din ba gyara ta nufi
dakin nasa daga kofa ta tsaya tana gaidashi da wuni ya amsa yana kwance ya dago
yana fadin.
Wai Asmau sai yaushe zaki daina zama hakane don Allah kayane baki dashi kome da
kika zabi ki dinga zama a haka don Allah ?
Kiwa kanki fada Asmau kece babba a gidan nan wanan halin da kikeyi yasa kike
ganin kowa na rainaki don baki mayar da kanki abin kwarai ba Asmau don Allah ki
gyara banson haka me kika nema kika rasa a rayuwanki ?
Naji ta fada ta juya ta fita daga dakin tana jinini a zuciyarta cewa ai dama
ban taba fari a wajen ka tunda baka kaunata yanzu kome nayi banyi daidai bane.
Shiko tsuki yaja yana gyara kwanciyarsa haushine ya kumeshi Allah ya gani yana
son Asmau amma halinta sam baiyi masa ba kazanta da yawan da abu da muhinmanci
magana da har bata iya daukarwa kanta mataki shi yake damunsa da ita.
Yaso tun farko ya sameta irin yadda rayuwansa keson matarsa ta kasance bai samu
hakan gareta ba yayi gyara ta kasa gyarawa yakai karanta har gaban iyayyenta an
tsawata mata amma bata sauya dole ya gaji ya sa mata ido.
Yadda Saiba tazo mashi da karya ya dauka ta kwaraice ashe halinsu daya sak da
kawar nata kishiya kuma a yanzu dole yai hakkuri ya zubawa sarautan Allah ido
akansu.
Gashi shikan idan ka ganshi tsab tsab dashi zakice inda yake sai kin wanke kafa
ki shiga saboda tsabtanshi saidai kuma bai samu mata irinshi ba.
Ji don Allah wai wajen miji tazo a hakan ga wani riga duk jurwaye ta kawo wani
zani sama ta dora tayi daura gaba da shi wanan kayan takaicin ina zai