Showing 84001 words to 87000 words out of 328222 words
Chapter 29 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
samu wajen hadaki da mama ke nan bari yar iska kanta zamu
koma ksi ba ita ba har wanan mai ido kamar glove saita bar gidan nan shiri nakeyi
sosai wallahi.
Mutumiyar kin min daidai wallahi ina son ki wajen aiki da zafinsa ai dama kin
gansune yadda suke rawan kafa su kakansu ta yanke saka yan iska don a yabeau wai ?
Tsiyar banza wa zai yabesu din sunyi a banza wallahi zan matsa naga na dawo ko
wata yar iska saina koya mata wayau a gidan nan.
Ina yinki nawa Saare din ta kara fada har da fadin Allah yasa kin hada da wanan
yar iskan duk su tafi su bamu gida wallahi ni gaba daya haushi suke bani Allah na
tsani wanan maria din wallahi haushinta yasa bani kaunar kanwarta din itama.
Sun dauki lokaci suna sherin su har mama ta shigo ta sameta duk da bataji sosai
ba ta fahinci da Saiba take wayan a lokacin.
Saida ta fitone tayi mata kaca kaca ta zageta tas tace kuma zata dauki mataki
akanta tunda abinda ta daukowa rayuwanta ke nan munafunci.
In ba rashin sanin ciwon kai ba dakece za a hada kai ana mugunawa dan uwanki
saratu matan nan fa cewa sukayi suna kyamar shi.
Watau ya dauko mugun ciwo kada ya saka masu shine nufinsu ko ?
Mama ai cewa ake wai wanan ciwon mai karya garkuwan jiki ya kwaso a can wajen
kwatakwali shine,,,,,,,,,
Mama dubu bata bari wanan matar takai karshe ba ta karbe da fadin Allah ya kare
al,umman Annabi baki daya.
Duk wanda yaiwa yaron nan wanan sheri yaga abinsa insha Allahu watau su gasu
sakatkaru shine suka yarda da hakan ko ?
To mama kokece kikaji haka da ake fada ai zaki kama kanki tunda gari haka ake
fadi sai lokacin Nafisa data shigo tayi magana take fadin wallahi ba kowa ba kan
sai dai yan sheri .
Amma kowa yasan ciwon yaya kamar sammu ko jinnu ke damunsa ta ina ciwonsa yayi
kama da wanan ciwon don Allah ?
Koma an fada banda jahilci ai suma ke nan suna dashi ko tunda mijinsu akace yana
dashi har insun yarda.
Rana mama tayi kuka sosai saida kawu yazone ake mayar mashi yace shima yaji
wanan zancen kuma mutane dama haka suke meye na damuwa haka da zancen duniya.
Ni sai da yamma dana dawo anty Nafisa take min hiran abinda ya faru nace Allah
ya kyauta mutane akwai daukarwa kansu wahala.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,
2️⃣9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
A cikin yan kwana biyun nan na rage shiga part din yaya dubashi sosai nakan shiga
da safe na bashi magani da yamma kuma in koma in bashi dama sau biyune shan maganin
haka nice zan tsaya in gyaro dakin har bayi in wanke in hada kayan daya cire na
wankesu.
To dana gama nabar part din ke nan ba zan koma ba ina dakina kwace ina karatu ko
kuma ina game a wayata don rage damuwa.
Ba komai yasa hakan ba kuma don kaucewa surutun da anty Saare ta farayi a kan mu
nida yar uwarsu saiga anty Salima ta samu pass ta dawo.
Ina dakina naji muryanta suna gaisawa da anty na hakan baisa na fito ba saida
naji tana fadin ina Ramaah namike na nufo falon a daidai kofa na tsaya na rike
labule ina fadin sannu da dawowa anty Salima.
Come up kina jina ashe kika share haka zakiyi min oyoyo daga nisa nayi murmushi
na karaso tana dauke da Abbati a hannunta take fadin.
Wai sannuku da fama fa mama ta fada min irin kokarin da kukeyi keda Nafisa Allah
ya saka da alherinsa itama iya ance jikin ba dadi nace ai dole tana kallon
masoyinta zai chala ai dole ta damu.
Wallahi yaya kan yaji jiki Yanda tace wallahi maria saida naji tsoro dana ganshi
wai kuma yaji sauki ke nan yace.
Aiki bari abin akwai tashin hankali wallahi ni naga kokarin su Nafisa da Ramaah
da ke iya zuwa ko wani lokaci dasu ake jinyasa din.
Sunyi kokari ba kadan ba maria su yan iskan matanshi ai gara da mama tayi masu
haka ta korasu gidajensu tunda jira suke ya mutu wai har sune zasuce suna kyamatar
yaya don Allah fa maria ?
In banda aure mukkadarine me yaya ya gani a wajen wa yan nan yan iska abin
namijine kawai wallahi dama mama tace kada su dawo gidan nan tunda abin nasu
iskancine haka ?
Anty Salima kun gama ke nan nake tambayata saida kalloni tayi dariya tace da
saura Ramaah saura wata hudu mu karasa yanzu.
Nayi mata fatan Allah yasa a gama lafiya ta amsa min da amin ta mike dauke da
yaron a hannunta don ta hadashi da sweet din da yake kokarin budewa a lokacin.
Ramaah taso muje mana ta fada adaidai kofan fita daga part din data tsaya hakan
yasa na yunkura na nufeta.
Wayana da yai kara shiyasa na koma dauka har ta wuce ban samu binta ba wata
course mate dina ta kirani take fada min zancen test da za ayi wanda asali ban samu
labarin hakan ba mun dan jima muna magana kafin mu kashe wayan.
Salima ta jima da fita don shi ban bita ba don bansan inda ta nufa ba a lokacin
dama kuma banda niyar fita lokacin na share muna fira da yar uwata.
Tana fita part din ya J ta nufa da yaron a hannunta suka shiga mama na falin ita
da baki suna hira don haka direct dakin yaya din ta nufa ta kara dubashi don ta
jima wajenshi dazun kafin ta fito zuwa part din mu.
Zama tayi tana mashi ya jiki ya amsa da sauki yana zaune ya jigina jiki da gado
laptop dinshi a saman cinyarsa ya mike kafa yana taba system din.
A ina kika daukoshi yake tambayanta akan yaron take bashi amsa da part dinsu
naje na daukoshi aina zata yana da kiuya har yanzune ?
Bai yarda da kowa a gidan banda Ramaah sai uwarshi dasu kadai yake yarda su
daukeshi.
Tana ina ita Rahaman yake tambayanta ba tare da ya dago daga abinda yakeyi ba a
lokacin.
Tana can ai tare zamuzo sai ta tsaya recieve din call ba zata zo ba ai don yanzu
itama kamar gudana takeyi .
Gudunka kuma yaya No ba ina nufin na kyama ba kullum itace ke ban magani safiya
da dare ta kuma gyara min dakin nan but saidai kamar akwai abinda wani ya fada mata
game da hakan da takeyi.
Haba dai ya J ban tsanmanin akwai wanda zai fada mata wani magana game da kai ta
yardda kawai dai kila don taga ka fara samun lafiyane yasa haka ?
Amma Ramaah mutum ce mai kaifi daya tana da gudun zuciya ai kaga duk abinda zai
hadata da Saare tana kaucewa don nasu baizo daya ba .
Duk kokarin yarinyar nan a kan mu wallahi saida Saare tasa ta canza mata indai ba
yanzu a bayana suka shirya ba ko shiga komai daya shafi saare batayi a gidan nan.
Laptop din ya rufe ya dago yana sauke ajiyan zuciya yace abinda nake zargi ke
nan a zuciyana tun dawowan saratu gaba daya yaran suka dauke kafansu da part din
nan don haka akwai abinda tayi masu da ba,a sani ba game da shigowan nasu.
Sosai ya sake jiki da salima suna magana wanda ba wanan bane farkon hakan sukan
danyi shawara a tsakanisu wani lokaci dama.
Shigowan mama da bakin suke fadin zasu tafi Allah ya bashi lafiya ya kara
tsarewa wanan yasa suka daina hiran da sukeyi din a lokacin.
Koda yamma yayi anty Maria ce ta tuna min don ina daki ina duba takarduna hakan
yasa na fito zuwa part din iya inda na samu anty Saarece kadai tana girki gaida iya
da yanzu ba kasafai take fita ba ko yaushe zaki sameta a falonta zaune don bata
dogon tafiya.
Saidai da safe zata kokarta ta shiga wajen jafar din kafin rana ya haska kuma ta
fito idan ta zauna sai kuma washegari zata koma fita wani lokaci kuma zaikai sau
biyu tana lekashi.
Lafiyane bata dashi yasa akace ta dinga zama a waje daya kada ta dinga yawan
fita rana saita dauki hakan ya zamo mata dabi,a yanzu.
Mun dan taba hira na fita don in samesu a can din ban kaiga fita nake jin Saare
na fadin ashe iya mama ta hakkura ta janye kudirinta akan matan yaya J jibi zasu
dawo ?
Iya tace to ai gara ta janye din su dawo ko yaran nan zasu huta duk da ko sun
dawo din aiba wani tsiyar zasu tsinana banda fitina da bakin kishinsu.
Ai gara dai su dawo din duk wasu masu rawan kafa saboda kwadayi da munafunci
suna jin dadin sun tafi ai zasu kama kansu yanzu kam.
Keko kikan fara tsiyar ki ke nan na zata maganan kirki kike min ashe da wata
manufa kike wanan maganan ?
Da wata manufane mana in bashi ba iya daidaine ace wai don sun tafi su suzake
haka suna wanan shishigin akan yaya don Allah ?
Wai fa yarinyar nan Ramaah itace harda gyaran dakin yaya tayi wanan tayi wancan
saboda kilibibi irin nasu.
Inma kilibibine dai uwarki ta saka suyi ai don haka itace babban kilibabban ke
nan ke bakiyi ba Allah ya kawo masuyi baki a laikum kuma zaki dauko sirfa ki saka a
zancen waiko yar nan kina tuna mutuwa kuwa don Allah ?
Yanzu laifine zaman amanan da yaran nan keyi damu a gidan suna iya bakin kokarin
su wajen ganin sun kyautata muna amma ke ko yaushe kushesu kikeyi ?
Anya kuwa saratu kinwa kanki tanadin alheri kuwa haka kikaga yar uwarki nayi
gidan nan baki da zance sai bakin ciki da hassada da hade haden fada tsakanin matan
yan uwaki da duk wanda ya zauna a gidan nan don ya lakaci arziki.
Daga daki da salima take kwance tana jinsu ta fito tana fadin balle ba wanan
zancen don yaya yace sai sun fadi wanda ya fada masu yana da wanan cutan a jikinshi
a zauna kotu.
To ai kinji irinta banga laifinshi ba wallahi gara yai masu hakan tunda basu da
kwabo a idanuwansu banda shirme kalar tasu yau in yana da cutan nan ai sungama
kamuwa suma yadda ake fada.
To Iya ni kuma su sukace na fada masu hakan kome iya taja tsuki tana fadin ke
arr tir da wanan halin naki tunda sunce a bakin yan gida sukaji wa zai fada masu in
bake ba ?
Sai ki shirya don ba zancen dawowansu gidan nan da har kike murnan hakan da zasu
dawo ko zasu dawo gidab nan ba yanzu ba kuwa .
Sam bata san Salima tana dakin ba da bata dauko zancen da iya ba don a zatonta
Salima na can part din jafar din data barta yasa take wanan hiran da iya din.
Tsuki taja ta koma daki kayanta take gyara dama tagama ta fito daga dakin a
dan fahintar ta akwai kamshin gaskiya ga abinda suke zargi don wanan zancen da yar
uwarta tayi tabbas da yarinyar nan Rahama takeyi.
Suna falo zaune da baki da suka shigo daga wancan unguwar tasu don haka bayan na
gaidasune nake gaida yaya din da jiki ya amsa da Alhamdullahi.
Jikin idan yabi da hakan insha Allahu an take Allah ya mayar da aniya ga maishi
wata daga cikin matan ta fada.
Kai tsaye na nufi dakin na shiga na gyara na fito na gyara wasu part din da babu
kowa a wajen lokacin matan suka mike har mama zasu tafi ita kuma zatayi masu
rakiya.
Bayan fitansu nayi kokarin share tsakiyan falon duk yana zaune muryanshi naji
yana fadin meke hanaki zuwa gaidani yanzu ?
Cak na tsaya da sharan na dago ina dan dubanshi yace bakiji me nace ba meke haki
zuwa dubana kamar yadda kikeyi a baya ?
Ba komai yaya ina zuwa school ne yanzu din na bashi amsa a saukake don gudun ya
fahinci wani abu.
Amma sai naji yace ba gaskiya bane da can baki zuwa school ne kike tsayawa kulani
?
Shiru na danyi don ban san me zance dashi ba again ya sake fadin kin taba ganin
likitan da bai duban mara lafiyansa a kai akai ?
Hakan ya bani dan murmushi kadan wanda dana sakeshi a fuskana ba tare dana san
da zuwansa ba ,wai nice likitanshi yake nufi.
Sosai abin ya ban dariya Ramaah dama ashe nan kika nufo muryan anty Salimace na
dago ina fadin nazo ance Iyatu bata nan yau shine nake dan gyaran wajen.
Dazun fa naga Nafisa na gyaran wajen nan ban kula taba naci gaba da aikina ta
zauna suna zancena da dan uwanta dake zaune ya harde kafafuwanshi saman table.
Sai dana gama na fesa kamshi na dan rakube ina fadin yaya a zuba maganin yanzu
ko sai anyi magariba ?
No banda zabi ai duk lokacin da kika ban zansha idan yanzu ko sai anjima din duk
dayane hakan yasa na juya zuwa inda flask ke ajiye a ciki muke zuba mai kunnu koda
zaki buda yana turiri da zafinsa.
Sabon flask mama taba Nafisa ta sayo don hakan suna kallona na dauko maganin na
hada na dinga juyawa daga tsayen da nake.
Saarece ta shigo falon fuskanta a daure saida ta kallo inda nake takai zaune
tana gaidashi yace ina tashiga tun safe bai ganta ba ?
Dan kame kame ta soma wai ai tazo yana barci sai kuma bata dawo ba lokacin dana
kowa kai kunnu na mika mai ya karba yana min godiya bai tsaya jirab komai ba yayi
bissimillah ya kafa kai ya soma kwankwada.
Yana sauke cup din mukai mai sannu ya amsa yana gyara zama Saratun ke fadin
amma yaya gaskiya kabar shan magani haka barkatai da baka san asalinsa ba .
Wanan abu haka kamar wani,,,,,.
Shima ai lalurane ya jawo hakan haka kawai mutum ba zai dinga turawa cikinsa
magani ba ai, salima ke bata amsa.
Ki bari na fada mashi tunda akwai wanda asibiti suka bayar a dinga sha wanan
aisai a cutawa mutum wani ciwo na daban kuma yazo ya kama mutum wurin shaye shaye.
Saare ko guba Rahama ta ban zansha a yanzu don kwai taji dadi saboda yadda
hankalinta ya tashi akan ciwona lokacin da aka fara kyamatana su din basu gujeni
ba.
Suna tare da mama a part din nan suna taimaka mata ko ciki daya muka fito iyakar
ke nan ai abinda yaran nan ke min Allah ne kadai zai saka masu da alherinsa amma ba
zan iya masu kwatan kwancinsa ba.
Baya na koma na sake shigewa cikin kitchen din nasu don banson su san da naji
zancensu don saida ta bari na juya zuwa dauraye cup din ta soma fadin hakan.
Ina jin amsan daya bata din yasa na fahinci ya gane me take nufi.
Daidai ina fitowa naji ta sake fadin Allah sarki su anty saiba sun damu su dawo
dakunansu wallahi amma mama taki yarda kome yasa mama takeyi hakan oho ?
Shine ai Saiban ke fadin kodai ana zarginsu da wani abu na dabanne yasa mama
cewa su koma gida su jira Allah ya baka lafiya.
Da suna da wayau aida basu tafi ba saidai su turo mutane a bata hakkuri amma
sun nuna abinda take zarginsu dayi hakan gaskiyane ke nan a yanzu.
Nidai har na bar part din suna zaune ban kuma koma wajensu ba na fice zuwa part
din mu na zauna ina tunanen kalamin ta tana nufin mune zamu cutawa yaya J din ke
nan ko ?
Dama abinda yar uwata ke gudu ke nan gashi ko hakan ya fara baiyana a bakin
saare din nidai bansan me muka tarewa wanan matar ba na fada a raina.
Da ace tasan cewa nice sanadin samun wanan maganin ga yaya aida abin yafi haka ke
nan da yanzu ta zarga min wani sheri da zancen yar uwata ya tabbata ace mudin yan
tsafe tsafe da gaske.
To zancen yaya nasan kamar a kunnen matanshi ya fada don sai ta kwashe komai ta
fada masu kamar yadda anty Nafisa tace ita ke kwasan sirin tana fada masu wanan
wani irin sune takewa matan dan uwan nata hakane wai ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,
3️⃣0️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Zan iya cewa a yanzu har da wasu aiyuka na daina shiga taya mama a part dinsu sai
dai lokacin