Showing 129001 words to 132000 words out of 328222 words

Chapter 44 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

kowa ban kula dashi ba mama
wallahi banjin cewa a duk garin nan kaf akwai wanda ya fini kula da yan uwana da
iyayyena ko banzo na daya ba ba zan wuce na biyu zuwa ukku ba in sha Allahu.
Aure kuma da nayi ra,ayinane mama bana wani ba ban dauki kudin kowa na auro
Rahama ko saiba ko Asmau ba ni na nemi kudina na auro matana dashi mama.
Haka kuma lalurar da nake masu da kowa da abinda Allah ya hore min nakewa kowa
tasa laluran dashi bada dukiyan wani ba.
Fada masu dai Jafaru don kona fada ba yarda da hakan zasuyi ba tunda shedan ya
rufe masu idanu akan dukiya suna son su tozartaka a yanzu don kawai abinda bai
shafesu ba kanka.
Haba dai Iya zancen nan dai nace na ari bakin kowa nace nina fadi hakan ko to
abarshi mana a haka idan zaiga laifin wani yaga nawa ni kadai ?
A lokacin hankalinsa yana ga waya da yake neman lamba a ciki ya danna kira aka
dauka yake fadin kai Nura fadawa Salis kuzo min da sakon nan ganinan gida part din
iya zaune.
Meshi ya tsaya fadin kadawone ashe yace na dawo tun jiya ya kashe wayan yana
dagowa yace mama ita anty baraka tace ban kulata ko habu ko yazid ko yaran nan su
saratu ?
Ya akeso mama anty baraka gaki dai har account naje nasaki gaba don in zan maki
sako ina shan wahala naje garinku na dukeki muka bude maki account da nake tura
maki kudi duk wata.
Koda banda lafiyan nan ina kwance haka nake tura maki kudi ko yaushe daidai
abinda Allah ya hore min shi kuma yazid dake sudan a kirashi a tambayeshi nawa nake
tura mai ko wani wata.
Balle yanzu da yake shirin dawowa gida din nan gaba daya yaran nan kuma a cikin
su waye ban tare masa lalurashi mama ?
Har wajensu kawu su fada idan akwai wano wanda ban dauke wa wani matsalan
gabanshi ba don Allah shi habu wanan tsakanina dashine ba sai na fada ba nayiwa
banza balle habu nawa ?
Kai Jafaru anji kayi hakan wanan ai ina zumunci kayiwa ko yanzu zancen hakinsu
akeyi ka,,,,,,,,
Sallaman su Nura da suka zo da jakkar bako niki niki suke shigowane ya katse
mata zancen data soma tana binsu da kallo suka shiga gaidasu suka zauna yace ku
girka a gaban kowa a gani nawane a ciki.
Habu ya shigo fuska daure yace Habu ka zauna a kirga kudin nan bari na leka su
Asmau indawo acigaba in dauko wasu takardu a can ya mike ya fita a cikon kamshin
turarebshi daya gauraye part din dashi.
Jin fitan shi daya bayan daya suke fitowa daga dakin kowa ya samu waje ya zauna
su Nura din suka shiga kirgan kudin hannunsu din tare da Habu dake lissafa masu
suna hadawa a waje daya.
Part din nasa shiru kamar ba kowa a cikinsa har ya shiga dakinsa ya dauko wani
file ya fito dakin Asmau ya shiga tana kwance kasa saman tieles tana barci ya dan
bugeta ta farka ta bude ido tana fadin ka dawo ashe ?
Yace eeh ya gida lafiya kalau ta fada tana mikewa zaune yace ina zuwa yasa kai ya
fita zuwa na Saiba daya sama kwance tana waya.
Ta jiyo ta kalleshi taci gaba da wayanta ya dan tsaya cike da takaici ya kuma
juya zuwa waje ba tare da yayi mata maganan komai ba a lokacin.
Yasan idan yace zai tsaya mata magana a yadda yaga tayi din nan ransane zaifi
haka baci haka yasa kai ya fice ya gama da wanan issue din dake gabanshi kafin ya
dawo nata a yanzu.
Kodaya koma an gama lissafa kudin kawu yana zaune sai faman gyaran zama da
yakeyi yana harde kafa a waje daya ya shigo yana fadin ya kun kammala ko ?
Habune ya bashi amsa da fadin an kammala J miliyan ashirin da takwasne da dubu
dari biyar da hamsin da tara gasu.
Yace good Nura wanan milliyan bakwai kenan dana baka ko yace ehh maigida Nura
jirashi a waje salis kai ina wanda na baka milliyan biyar ka juya din ya nuna mai
yace gasu yanzu sun kai miliyan ashirin da daya da da dubu dari biyu ga yadda muka
lissafa su.
Good Nura ina son ku zamo cikin sheduna tun a nan duniya don don Allah tunda na
baku kudin nan a juya na taba karban kwandala a hannun ku ?
Haba maigida wallahi banda lissafi da in kazo mukeyi dakai na riban da aka samu
a shekara ka debewa shago da namu hakkin ka bamu nikan kam kwandala baka taba karba
a hannuna ba.
Shima salis ya fadi to na gode idan na fito zan nemeku a san yadda za a dawo da
harkan ba tare da an samu tangarda ba in sha Allah.
Suna fita ya bude file din hannunsa yana fadin mama ga kudin nan milliyan
gomane akan ba a lokacin ni kuma na fara juyasu shine kikaji ribansu ya hau din nan
sai na samu wani business naga gara kawai in bar masu shi su dinga juyawa su na
kama tawa business din.
Wani ajiyan zuvciya ta sauke ta dago kai tana kallon kawu daya kurawa kudin ido
tace yaya kaji bayaninsa ga kudin nan yanzu meye abin yi ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

4️⃣4️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Wayansa yai kara alaman kira ya daga yana fadin ina gari ai jiya na dawo gani
fitowa yanzu insha Allah ya gama wayan ya kallo Habu yana fadin musa ne ya kira zan
fita yanzu muna son muje mu gana da mai,martaba dashi kan wani zance.
Lokacin kawu da ya kasa motsi ya dago yana fadin ai baka tafi ba ba a san yadda
za ayi da kudin nan ba yanzu Jafaru ?
Yace a,a kawu ayi yadda ya dace a kasa kudi dai anga yadda suka kama ga takardan
nan Habu sauran bayani suna ciki kaima kuma nayima bayani a baya.
Akwai gina dana dora dakai da Yazid wanan nayi niya ba zan fasa ba in sha Allah
don ma wanan gidan da zan maida matana a can da ake gyara da yanzu na kammala maku
ginan ai amma na dakatar ina wanan gyaran a yanzu.
Duk dai wani bayani leter on zakaji idan mun zauna yanzu barin je in samu musa
mu karasa dashi don tafiyan nada muhinmanci sosai a wajena.
Har ya daga ya juyo yana fadin anty baraka yau ne zaki tafi idan an raba ko
kina nan tukunna ?
Kafin tayi magana iya ta karbe da fadin yoo me zata zauna yi an raba an bata
kasonta tunda dama donshi tazo mijinta nacan yana jira ta kawo mai kasonta shi da
yayanta ai gara dai ta tafi tun yau din zai fi ai ?
A gaskiya mama zamu samu matsala fa da Iya ni kadai iya ta gani da zata
tsargeni kan zancen nan in ma tsarguwane ai saratu ya kamata ki tsarga iya bani ba
ita data daga waya ta kirani inzo ga halin da ake ciki.
Amma in aka tashi magana iya tace waini haba iya kada ki hadani da dan uwana mana
don Allah ?
Iya tace ai ke kikazo da zafi kina sakina sakin magana akan dan uwan naki yanzu
aikin fada da bakinki cewa ga haddasanar data jawoki ta fada maki karya da gaskiya
kuka hau ke da iyayyen ki da suka biyewa haukan ku.
Har cewa kikayi a nan jafar baya taimaka maki da komai a rayuwa sai kin rokeshi
amma baki fadi alherin dan uwanki zuwa gareki ba sai yanzu daya fada a gaban mu.
Nina sani kuma na fada ko a bayanshi jafar namijine namijin dutse da ba a gane
gabanshi sai dai bayanshi .
Yaron nan kamar yadda ya fada yana iya kokarinsa wajen ganin ya daga gidan nan
ya kare martaban kowa amma kuka fahinceshi a mumunan zato irin haka ?
Yanzun dai aiga kudin nan ya aje maku agaban ku sai ku rike kuda kuka fishi iya
rikon ya dai fita bakinku yanzu kan ya cinye kudi ya handame komai shi kadai yana
aure aure yanzu sai ku samu sabon camfi ku zarga mashi kuma tunda kun zama yan
sheri.
Kai dauda ga kudin nan sai ka dauka tunda hakkinkane yadda naga ka damu akan
zancen nan bai kamata yadda kake da yaron nan ace ka goyi bayan haka gareshi ba ai.
Nifa iya ba goyon baya nayi ai masa wani abu ba illa goyon bayane tunda masu
abu suna bukatan abinsu ai masu abin kafisu bukanshi nake gani iya ta fada.
Habu ya mike da niyar fita lokacin mama da jikinta yai sanyi ta kasa magana tace
kai kuma ina zaka ana batun kasa kudi shi ya fita yace yana da uzuri kai kuma zaka
fita yanzu ?
Mama ai dole sai an kira malamai a cikin harkan nan bamu zamuyi bugun gaban mu
ba wani yazo daga baya yace an cuceshi kuma.
Zanje tudun wada in dauko su malam idi suzo a yi yadda shari a yace bayan sunji
abinda kowa ya mallaka da farko aka hada akai wanan abin.
Wani malam idi zaka kira anan ko iyamu bamu isa mu fasala kudin nan ba ba tare
da mun kira wani bare ya shigo ba kawu ya fada.
A,a kawu Allah yace Annabi kuma ya fada ya umurce mu dayin adalci a cikin
lamarin mu don haka kudin nan ba wanda zai tabashi sai masana sunzo su kasa subawa
kowa nasa a hannunsa kamar yadda yake a shari,a.
Kuka mama tasaka ta mike zuwa daki wayan habu dake ta haske a hannunsa ya kasa
dauka saboda maganan da yakeyi a lokacin.
Anty Baraka ke fadin wayan ka habu tun dazun ake kiranka fa ya kai hannu ya
dauka yana fadin yazid ne ashe ?
Ya daga wayan yana sallama yace yazid ya akayi suka tsaya gaisawa sai ya saka
wayan a hands free kowa naji yazid din yace zancen kudi idan an raba a mayarwa J da
nawa kason yacigaba da juya min sai nadawo.
Nima yaya na fadama abawa yaya J ko kai nawa salima ta fada daga gefe kawu ya
dago kai ya kalleta tace kada abawa kowa nawa abarshi a hannun ku don Allah.
Kai wanan abin dame yayi kama yau ace yanda yaran nan suka taso maku a cikon
biyayya wai kune kuma masu raba kan yayan nan yanzu ?
Ban taba zato ko tsamanin haka ba gareku dubu yau ace kune kuka fitowa yaran nan
da wanan lamarin don mutum daya ko biyu zuwa ukku sun zugaki suna son ganin
farincikin ahalinki ya ruguje.
Yau badon yaran nan wasu nada hankali a cikin su ba kin hada fitinan da koke
baki iya rabashi dubu saukin abindai ba a taru duka an zama daya ba.
Bayan fitan su da salima na kwashe kayan abincin daga dinning zuwa kitchen na
tsaya ina wankewa nan anty Nafisa ta sameni a kitchen din.
Muka gaisa take tambayana yayama ya fitane nace tare suka fita da anty dazun nan
muka tsaya muka dora abincin rana wanda muka hada sakwara dakan hannu tunda ba wani
yawa garemu ba leda hudune har maigadi itace ta daka nayi miya muka gama nashirya
komai kafin mu shiga daki yin azahar.
Daga nan na dan kwanta don in huta sai wajajen karfe hudu saura ya dawo gidan
shima a gajiye ya shigo don tun fitansa bai samu ya huta ba yana ganawan da yace
zaiyi din ya fito mutane kuma suka taru akansa.
Tunda sunga har yayi matsayin da zai gana haka da mai,martaba to lalai yaron
akwai kudi ko ilimi a wajensa ke nan dole dai yana da madafa.
Irin kudin daya basu yasa suka gaskanta hakan da suke zargi ana tambayan
dangidan waye ana fadi suka gane mahaifinsa kowa waye shi agarin.
Ina kwance anry Nafisa ta shigo dakin tana fadin Ramaah ina son inje gida in dan
leka su inna kada ace nazo nan na zauna kuma .
Haba dai anty amma zaki dawo ai na fada da sauri tace bako yau ba sai idan yaya
baya gari kada inyi rashin hankali mana Ramaah in yaya ya girmeni aike baki girmeni
ba ?
Hankali kuma hanjine ai mai yasa kikaga ya raboki da gidan yawa ya kawoki nan ke
kadai aidon ku huta dukkan ku yayi hakan na noke fuska ina murmushi.
Tace to kingani in sha Allahu idan bai gari nayi maki alkawarin zuwa har in
kwana amma yanzu kan nima ina son dan uwana ya samu natsuwa a rayuwanshi ya gane
yayi auren zamani shima irin na sauran maza.
Na mike tsaye na sake fadin da kijira yaya din ya dawo sai ya kaiki mana tace ai
banson ya dawo ya sameni dinne yasa zan wuce yanzu.
Don Allah Rahama kiba marada kunya ga wanan aure ido aka saka aga matsala koda
kadanne kema daga wajen ki ace mashi gwai don haka ki daure ki koyi son shi a
zuciyarki.
Har duk wani abinda kika iya ta bajinta ki gwadawa yayashi Rahama ki kawar da
kunya dajin nauyi a yanzu shi mijinkine ba wa ba don haka saikin zage kin dai san
bakin ramin kura kike.
Haka kuma ki kara hankali da mu yan uwansa kindai san komai za azo a dinga bukin
cikinki kamar da gaske sonki akeyi sai idan anji sirinki a koma bayan ki ana zunden
ki.
Duk abinda ya shige maki kai ki kirani in sha Allahu har idan na sani da yardan
Allah zan haska maki shi a yanzu zan nisanceki kada a zargemu amma akwai waya na
nan komai ke nan zamu dinga waya dake in sha Allah
Na dago kai cikin yanayin damuwa ina fadin nagode anty Nafisa a gaida ummu amma
ina zuwa don Allah na fada zuwa dayan dakin dake rufe turmin zani na dauko mata da
wani dogon riga sai su sabulai da turare na dibo kayan buki mai yawa na kawo mata
ina mata godiya.
Har bakin kofan falon na rakata tace na tsaya nan ta tafi na sauke ajiyan zuciya
na juya zuwa ciki ko ina na gidan nabi da kallo wai yau ni Rahama nice ubangiji
yaiwa wanan baiwan a lokaci guda haka.
Alkawari na dauka zan zauna da yaya tsakani da Allah in masa biyayya kamar yadda
shari,a ya kidanyawa mace tayiwa aure biyayya kamshi na fesa a falon har zuwa
dakinshi dana shiga ns gyara mai hakan yana daga cikin abinda ke hadashi fada da
matansa nasani yasha korafi kuma a gabana cewa ko muhalinsa babu mai iya gyarawa a
cikinsu sai inya gyara da kanshi.
Na koma daki ke nan na tayar da sallah naji dawowanshi bai shigo ba sai daidai
na idar ya shigo har dakin nawa da sallamanshi na na shafa addu,an na juyo ina
amsawa tare da furta sannu da dawowa a gareshi.
Yauwa amarya ta yaya kike ya amarci kuma ya fada yana karasowa inda nake zaune
saman sallayata ya rage tsawonshi zuwa tsugunni yana fadin ya gidan Rahama hope ba
matsalan komai dai ?
A,a bakomai na fada ina kokarin dagawa ya mike yana miko min nasa hannun alaman
in kama in mike ai zan iya na fada .
Baki son na taimaka maki ke nan ya fada a,a kada dai in wahalal dakaine kawai
banso amma da karfina ai zanyi iya mikewa.
Wayau ko ya fada to ban yarda ba ya fada banyi aune ba sai naji ya sukuceni baki
daya zuwa bakin gado dani ya aje zakice ba yaya Jafar bane a lokacin.
Hijjab din wuyana daya kula ya tauyeni kamar ya shake min wuya don yaga inata
kokarin sasautawa da hannuna hakan yasa ya dan kara rankwafowa saitin fuskana yana
kokarin cire min daga jikina.
Ina jin yadda ya sauke ajiyan zuciya lokacin da yayi arba da suran jikina daya
dan baiya afili daga yanayin dinkin rigan jikina.
Dagawa yayi daga rankwafin da yake naga yana shafo suman kanshi da hannunsu wani
irin soyayyata yana fisganshi lokaci guda duk ya dan daburce yana fadin kinci
abinci dai ko ?
Bana jin yunwa na bashi amsa a takaice ina mikewa daga yadda ya barni a kwance
don irin kallon da naga yana kare min sai lumshe ido yakeyi a cikin wani yanayi na
gajiya.
Da alama baki son cin abinci Rahama kosai na zauna kwana biyu ina baki da kaina
zakicine ina kula ko dazun bakici komai ba koso kike antyn Abuja tace ina maki
sakacin kiyon ki ?
Ni ba sai ka zauna ba dama haka nake ba ko yaushe nake cin abinci ba sosai nafi
son abu mai ruwa ruwa dashi na saba rayuwata da nake zuwa kiyo a rugga.
Hannu yakai ya ja min hanci yana fadin bazan taba yarda da hakan bani donki na
aje komai a gidan nan Rahama.
Kici sai kince min kin gaji da nau,insu na cabza maki wasu don kanki saina turo
baki cikon shagwaba ina dan kauda kaina gefe daya.
Yayi murmushi yana fadin watarana basai nace kici ba Rahama kece dai zaki
dameni da inci din ranan da kika haifa min kyawawan yaya masu kama dake ba zakiso
ko kudi ya sauka a kaina ba lokacin.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login