Showing 45001 words to 48000 words out of 328222 words

Chapter 16 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

ya samu har iya din mun
shirya muna jiransa bayan an gaisa muka fito da kayan muka kwasa zuwa asibiti gaba
dayan mu yan part din aka rufe shiyan.
Sam ummah bata sake ba har muka kai asibitin cikin nauyi da kunya take don ta
shiga motar surukinta koshi don ba wanda ya santa a zaria ne yasa har ta yarda ta
shiga Ya Habu ya jata.
Duk ko da dan wayewan kai da ummah kedashi wanan baisa tayarda akidan mu ta
fulani ba don anty Yanda yar farice a wajenta kuma yarta ta cikinta suruki zai
dauka a mota haka ?
Ba laifi gaskiya don ba zakice asibiti bane ba ,a kuma kilance wajen ba dakin
masu irin lalurar yar uwata din itama aka ajeta munje daidai visting hour don haka
kofa a bude take lokacin.
Aka gagaisa da juna tsakanin ummah da mama ana satan kallon juna a tsakaninsu
sukaiwa juna jaje akai tayiwa ummah yaya hanya da mutanen gida.
Gadon da anty Yanda take mukaje gaida ita ga kayan more rayuwa nan an baza
gwanin ban sha,awa zakice ba asibiti bane na fada a zuciyana ina kara bin wajen da
idanu.
Munkai kamar minti talatin matan ya J suka iso tare dashi suma da nasu abincin
nasan shine yasakasu yi dole saidai yadda suka samu yar uwata din akwance haka ya
tabbatar masu bata da lafiya dai kan saidai ba wani sosai ba.
Ban da sakin jiki dagani har ummah a wajen su dai keta hiransu da kuma baza ido
suna gulman wasu mata da muka hango dan nisa damu masu irin matsalan nata.
Shigowan yaya J dakin da ya Habu ya sa duk akai shiru inda suka karaso bakin
gadon yana gaida ita nan yake tambayan mama ko anzo an mata alluran da safe mama
tace anya basuyi ba kan.
Ya juya yana fada ya habu yabi bayanshi suka fice daga dakin sai lokacin saiba
tayi magana take fadin.
Wani kan ba zan yarda in kwanta a dinga surbuda min allura haka ba gaskiya daga
can inda mama take zaune ta bata amsa da fadin itama ta kwancen ba da son ranta
hakan ya sameta ba ai ?
Komai da ya samu bawa mukkadarine nata kaddaran haihuwan ke nan yazo mata a
hakan kuna magana kamar baku taunawa wani zubin duk wanda kika gani a nan ba dadin
rai ya kawoshi wurin nan ba asibiti fa akace ba gida ba ?
Shiru tayi don tasan abin ya taba zuciyar mama din don ba wanan karon suka fara
tsegumi kan matan Habu din da mama din ba.
Suna fadan mama tafi son matar Habu dasu tana nuna banbanci a tsakaninsu ta
fifita matar Habu alhalin duk wani moriya a gidan mijinsune .
Taba wace suka gulman da ita sakon da take kyautata zaton yakai masu da cewa ta
fifita din don ance ka kyautatawa wanda yasan darajan ka.
Kuma da sauki tunda ba habu ta fifita akan jafar ba ai idan sune aida sauki suyi
mata yadda matar Habu din ke mata idan basu ga canji a wajenta ba.
Wanan yasa suka kama bakinsu don ta fadawa yar sakon cewa su shiga hankalinsu
don lokaci guda zata iya fyacesu gaba daya a gidan kirsis take jira ga hakan.
Don saita sa ya j ya sakesu ta aura mashi masu hankalin ya zauna dasu tunda basu
iya cin arziki ba su kuma su tambaya suji ita a ratuwanta bata gaji tsiya ba ko
jafar din da arzikinta yake barazana.
Aiko da J din yaji yai masu tsiya sosai lokacin har yana barazan sakinsu run
wanan lokacin suka shiga hankalinsu da mama din ta samu lafiya dasu .
Sai a yan kwanakin ma suke dan ganin fuskanta idan tazo gidan wanan yasa a
yanzuma sukai gum kamar ruwa yaci su a dakin.
Tare da likita suka shigo dakin hakan yasa muka fice waje sai mama aka bari a
wajen nan muka zauna saman babban tabarma a wajen .
Mai hali dai baya barin halinsa akace don ko a nan gulman wata mace mai tsohon
ciki sukeyi ina mamakin yadda halaiyansu ya kasance a hakan.
Banga abin tsegumi ba a nan duk da yake basu irin hakan ya sama ba a yanzu dole
su mayar da abin kishin tsakar gida su da yar uwata da suke ganin ta shiga rigan
arzikin mijinsu a yanzu.
Don ni a zatona shine mai dukiyan gaba daya don bansan cewa dukiyan yan uwansa
kaf da suka gada yana hannunsa ba lokacin.
Sun dan jima ya fito yana fafin muje ko kafin ya juya wajen iya yana fadin to
iya ni yau zanyi tafiya fa zan koma port,harcurt wajen sana,ata .
Ayya Jafaru zaka koma yau ke nan sai kuma yaushe eeh to iya saidai kun ganni
yanzu kam amma insha Allah kafin azumi zan dawo na dan fara azumi a nan din.
Hakan na da kyau Allah ya tsare ya kare ta fada gabanta ya gurfana yana fadin to
muka hannun ki mana a cikin hijjab dinta ya dunkula mata kudi sai murmushi iyan ta
sake a fuskanta tashiga mashi sabon addu,a kuma.
Ya mike tsaye yana kallon kannesa yana fadin to ku yaya za ayi nifa zan tafi
yau din nan ana nemana a can .
To yaya zancen kudin da nayi maka fa Saare ta fada yace ban manta ba saratun
mama ba kince sai next mont bane saiki tuna min ko ina can din in turo maki.
Ya dago ya kalli Salima yace yan mata nasan kedai na shan ice cream ne ko ko
yanzu kin dainane tayi murmushi tana fadin ban daina ba yaya yanzu kan harda na
powder da jan baki .
Ya nunata yana fadin see you nine zan baki kudin jan baki ina saurayin ki dan
karya ta kebe baki zakice wata karamar yarinyace kudi ya mika masu .
Kamar zai wuce sai kuma ya kallo inda yake yana fadin nakan manta da sunanta fa
Ramaah ko ka kirata da Rahama wai dama sunanta ke nan aka sauya da wanan din.
Ke kuma kudin me zan baki ya fada yana kallona murmushi nayi ina fadin nagode
yaya yace shike nan kin hutar dani ?
To ku kunji yadda akeyi ba kamar ki ba Saare da kullum kedai a baki kudi nakan
rasa me kikeyi da kudi haka wallahi yana magana yana kokarin cusa hannunsa a
aljihunsa na gefe daya.
Sweet J muje mana kasa mun taso kuma ka tsayar damu haka a rana ya juyo ya dan
kalleta hakan bai hana ya fasa abinda yakeyi din ba Salima naga ta kebe baki data
fadi hakan tana magana kasa kasa tace akgunguma duk ranta ya baci ana bamu kudi.
Nice kusa da ita a zaune ninaji hakan data fada ya miko min kudin yana fadin kin
gani ko kin fisu sa,a ke yan dubu dubu kika samu.
Na karba da hannu bibiyu ina godiya rakasu mukayi har bakin mota suka shiga ko
anan ma din saida ya tsaya da kannesa suka dan taba barkwanci a tsakaninsu suko duk
sun sha toka a motan .
Nice na fara juyawa ganin ya tayar da motan tare da mamakin irin zama da naga
sunyi a tafiya dukkansu suna zaune a bayan motar shi kadaine a gaba da yake jan
motar.
Suka tafi su kuma suka dawo inda nake zaune da tsohuwar kakan tasu dake
kiciniyar boye kudinta cikin lalitarta dake manne a jikinta.
Kai yaya ho daga shi dai sai matansa shike nan sunyiwa kansu tsiya babu wace
zata shiga gaban mota ta zauna tare dashi don jidalinsu din.
Ai maganinsu ke nan yan iska masu fitinan tsiya kawai haka kawai akan shiga mota
su kama dabe a gaban mutane sun zubarwa mutane da mutunci.
Ni na rasa yadda mutum irin yaya jafar mai hakkuri da kirki yake iya zama da wa
yan nan matan da basu son suga wani komu nan mun rabeshi.
Jifa yanzu kudin nan da Saiba taga zaibawa Ramaah shine ta kasa hakkuri take
fadin wai yazo su wuce ya shanyasu a rana wai ita yar iska mai wayau banza.
Ai shima ya gane me take nufi bakiga ya fita batunta ba ko kwanaki daya dawo
tafiya ta aikawa part din ya Habu da tsaraba suka ki saida ya dawo ya diba da kansa
bayan yai masu cin mutunci yabani na kai masu.
Tsam na mike na nufi wajen mahaifiyar mu dake can dan nisa damu a zaune cikin
damuwa nasan ba komai bane sai halin data samu yar uwata a cikine ya daga mata
hankali.
Ina isa naji salima na fadin ummah kin zauna kinyi shiru kamar baki wajen tayi
murmushi tana gyara mayafin jikinta da ya rufe mata jiki lif har kasa.
Idan kinga Ummah duk da wahalan da take ciki zaki rantse kice ba itace ta haife
mu ba sai kice ita din yar muce ba mahaifiya ba.
A cikin yare take tambayana da shi wanan din yayan Abu ne ko na amsa da ehh
shine babban yayansu namiji amma suna da yaya mace tana aure a wani gari ita.
Ayyo suna ko da kama sosai da Abu din saidai haske dashi ya dan dara Abu din
dashi nace shi Habu din kebiwa shima dan mamane su kuma su Salima da Saare kanne
sune duk uwarsu daya.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC


MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

1️⃣7️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Nan muka bar mama da ummah muka dawo gida saboda abincin da part din yaya suka kawo
mama tace ba sai munyi wani abinci ba a ranan mu barshi kada ya zama barna.
Hakan yasa koda ya Habu ya sauke mu gida barci sosai mukayi sai wajajen la,asar
muka tashi mukai sallah Salima tace zan rakata kasuwa .
Banyi mamakin hakan ba don nasan tana kudi ranan kudin da dan uwanta ya bamu da
zai tafi ni banko tsaya duba kudin ba tunda na saka a kasan jakkata a lokacin.
Kayan gyaran jiki ta kwaso su man shafi sabulai turare har ina mamakin hakan
yadda ta iya fidda kudi ta biya kudin ba tare da jin komai a ranta ba.
Saita tuna min da anty Salman Abuja a lokacin har nake mata hiran tana min shige
da ita don haka halaiyanta yake itama.
Bayan mun dawo gidane tace na kwashe wanda take amfani dasu da farko don ita bai
mata ba a cikin murna na kwashe zuwa inda nake aje kayana na jera kamar yadda suka
jera nasu gefe daya don kowa nada inda yake aje kayansa a dakin.
Tun a hanya ta gargadeni da cewa kada in yarda in fadawa anty saare ko nawa aka
ban in mace kawai dubu biyar ne ko goma.
Nayi mamakin hakan data fada amma na share muka dawo gida a falo muka sameta
zaune tare da iya muka zube kayan a nan falon.
Duban kayan tayi tana fadin kasuwa kukaje Salima baki fada min ba aida na baku
sako kun sayo min tana duban kayan take magana .
Kudin ba zasu azu min ba hakana zan iya kashesu ban mora ba ko kuma in rasa me
nayi dasu amsan data bata ke nan lokacin.
Ga mamakina sai naji Saare din na fadin ke Ramaah nawa ya baki halan nace dubu
gomane sai tayi shiru bata sake magana ba sai can take fadin baki sayo komai bane
ke nace a,a ban saya ba anty Saare.
Mikewa Salima tayi zuwa daki da ledan kayanta a hannu na dan kai kwance a inda
ta tashi ina kallon tv dake aiki iya ke fadin ki lalubo muna Jafar muji koya sauka
lafiya.
Ta dauki wayanta tana neman layinsa din yashiga take gaidashi tare da fadin iya
tace ka sauka lafiya ko yace Alhamdullahi ina kaduna sai yamma zamu shiga jirgin
Rivers din .
Muryan Salimace ke kirana daga daki na amsa na tafi ba tare dana san yadda
sukayi ba kayane saman gado ta zuba dana shigo take fadin ki kwashi kayan nan
Ramaah kiyi amfani dasu tun wanda yaya ya sayo muna ne da yaje tafiya da wasu na
sallah ba amfani nake dasu ba don ban faye son dogon riga ba idan zan fitani.
Godiya nayi mata na kwashe kayan zuwa wajena na aje ta mike zuwa gaban mirrow ta
kwashe kayanta kaf ta miko min tana fadin zaki iya amfani da su zai maki kyau sosai
ya gyara maki jikin ki don ni bai kara min wani haske ba.
Na fararen mutanene na kwaso sai daga baya nagane hakan kinga idan ya karbeki
kya dinga sayensa daga baya kina amfani dashi.
Kwasa nayi na kai wajena tunda yanzu a nan dole zan rika amfani tunda yaya Habu
yana nan sai gashima washegari shima ya koma wajen aikinsa .
Duk daya tafi ban koma ba a nan muke kwana saida mama tayi wajen kwana uku
asibiti tare dasu ummah ta fahintar da ita komai game da antyna ta dawo gida ta dan
huta.
A ranan ne kuma muka wayi gari da an shiga part din nasu saidai bamu san me aka
dauka ba tunda masu wajen basa nan.
Wanan dalilin yasa ya J daukan maigadi a gidan dama yana da niyar hakan ga
iyalinsa din ya kasance a yanzu muna da maigadi sai kuma mama tace nida salima mu
koma kwana a can har ya Habu ya dawo wanan dalilin yasa muka koma kwana din a part
dinsu mu biyu.
Acikin yan kwanaki na kara fahintar waye salima don gaskiya muna zaman mu na
lafiya sosai tsakanina da ita duk da ba wani girma na sosai tayi min ba amma haka
bai hana in bata girmanta ba.
Itama din na fahinci tana daukana tankar yar yar,uwartace ta jini don yadda take
zama ta fada min komai nata ta dai sake jikinta sosai dani tunda tasan ba wanda zan
fadawa .
Wani saurayi take so sunansa yazid amma iyayyenta da yayyu sunce yayi yaro
kwarai a gareta ita kuma ta nace akan shi take so .
Duk da yazid din zai girme mata da shekara biyar ko fiya da hakan amma sun nuna
basu son alakanta dashi gashi kuma sun shaku sosai dashi din.
Da muka dawo da kwana part din antyna sai hakan yai mata dadi sosai sai sukai
wani lokaci dashi a waya nikan ina kwance ina sharan barci na.
Idan ko idonshi biyune zata ban waya mu gaisa dashi ya dan jani da fira har in
gaji in mika mata waya don bai gajiya da rokona in kafa masa gwaunatinsa gasu yaya.
Shi baisan banda power hakan ba garesu nima cin arzikin yar uwatane ya hadani
dasu idan bashi ba ina rugga tare da dabbobin mu da baffa ya kwace muna.
Rai da kwade irin na dan adam a zaman mu wajen Baffa saida muka gano shanayen
maihaifin mu kuma muke basu kulawa sosai a lokacin.
Don sai ince yawancin shanayen da baffa ke alfahari dasu na mahaifinmune don
sunfi yawa sune masu dabbara dabaran baki da fari a jikinsi kinsan shanun mu na can
suna da babbanci da shanayen ku na nan mu namu gudale sinfi yawa sunci sun koshi
sosai suna bunkasa don hakkin da suke samu.
Yayin da yar,uwata take har lokacin karkashin kulawan likita kuma tayi kyau
sosai su mama dabu da mahaifiyan mu suna kwantat mata da hankalinta.
Hakan yasa jikinta yayi kyau ta murje ba kamar yadda aka kaita asibitin ba ga
kuma rubutun da a kullum sai an wanko mata tasha.
Yauma shiri muke don mama tayo waya da muje gidan malamin bayan kwatancen da
tayowa salima tace tagane gidan zamu karbo mu sameta dashi asibiti.
Zafin ranane a lokacin amma haka muka daure muka fita bayan la,asar dakyat kuma
muka sami abin hawa da zai kaimu unguwar mu karba mukai asibitin.
Gidane mai fadin baranda daga waje sai ciki inda tulin kayan da muka gani ya
nuna na almajiran gidan ne muka karasa ciki kuma zaure biyu ne a gidan nan muka
sami malamin muka karba ya tambaye mu mai jiki ?
Salima tace da sauki idon da bawan Allah ya kura min yasa na shiga tsarguwa da
irin kallon da yake min har dai muka samu ya mika muna mukai mai sallama.
Karfe biyar a asibiti yayi muna mun samu su mama a waje suna shan iska muka
gaidasu tare da mika mata sakon tana ta saka muna albarka.
Nan take fada muna cewa almajirin dake kawo masu kullum yau baida lafiya ita kuma
ba dadin jiki ta tashi dashi ba don saida tasha magani.
Tausayi ta ban don akan ciwon yar uwata ta hade nata ta zauna a asibitin duk
akan neman saukiwa danta take wanan abin mun dan jima a wajensu din.
Nan mahaifiyar mu take min yare da inzo in mata kitso kanta yayi mata nauyi da
yawa na bata shawara akan tazo gida zaifi .
Don ta samu ta wanke kan saboda kitson ya jima akanta idan anyi sabo duk a cikin
harshen fulatanci muke magana da ita don haka basa jin mu.
Inda ummah ke fadin ya zatayi tazo gidan da sunan kitso gara dai inzo nan in
lalaba mata kan nata duk da maman mu yar daji ce amma gaskiya tana da tsabta sosai
kafata da kanta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login