Showing 171001 words to 174000 words out of 328222 words

Chapter 58 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

data dagawa mutane hankali tunda
safe wai tun cikin dare ta kira waya ashe zata dawo gida ita mama dubu ta hanata
dawowa dagani har yar uwata bamu ce kala ba don ba abinda ya shafemu bane .
Muna zaune kanwar Asmau matar yaya J tashigo tana fadin amarya angonki yana
neman kifa ?
Wai ashe suna zaune falon gaba dayansu ya fito yake fadin ina Rahama ?
Sukai shiru ya bisu da kallo kafin yace ke Rashida kira min ita part din habu
don Allah ya juya ya koma dakin nasa shine ta taso tazo kirana din .
Jiki a sabule na mike cike da mamakin don me zai aiko nemana a wanan lokacin
gidan matanshi irin hakan zai iya kawo wani matsala kuma tunda dai gidansune na
shigo ai ba nan din nake ba.
Namiji oho donshi ko a jikinshi a dole zai saka mata kunci a zuciya ya nuna
hakan ba komai bane ai tunda nima hakinsace na karasa falon na shiga gabana sai
faduwa yakeyi suna zaune ana surutu sai sukai tsit lokaci guda.
Yana ciki Rashida din ta kara fada na nufi hanyan dakin nashi da sallamata yana
kwance yana waya na sameshi ya dago yana fadin.
Kije wajen Iya ki dubo min abincin da kikazo masu dashi din nan yunwa nake ji
zuwan kawu dazun ya hana in tsaya in karya da kyau a gida.
Na juya zan fito muka hade da saiba da zata shiga fuskanta kawai na kalla nasan
akwai magana a tare da ita lokacin.
Ni dai kala bance da ita ba na dan rabe ta shiga ni kuma na fito daga dakin yan
falon ko na samesu sunyi tsit sun kashe kunnuwa suna sauraren abinda zai faru a
lokacin.
Part din iyan naje na samu har lokacin dai ba dadi a yanayin dana samu mama din
don itama waya takeyi lokacin don haka da iya na samu yin magana ina fada mata
sakonshi din.
Iya ke fadin shi kuma jafaru baici a gidan bane da zai kwashe muna wanda aka
kawo muna nace kadan zan dibar mai ai iya.
Na bude na kyafata mai komai na rufe ina jin Saratu na fadin bari dai in diba
kafin ya kare naga an fara kwashewa haka kowa baici ba.
Kai wanan matar bata san harara ba ban taba kawowa a raina zata ko kalli abinda
na daho din ba balle tayi fadan taci har nakai kofa naji mama na fadin idan kinje
ki kira min shi daga nan ana magana ya mike ya fita ni zasu bari da tashin hankalin
da baraka ke son ta dauko muna akan mijinta ?
Tunda na doshi kofan nake jin muryansu daga dakin hakan yasa naja na tsaya naji
yana fadin har ke kin isa ki kafa min doka a gida Nusaiba ?
Na fada na kara Rahama matatace kamar yadda na auri kowa a cikinku tana da ikon
shiga duk inda taga dama a cikin gidan nan ko da kudinki na hada na gina gidan nan
ne ?
Nace ki koma gidan ku kince ba zaki koma ba to ki zauna tunda zaman mama kikeyi
bazan koreki ba don kin zauna zamanta amma kada kice zaki takurawa kowa a gidan nan
cikin iyalina kinji na fada maki .
Kikace zaki tayar min da fita a yanzun nan ba sai anjima zan shayar dake mamaki
cikin gidan nan oho ashe ba dadi lokacin da kika zarga min ciwon fitana a kaina ita
kuma sakaran nan ta mara maki baya kuke gudana.
Don yanzu na samu wace bata gudana tana iya zama dani ko wani hali nake ciki zaki
kuma ce baki yarda da hakan ba kije nace ki samu mai lafiya irin ki don Allah ki
barni in huta hakana a rayuwata.
Dakin na fada dauke da abincin ta zaburo kamar zatayo kaina na gwauce Allah ya
gyara abincin bai zube ba har na falon duk suka mike tsaye saboda muryan yaya dake
fadin kika taba ta wajen nan yau sai kin kwana asibiti Nusaiba na fada maki inkon
zata karyane ki gwada taba Rahama ki gani a gidan nan.
Ni basai ka rama min na ina da hannuna nice zan ramawa kaina ai amma wanan abin
baikawo kallo ba a tsakanin ku a cikin jama,a don Allah .
Kaje mama tana magana da kai idan ka gama na fada na aje abincin na fito daga
dakin na barsu a ciki yan falon tsuru tsuru ban tsaya ba na fita daga part din.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: [3/5, 8:46 Yamma] Seenabu Makawa: Follow this link to join
my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/C8kkr4INYY7FydHKKKRVhL
[3/5, 8:50 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

5️⃣7️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

Kinji meta fada ai ashe baki cika yar iska ba tunda baki doketan ba a yanzu get out
of side kafin ki kaiga abinda kikeso ki samu a gurina yanzu.
Tana tsaye har yaci abincin yayi hamdala a gabanta yasha ruwa ya mike don ya
fita a kofa ya tsaya baiji kunyan idon da yan falon suka kafa masu ba a lokacin.
Nan ya tsaya tafito ya rufe kofan nasa dakinta ta nufa rai bace ta kira yar
uwarta nan ta karfafa mata akan tayi hakkuri duk abinda zai mata don ya kureta kada
ta yarda ta kara barin gidan har suzo.
Zuciya dai bata da kashi duk maganan da yarta tayi mata haka baisa ta hakkura
ba can dai ta sameshi part din mama suna magana kan zancen anty baraka din ta fado
falon cikin fitina.
Nan ya wanwanka mata mari duk da mama na magana ido rufe yake fadin shi zata
kawowa rashin mutunci yana magana da mahaifiyarshi ta zo mai haka.
Sai lokacin ta fahinci irin kuskuren da tayi don duk abinda sukeyi bai taba daga
hannu ya duketa ba sai wanan ranan kuma a gaban kannesa dani da muke dakinsu muna
kallon wani dinki da salima ta jawo mu gani.
Abin dai ba dadi a lokacin wanan yasa ba a jima ba yace mu fito mu tafi duk da iya
tayi mashi magana akan ya barmu yace yana son muje mu gaidasu mamane can family
house din su.
Dole iyan tayi shiru ita mama abu yai mata yawa saukinta ma shi J din daya kira
anty barakah din ya bata hakkuri akan ta daina zancen ta bari zasuyi magana dashi
daga baya .
Wanan ya kwantarwa mama din da hankali saidai muna fita daga gidanne kuma Habu
ya kirashi yana fadin kada yace zaiyi wani abu ya kyale yar tasu sai ta koyi
hankali.
Shima bai samu dogon magana a wajenshi ba saboda ranshi dake bace na daiji yace
dashi zai kirashi idan ya sauke mu .
Nidai nasan badon hudubar dana samu gun anty salma ba dana kade a wajen Saiba
don yadda ta sakani gaba dani da mijin.
Amma sai Allah ya taimakeni nayi amfani da wanan huduban na anty salma nacire
tsoro da fargaba ina bata amsa ba tare da rashin kunya ba ko fitsara daidai da
yadda tazo min nake daurewa ib dauki mataki a lokacin.
Wanda ni kaina har mamakin irin daurewan da nayi din nake ji ina fuskantanta
garan da garan gaba da gaba ba shamaki ko tsoronta.
Mun shiga cikin gidan da kedojin da muka riko masu inda ko wani daki muka shiga
muke aje masu sabulun wankine da omo sai manshafi dana hado dashi din.
Ina dakin inna inda na yadda zangona dama tun kan na auri ya J idan nazo gidan
nan muke dasu anty Nafisa kiran Maria ya shigo min.
Da harshen fulatanci muke magana don su inna dake dakin zaune inda maria din ke
tambayana ashe abunda ya faru ke nan.
Yanzu take ji a wajen iya cewa Saiba tayiwa yaya rashin mutunci a kaina ya mareta
har idonta daya ya rufe wai sun tafi asibiti da Saratu.
Nan na fada mata abinda ya faru don ganin su salima ban samu mata bayanin komai
ba har na fito a lokacin.
Take fadin dama ta fada ashe duk ranan dana zo gidan saita wullakantani a gaban
kowa gashi ni ban wullakanta ba ita ta samu duka haka.
Inda take fadin yanzu ta shiga duba jariri ake fada mata abinda ya faru nace a
cikin yarenmu na fulatanci ban taba bin kowa da mugun nufi a rayuwana yanda amma
idan kace zaka bini da wani nufi akanka abin zai kare ai.
Shigowan Nafisa har lokacin ina waya nan ta zube tana fadin ke kunbar gida da
jidali Saiba ido ya kumbura saida mama tace a kaita asibiti ashe fada sukayi sosai
har yaya na fadin zaman mama takeyi ai a gidan ba zamanshi ba.
Kiji min mata wai kuma ashine take zaune bata tafi gidansu ba ko hakan aita
wullakanta dai data sani ta bar zancen nan tayi hakkuri har lokacin da aka gama
hidiman nan sai tayi abinda zatayi din.
Amma yanzu har wanda bai wajen sai yaji zancen nan ta dauka irin bayane da take
kada iskancinta yadda taso kuma a zauna lafiya.
Wai ita Nusaiban ce ta tayar da fitina inna ke tambaya don ni tunda ta soma
magana ban bata amsa ba nan take fadawa mahaifiyarta abinda ya faru zancen bai
tsaya a nan ba don duk gidan kowa saida ya tofa albarkacin bakinsa.
Maman fambeguwa uwar gidansu mama Dubu ita ke fadin duk wani shashancin da matan
Jafaru keyi laifin dubune.
Don bata son a fada bata kuma yarda wani ya tsawata masu idan matsala ya faru
haka kiri kiri suka tauye yarinyar nan Asmau a gidan bata da wani power matsayinta
uwargidanshi sai abinda yar nan Nusaiba tace shine yanzu suke son ya faru da
yarinyar nan.
Idan Jafaru ya yarda aka hadashi da yarinyar nan bai kara samun mace irinta a
rayuwanshi diba a yan watanin nan yadda shi kanshi ya koma ya samu natsuwa da
kwanciyan hankali a tare dashi fiye da baya.
Aini ina dauka tana hakane kan son da takewa yayanta din amma sai daga baya na
fahinci wani abune na daban ga hakan kamar yarinyar nan ta asirceta za ace.
Daga daki nake jiyo zantukansu irin na yan babban gida da idan an samu magana
kowa saiya tofa albarkacin bakinsa inda na kula da rikon Biba da yaya ya dauko muna
yaiwa kakan yarinyar dadi sosai.
Sai haba haba takeyi da jikan nata duk da nasan an sakata daki an mata bincike
akan zaman namu da ita duk da nasan ba zata fadi wani mugun abinda rai zaikai ga
baci ba saidai wanda ba aka rasa kawai dan dole a samun hakan ga rikon da.
Daga gidansu muka wuce gidan anty Rukkaiya taji dadin zuwan namu sosai bamu jima
ba muka nufo gidan yaya Ai nan mukai magariba muka koma gida a cikin dadin rai don
ya zauna da yar uwarshi sunyi magana ta fahinta kan yaya baraka da matsalanta inda
muka bar gidan da shawaran da suka yanke a kanta inda yaya Ai da yaya Rukkaiya zasu
can garin wajenta din duk wanan hukuncin mama dubu bata sani ba a lokacin.
Saidai na kula da yanzu kamar yaya ya tsame kawu a cikin lamarinsu a hankali yake
abubuwa bada sanin kawu din ba wanda a baya ba haka suke dashi ba.
Tunda muka dawo gida ban tayarda zancen matarsa ba shima haka baiyi wani zance
kan abinda ya faru din tsakanin mu ba.
Ranan dai da dare yake fada min su yaya Ai zasu tafi gasau wajen anty barakah
dan tarewan amaryanta da za ayi kada ayi babu kowa nata a kusa.
Allah ya kaisu lafiya hakan kuma gaskiyane don ba dadi ace ba kowa naka kusa
irin haka ya faru don koba komai zasu dan rage mata damuwa da zuwan nasu.
Zanje gida in sanarwa mama koda abinda zasuje mata dashi don tunda safe ibrahim
zai kaisu gobe in sha Allahu nayi mashi a dawo lafiya ya fita.
A zuwa lokacin na sakankance dai kamar aurensu da Saiba yana rawa kamar yadda
naji wajensu nafisa da salima shima kuma ya fada ranan a gabana da yace zaman mama
takeyi gidansa aiba zamansa don haka tabar saka baki a matsalanshi da matansa.
Na dauka a ranan zatayi yunkurin barin gidan don cin fuskan da yayi mata a gaban
mutane sai gashi naji Salima da muke waya tana fadin wai Saiba ta samu yaya kan
abinda za ayi na suna yace a gidana za ayi komai nasa da jama,anshi don haka zasu
shigo su tayani aiki ke nan.
Nayi mamakin jin ta saura a gidan ashe batayi fushin zuciya irin na mata masu
jan aji ta tafi ba har lokacin wanan ya kara min wani haske game da zamantakewa.
Don hakan ya nuna itace mai cutarshi bashine yake cutarta ba don da shine ke
cutanta nasan ba abinda zaisa ta zauna tunda har hakan ya faru koma dai maiye
tsakaninsune ba zan saka hakan a raina ba don tare nagansu bani kuma fatan a
sanadina tabar gidan in sha Allah.
Koda ya isa wajen mama yake sanar da ita cewa gobe da safe su yaya Ai da anty
Rukkaiya da inna amarya zasuyi sammako zuwa Gusau wajen anty Barakha don suga
halinda take ciki.
Budan bakin mama cikin mamaki sai cewa tayi da dan nata akan me zasuje duk bai
isa mu walwale matsalan ba sai sunje ba Jafar ?
Kafin yai magana iya ta bata amsa da fadin keko dubu wani lokaci kikan yi abu
kamar mara tunane .
Idan su yan uwanta basuje sun nuna mata gata ba kece zakije da kanki kowa wanan
shawaran da yaron nan ya yanke ko ita barakha din zataji dadin hakan ai idan ta
gansu tare da ita.
Hakan kuma zai kwantar mata da hankali don za a san tana da gata idan anyi mata
hakan don Allah kadai yasan bakin cikin da take can ita daya take kumsa ?
To shike nan idan hakan yafi ni a zatona iya za ai mashi magana akan kudin tane
ya bata abinta idan anje ai sai ya dauka ayi na,am da zancen aurensane yasa sukazo
din.
Kaiya ni kikan bani mamaki wallahi dubu sai in rasa ina hankalinki ya shiga ki
barshi da dabaran nan da yayi namijine fa yafi tunane abinda zaije ya dawo akan
komai .
Tunda kikaga ya shirya hakan dole akwai wani hikima da hakan ke nufi ai ga
Barakhan dole idan za ai wata tsiyar ganin idon yan uwanta dole a raga mata ai .
Banda abinkima Dubu yau in ba Jafar din da kuka samu kamar ruwan sanyi ba wa zai
tsaya har yai hakan yadda kuka rufe ido ke da yayanki kuka so ku tozartashi gidan
nan kan kudin nan .
Gashi ai shi baici ba wani kato yaci a banza har da tukwaici ya dora maku dashi
kuma ba yadda kuka iya dole ku barshi da kudin ko don haihuwan dake tsakanin su.
Irin abinda nakewa gudu ke nan tun farko da yaran nan suka zo da zancen a fito da
kudin nan a raba abawa kowa nasa to gashi an raba din sun kuma salwanta don da
kudin na hannusa da yanzu tana tsakuran abinta tanaci hankali kwance ai.
Kuma da duk haka bai taso ba ai irin wanan abu ina yai dadi in zaki sake hali
gara ki canja akan mu,amulanki da yaran nan.
Shi miskilin daki ai kinji amsan daya bada ko yace ai mijintane don yaci kudinta
to meye aure kuma aiba za a hanashi ba tunda yana da ra,ayin hakan aita sani ta
bashi kudinta din.
Kai iya wake zancen habu don Allah koshi Jafar din ai nasan yaki saurarensane ya
yanke wanan hukuncin amma Habu ai sam baiyi ba wallahi.
To koke fa amma yaro yazo da abinda zai fishemu kina wani zance so kike ke kije
idan su yan uwanta basu je ba kome gashi har da abokiyar zaman ki za a tafi me yafi
haka dadi don Allah kin kuma san ba zai kyalesu su tafi hakana ba ai.
Yanzu dai zan hada da Saratu ko salima su tafi tare don kada ya kasance nan dakin
ba wanda yaje a cikin mu hakan zai kara kwantar mata da hankali ai idan taga dayan
yaran nan cikin su.
Yanzu dai ke akeji kuma shi dai ga abinda yazo ya fada ai idan saratun zata tafi
ba sai a fada mai ba idan akwai waje ?
Akwai waje mana iya tunda su uku ya lissafa zasu tafi saida ya dawo take fada
mai cewa da saratu ko salima za a tafi yake fadin .
Mama banson abinda za aje ayi tashin hankali a can don Allah wanan yasa ban saka
kowa acikinsu ba har Nafisa.
Ka dai bari dayansu taje zanja masu kunne kada hakan ya faru bashike nan ba shi
dai baice komai ba saida zai tafine yace da karfe bakwai zasu wuce fon haka mai
zuwa ta shirya a cikinsu din.
Washegarin din kuwa hakanne ya faru bakwai na safiya suka biyo daukan saratu
din don ita tace zata salima tace itama ba zata ba don zasu tsaya shirye shiryen
suna a nan kafin a dawo.
Yaba dukkansu dubu ashirin inda inna yabawa kudin tabawa kowa don haka saratun
nashiga motan ta mika mata nata kason tayi wani kata ta bata rai alaman don me za
aba inna din kudi ta bata.
Haka dai suka dauki hanya karfe dayan rana suna gidan barakha din inda suka
sameta cikin tashin hankali


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login