Showing 24001 words to 27000 words out of 328222 words
Chapter 9 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
juya harshe a cikin turanci tana
fadin muje mana me zamu tsaya yi kuma ta juya tana fadin excuse me please a cikin
sallon turancin dake bakinta.
Kallon juna sukayi tun lokacin suka fara mamakin anya bafulatan dajice wanan
kuwa suke tambayan kansu cikin zuciyarsu.
Bana fada maku ba babu inda tai kama da yar daji yadda kuke fada yaya Habu fa
duniyane dama nasan za a rina kallon kowa yakeyi kar a gidan nan.
Leda ta kawo masu shake da kayan buki ta mikawa Sare data santa tun jiya tasan
kanwarsu Abubakar dintane ita.
Ke wanan kuwa anya yar dajice wayewanta yayi yawa ko fuskanta kagani kasan wanan
ba yar kauye bace.
Ai ba wayewa ko kauyanci akajawa a aure ba hali ya kasance tana da halin kwarai
shine zaman lafiya ga ko Asmau ta fada.
A harzuke ta juyo tana fadin to me kike nufi da zancen ki da bani wanan amsan a
yanzu Asmau nifa irin zancen nan naki na gugar zana kin san shike hadani dake
Asmau.
Nan fada yaso ya fara a tsakaninsu Sare ce ta dakatar dasu da take fadin wanan
ai saiku nuna mata irin zaman da kukeyi a nan itama ta fara.
Jin hakan yasa Asmau tayi gaba ta barsu a baya son ita dai bataga abin laifi a
cikin zancenta ba kawai dai Saiban ce kamar a jirace take da ita lokacin.
Fitowan Ramah daga wajensu mama dubu yasa su duk binta da kallo suna mamakin
yaran don wanan koba a fada ba kanwar wanan amaryam Abubakar dince da suka fito
wajenta.
Ya Allah wa yan nan diya akwai halitta dole yaya Habu ya rude a kansu ji wanan
karamar don Allah zakice itace ta halicci kanta wajen kyau.
A can wajensu mama dubu baki yan kawo amarya suka sauka don iya tace ba mai
zama a wajensu a bata masu part din don akwai dakuna a wajenta shine aka gyara masu
daki guda suka sauka a ciki.
Babu wani laifi a nan din don ina aka saka ake faman yi dasu tun jiya da suka
iso garin abincine iri iri kafin su bude wanan wanan ya iso sun rasa wani zasu taba
a ciki.
Karasawa rama tayi cikin dakin tana fadin a cikin fulanci anty Yanda baffa yace
ki fito kiyo hakan ne ya basu dariya ita da kanwar nata lokaci guda suka zauna suna
hiran baffa Buga da shu,umancin daya nuna masu a baya.
Allah ne ya kwatomu Ramah don babu da amanan baffa Abban mu baici amananshi ba a
rayuwansa amma ya azabantar damu haka a gidansa.
Kinga matan gidan nan da suka fita yanzu matan yayan Abubakar ne sune abokan
zamana a gidan nan saidai na fahinci kamar akwai zaman lafiya a tsakaninsu don suna
fita nan suka soma fada.
Tsoro nake ji Ramaah zama da irin matan nan akwai fitina da barazana irinsu ba
zasu barka ka huta a rayuwanka ba da ace ba gida daya muke a zaune dasu ba hakan
yana da sauki.
Babu ruwanki dasu tunda ba a bangare daya kuke zaune ba suyi harkansu a can muyi
namu a nan dani dake.
Murmushi tayi tana bin kanwar nata da kallo tasan Ramaah da iya fadin zance kalma
daya zata fada ya wadatar da abokin zancen ta.
Kwana biyu yan rakiya sukayi suka juya bayan nasiha da kuma jan kunne da sukaiwa
yaran nasu da sanadin aure ya rabosu dasu zuwa nan yanzu.
A dan zaman da sukayine suka har sun fahinci wasu abubuwan dake faruwa a gidan
wanda suke son natsuwa da gyara a kansu donshi suka tsawatawa ita Yanda din.
Sun tafi a ranan kuma Yanda ta fara girki a gidan bisa umurnin mama data bata
baki data dora abincin darewa mijinta.
Hakan ya bata daman zagewa ta dora girki tare da amfani da sanadaran da sukasa
gidan gaba daya ya dauki kamshin dake tashi a girkin.
Tuwon shimkafane da ya tuku yayi laushi kamar ba shimkafa aka sarrafa ba ga
danko ga leda fara data kwashe a ciki daga nan suka kara mayar da hankali ga miyan
da suka dora wanda kowa ke son ya dandana yaji dadinsa.
Miyan bindin saniyace ta dora sai miyan yauki na agwano da dan karkashi kadan
yaji daddawa da kayan kamshi a gargajiye.
Tayi hakanne don hiran da sukaji iya nayi cewa mama ta huta da tambayan tuwo yau
maciyi tuwo yakai ga matar da zata tuka masa tuwo yadda yake so yaci sai ya koshi.
Sun kammala an zuba waje uku suka shige yin wanka don itace kusan karshen shiga
wanka a lokacin.
A falon ya J Saiba ce ta fito rugume da yarta tana fadin yau kamshin meke tashi
hakane a gidan nan ?
Asmau dake zaune ta dago tana fadin nima tun dazun nake jin kamshin nan yana
shigo min wata kila a part din iyace kamshin ke tashi.
Baki saiba ta tabe ta gyara zama tana fadin kamshi kamar wani girkin kwarai ina
bafulatana ta iya girki banda tatsan nonon shanu.
Badai gyaran gyaran ba tayi mai wanan da gani daban take a cikin fulani don tayi
kama da wace ta zauna a birni ba a cikin daji ba.
Bayan magariba Ramaah tayi sallama part din Iya ta sauke kayan abincin data
dauko niki niki tana gaidasu inda suke zaune.
Abincine Yanda tace na kawo cikin murmushi mama tace a,a abincin hardamu aka
sakawa angode aida tayi iya bakinku sai mijinta.
Sare ce ta mike ta karba suna fadin sun gode har Ramah din ta juya taji muryan
mama na fadin.
Nace ba idan kun karasa aikin a can anan wajen Iya zaki dawo da kwana idan kin
karasa saiki dawo nan din ki kwanta kinji.
Ta amsa a ladabce ta fita na part din ya J ta dauka ta mika masu inda ta samesu
zaune a falo duk da hiran nasu ba wani hiran arziki bane mai tsawo.
Amma ya zama dole garesu don dokan da maigida ya kafa a kansu yanzu kuma kowa
na tsoron yayi abinda zai bantale masa auren a lokacin da suke jin dadinsa.
Gaidasu ta fara a falon ta dire abincin acikin wani kula mai kyau tana fadin
abincine daga wajen amarya a gyatsine Saiba ke fadin ta aje a saman table din.
Babu wace tace angode a cikinsu ko a gaidasu da mai girki ba wace ta iya fadan
hakan a cikinsu haka yarinyar ta fita tana mamakin hali irin nasu.
Part din yar uwan ta koma taci abinci saida ta gama ta mike take fada mata abinda
mama dubu tace dan shiru yar uwar tayi indai son samune taso a barta da yar uwanta
da take amana a wajenta yanzu ta zauna a wajenta din.
Saidai ba yadda zatayine don umurnin mama dubu ne hakan tayi mata saida safe ta
fita zuwa part din tsofin don ta fahinci ana son ta bar ango da amaryansane
lokacin.
A bangaren yaya Jafar kuma Ramaah ta fita bada dadewa ba saiga maigidan ya shigo
suna mai sannu da zuwa ya amsa tare da bin kulolin da kallo ya kai zaune yana fadin
wanan abincin fa ?
Daga bangaren amaryan Habu aka kawosa Saiba ta fada tana mikewa donta dauko
mashi abincinshi da suka girka a part din.
Saidai taja ta tsaya tana bin maigidan da kallo wanda ta sama ya bude abincin
yana zubawa tare da yaba yadda aka tsara komai cikin nuna wayewa da zallah gwaninta
tare da iya tsabta da kuma sanin darajan dan adam.
Bai jira wani cewa ba ya mika hannu ya fara serving din kanshi saiga Saiba ta
fito da only warmer din data zuba mai ja,loop din taliyan da tayi na manja.
Tunkan ta karaso ta soma magana tana fadin wanan abincin yarincan ne fa ga
abincin ka nan na dauko maka ?
Bai kullata ba yacigaba da zuba abincin a cikin plate iya yadda zai iya tare da
fara zuba miyar yana jin wani irin tukuki a da zafin matan nasa na yadda basu iya
tsayawa suyi girki haka irin da malam bahaushe ya sani saidai shiririta irin na
shirmey din nan da matan yanzu keyi saboda sakaci.
Mikewa yayi ya wanko hannunsa ya dawo ya zauna yana shirin zamane ta kara fadin
J fa bafa nina girka ba wacan yarinyar ce matar Habu ta aiko muna dashi.
Bissimillah taji yayi yana yankan tuwon ya fara kaiwa a bakinshi tare da lumshe
ido don jin yadda tuwon ya hadu tsab rabo da yaji tuwo haka tun suna gida
mahaifinsu yana raye mama na girki ta saka masu.
Komai yaji acan acan kayan yaji na gargajiya sai dandanon daddawa ga kuma
kamshin man shanu dake tashi gwanin ban sha,awa.
Daidai Asmau data gama shirya danta ta fito dashi rugume a hannunta itama
tabishi da kallo tare da mamaki ta zauna a saman kujera.
Wai ikon Allah yanzu girkin nata zakaci J ya dago yana kai loma a bakinsa ya
hade yake fadin wai wanan din sunansa me kin isheni da wanan abin da kike dafa da
sunan abinci.
Wanan din shine muka sani da abinci a gidan nan ba wanan shirmen da kukeyi ba ku
diba yarinya karama tasan ta girka wanan abincin hakawa mutane ?
Ku me yaci karfinku da ba zaku iya ba ya dauko gutsuren nama ya kai abakinsa ya
lumshe ido kallon Asmau saiba tayi cikin mamaki itama ta lumshe idanunta.
Tana fadin wai bari dai nima naci naji hannun ta da akewa yabo haka ta fara
serving din kanta itama saida ta loda taja plate din gefenta ta fara ci.
Loma biyu taci ta dago tana fadin kici kiji abincin ya hadu gaskiya ba laifi
kici don Allah murmushi tayi cikin takaici tana kallon kulan dake hannunta ta
dangware tana fadin wanan ai baiyi ba.
Ta fara jan plate din ta bude ta zuba kadan don ta gano matsalan abincin ta fada
ta soki wanan girkin da taga suna santinsa.
Saidai ta cinye wanda ta zuba din ba tare da tasan tayi hakan ba shiko maigidan
ya tashi da duk abincin ya koma cin naman da bai jin zai gaji da cin wanan naman da
kamshin sanadarin girki ke tashi a cikinsa.
Da sallama ya shigo tana zaune tana addu,a saman sallaya ta juyo tana amsa
mashi sallaman babban rigan sa daya ishe,shi a jikinsa ya debe ya sagalo a hannunsa
ya dora saman kujera yana zama.
Shafa addu,an tayi ta mike tana fadin sannu da dawowa yaya Habu kai ya dago ya
kalleta jin yadda ta kirashi a ranan sabanin yadda ta saba kiransa da dan zaria.
Murmushi yayi yasan wanan sunan a bakin su Sare tajishi kallamane da kannesa ke
kiranshi dashi dole a wajensu taji wanan sunan.
A cikin muryanshi mai natsuwa yake fadin amaryata ya zaman kadaici ina Ramaah ya
dan fara dube dube yana neman yarinyar a zatonshi tana daki zaunene.
Rigan daya aje ta dauka tana fadin tana wajen su mama tun dazun au ke kadai ta
bari nan ke nan ya fada yana kallonta cikin so da kauna tare da godiya ga ubangiji
Allah daya nufeshi da samun wanan tsatsiyar yarinyar a matsayin mata a gareshi.
Wanka zakayi ko sai kaci abinci muryanta ya katse mashi tunanensa ya dago ya
sauke mata kallo yana fadin bari muci abincin sai na shiga gaba daya.
Ta juya ta shige ciki ta aje rigan ta fito ta sameshi ya lumshe ido yana godewa
Allah indai Yanda tacigaba da hakan a rayuwanta zaifi kowa murna da aure a
rayuwanshi.
Ga abincin can na jera a dinning ta fada ya kalli daning din ya hango kuloli a
jere gwanin ban sha,awa ya lumshe ido yana mikewa tare da kamo hannunta .
Idonta tayi saurin lumshewa lokaci guda tana maijin wani iri a zuciyarta basu
nufi dining din ba sai ji tayi yakai mata runguma yana sauke ajiyan zuciya da itama
shita sauke lokaci guda tana hawaye.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
11️⃣00️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Rayuwan aure mai tsabta suka shimfida a tsakaninsu a ranan inda yakwana yana
lalashin amaryan nasa wace ya sameta da mutuncinta da kimarta na ya mace.
Zamanta a daji ko rayuwan birni baisa ta zubar da kimarta na ya mace ba a waje
daga shi har ita sun shiga wani hali bayan zazzabin daya rufeta zuwa safe hakan
yasa ya fara tsaguwan kansa tare da tuhuman kansa dabai rangwanta mata ba.
Wanan yasa daga masallaci part din iya ya nufo ya samesu a falo suka gaisa nan
yake fada mata cewa Maria ce ba lafiya.
Wallahi tun asuba jikinta yai mugun zafi tana kuma rufe da bargo tana rawan sanyi
ko asibiti zasu tafine da ita ?
Haba dai kaje iya na tafe mama ta bashi amsa lokacin na fito da tsinya a hannu na
tsuguna ina gaidasu da kwana na wucesu ban tsaya ba.
Tsakar gidan kamar yadda muka saba share gidansu hjy a abuja hakan na duka na
fara shara.
Don gidan yana bukatan gyara saboda gidan tunda akai buki ba a samu wanda ya tsaya
ya gyara wajen ba ganin hakan yasa na kwana da niyar gyara wajen na fito tunda safe
.
Daga bangaren Anty yanda na fara na gangaro dayan part din da babu kowa a
cikinsa har zuwa part din wa yan nan matan dana shiga jiya nakai masu abinci.
Duke nake na shagala naji mutum a kaina yana gaidani na amsa kafin na duka ina
gaidashi farine dogo yana saye da jallabiya a jikinshi suna da kama sosai da yaya
Abubakar.
Saidai yaya Abubakar bai kai wanan fari da tsayi ba shi wanan jin dadi ya huda
jikinshi kallo daya zakiyi mai ki gane yana jin lokacinsa.
Duk a kallo daya da nayi mai na zayyano wanan kamanin nasa dana hango lokaci guda
tas nayiwa gidan kafin na samu komawa part din iya inda na fara gyara tare da
tsabtaceshi na fito falon daga kitchen dinsu dan soma sharo falon na iya a lokacin
ya kara sallama ya shigo wanan karon ya sauya tufafin jikinshi zuwa wasu kananan
kaya zakice shidin ba dan hauwa bane .
Kayan sun matukar karban jikinshi sun fitar mai da kurciyansa a fili saiki rantse
bai taba auren farko ba suna fadin Abubakar yayi rigima wanan mai mata biyu din
ashe shine mai rigima din.
Mama dake zaune tana jan tasbaha a hannunta ya kalla yace wai ina kuka samo
wanan yar mama tun dazun naga tana aikace akaice gidan nan ?
Kai dai bari yar albarka yar uwar amaryan Habuce da suka bar mata ita a nan
shine ta tashi da wanan aikin ina su Sare ya tambayi kannensa mata .
Wa yan nan mashiriritane ai suna daki kwance ko gyaran kwanciya basuyi ba balle
susa niyar tashi iya fa ya tambaya ?
Ta shiga gun Habu ta duba amaryansa ina ganin yarinyar yar albarkace yazo wai
zai kaita asibiti nace iya ta fara duba mashi ita a gani.
Fuska ya daure a cikin wani yanayi ya kai zaune yana fadin da anbari sun tafi
asibitin kada wani matsala ya biyu baya kuma.
Inba zamani ba ba komaine ake zuwa asibiti ba rashin sabone ga dai iya din can
taje ta dubata ai tun dazun wayansa aka kira ya dauka ya cigaba da wayan karshe ya
mike ya fita.
Saida nagama aiyukan gyaran ko ina na nufi part din antyna inda nayi mamakin
ganin tsohuwar a wajen ban tsaya ba na gaidasu na shiga dakin da kayana suke ciki
wanka nayi na gyara jikina fes kafin na fito na samu tsohuwar ta fita daga wajen.
A hankali nakai zaune ina duban kofan antyna din duk da ake cewa mu fulani bamu
da hankali kankantana a lokacin baisa na fada dakin nata ba kai tsaye don muna da
tarbiya zaman muna birni bai barmu da duhun kai ba.
Bayan hakan kuma gwargwado muma fulani muna da namu addinin munsa abinda yake
daidai da wanda bai dace muyi ba balle bamu taso cikin duhun kai ba ai.
God so kind na iya kunna gas tun a abuja wanan yasa jin yayata shiru na fada
kitchen tare damu mahaifiyar da yayata sukewa hjy Yaghana girki da mijinta .
Haka diyansu su anty salma idan suna kasan nan mune suke sakawa muyi masu duk
wani girki da zasuci har su bar kasan nan.
Zaman na shekara biyu da rabi ko ukku a wajen baffa baisa komai ya fita kanmu ba
tunda a cikin hakan muka tashi.
Haka yasa na dora ruwan zafi na debo dankali na fara ferewa ruwa yayi zafi na
juye a flask na dora suyan dankali duk a zatona suna dakinsu kwancene basu tashi ba
kafin wani lokaci nagama hada breakfast na zuba a kula na fito daidai lokacin ya
Habu ya shigo gidan da ledan magani a hannunsa.
Zaka gane anyi girki don kamshin da gidan nasu keyi gaidashi nayi da dawowa na
juya zan fita ya tsaya yana fadin kinyi breakfast ne Ramaah ?
Ehh na hada yaya gashi can a dining na fada a dan ladabce yadda mukewa su anty
salma a