Showing 81001 words to 84000 words out of 328222 words
Chapter 28 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
nufi ba ato shiyasa ban damu da
zuwa ba son gudun hakan da kayi magana ayi kokarin juya maka zance zuwa wani daban.
Kallon mamaki nake mata nasan dai sabodani take wanan zancen a kofa suka hadu da
mama dake shigowa tana fadin hayaniyar me nake ji haka wai ?
Banda wanan figagiyar mai zubin yan ruwa kinsan ita bata rabo da abin fitina na
rasa yadda yar nan ta koyi tsegumi a gidan nan.
Meya faru Nafisa tace ba komai mama ba zaki fada ba kina tsoronta ne tace wai
cewa tayi munji dadi an sallami matan yaya mun maye gurbinsu da mu barki ke kadai
da kika koresu kiyi jinyar yaya din .
Allah sarki ke kan kinyi hasara wallahi baki san takaici ba sun maye din sai ki
dawo dasu dakunan su insan kin cika yar nema mara hankali.
Daga zuwanki kina son ki haddasa min bacin rai abinda yaran nan keyi min ko
biyansu nakeyi zan iya basu hakkinsune jinya wasane halan ?
Kedai baki san harara ba wallahi ashe kema kyamar dan uwan naki kikeyi yasa kina
cikin garin nan kikaki lekowa ki gaidashi ?
Haba mama kyamarshi kuma to na sani tunda zancen ku daya dasu baki wanka ki
bushe kina wajensu kina koyon iya shege don bandashi banga abinda suka karaki dashi
ba.
Ke Rahama yayanku Habu ya baki maganin da za a dinga bashi din ?
Jin ta ambaci sunana yasa na dago ina fadin a,a mama bai bani ba bari dai in
koma in karbo mashi na sakai na fita na barsu zaune.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,
2️⃣
2️2️⃣
8️⃣8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Daga kwancen da yake yake tunanen halin rayuwa yau shine a haka ake fama dashi
mutumin da baisan dadin zama a waje daya ba ko yace yasan dadin hutu shiko a yaushe
cikin ujula yake haka ya taso ya kuma saba da wanan rayuwa hakan yabi jikinshi
sosai kuma don bai iya zama ba tare da yana wani abin da zai taimakawa rayuwansu ba
a gidan.
Yau sai gashi ubangiji yana ikonsa a kansa hutun dole na wahala ya sameshi irin
hutun da bawa bai kauna a rayuwanshi sai in dole ya kama irin haka din.
Yaushine matanshi suka hada mashi kai suke nuna mashi kyama da yake gani a
idanuwansu karara tun suna boyewa har ya fahinci hakan da gaske.
Gashi har Asmau don wauta irin nata har yarshi ta cikinshi take hana zuwa
gareshi don kada cutan jikinshi ya shafesu tunda ance dasu ana kamuwa da wanan
cutan .
Don haka su kiyayeshi kada su kama dashi suma bai taba zato ko tsamanin ko kowa
ya gajushi a duniya su zasu iya gudun shi ba haka yadda sukeyi.
Hawaye masu zafine suka zubo a idanuwanshi duk yadda ake kai zuciya nesa yana
kai akan matan nasa da ba haka yaso dasu ba sai gashi shi bai watsa masu kasa a ido
ba sune zasu watsa mai akan cutan da Allah ya dora mai na jerabawa imani.
Ajiyan zuciya ya sauke yana kara kallon part din nasa da yai shiru alaman ba
kowa a lokacin tare dashi mamace da a zaune wajen ita kuma ta fita zuwa wajen iya.
Su kuma yaran nan tun safe baiga gilmawan su ba dama sukanyi hakan suje su dan
huta mama ko kawu su zauna dashi din tashi yake son yi ya gaza tun dazun so yayi ya
dan mike ya kewaya bandaki amma babu kowa a dakin wanda zai taimaka mashi ya tashi
daga inda yake kwancen.
Fitowana daga part din iya naji gara naje can din in dubashi don yaya Habu
nagida kada in takura masu wanan yasa na zabi hakan na nufi can da yaro a hannuna.
Falon babu kowa banda niyar shiga dakin amma naga na dan lekashi ko idonsa biyu
in gadashi lokacin hakan yasa na yunkura saiga Saare a bayana batayi min magana ba
nima banyi ba .
Na leka nishinshi naji yana yunkurin tashi zaune itama ta fado dakin da nata
sallaman tana mashi sannu taimaka min in tashi ya fada a cikin yar murya.
Ba tare daya amsa gaisuwan da take mashi ba sai naga ta dubi inda nake tana
fadin meyake fadane banji shi ba nace yace ki taimaka mashi ya tashi.
Bari dai in kira mama ta fada tana juyawa da sauri har tana bangazana a lokacin
yaron na aje a gefe na karasa na kama hannunsa da sai ranan na taba kamashi irin
haka.
Ina mashi sannu ya mike zaune yana nishi Allahu akbar wai yaya J ne Allah ya
mayar haka cikin dan lokaci fitsari nake son zuwa don Allah ya kara fada.
Zaka tashine na fada a rude ya kada min kanshi dake duke yana maida numfashi
hakan yasa na kokarta na tayar dashi tsaye na kamashi zuwa bandaki yana kokarin
zama a toilet na fito daga dakin saiga mama ta shigo da saurinta tana fada.
Yaya zaice ki kamashi kice baki iyawa inba shashanci ba mutum kamar jafar yana
da lafiya zai tsaya sai an kamashine ?
To kedai kina kusa ashe ya samu ya mike ko nace ehh mama na kaishi bandakin
kingani ba shiyasa banson mu barshi shi kadai wallahi.
Ta karasa kofan tana kiran sunanshi ya amsa daga ciki banji meyace da ita ba dai
a lokacin na dauko yaron na fito falo tana zaune tana waya nayi niyar zama a
lokacin amma sai na canza shawara zan fita.
Ke wallahi ni tsoro naji ina zan iya zanga kamar zai sai gani tayi shiru tana
watso min harara a fakaice fita nayi daga falon gaba daya.
Don yanzu ban kaunar wani abinda zai hadamu kuma da ita kowa ya tsaya matsayinshi
a gidan shiyafi sauki baya da gaisuwa ba abinda ke hadani da ita kuma.
Na fita muka hade kuma da abokanshi da suka zo dubanshi mun gaisa zan tafi suke
fadin don Allah yi muna sallama munzo duba J ne magaishe shi kice su umar ne da
musa .
Na juya ina fadin ya kewaya amma bari in fadawa mama idan ya fito na shiga na
samu mama a falo take fadin ashe kin fitane Habu ya bada maganin ?
Ban shiga wajensu ba mama yanzu can na nufa dai akwai wasu a waje sunzo gaida
yaya umar da musa gashi ko ya kewaya nace na fada masu ai yana bandaki.
Bari mugani idan ya fito kice ya shigo ta shiga kuma naji tana kwala kiran
sunana hakan yasa nabi bayanta ina amsawa.
Kinga kayan nan nake son akwashe na manta dazun in shiga dasu ciki nace barin
kwashe mama na gyara gadon kafin naji fitowansu tana mashi sannu take fadin ya taka
a hankali dai.
Magana yakeyi banji ba naga tayi dariya tana fadin yace ki fesa mashi kamshi a
dakin kinsanshi sarkin son kamshine.
Na dauko kamshin na fesa har zuwa bandakin sai kuma na shiga nayi flushing na
wanke wajen nagama na fito yana zaune bakin gado yake gaidani da kai na kawar da
kaina gefe ba tare dana amsa ba.
Ni har ga Allah bala,in tausayin bawan Allah nake ji mutum mai kawaici da mutunci
irinshi shine a haka yau lalai bawa ba a bakin komai yake ba a wajen Allah.
Muryan mama ya katseni da take fadin kicewasu umar din su shigo na amsa da to na
koma daukan Abbati in fita dashi saidai hannusa yana cikin nasa hakan yasa na isa
nayi masu iso suka shigo.
Ina gaba suna biye zuwa dakin hakan yasa naji jan tsukin da Saare keyi bandai
kulata ba na dauko yaron na fito suna gaisawa don da shiga umar din ya soma fadin
ikon Allah Alhamdullahi J kaine a zaune yau ?
Masha Allah gaskiya jiki ya soma kyau Allah yasa hakan kaffarane a gareka mamace
ta amsa da amin gaskiya mama naji dadin ganinshi a yau din nan ikon Allah mama ta
karbe da ikon gaskiya.
Na samu ya habu a falo yana cin abinci na sake gaidashi zan shige yake ambatan
sunana hakan yasa na juyo gareshi alaman akwai maganan da zaimun ke nan na karasa
gabab shi na tsaya.
Ki zauna yace dani hakan yasa na samu waje na zauna dan nisa dashi kadan ya dan
dauki lokaci kafin ya ture plate din yana aje cokalin ya kalloni yana daukan abin
goge baki yace.
Rahama tambaya nake son maki kuma banson ki musa ki fada min gaskiya iya abinda
kika sani zanj dadin hakan idan baki toge ba.
Gabanane ya fadi yace wani magani kike ba J a ina kika samoshi kuma waya baki ki
bashi shi ya jero min tambayan a lokaci daya ?
Magani ?
Na fada a sanyayye ya amsa da eh magani wanda kike bashi nake son jin karin bayani
daga bakin ki ?
Ke Rahama kece keba yaya J magani as how hakan ya faru Ramaah waya baki magani ki
bashi Ramash innalillahi wa inna alaihim rajiun kin kasheni Ramaah ?
Kaina dago na dan kalleta da mamaki a daidai lokacin ya habu ke fadin haba mana
maria ki bari mu saurareta.
Dole tana da dalilin yin hakan wa zai turota wajen mu balle kiyi tunanen zatai
poisoning din shi kawai ina son ji daga bakintane kawai yayi maganan a cikin
hikima.
Jin abinda ya fada yasa hankalina ya dan kwanta ina fadin ni ba kissa zanyi ba
taimakonshi nayi don ganin irin wahalan da yakeyi.
Ki taimakeshi Ramaah ina kika san wani magani da zaki iya taimakawa dashi
Ramaah ?
An fada maki haka ake shan magani ba tare da kasan aikinshi ba haba anty maria
nifa Dage ya ban makaru lokacin da muka je ruggan mu shine nake bashi yana amfani
dashi yadda yace ayi.
Ina fadin Dage ne ya ban naga takai zaune rugwaf saman kujera tana dafe kirjinta
da hannunta biyu ta kara maimaita sunan da fadin Dage Ramaah ?
Baki na turo ina fadin to meye a dakin baffa fa ya debo maganin tunda yasan duk
aikin da sukeyi ninace ya debo min shi kuma ya debo.
Ramaah baki tsoron baffa ya sani koya sani tsakaninshi da dagene nidai na karba
kuma na bashi kudinshi.
Kasa magana tayi sai bina da kallo da takeyi baki sake ga kuma alaman tsoro a
fuskanta saida mijin nata yai magana ta juyo da kallonta gareshi.
Koma dai meye maganin yayi don haka shi za,acigaba da mashi har muga aikin
maganin don tun ranan data fara mai amfani dashi ya soma samun sauki a jikinshi.
Ban son wanan zancen ya fita ku kama bakinku kawai ku dai san halin gidan nan
yanzu dai zaki dauko min maganin in kaiwa mama da sunan nina karbo mashi a daina
bashi a boyen da akeyi.
Jeki dauko maganin mu gani haka na juya jiki ba kwari zuwa cikin dakina na dauko
maganin can kasan jakata inda na boye mai yawan saidana rage na fito da sauran na
kawo mashi.
Shane da kunu ko da madara ko wani abu dai hakka mai dan ruwa saidai idan ana
amfani dashi mutum zai kiyayyi duk wani abu mai yauki kada ya cishi.
Na bashi na magarya da dutsen tama da za a nemo ya amsa yana mamaki ya fice daga
part din sai lokacin ta samu daman magana.
Fada sosai tayi min tare da min kashedin irin wanan babban kuskuren dana tafka
din da kada in kara irin wanan wautan idan wani abu ya sameshi fa ta sanadiyana ?
Ni dai kasa magana nayi don sai a lokacin tsoro ya kamani don sam tunanen hakan
baizo min ba da farko sai yanzu din data fada.
Saare aka turo kirana nazo suna zaune har da kawu yaya Habu ke fadin ki duba
wanab maganin da kyau kece zaki dinga ba yaya J shi safiya da yamma don Allah a
kula akwai wani na wanka da za a kawo shima nayiwa mama bayanin komai.
Na amsa da to ina karban maganin da yafito a wajena gashi kuma a yanzu ya sake
dawo min mikewa nayi jiki na rawa sai lokacin naji yaya habu na fadin ita Nafisa
don dan magana ya hadata da Saratu shine zatayi fushin zuciya tace gida zata tafi ?
Ke Rahama kira min Nafisa na amsa da to na fita da sauri don a tsarge nake dama
a falon ganin daga kawu har ita mama basuyi magana akan maganin da yaya din ya miko
min ba.
A zaune na samesu dasu iya ga jakkar kayanta a gefe daya tana duban wayanta nake
fada mata sakon yaya din.
Na fita don ban tsayawa saboda Saare dake falon kwance da waya a hannunta tana
charting part din mu nakoma yayata tana zaune tayi tagumi cikin damuwa.
Yaya kukayi dasu take tambayana maganin na fara nuna mata kafin na zauna ina
fadin Allah ni da zuci daya na bashi wanan maganin kuma Nafisa tana wajen itama.
In Nafisa na wajen fa Ramaah kiyi tunanen Nafisa aiba uwarsu daya ba dasu baki
gudun ace an hada baki dake a cuta mashi.
Shiru nayi ina wiki wiki da idanu don sai yanzu nake hango zalla yarintar danayi
na daukan wanan risk din don ba karamin magana bane idan ya fita anji .
To ya zanyi aikon gama ya gama sai fatan Allah ya kiyayye yanzu kan don mai
faruwa ya riga da ya faru magani kusan sati daya ana sha yanzu meya rage kuma.
Da yamma saiga su yaya sun dawo da wanan abinda na fada na karya asiri ba a bata
lokaci ba mama ta dafa aka kai mashi ya diba yasha yayi wanka.
Yana fitowa ina tsaye na kada wanan maganin kamar yadda yay habu ya fadi dokansa
ya amsa ya shanye gaba daya ya miko min cup din tare da godiya.
Ya tambaya ko magariba yayi mama tace kamar da sauran lokaci nafisa dake shigowa
tace an fara kiran sallah a wasu wuraren ai.
Saida yayi sallah magariba kafin ya kwanta kamar karamin yaro ya dunkule a waje
daya lamo kallo daya zakiyi mai ya baki tausayi.
Ina ganin haka na nisa ina fadin Allah ya sauwaka na fita da kayan wajen zuwa
kitchen dinsu da yanzu yake samun gyara don anty Nafisa ko yaushe tana tsabraceshi.
Tunda na dawo nashige dakina ban fito ba sai washegari nayi shirin school na
fita na biya part din na gaidasu mama ke fadin jiya ina ta jira ki dawo baki dawo
ba kodana aika akace barci ya daukeki.
Nace ko kema kin damu da zancen shashan nan Saratune ai ita tazo muka kwana tare
tunda Asuba ta gudu wajen iya wai batayi barci da dadi ba a nan.
Nayi murmushi ina fadin mama maganin fa ina son shiga school kada in makara to
sai ki hada din ki bashi tunda maganin yana da ka,idan sha ?
Nayi mamaki jin furucinta na ka,idan sha watau yaya habu shima ya nunke su mama
a baibai ke nan don kada su gano wani abu kome ya fada masu oho ?
Da sallama nashiga duk sa safiyane sosai amma na samu har yayi wankan maganinsa
yana kwance yayi rigingine jikinsa saye da farar jallabiya mai dogon hannu.
Gaidashi nayi da yaya jiki ya amsa da Alhamdullahi nagode na sada kai kasa ina
fadin zan shiga school ko za a hada maganin yanzu ?
Har na gama kadawa idonshi yana kaina har na gama na miko mashi ina fadin gashi
yaya don yanzu ba sai an rike cup din ba yana iya rikewa yasha da kanshi.
Ya dan dago daga kwancen ya karba yasha ya miko min cup din yana godiya ya koma
ya kwanta a yadda yake bankai ga fita ba naji yayi wani irin gyatsa yana hamdallah.
Kodana fito ban tsaya ba nayi masu saina dawo na samu Nafisa zaune da mama suna
magana a lokacin bandai san akan meye ba.
Daga kwancen da take daki lamo jin ba motsin kowane ta daga waya yana ringing
sai can aka daga ta wayan ke fadin ai wallahi Saare nayi fushi.
Ta amsa da fushin me tace wai ace tunda nazo kaduna baki kirani ba haba saaratu
amana baice hakan ba ai, na zata kece ta farko da zata nemeni sai naji shiru Allah
nayi fushi sosai da hakan.
Haba dai tawa nifa sai jiya na samu ya kara dawowa sai kuma na samu wai baku nan
dukkan ku iya ke fada min shirme wai kuna kyaman yaya yasa mama tace kuje gida har
ya samu lafiya.
Humm ni bansan me zance ba banda wanan sakariyar Asmau data fitar muna da zance a
fili yar iska ko an fada mata inma kanjamaune haka ake kamuwa dashi ?
Ba kanjamau bane wallahi don yanzu yaya yaji sauki sosai ba kamar yadda nazo a
ranan na sameshi ba yanzu har tafiya yakeyi da kansa.
Don Allah ki bari !
Tace wallahi ko saidai abinda banji dadinsa ba shine wai fa Nafisa da yarinyar nan
Ramaah suke taya mama jinyarsa.
Su kuma wallahi iam telling you don nayi maganan hakan baiyi ba shine munafuka
Nafisa waina nuna ba mama ta haifeta ba kar kiso kiga fadan da mamake min fada
wallahi akanta.
Nafisa fa ita har ta