Showing 204001 words to 207000 words out of 328222 words

Chapter 69 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

halin da ba aso yanzu dadin kuke nan anyi ba ayi ba ke
nan wanan abin kana ganin idan yaron nan ya mutu a halin nan zai yafe maku dauda .
Iya kinsan halin hafsatu fa kinsan ta da yarda da irun abin nan balle da taji
ance ba zanyi arziki ba sai yar uwata ta haihu a duniya tun lokacin hafsatu
tasakawa kanta damuwa.
Kaji wani shirme dan Allah diyan dubu diyan kune kai da hafsatu ko diyan Dubu ne
ita da mijinta ko yanzu da sunan ku suke amfani ?
Ni dama nasani nadade da sanin da manufa kuke wasu abubuwa akan yaran nan ka taba
jin inda dan wani ya zamo jinin wani inba shirmen ka ba dauda ?
Yaron nan Jafaru yana da kawaici yasan komai ya dade da sanin komai da kuke
kulawa akansa kaida matar ka amma ya kyale yake binku a hakan .
Yau na tabbarta da ba jafuru bane abin nan ya sauka a kansa haka har ya sani
kana ganin bayanshi akwai wanda zai kyaleku haka a cikinsu ?
Dauda kaji tsoron Allah ka daina wanan rayuwan banzan yau gashi saboda son
kanka dana matarka kun jefa rayuwan mu a cikin wani hali mara dadin fada ?
Yaran nan sun san komai ido kawai suka saka maka dauda saboda kawaicinsu da
uwarsu ita kuma tana shirme kamar tababiya ta kasa kwantar da hankali ta fahinci
hakan a gareka.
Sun sani fa iya kikace kawu din ya juyo yana tambaya tace kwarai ga habu nan
sun jima da sanin komai a kanka har uwar tasu sun dai kyaleku kawai ne .
Zufane ya fara karyowa kawu lokaci guda da har yakai ga cire fulanshi dake
kanshi yana fitara dashi lokaci guda.
Kalloshi Habu yayi yana gyada kai kafin yace kawu abinda nake so dakai yanzu
shine ka fada muna gaskiyan zancen nan tun a nan ba sai munje gaban mutanen nan
ba ?
Menene asalin abinda ya kawo hakan don Allah don a gaskiya ni dai ina yawan
mafarki da wata mace kai bama mafalki ba wallahi matar nan sau biyu ina arba da ita
a zaria .
Na farko a gidanmu nan tudun wada ta shigo da kwalan maciji tana tallah muka bata
sadaka a ranan da zanyi tafiya zuwa kasan su maria a bakinta naji cewa zan hadu da
maria.
Bayan na dawo kuma da kwana biyu na sake haduwa da ita take fada min in fadawa
mama tazo ta ganeta tun kan mai faruwa ya faru damu.
Saina dauka zance ne kawai irin na mutane don haka ban dauki zancen da
muhinmanci ba amma na fada ma mama a lokacin.
Koda ka fada min ai munje bamu sameta ba ta tafi mama da damuwa ya dama ta tsoma
masu baki karo na farko a motan .
To bayab haka ban kara tuna komai ba akan zancen sai lokacin da Jafar ya kwanta
ciwonsa na farko nayi mafalki da wanan matar tana min gargadi sosai kan wanan
maganan .
Kodana dawo kuma saina samu J a cikin wanan halin tun lokacin na san zancen nan
ba karami bane haka kuma yana cikin abinda yasa kukaga J ya auri wanan yarinyar
Rahama.
Don yadda matar ta fada haka ya faru bazan boye maku ba yau don boyo baida amfani
ita Rahama itace tayi amfani da wani magani a lokacin da j ya kwanta wancan karon
itace wace tayi amfani da daman data samu ta dinga mai amfani da wani magani na
gidansu har ya samu sauki.
Rahama mama ta fada yace wallahi ba wanda ya sani sai Nafisa dani a lokacin don
saida ta kafa huja kada a zargeta yadda wallahi nayi mafarki akan gun Rahama za a
samu maganin nan haka abin ya faru shi j ya fada min komai a lokacin.
Shine kukaga yayi hanyar daya aureta ake ta zarginsa dayaci amana ya fifitata
akan matanshi.
Amma ai baku fada muna ba mama ta fada yace ko mungaya maki mama ba yarda zakiyi
ba saima ki juya zancen ta wani tsiga tunda gashi kuna fadan sun mallakemu.
Ni dama nasani wallahi nasan dole akwai jafaru ba zai amfakawa yarinyr nan haka
a banza ba dole akwai abinda kuke boye muna wanan ai taimakon kaine tayi balle ace
za a zargeta akai iya ke fada.
Iya kinsan su wanda suka tashi wajenshi aikinsa ke nan bada magani kaf nahiyarsu
asan dashi zuwan da mukayi nakaisu ganin gida lokacin dansa ya bata maganin akai
dace kuma ta gwadawa jafar din yayi amfani.
Dole taji tsoron fitowa fili ta nuna tana bashi magani irin haka don gudun
zargin matansa shi kuma dayaga ya mike shine ya ban shawaran yana son ya aureta
tunma da ita Saiba tayi masu wanan zargin suna tare saiya kasance kamar ta
zugashine akanta.
Aida kun fada da duk hakan bai taso ba nasan Rahama zata iya komai daka fada habu
don yadda ta nuna damuwata akan shi lokaci ko ciki daya suka fito ya tsaya a hakan
mamake fadi.
Tacigaba da fadin na dauka daga baya tayi hakan ne don kawai ta samo kansa ya
aureta tayi wanan ladabin shegu din a lokacin.
Ko ladabin shegu tayi ai ta cancanci hakan don ni jafaru yayi min daya aureta
kece dubu yakamata ace kin gane hakan tun lokacin.
Yarinyar da bata kyamarsa bata gudun ta dauki ciwon dake tare dashi wanda matansa
na sunna da yan uwansu suna gudunsa don yadda fatan jikinsa kuraje suka feso masa
banda ita da Nafisan a lokacin waya tsaya ya taimaka masa bai kya macesa ba ?
Amma haka kika rufe ido kina nuna baki kaunan yaran nan har jininsu kada kice ko
ba a fahinciki bane har yaron nan dan wajen Habu kirikiri kike nuna laifin
iyayyenshi ya shafeshi kowa kuma yasani.
Yanzu ga komai ya lalace maki magani a gonan ki kin kasa tsayawa ki fahinci
hakan sai bin yarinyar banzan nan da kikeyi tana cusa maki bakin ciki a banza.
Idan har Jafaru ya mutu a halin nan wallahi ki nemi gafaran ubangijiki biyu don
alhakin yaron nan sai ya kamaku dake da dauda bama shi kadai ba tunda alama ya nuna
akan diyan kaf abin yake.
Innalillahi mama din ta ambata tana fadin nifa iya ba wanda ya taba tsayawa yayi
min bayanin wanan abin haka inba yanzu ba.
Ni yaya ake son nayi don Allah shi yaya bai tsaya ya fada min gaskiya akan
maganin ba lokacin daya kawo min balle in dauki abin da muhinmanci a raina ?
Dubu laifin hafsatune wallahi kuma ba komai yasa hakan ba ta hana in fada maki
hakanne don cewan da akayi da arzikin yaran ki zamuyi namu arzikin .
Saita dauka idan har mun fito fili mun nuna maki abinda ke nan keda yaran naki
zaku juya muna baya ko nayi yunkurin fada maku saita kawo min musalai na banza akan
illan dake cikin fadin da zanyi din .
Kuskure kan nasan nayi wallahi saidai kawai ayi ,,,,, kai rufe muna baki shasha
kawai kaji kunuan duniya wallahi sauran ka na lahira ka rasa wace zaka cuta sai yar
uwarka tillo ciki daya dauda akan matar ka ?
Hansatu mutumiyar banzace kasani kuma kake take sanin don son kai meye yaran nan
suka rageka dashi don Allah koma meka boye muna yanzu ai zamuji tunda anzo wajen
insha Allahu.
Don Allah ku gafarceni nasan nayi kuskure kuma nayi nadama ku yarda dani hakan
nima banyin kaina bane laifin hafsatune wallahi.
Wani dogon tsuk iyan taja tana kauda kai yayin da mama keta wani irin gumjin
kuka ta kasa magana sai can tace yaya daka fada min tin farko da banyi amfani da
maganin nan ba tunda baka fada min ka,idanshi ba a lokacin.
Habune ya kallo kawu dake faman zufa rai bace don har lokacin kawu yana hitarane
kanshi yana faman zubar da zufa .
Yace munzo ta wani hanya zamu dauka yace ka dauki hanyar dama shi zai kaimu garin
da zamu dauki hanyar zuwa kauye daga nan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join
my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ
[3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

6️⃣5️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Wani kallo tayi mai ta juya ta fita daga dakin bata tsaya ba ta nufi hanyar fita
daga asibitin kai tsaye Saarece ta hangonta ta nufeta tana kiran sunanta.
Ta juyo a hasale tana fadin akan me za ace bamu shiga wajen miji mu ko Rahama
ta fimu ne don kawai tana kanwar matarsa zai dinga nuna muna bambamci da ita ko
me ?
Haba dai kinga haka yana yuyuwa ita kadaine halan da za ai hakan wananma ai
maganam bamzane watafi a cikin halan da zaice hakan ?
Idan bata fimu ba aiba zai fadi hakan ba zaman me zan zauna nayi tunda ba rako
mata nayi duniya ba zo muje ga mama can kada ki tafi idan kin tafi ai taci bulus ke
nan a kanku ?
Jin hakan yasa ta biyo saare din zuwa wajensu mama din inda suke zaune saman
tabarma da abokan zamanta suna tattaunawa kan jikin jafar din.
Mama kinji wai ya Habu kada su saiba su shiga dakin da ya J yake sai Rahama
kadai aka yarda ta shiga wajensa amma banda su ?
Wai meke damun habune haka mama dubu ta fada kafin ta rufe baki mama tace haba
dai dubu tunda kikaji yace hakan ai dole akwai dalili tunda ciwon yaron nan baison
damuwa ko dogon motsi a kusa dashi.
Amma sai ace matansa ba a yarda suje kusa dashi ba sai wace aka so taje din
zata tafi wanan wani irin danyen hukuncine haka yaya ?
Habu din ne ya fito daga dakin da saurinsa hankalinsu ya koma kanshi ya karaso
yana fadin ya isah fa lafiya dai suka tambaya don yadda suka ganshi a hargitse.
Baba Tanimu ne yayi waya akan wani yaje ya karobo wani abu azo dashi banda
lokacin zuwa yanzuni don tafiya zamuyi dasu mama zuwa wajen wani mai magani kuma.
Aiga Auwal can ya dawo ina ganin gida suka danje zai tafi mama ke fadin kai habu
meye hujjanka nacewa yaran nan kada suje kusa da mijinsu sai wace zuciyar ka ya
yarda da ita ?
Ni kuma mama yaushe nace hakan aina fada dole akwai dalili yanzun nan saratu
tazo da wanan tana nuna Nusaiba tace wai kace kada su shiga mama uwargidan su mama
dubu ke fadan hakan.
Mama yaya za a bari suna shiga haka barkatai wajen mutumin dake son natsuwa a
yanzu tashigo tana fada wai ko don me zansa likita su kira Rahama ?
Nace don itace kadai ke zuwa kusa dashi ya gane tazo hakan laifine ko tsoronta
akeji da zata dinga zuwa tana tayarwa mutane da hankali bayan wanda muke ciki
saboda bakin kishi irin nata ?
Bako za a bari ba tunda haka dama jinya ya gada ba kowa bane zai shiga haka kai
tsaye aiko lokacin da Alh ke jinya ke dubu daga ke sai nice muke bayayyan shiga
gurinsa a lokacin.
Jinya abune fa da yake son natsuwa da maida hankali illa iyaka a bishi da addua
Allah ya bashi lafiya ya mike shine abinda yake bukata garemu yanzu.
Ke kenan da kika san hakan ai kin fada iya ta tsoma baki daga gefen da suke
zaune suna saurarensu .
To umma tsoronta za aji tunda ga gaskiya aki fada saboda ana gudun kada zuciyarta
ya baci ita idan tana da tunane ai wanan abin yanzu na kowane bana mutum daya ba.
Ke Nusaiba ki natsu kada ki tayarwa mutane da hankula a nan muna fama da kan mu
da abinda ya damemu ke inkina da kunya ya kama aji hakan a wajen ki yanzu ?
Ina wanda kike fadan kansa shine a kwance rai a hannun Allah idan kina da tunane
har aji wani zance haka a bakinki yanzu kuma ?
Meke faruwane mama ya Auwal yake tambaya bar yariyar nan tana son dagawa
mutane hankali bayan wanda muke cikinsa a yanzu don ance su fito aba majiyanci waje
ya huta take fada da Habu.
Dama naso cewa a rage wanan shigowan da akeyi abar wa yanda zasu tsaya kawai
tunda ba ganinsa akeyi ba zama kawai ake zuwa ayi ta hira a zauna gida abishi da
addua zaifi.
Wanan yarinyar amaryan shi ita damu zamu iya kulawa dashi tunda zuwanta yana da
ma,ana a wajen nan ko dazun ya gane tazo don ya amsa mata adduanta da take mashi .
Kunga gara din tana zama a kusa dashi ko yaushe zaifi mama ta katseshi da fadin
abinda likitocin da habu suka fada ke nan ya zama matsala a gareta.
Ai ba ance kada ku shiga bane hayaniyace ba a so a wajensa yasa aka fadi hakan
amma ku da mijin ku a hana ku shiga ku ganshi.
Dole dai me jinyar tasa idan tana da tunane ai ta bada wuri kuma ku zauna dashi
din tunda jinya shina kowane bana mutum daya ba .
Saiba tana gefe tsaye tana sauraren mama din don a gaskiya zatace wanan matar
tana yawan shige ma lamarinta ko wani lokaci ta gaji da irin halin da mama ke nuna
mata ko yaushe idan magana irin haka ya taso zata nuna itace mara gaskiya a cikin
zancen.
Wani bangare na zuciyarta ya gargade da kada ta yarda ta soma yiwa mama rasgin
kunya duba ga yadda gaba daya family din suke ba mama girma.
Yin hakan zai iya haifar mata da wani matsalan da zai jawo barin ta gidan kai
tsaye donshi tayi shiru kamar tana daukan nasihan da mama din ke mata a lokacin.
Saiga mama din ta koma magana kamar na lalashi a gareta tana fadin kuyi hakkuri
wanan aiba komai bane idan anyi hakkuri duk hakan mai wucewane fatan mu dai Allah
ya tayar da kafadan yaron nan ya samu lafiya ku koma zaman ku yadda kuke shine
fatan mu kinji a dinga hakkuri da kuma saka basira cikin lamari.
Hakan yasa ta danji sanyi a zuciyarta har ta nemi waje ta zauna daga gefe tana
sauraren kowa a wajen .
Har zuwa lokacin dasu mama har iya suka mike suka bar cikin asibitin tare da habu
suka tafi inda ba wanda yasan inda zasu din sai su kadai.
A cikin rashin sanin hakan na fito da wanan kayan nasa da aka cire mashi da
niyar zuwa in wanke su a bakin famfo saidai kada in barshi shi kadai yasa dana fito
na nufo inda suke zaune na dan duka a tsakaninsu ina fadin.
Zanje in wanke kayan nan daya bata ko wata a cikinku zata shiga ta zauna dashi
mama din ke fadin ke nusaiba ki shiga tunda yar uwarki nada goyo.
Kamar ba zata mike ba ni dai na bar wajen na nufi wajen famfo don wanke kayan a
can Maria da salima suka sameni mun jima tare dasu a wajen don dana gama zama
mukayi muna hira dasu duk akan ciwon yaya din.
Maman tudun wadace ta mike ta shiga dakin inda ita da umma inda suka sami saiban
zaune tana waya sundan jima tsaye a kansa suna kare mashi kallo kafin mama din ta
fara magana tana fadin.
Gyara mashi hannun can daya taushe ta dakatar da wayan tana kallon hannun nasa
tace haka na sameshi na zata ko hakan yake jin dadin kwanciya din suka barshi.
Suwa ke nan fa ke yar nan ki iya kanki don Allah abinda ake fadi ke nan kuke
ganin kamar an barku baya shi jinya kula yake so kaba maishi kinga ko wayan nan
bai dace ace kina daga murya haka ba gabanshi.
Wani irin kallon rashin kunya ta jefawa mama din kafin ta mike tsaye ta nufi
wajen hannun da suke magana din tana kokarin dagawa a cikin karfi.
Haba dai yi mashi a hankali mana kinsan jikin ba karfi sai a sannu dole za ai
mashi komai yanzu umma ke fadin hakan a gefen mama din.
Ganin ta kasa dabaran yadda zata dagoshi yasa ita umma din mikewa suka kama mashi
daga shin da zasuyine suka gane yayi lalura a lokacin .
Umma din ke magana tace yanzu yaya za ayi don sai an dagashi gaskiya daga inda
mama take zaune take fadin sai takira yar uwata su dagashi a sauya mashi kayan
tunda ya bata wa yan nan.
Gabatane ya fadi ta yaya zata iya hakan amma bari ta nemo Asmau tagani suma su
nuna tasu bajintan da ake ganin basu iya din.
Fita tayi ta nemo Asmau din ta shigo take fada mata abinda zasuyi abinda Asmau
ta fada shine ta yaya zamu iya daga shi har mu cire mashi wanan kayan Saiba ?
To ya zamuyi su mama sunce mu canza mashi in bamuce haka za a barshi cikin
lalura tunda mazan basu kusa a yanzu kune dai dole a yanzu zaku sauya mashi ai.
Kayan da ya habu din yasa nazo dashi suka dauko sai nan suka tsaya dabara fita
su mama sukayi suka barsu dashi a dakin saidai sun rasa yadda zasu fara tsarkakeshi
balle su sauya mashi kayan jikinsa din.
Ita saiban ce ta fito nemana dole nice nazo a cikin karfin hali na tare da
taimakonsu muka samu aka sauya kayan na goge mashi jiki muka saka mai wasu tufafin
a ranan na kara sheda cewa dan Adam ba a bakin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login