Showing 114001 words to 117000 words out of 328222 words

Chapter 39 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

daddy a kaina.
Yadda duk na fara fita hayyacina tunma basu fada min kome yake faruwa ba kaina
dago cikin yanayi na damuwa da alaman tambayan ku fada min kome yake faruwa mana.
Sai naji daddy yace kiyi hakkuri Rahama a matsayinki na musulma ya kamata ace
kin yarda da kaddara mai kyau ko akasinta.
Don haka ki kaddara hakan da zan fada maki kaddaran kine haka muma iyayyenki
bamu isa mu sauya maki kaddaran kiba Rahama ?
Kai na gyada a hankali haka kuma indai har kin yarda da mu iyayyenkine kinsan ba
zamu cuta maki ba to ina son ki kara daukan hakan da gatan iyayye akai maki aka
daura maki aure ba tare da sanin ki ba.
Zubur nayi na mike dakyau zaune ina binsu da kallo ga anty salma kallona ya
tsaya sai naga tana min murmushi da a lokacin na fassarashi dana kiyayya a gareni.
Mama ta karba da fadin kakanku hardo ya daura maki aure kwana ukku da suka wuce
da dan uwan mijin Maria yar uwarki.
Ina fatan zaki dauki hakan a kaddaranki kin dai san ba za a hada kai damu a cuta
maki ba Rahama ?
Don haka kamar yadda daddynku ya bukata ki zamo mai biyaya ga mijinki haka kawai
da zakiyi shine zaki nuna matsayin mu na iyayye a wajen ki yanzu.
Haka muma zamu san Abdullahi ya bar muna marayun Allah mun kuma runguma a bayansa
.
A iya binken daddynku wanan yaron baida matsala asalima taimaka muna yayi a namu
ganin da wani yazo wanda ba a sanshi ba ba asan halinsa ba ya aureki daga baya azo
ana samun matsala kuma?
Hakan yafi muna kwanciyar hankali dake har mu don ansanshi ansan koshi waye haka
kuma ki zauna gashin kanki yafi zamanki a haka hankalin mu kullum a tashe kanki.
Shi aure rahamane ga bawa alherisa yawa garesa don ba akanka kadai kaida kayi
auren abin ke tsayawa ba yakan shafi har wanda baka taba sani ba.
Allah ya taimaka hawaye sun zubo min don sune saukina a lokacin da ace ban samu
sunzo min ba a lokacin komai yana iya faruwa dani wajen.
Kinsan mu fulani da busashen zuciya toni a wajena wanan hawayen da suka zubo min
sune saukina a lokacin saidai duk da hakan saida faduwan gabana yakaini ga sulalewa
kasa cikin kaduwa.
Salma da mama sukayo kaina da sauri suna kiran sunana da Rahama Rahama haba dai
wanan abin ai bakai har na daga hankali haka ba ke nan baki yarda da hukuncin mu da
kakanki hardo akanki ba ke nan Rahama ?
Mamace ke fadin hakan cikin kaduwa da halin data gani a ciki shiko daddy namijine
yana zaune ya harde kafa yana zuba murmushi kawai daga inda yake zaune yana magana
a cikin yaren kanuri yake fadin.
Su kamani zuwa daki ba komai bane kaduwane zan sake idan zuciyana ya samu nasuwa
amma a kira doctor zainab ta dubata.
Haka suka kamani zuwa dakin mama saman katafaren gadon mama din suka kwantar dani
tare da kunna min AC dakin daya kara sakarwa jikina yanayin zazzabi sai gashi na
fara rawan dari a hakan doctor din tashigo ta sameni kwance.
Allurai tayi min dama shine nasu tare da maganin da zansha indan watsake tace a
barni in samu barci idan na tashi komai zai tafi in sha Allahu.

ZARIA
Suna zaune gaba dayansu falon iya ga abin karyawa a aje amma sun kasa karyawa
sai Salimace data fito ta zauna ta dauki kofi tana tsiyaya ruwan zafi a ciki.
Iya ta nisa tana fadin tsiyaya min ruwan zafin nan yar nan kada hanjina ya nade
ga banza banga abin tsayawa tashin hankali wajen nan ba.
Don yarinyar na tafi gidansu kan mijinta ya kara aure za a zauna a daga hankali
haka ?
Ita da aka aurota ba hakkuri taga yar uwarta tayi ba wani irin iya shegene basuyi
ba a gidan nan da aka kawota saida aka koma ba yan uwan uwargida hakkuri.
Ke dubu lamarinki yana daure min kai wallahi ni banga abin daga hankali ba
wajen nan
Yaron nan aure ya kara ba wani mugun abu ya aikata a rayuwansa ba amma kin daga
hankalinki haka ba tunane ?
Iya ba haka bane ban damu da aurensa ba don shi yaga yana iyawa ni damuwata
shine ya bada dukiyan yan uwasa dake hannusa .
Ba zan zuba ido ina kallo yana facaka da dukiyan yan uwasa a saka mai ido
Iya yaran nan sun san da dukiyan su yana hannun Jafar yau ace kuma Jafar baida
aiki sai aure aure yana facali da dukiyan yan uwansa na kallo ?
Haba mama haba yaya jafar ba zaiyi hakan da kike tunane ba wallahi in ma wani ya
zugaki wallahi ya dauki alhakin shi don,,,,
Ke kinci gidan ku zan saba maki rai yanzun nan kul kika kara tareni idan ina
maganan nan me kika sani ke da shirmen banza ?
Salima ta hada shayinta ta fita daga falon zuwa waje bayan ta mikawa iya nata
part din ya Habu ta nufa ta samu ya fita tunda safe sai Maria data samu zaune ga
Abba yana wasa a gefe ita kuma tayi tagumi idonta yayi ja jajir alaman taci kuka
har ya isheta a lokacin.
Haba dai Madam ba dai kuka kikayi haka akan wanan zance ba kada ki zama wata
mara godiyan Allah mana naga hakan farin cikinkine gaki ga yar uwarki a gida daya.
Yau dai kinsan ko waye yaya Jafar kinsan kuma tunda ya zabi hakan ya shiryawa duk
wani barazanan da za a tunkareshi dashi gidan nan.
Takai zaune da kofin shayinta a hannu tana fadin ni ina mamaki da kuka kasa
gane waye yaya J ?
Ai ki zuba ido kawai kiyi kallo ina fada maki duk abinda sukayi a baya suna
ganin sun gama dashi a yanzu zasu girbi abinsu bawan Allah nan ya dade da bakin
cikin wa,yan nan matan nashi a zuciyar shi amma an kasa gane hakan.
Mezaisa kike fahintar yau da sune ya habu yaga yan uwansu yace yana so da gudu
zasu bashi ya aura don kiyayyan da suke maki suna bakin cikin kasan ,cewarki matar
yaya Habu.
Nasani amma nidai a wajena hakan ba daidai bane Salima don ko rantsuwa nayi ban
kaffara nice za ace na hada wanan abin.
Ai ashe kinsan da hakan to me zaisa ki damu da abinda zasu fada a kanki damuwa ba
naki bane don inkin nuna hakan za a samu sa,an gaya maki maganan banza.
Amma idan anga kin dake ko za a fada ba yadda za a sake a fada maki cikin takaici
ba don haka gara tun wuri ki marawa yar uwarki baya Maria.
Sun dauki lokaci suna magana a tsakaninsu kafin ta mike zuwa part dinsu ta samu
kawu ya shigo yana fadin abinda yafi dai yanzu ya fito da dukiyan a kasa abawa kowa
nasa kaso ai yanzu kowa acikinsu yanaa iya rike nasa.
Kaiyya yaya nifa ban tunanen akwai wanan dukiyan a yanzu illa kawai ya kawo
abinda ya saura a hannusa a kiyasta a bawa kowa hakama wanan gidan.
Kaga idan anyi haka zanga inda zai saka yarinyar nan in tunanesa wanan part na
yazid to tun yanzu ya canza dabara nayi waya da Baraka ta taso tazo asan abinda za
ayi dama mijinta ya matsa ta karbo dansu ya fara juyawa tunda ya gama karatu ba
aikin yi.
Hakan yana da kyau kwarai saidai nasan koshi nasa tunanen ke nan a yanzu wanan
wajen na dan uwansa zai saka yarinyar tunda ba wani ginan yayi da zai sakata ba can
na daban.
Allah sarki idan kin hanashi saka mata a wajen dan uwansa haya kikeso ya fita ya
kamawa matan nasa Dubu ?
Duk yadda zaiyi shiya sani mama ai yasan baida matsuguni ya daukowa kanshi zancen
aure kina gani iya ko wanan filin daya kara yayi ginan wanan daya dauko kaduna ai
cikin filin gidan ya diba ya kara yayi.
Iya sai a kyashi ya mamaye duk kason yan uwansa shi daya nan gaba su koma suna
zargina nice na mara masa baya da yayi masu hakan ?
Yanzu dai maganan gaskiya ke iya a bari ya kawo dukiyan a raba abawa kowa nasa
idan yaso in zai dauki hanyan wajen shi yazid kafin ya dawo sai ya dauka a dinga ba
uwarsa kudin ina ganin haka zaifi sauki tunda abin magadane .
Anya Dauda kuyi tunane kafin ku yanke wanan shawaran yaron nan shine tsaye da
gidan nan da yan uwansa yau don abin duniya zaku rufe ido kuyi mashi hakan ?
Iya ai ba tozarci bane nauyine za a sauke mashi kada daga baya abin yazo yafi
haka rayuka su baci tsakanin gara tun wuri ayi maganin abin zaifi.
Kit Salima da tayi recording din muryoyinsu ta mike zuwa daki bayan ta kashe
wayan bata jira komai ba ta bude ta turawa yayanta komai.
Sun kai wani lokaci a falon suna tatauna zancen kafin suyi sallama da juna
ranan mama bata nemi yar uwata ba saboda har ita wanan lamarin ya shafa.
Sai take ganin laifin duk natane da badon ita ba babu inda Jafar zai ganni ai
zancen kawune da yace da ita mudin fulani abin tsorone.
Zamu mallake mata yaya ta koma bata gane komai ba har gara wa yan nan matan na J
ai damu bata ganin habu komai da yake ciki ba a taba sani saboda boyon kurwa da
yakewa mutune.
Wanan zance mama ta haushi ta zauna sosai donshi ta kara hawa zancen cewa a raba
gado a warewa kowa nasa kaso a yanzu don ta kula Jafar ya salwantar da dukiyan
nasu.
Bai tashi ganin sakon salima ba sai da dare bayan ya gama abinda yakeyi ya bude
data yaga sakon mutane lokacin ya kula da sakon kanwar tashi.
Ya bude yaga sakon muryane kusan guda hudu daya bayan daya yake bin sakon yana
saurare a ranan kasa barci yayi don zullumi da tunane.
Habu ya fara nema akan zancen ya nuna mashi yasan da zancen shima an fara a
gabanshi amma ya nuna rashin dacewan hakan sai aka baryi dashi.
Haba dai Habu shine ka kasa fada min komai a cikin lokaci tun tuni idan nasani da
ban fitar da kudin nan an raba a bawa kowa nasa ba ?
Yake tambayansa waya turo mashi wanan murmushi yayi shi habun yace salimace don
ra,ayin mu daya da ita tun a waje ta fada masu gaskiya abar nata a wajeka kome
zakayi dasu kayi.
Sun dan jima suna zancen tun bayan kashe wayansa ya kira nura da yunusa abokansa
da suke kasuwance a asirce ya bukaci da su hada mashi kan kudin a waje daya.
Ya kuma kara umartan Nura da ya mayar da hankali wajen ginan daya saka suna gama
waya ya kira wani ya bashi cigiyan gida.
Allah sarki da ace mama tasan abinda ta haifa da bata yarda har kawu yayi amfani
da damanta ya bata wanan shawaran ba duk da bai kyautata zaton shawaran kawune shi
kadai dole akwai wasu yan uwa dake kwadayin dukiyansu a hannunsu.
A lokacin kuma ya kara yarda da maganan hardo kalai kawu ya dade yana bin
duduniyarsu ba tare da sanin hakan garesu ba duk da alama Habu yasan wani abu
shikan dip yake banda kasuwanci baisa komai a gabanshi ba.
Bayan kwana biyu ya bar kasan zuwa South Africa da niyar sati daya amma saida ya
share sati ukku a can wanan yasa mama dake ta neman layinsa dare da rana ta kasa
samun shi .
Ta kira Habu shike fada masu baya kasan nan Saaratu ke fadin kin gani ko mama da
kudin yake ta facaka ya dauki yarinyar nan sun fita ke nan yawon amarci ya barmu
nan ko Lagos bamu taba zuwa ba.
Shi kuma kawu cewa yayi dubu na fada maki yaron nan yana dawowa a kwace komai na
hannusa a rabawa yan uwa ko gida in bai tsira da komai ba dole ya sayarwa yan uwa
da part dinshi a basu hakkin su.
Mama da bata data cewa sai kara hasala da zancen ke sakata a kan danta takeyi
haka yasa ido rufe ranan data zo gidan ta shiga part din habu .
Yanda na kwance sai ganinta tayi ta mike tana gaida ita cikin rashin walwala take
fadin yar uwarki tana inane Maria ?
Ta dan sasauta murya tana fadin tana Abuja mama tace kira min ita yanzun nan a
waya hakan yasa yanda daga wayan takira layina na dauka na fara mata yarenmu na
fullanci tace bani ita nan ta mika mata wayan.
Naji muryanta a lokacin yasa tana karban wayan tace hello Rahama ina jafar yake
ne ?
Na maimaita sunan a cikin mamaki ina fadin mama bansan inda yake ba don rabona
dashi tun dana barshi gida nazo abuja ban kara ganinsa ba sai naji ta kashe wayan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

4️⃣0️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Kwana biyu a cikin zazzabi na samu sauki har lokacin ina gidan mama saidai anty
salma takan zo ta dubani lokaci lokaci amma ba wanda ya kara min zancen auren Jafar
dake kaina yanzu.
Saina dauki hakan da kila gwadani sukayi ko zan yarda da zancen amma ganin ban
yarda ba yasa aka fita zancen nasa.
Hakan ya bani karfin gwiwan sakin jiki da har na fara fitowa falo muna dan hira
da mama satina daya cur a gidan anty salma tazo a wani yammaci zata tafi na mike
nima nace tare zamu tafi ai.
Ta juya ta dubi mama mama din tace kuje mana duk da daddy bayanan idan ya dawo
zan fada mashi ta koma gidan ki hakan yasa muka tattaro muka dawo gidan anty salma
din.
Sai a ranan kuma ta ban wayana dake hannunta duk da ina son wayan a tare dani
ganin bata ban ba nima ban tambayeta ba saina share zancen wayar tawa din.
Sai gashi ta mika min abina ba tare da kona tambayeta din ba wayan da cajin shi
full haka yasa na kunna don a kashe take nayi tunanen mutane da yawa zasu nemeni
sujita a kashe.
Data na kunna na aje saman gado inda sakonni suketa shigo min kai tsaye bandaki
na shiga nayi alwala don magariba daya kawo jiki idan na biyewa wayan za a samu
matsala dani lokaci don shedan zai rinjayeni in shagala da zancen sallah.
Na idar nayi addu a na shafa naji wayar tana sauti alaman kira yake shigo min
lokacin na mika hannu na duba anty Nafisa ce akan layin.
Ina dauka tayi sallama na amsa naji tana fadin haba matar yayana duk sallon
amatcin ne haka ko waya baki dagawa sai kinga dama halan angon ya fitane.
Ke kuma shike nan ko buki kinki fada muna muzo musha wallahi Ramaah ban zaci
hakan daga gareki ba sam na dauka kome ke nan nice ta farko da zaki fadawa ai.
Anty Nafisa ke nan nida ke kwance banda lafiya mezan fada maki satina daya ina
gidan mama banda lafiya wallahi sai yau na dawo gidan anty salma dazun nan taban
wayan na kunna kece ta farkon kirana yanzu.
Haka madam Maria ta fada min cewa baki da lafiya to yaya jikin naki nace da
sauki anty Alhamdullahi ya kuke ya su mama dasu inna ?
Lafiyansu kalau Ramaah ga inna ma tana gaidake da jiki sai naji taba inna wayan
ta soma fadin halo Rahama yaya jikin ya mutanen wajan ku ?
Lafiya kalau inna na fada take fadin to kiyi hakkuri da kaddara kinji auren jafar
alherine a gareki in sha Allahu ki fita zancen kowa ki kama mijin ki.
Kada ki damu da zancen su yaya Dubu duk bari zasuyi tunda mijin ki yana kaunan
ki kowa tasa ta fisheshi haka zaman gidan miji yake dama.
Kada ki kula kowa kiyi abinda zaki burge mijinki dashi Ramatu ita wanan da tayi
yaji karma ki tsaya kula ta ki zage ki nuna masu akwai banbanci a tsakanin ku.
Barta can ko Allah yayi dawowan ta gidan kada ki yarda ki biyewa shirmensu na
rashin hankali kin daiga yadda yar uwarki take dasu.
Jafar mutumin kirkine yasan ya kamata kwanciyan hankali da kulawa yake bukata in
sha Allahu zaki alfahari da hakan na gode inna na iya furtawa a cikin kyarmar
murya.
Na sake jin tana fadin na fada maki ki fita zancen su yaya dubu da sukeyi na
asiri kikaiwa Jafaru keda yar uwarki har ya aureki.
Lokacin naji muryan Nafisa tana fadin nikan inna zaki cinye min kudin waya
bamuyi magana ba ta amshi wayanta badon inna ta gama zubanta ba.
Naji tace min Ramaah to yaya jikin naki nace lafiya kalau anty Nafisa ta sake
fadan yaushene tarewan naki koda yake ai kamar ba yanzu ba ko don ance yaya baya
Nageria ya tafi kasan waje.
Wallahi ban sani ba na fada maki ai dazun nan na dawo gidan anty sallma bansam
komai a kai da suke shiryawa ba.
To bari na barki saina sake kira mukayi sallama ta barni da waya a hannu ina
mamaki a raina nace watau zancen auren dai yana nan a kaina ke nan ?
Ni Rahama yaya zan iya rayuwa da yaya Jafar a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login