Showing 39001 words to 42000 words out of 328222 words
Chapter 14 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
dashi
ba balle ita.
A gaban mu ya fito da wani babyn roba mai gaba gaba zakice mutum ne kamar wata
jaririyace a hannunsa ya shiga dakinsa dashi a hasale.
In gajarce maki labarin nan duk lokacin da baffa ya murda wanan babyn roban idan
kafa ya murda haka hanne zatayi ta tsala ihu da sai mujita a namu ruggan saboda
azaba.
Idan hannun roban ya murda ranan hannunce zata lamkwashe ta dinga ihu tana neman
taimako masu magani sunzo kala kala ankai hanne asibiti birni an kashe kudi yafi a
kirga amma hanne bata samu lafiya ba.
Ranan da na girsheshi yana murda kan wanan babyn roban cikin mugunta daya
bayyana afuskansa yana wasu suraita naja baya a hankali don baisan ina wajen ba.
A ranan muka samu labarin wuyan hanne ya kare tana batun mutuwa haka da baffa
din ya fito daga daki idonsa a kaina ya sauka yana min alaman gargadi ban nuna
nasan abinda yake nufi akaina ba lokacin.
Don zuwa lokacin na daina tsoron baffa tunda yake kirana da shu,umma idan dare
yayi yaji ina rewa kira,an da muka koya a abuja don mu din mun sauke alkur,ani a
lokacin gidan Alh tun barinka nono zaka fara bin yan uwa karatu don haka ya
gargadeni da na daina naki sai dai in rage sauti yake kirana da shu,umma abakinsa
ni kuma tsoron shu,umancinsa ya fita raina.
A wanan case na hanne na yarda baffa shu,umine na gaske don dashi mahaifin Hanne
ke fadi tashi dashi aketa zuwa asibitin birni ana kashin kudi wani lokacin shine
mai zuwa amso maganin kan matsalan hanne din.
Shiyasa bahaushe yace makashinka yana tare dakai ko wani lokaci muna tare da
makiyan mu bamu sani ba a duniya.
Haka Hanne ta wahala sosai dukiyan mahaifanta yana tafiya baffa yana mata
dariyan mugunta yana bin babyn roban daya sihirce da sunan hanne yana lugudewa
karshe shanayen mahaifin hannene sukai rauni.
Saida Allah ya nufi hanne tana da sauran rabon shan ruwa a duniya ranan baffa
din ya tafi Adamawan cameroon wajen wani amininsa aka ga wuta ya kama a bukkansa.
Ko yaji tsoron kashewa andai zuba ruwa har angaji wutan saida ya lashe bukan
Baffa kaf yadda wuta ya kona roban haka jikin hanne yaji amma ta samu kubuta.
Da Baffa ya dawo daureshine kawai ba ayi ba don duk wani kayan tsafinsa ya kone a
wanan gobaran wasu tun yana yaro wasu kuma da girmansa ya karbo sihirin yake
aiwatar da sherinsa akai.
Har yau kuma ba a san nice na hada baki da dan uwan hanne yazo ya saka wuta a
bukkan baffa ba a cikin wa yanda suka samu saukin hakan har da mahaifiyar mu da
yanzu take iya mayar da magana a cikin iyalan baffa din daya rufe mata baki haka
yasa na gane muma baffa ya kullemune a lokacin da sihirinsa don a lokacin muka fara
samun sauki a cikin hakan kuma zancen auren Yanda ya taso har ya rasa me zaiyi yace
ya barwa hardo mu da sharadin baiba da ko Nagge guda don shanun babanmu sun zama
nasa a yanzu.
Baffa mugune ko cikin muggai nasan zai iya illanta anty Maria tunda ya kufulemu
a cikin ransa zai iya aiwatar da wani mugun nufinsa akanta yanzu.
Allah yafika baffa na fada a hankali wa Allah yafi Ramaah naji muryan ya Habu
yana tambaya nace baffa na juya na fita daga dakin rai bace.
Part din iya na koma suna zaune dukkansu a falo mamace ke tambayana da Ramaah
kin karya kuwa tana kallona.
Kai na girgiza mata don shiririta Ramaah zaki zauna da yunwa a cikinki har wanan
lokacin maza dauko kofi kizo ki hada shayi kisha ga kuma dankali a wanan roban ki
diba kici tafada.
Nima takan ban mamaki wani lokacin idan tace bata karya ba mutum ya tashi yayi
wanan uban shara da wanke wanke amma kuma yakai wani lokaci yace baici komai ba.
Zama nayi kamar yadda mama dubu ta umurce ni dan zuba ruwan zafi kadan na hada
shayin na dan dibi dankali ina tsakura a hankali.
Suna hiran su sai iyace ke fada dani kan na dibi abu kadan kamar za abawa
jariri murmushi kawai nayi don zuwana dake tuna min da baffa a lokacin.
Banda natsuwa a yau ina tunanen shu,umancin baffa a raina zai iya fiye da hakan
a kan yar uwata tunda ya fada da bakinsa taje koba aure ba taji tayi auren kado din
data saka kanta ya gani.
Waiba muryan anty Asmau nake ji ba anty Saare ta fada tun dazun nake jin
muryansu ai inji salima sai mama dubu tace yau kuma me suka tashi dashi da wanan
fitina ?
Turo kofan da akayine yasa mu kallon kofan don kofan yana bada kara idan an
tabashi wanda naciki zai gane anshigo dakin a lokacin.
Asmauce matar ya Jafar ganin mu a zaune gaba dayan mu yasa ta soma gaida tsofin
da kwana kafin ta dora da fadin mama kiwa Nusaiba iya dani dan Allah.
Mekuma ya faru da safen nan kasa magana tayi sai hawayen dake zubo mata hakkuri
suka shiga bata suna fadin kiyi hakkuri Asmau kinsan halin abokiyar zaman ki sai
kici magananin zama da ita ta hanyar kawar da idonki a kanta.
Mama don Allah wani irin kawar da ido ake son inyi ga Nusaiba yanzu kuma bayan
wanda nakeyi yanzu akan mimi fa da yarta Nusaiba ta dokan min yarinya har wani
wayau sanin haka mimi tayi mama saboda Allah ?
Duka kuma me yarinya kamar wanan zatayi mata har da duka duka sosai tayi mata
mama ki duba yadda bakin yarinyar nan ya fashe wai don kawai suna wasa a falo fada
ya hadasu ta kayar da yar uwar shine Nusaiba ta fito ta duketa fa haka ?
Tir da halin wanan yarinyar wallahi banda abin namiji banga abinda yaron nan ya
gani a jikin wanan yarinyar mara mutunci ba wallahi.
Iyace ke fadan wanan maganan inda tacigaba da fadin wanan yar yadda take baka
haka zuciyarta yake baki ba digon rahama a tare da ita,,,,,,
Iya baki san kan zance ba kin zauna kina zagina ai tana tsaye yaran suke fada
bata rabasu ba har ta kayar min da ya tana duka don rama kuma shine wai nayi laifi
ni wallahi ba zan yarda da irin wanan ab,,,,,
Ke don Allah ku fita ku fita masu daga shiya kuje can ku kashe kanku da yayan
naku kada kuzo ku tayar masu da hankali a nan kuma ?
Ya Habune ke fadan hakan da yashigo part din ransa a bace yana binsu da idanu
duk suka juyo suna kallo shi.
Wanan wani irin rashin hankaline da zaku dinga fada akan yaya tun suna kanana
ku koya masu mugun dabia wani irin halin banza kuke son yayan ku su taso a
cikinsa ?
Indai hakane zan karbe yaran a waje da zaran kun yaye kada wace ta raba min kan
jikoki mama dubu ta fada garesu .
Ace mata baku da abinyi sai fitina a kullum ku kwana jidali ku kwanta da jidali
mama sin tacigaba da fada tana fadin maganganu akansu.
Dama ace fitinan nan naku shine halin arzikiku da mijin ku zai dawo ya sameku a
cikin farinciki da jin dadi da walwala ba yazo kulum ga jidali kuma ya sameku a
cikin kazanta da doyi ba.
Iyace take wanan katobaran a gabansu daya saka aka kwashe da dariya bandani dasu
da suka hade rai tace Allah ko banda kazanta da tijara ba abinda suka koya ga
uwayesu da zasu barwa diyansu gado suma.
Iya da banda tarbiya ai Jafar ba zai auro niba gidan nan fada kuma kowama yanayi
idan antabashi ai ta juya ta fice daga part din ranta a bace.
Anan tabar kishiyar nata su mama suka haita da fada ya Habu yaja tsuki ya juya ya
fice daga part din a hasale yana maijin haushin abinda yake faruwa din.
Iya kin damemu da fada don Allah ki bari idan mijinsu ya dawo ki fada mashi mana
Saare ta fada tana kallon iya din dake faman jinini ba fada bane fadan gaskiyane da
bakwaso ayi mama ta fada.
Nasan maganin su ai idan na hade kan yaran na tafi dasu can babban gida sai
muga ta tsiya kuma da sauri Saare din ta kara fadin a,a mama barsu da yaransu don
Allah matan nan basu da mutunci .
Har sukayi suka gama ban ko daga kai na kallesu ba ina faman tunane kasan raina
dan na dauka matsalan yayata din wani babban lamarine na tashin hankali lokacin.
Duk da ance mahaifiyanmu zatazo zama da ita hakan baisa naji dadi ba a raina
idsn na tuno da sheri baffa a ranan haka na wuni a cikin damuwa da fargaba ina
zullumin abubuwa da dama a raina.
A haka barci ya daukeni sai wajajen yamma na samu na tashi sallah nayi na fito
da niyar zuwa part din anty na sai na samu sin fita da mijinta basu gida ban san
dai fitansu ba a takaice.
Ga kuma kaina yana ciwo don haka na yanke shawaran zuwa wajen matan ya J in samo
ko paracetamol insha ya dan fada min.
Sam ban kula ba da shigata nakeyi sallama anty Asmauce na sama kofa don hakan
ban hango na cikin falon nake fadin anty don Allah kuna da Paracetamol insha kaina
ke ciwo ?
Ayya banda shi Ramaah ta fada a takaice nace ko maman sultana tana kusa sai ta
dago murya tana fadin gaskiya bansan inda na ajeba a yanzu jin hakan yasa na juya
zan fice daga part din.
Muryan maigidan da bansan ya dawo ba a lokacin naji acikin tsawa yana fadin you
are very stupid all of you ina maganin dana aje agidan don irin hakane wai ?
Wai me kuke nufi da wanan halin bamzan a yanzu shekaran jiyan nan mama ta gama
yi min complain a kan kayan dana bayar aba kowa gidan nan kun hanawa yarinyar nan
da yarta.
Niyi magana kunce ban lissafo da suba ai niko nasan abin da nakeyi da badon mama
ba wallahi duk inda kuka shiga da kayan nan sai kun fito dashi a gidan nan.
Yanzu kuma gashi to tazo neman magani kunce wai baku da magani for god sake wani
irin halin banzane haka wai kukeyi kun kuwa san hakin makwantaka balle na wanda
kuke rayuwa a gida daya dashi haka kuwa ?
To aini bansan ko wani take nufi ba balle in bata Asmau ta fada itako saiba cewa
tayi nifa cewa nayi bansan inda yake ba ba cewa nayi ba zan bata ba ai.
Kaji takwal Asmau bansan irin bokon da kikayi duniya ba wallahi karatun ki ke
kan bai maki amfani ba wallahi ke kuma Saiba bakin hali da iskaci ko ciwo ai yana
kan kowa yasan kofan kowa a gidan nan.
Ban tsaya jiran karasan zancen su ba na juyo zuwa part din iya na samu kujera na
kife ina rufe idona an dan jima kadan sai gashi ya shigo iyace a gida mama tare
suka fita dasu yaya Habu daga gidan.
Ina yarinyar nan yana tambayan iya yakai zaune a kusa da ita tace wace ke nan fa
yana fadin wanan yar uwar matan Habu din nan mana dake gidan nan.
Dazun taje wajen marasa hankalin nan neman magani ta hade wai kanta yana ciwo
don rashin hankali iya ace wai magani ma rowansa sukeyi a gidan nan sai cewa sukayi
da ita wai basu dashi.
Kaji marasa kan gado ko dazun fadan sukayi aikan diya nan ta kora mashi yadda
abin ya faru ransa ya baci sosai ya mike yana mikawa iya din ledan maganin daya
dauko yace tabani.
Ai gata kwance iya ta fada tana nuna mashi inda nake kwance abayanshi au itace
nan a bata tasha idan ta tashi ya fada ya fice daga gidan.
Ficewa yayi daga gidan kai tsaye unguwar iyayyensu yaje ya samu abokansa na
unguwar yakanyi hakan idan yana gari ya zauna wajensu suyi hira sai yayi sallah
magariba da isha yake nufowa gida.
Saida ya tsaya ya sai kayan sanyi dana tabawa ledoji daban daban ya nufo gida
dasu kai tsaye falon iya ya nufo inda ya samesu zaune suna hira ni ina zaune a inda
na idar da sallah na ina addu,a.
Saare karbi wanan ledan kowa da nasa kada kociwa iya nata ya fada sai iya ke
fadin ka sako dana yar nan wace ya tambaya yana rabon ido ta nuna mashini da ido
yake fadin ya saka ya fita .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
1️⃣5️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Ledan ta fara budewa ya kara lekowa yana fadin ke Salima karbi wanan ki mika a part
din Habu ta mike da sauri tanufi wajensa tana karba.
Irin ledan daya mikawa saarece da farko mai tambarin shagon dayayo sayyya a
wajensu yan banzan matan ka dole su zama haka kana gari ko baka gari kullum a cikin
cin kaji suke gidan nan suna tauna dadi su zuki dadi da safe su tayar da mutane da
fitina don gata.
Iyace ke fadan hakan a gareshi shi Habu ya samu yar mutumci yarinyar nan kome ta
kwaba a wurinta saita sako min shi a kwana banda wanan matan naka masu rowan tsiya
da bakin gado.
Shiyasa abotansu yazo daya tun farko halinsu dayane yanzu sunawa mutane iya
shegen banza a gida haka ni yaushe zan tsaya ina kamarka ,,,,,,,,
Iya ina ruwanki wai kema waya sani ko haka kikayi zamanin zaman ki da baban gona
da kishiyoyinki ?
Ke Saratu ki koma ki tambaya kiji da kyau a zamanin kurciyana kisha labari
labarin arziki kuma bana tsiya ba ai maganin Asmaun ke nan bata da halin arziki
gara da kawartata tayi mata hakan ai.
Wanan yar akwai bakin rowa da kazantar tsiya kamar mai bakin uwa saare din ta
katseta da fadin aikuwa nagani don saida kika korewa baban gona duk matansa kika
zauna ke kadai a gidan don iya yi.
Dakuwa mama tayi mata shiko ya kasa tafiya sai murmushi yakewa tsohuwar kamar
yadda ta saba idan tana aibanta matan nasa.
Iya ai yanzu nayi magana da Nura za a samo mai aiki gidan nan don kazantan nan
nasu yayi min yawa iya kuma basu da niyar tsayawa su gyara hakan .
Yar aiki kuma Mama Dubu ta fada irin fitinan nan nasu yar aiki ba zatayi karko
a cikinsu ba ai don fitinansune zai koreta adai gwada din a gani kawai.
Lalacewan nasu yakai ga sai andauko masu yar aiki a gidan nan kuma har yaushe
da karfinsu da lokacinsu zasu tsaya ga aikin yar aiki kai kuma mijinsu ka yarda
wanan kam tauye kaine da rayuwa Jafaru .
Komai haduwan macen data amsa sunanta na macen kwarai to bayan ibada da tsabta
sai girki kumadon yana daga cikin halaiyan mace tagari wace take iya bawa zuri,a
tarbiyan da akeso.
Duk da na kula kuma taku uwar tayi rauni a nan wajen bawa nata diyan gasu nan
tarbiya da suke fakewa da sunan boko a yanzu basu iya hasalawa kansu komai a
rayuwansu.
Iya mu kuma Saare dake duke tana jagulan naman daya so daga inda nake nafahinci
duba take koda bambanci ta wafce mai girma ko mai mai mai.
Saidai ruwan idonta baiyi amfani ba don duka ledojin ina ganin iri dayane aka
bashi wajene da ake amfani da kilo.
Hakan yasa ta fara ajewa Iya nata tare da mama ta mikawa salima dake shigowa
falon tana fafin sunce sungode yaya baiyi magana ba ta mikawa Salima din leda biyu
tana fadin ki dauka ki mikawa Ramaah nata .
Bata tsaya duban girman ledan ba kamar yadda yar uwarta din tayi take fadin
Ramaah ga naki ta miko min nasa hannu biyu na karba tare da fadin nagode kana na
dago kai ina fadin ya J mun gode Allah ya umfana.
Zance banda gaisuwa sai wanan ranan ce magana mai dan tsayi ya shiga tsakanina
dashi haka no kada ki damu ya fada yana tashi yace iya bari gobe ma karasa yanzu na
gaji sosai wallahi.
Ita Iya fa gulsu gareta sai saka ido da hana ruwa guda kowa a gidan nan idonta
yana akansa yau wanan ce fara gobe waccan sai kwadayin tsiya bari na cinye namana
na soma cin naki in debe ladan zagin mutane da kikeyi a nan.
Ta mike tana kokarin daukan nagaban Iya din da sauri ta buge mata hannu tana
fadin kaji muguwa mai zalaman tsiya kawai .
Dariya yayi ya fice yabar falon yana masu saida safe salima daga kofa take
fadin Ramaah taso muje daga ciki hakan yasa namike ina tattara kayan da nayi sallah
muka bar falon.
A falon kuma suka fara budan ledan suna sawa dan nasu albarka saida muka zauna
naji salima na fadin wallahi ya J yana ban tausayi.
Gashi dai mutum har mutum amma bai samu matan arziki da zasu debe mai takaici
kazantasu shiyafi damunsa dan gayene fa na sosai Ramaah son baki sanshi bane a
baya.
Duk unguwan mu babu dan gayu irinsa lokacin baban mu yana raye muna cikin gatan
mu da lokaci ba kamar yanzu ba da gidan mu kowa ta kansa yakeyi.
Aiko yanzu anty Salima kuna cikin