Showing 273001 words to 276000 words out of 328222 words
Chapter 92 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
basu tsaya min ba
Rahama wa zai tsaya min a garin nan ?
Na dauka koda ace ban raye su masu tsayawand suga sun kare min hakkin iyslina da
nasu gaba daya amma sai abubuwa akeyi barkatai wanda hanlali bai tunanensa.
Na kansa a raina wanan ciwon wani jerabawan rayuwace Allah ya aiko min dashi da
zan fahinci yadda lamarin duniya ya koma a yanzu.
Don mutane ko da ranka ashe sai kana da amfani ake rayuwan komai dakai sai kana
cikakken mutum duniya har dan uwanka zasu dama dakai Rahama ?
Sosai nagodewa Allah da dabaran da Allah ya ban nayiwa kaina haka kema haduwata
dake Allah kadai na barwa sanin dalilin hakan a tsakanin mu dake.
Don ta dalilin aurenki Rahama har Allah ya ban dabaran boye kudina a gidan nan
ba tare da nakai banki ba har ke dake zsune gidan ma bakin san da hakan ba don da
suna account dina yau Rahama da kudin nan dana aje anan suma an batar dasu kamar
yadda wa yan nan suka salwanta min mun koma banda komai.
A lokacin kallon mamaki nake mashi yayi murmushi ya gyara zama yana fadin
wallahi haka kawai nasa aka kawo min kudin nan nan gida kamar wani abu da niyar
idan na dawo daga tafiyan da nayi basai na tsaya shiga bank ba wajen miliyan ,,,,,,
Sallaman Yazid daya shigo lokacin ya katseshi duk muka bishi da kallo lokaci
guda don yaja ya tsaya daga kofan shigowa falon yana tafa hannayensa.
Kafin ya soma fadin wai don Allah yayane nan nake gani haka ko dai wani yaya J
din kika sauya munane yau din ?
Tsuki Jafar yaja yana kawar da kai ya karaso yana fadin to ina mamanka dake can
tana fada a kanka ko ita taga wanan sauyi yau haka sai tayi mamaki zata daina fadan
da takeyi dakai tun jiya.
Na fada mata dama kai keda jikinka da iyalinka ta barka kayi abinda ranka yake
so amma tace ba haka ba tunda bakaji sauki ba don me zaka dawo nan ka tare kuma ?
Bayan kasan har yanzu magani kake sha ni itace ma da fitinan ta ta tayar dani
tunda safe yau wai na kawo maka maganin nan kasha ya miko mai wani leda dake
hannusa fari.
Yace ba Rahama ita mama fadan me takeyi a kaina ko na zama yarone yau kuma da za
ace sai yadda akayi danine wai magani ko a nan nake ba zan sha maganin bane ?
Na rasa meyasa take haka wai akaina wallahi to dai kan ka shirya don wallahi
fada ta kwanayi ba don iya ba jiya data biyoka da daren nan iyace ta hanata zuwa
sai abin ya ba jafar din dariya haka yasa ya dan sake murmushi a fuskanshi kadan.
Don sheri sai ya juyo gareni yana fasin wai don Allah amarya nima ba zaki samo
min wata yar filo ba kuwa in kara don dai wanan abin akwai ban mamaki gaskiya ?
Ki duba mutumin ki don Allah yau shine a haka yayi clean wallahi yayi kyau kamar
bashi ba jiya jiya nan da daren nan fa yazo gidan nan amma dubashi don Allah ?
Idan ka gama ka kira min emanual zanyi magana dashi a gabanka yace abinne Allah
da ban mamaki kwarai da gaske ya J baka yadda kayi wani fresh ba ?
Kaji mena fada ai yake fadawa kanin nasa shima yazid din ya dubi wayanshi yana
fadin shi nake kokarin kira ai yanzu hakan .
Mutumin ya dauka suka fara gaisawa da yazid yake fada mai mr Jafar yake son
magana dashi yana fadan haka ya mikowa yayan nasa wayan ya soma magana na mike ina
fadin ya yazid a kawo breakfast ne ?
Wallahi madam dina ta cika min ciki kafin in fito amma zan dan taba kadan saboda
kwadayi ya fada yana dariya nidai na shige na kwaso mai kayan abincin da dan uwan
nasa ya karya dasu din na aje mashi a gabanshi.
Duk da ina aiki ban tsaya ba lokacin amma ina cankar maganan da Jafar din keyi
da mutumin akan kudine yake tambayanshi ba,asin su.
Zance na dashi tun dawowana jiya nake nazari a raina wanda na gama kai karshen
tunanena wanda abinda zuciyana ya ban shine dukiyan sun samu matsala saboda
dalilin kwanciya rashin lafiyan nan nasa.
Indai za a rasa dukiya Allah ya bar muna shi Alhamdullahi rayuwa ya nema dama
sai anema din daga baya in Allah ya nufa da sauran rabon hakan.
Kirana da yaya din keyi yasa na fito daga daki tare da amsawa cikin dan muryana
din nazo gareshi yake fadin don Allah dauko min wani file na nan a dakina a drower
kasa ki kawo min .
Na nufi dakin na duba nagashi na kawo mai ya karba yana budewa na juya da niyar
barin wajen naji sallama ko ban juyo ba nasan muryan yaya habune a lokacin ya shigo
gidan shima.
Hakan yasa na dakata don mu gaisa na gaidashi daga inda nake ya amsa min kan
kadaram kadaham nima na juya zuwa daki ba tare dana tambayeshi iyalinsa ba.
Ina shiga dakin naji ya sun soma magana tun baniin me suke fada har na gane
musayan magana sukewa junan su karshe dai na barjin muryan yan uwan saina jafar din
dake magana a cikin fada da bacin rai yana nuna sakacin da sukayi aiba shi kadai
hakan ya shafa ba dukkansune.
Ni dai naji yana fadi a karshe cewa yasan matakin da zai dauka idan ma na waje
sun cuceshi har dasu baiyi tsamanin hakan ba ai.
Nan na soma jin muryan ya habu yana fasin J ya kake son nayi kana sin kaga
laifinane a banza cikin zancen nan.
Kafi kowa sanin bakin jinin da nayi a zancen nan gida ba a barni ba J kasani
balle waje mutane yanzu basuwa Allah .
Ni dai tun ina saurarensu har barci ya daukeni bansan fitansu daga gidan ba barci
na samu sosai nayi a lokacin yana zaune falo bai tayar dani ba don yasan harda
laluran cikin dake jikina a cikin barcin.
Ban falka ba sai wajajen karfe daya na falka nayi mamaki yadda na samu barci mai
dadi haka a lokacin na fito falon na sameshi a inda na barshi yana duban takardun
dana dauko masa dazun din.
Gaidashi nayi hakan yasa ya dago yana fadin kin tashi na amsa da eeh ina zama
nake fadin sun tafi ashe yace tun dazun suka tafi me zasu fada min tunda suyi
shirme .
Zaune nakai a hankali ina fadin na zata ai azahar tayi yace da sauran time kin
fara zuwa awo ne ya jefo min tambaya ?
Hakan yasa nima nake mai kallon mamaki yaushe zan fara zuwa awo bai sani ba duk
da dai bangarin ai a lokacin don haka nayi shiru ban bashi amsa ba.
Saida aka dan dauki dan lokaci ya dago yana fadin bakiji mena fada ba na dan
rausaya ina kawar da fuska nace ni banjin komai ai yanzu.
Ko baki jin komai baki zuwa asibiti a duba lafiyan ki dana baby din a gani dole
ki fara zuwa awo zanwa yaya Ai magana tazo kuje tare ko kuma maman tudu .
Ni banje na gaidasu ba sai a kirasu suzo kaini asibiti kamar banda lafiya nidai
ka barsu karka kira kowa don Allah na fada a karshe.
To me kike nufi ba zaki ba ke nan ko dole kije asibiti don lafiyan ku idan can
gida zaki biya ki dauku mama din fine amma asatin nan ki je a dubaki please.
Shiru nayi na kasa cewa kkmai saidai nasan tunda ya fada sai anyi haka din don
idan ban manta ba sun taba fadan zuwa awo da Asmau a gabana kafin na aureshi da
shigan cikin dan nan nata data yaye din wanda aka haifa bayan an aureni .
Yana tafe a gajiye ya fito filin kwalo rigansa na kwalo yana rataye a kafadansa
saidai yana sharo kwanan gidansu ya hango dandazon yaran unguwa a kofan gidansu.
Sauri ya kara ya iso kofan gidan fada ya fara da yaran yana korasu duk daya
fahinci fadan da akeyi a cikin gidan nasu da yanzu ya zama kamar gidan haya suka zo
kallo.
Gidan ya shiga kanninsa mata ya fara hangowa a rakube cikin damuwa wucewa yayi
zuwa bakin randan ruwan mahaifiyarsu yana diban ruwa a cikin takaici a fili kuma
halin ko in kula yaron ya nuna ga abindake faruwa gidan tsakanin iyayyen nasa .
A yadda ya fahinta da kishiyar maman tasu da mahaifinsune suka tararwa uwar
nasu ake wanan masifan da zage zage a yanzu inda sabo ya saba da ganin hakan dashi
da yan uwansa din don zaman lafiya ya kaurace a gidan nasu tun shigowan wanan matar
gidansu.
Karan dukan da yaji mahaifinsu nakaiwa mahaifiyarsu tana kakarin neman taimako
ga yan uwansa na ihun ceto yasa ya yarda mudan ruwan kasa ya nufi wajensu da sauri
yana fadin .
Baba a,a baba ya haka kuma ka barsu suyi fadansu mana tunda bada kai akeyi ba
zaka kamata da duka kuma haka a gaban mu.
Uban ya nuna baima san yanayi ba shima haka baisan lokacin daya kai hannu yana
banbare hannun mahaifin nasu ba a jikin mahaifiyarsu.
Aminu zaka shigarwa uwarkane kome amayar baban nasu ta fada bai kulata ba sai
kokarin kwatar mahaifiyar da yakeyi rai bace ganin mahaifin nasu kasheta yake son
yi yasa ya nuna mashi karfi ya kwaci uwar yana dagota daga kasa inda uban ya shake
ta.
Baiyi aune ba yaji an kwala mashi abu a kai hakan baisa ya sake mahaifiyar ba
sai juyawa da yayi ya rike tabaryan dake hannun amaryan mahaifin nasu da hannunsa
daya yana fadin kika dukeni ?
Dan iska zaka ramane kai ga mai karfi kazo ka tureni ka ceci uwarka ko ta
kasheka ta kashe banza da iska mai halin uwarsa kawai.
Bai kulasu ba yaja uwarsa dake rusa kukan takaici zuwa dakinta rai bace yana
fitowa don bai tsaya a dakin ba suka hade da uban nasa ya soma fadin.
Kai san iska yau din nan saika barmin gidana ni zaka nunawa ka kawo karfi a yanzy
har zaka tureni don kana dan iska ka zabi uwarka dani ko ?
To ka fito dakai da uwar naka kubar min gidana bai kula uban ba ya nufi wajen
ruwan da yake diba din ransa a bace nan ma uban bai kyaleshi ba yabishi yana
fadin .
Nafika iskanci dan banza kawai kai har kana ganin kai wata tsiyace ko a yanzu ni
zaka daga kan uwarka dan banza kawai.
Shi dai yaron bai kula uban ba ganin hakan ran iliyan ya baci ya nufi inda suke
aje icce ya rarumo ya nufoshi nan yan uwansa mata suka hau ihu suna fadin ya gudu
ga baba nan da icce tafe hankali tashe .
Bai gudu din ba ya nufi bayi ai kuwa yakai mai duka da iccen zafin hakan yasa
dan dakatawa yana kallon uban dake fadin.
Nace ka fice min daga gida mara mutunci wallahi baka zama gidan nan damu dan iska
daga kai har uwarku ku barmin gidana gayan tsiya kawai.
Uwar ta leko ta hau bakin ta har yaron ya shiga bayi sai kuma ya fito ya nufi
hanyar waje ya fice daga gidan cikin bacin rai.
Hausawa sunce kowa yace ruwan wani bai tafasa nasa ko dumi baiyi ai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/24, 10:32] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
8️⃣6️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Nasa a raina ranan zai koma wancan gidan donshi ma banyi motsin girkin dare ba don
nasan a ka,ida dai kwana bibiyu mukeyi ga girki tun muna mu ukku.
Balle yanzu da mu biyune tare dashi muna falo zaune tun bayan fitansu yaya Ai da
sukazo min sannu da dawowa a cewarsu.
Muna zaune maigadi yayi sallama ya tsaya daga kofa yana gaidamu bayan ya amsa
yake fadin akwai wani yaro a waje tace daga zamfara yake a fadama sunansa Aminu ?
Kallon sa nayi naga ya daure fuska yana fadin to me yazo yi nan da baije can
gida ba wajen su mama zaizo nan kallonsa nayi nace ko dan yaya Barakhane ?
Yace shine mana don me zai biyuni nan kuma yaushema yazo garin na dubi maigadi
dake tsaye nace dashi ce ya shigo malam don malam nake kiran maigadin dashi.
Ya juya da sauri ya fice fada yaya keyi yana fadin don me zaizo nan barshi yazo
najima meya kawoshi ni ban daukan wanan iskancin a yanzu gaskiya.
Haba dai ba girmaka bane yaya yaron nan ai ya gansu ya nufo nan inda kake don
Allah dai kayi hakkuri kaji abinda yazo yi din.
Yaron ya shigo tun a kofa ya zube yana fadin kawu ina wuni ya amsa mashi fuska
daure yaron cikin in,inniya yasoma fadin dama naje can gidane na samu baka nan su
mama ma sun fita akace sai mama salima ita kuma tana barci.
To sai akace me ita Asmau bata nan ne ya tambayeshi naga yayi kasa da kai ganin
na mike tsaye yasashi fadin mummy ina wuni na amsa da Aminu anzo lafiya yaya su
anty ?
Suna lafiya kalau ya fada kafin mu gama gaisawa ya sake jefo mashi tambaya da
mekazo yi zaria ko baka fara school din bane har yanzu.
Nayi jam kawu basu fara dauka bane ya fada na katsesu da fadin kaci abinci kuwa
Aminu yace yanzu na iso mummy naje can ban samesu ba nazo nan.
To shigo mana kaja ka tsaya can a kofa kamar wani bako bari na kawo ma abinci
kaci ka huta sai ku tatauna ko na nufi kitchen din mu abinci na hado mashi mai
lafiya yaji ganye a sama da kayan hadi.
Inda yake zaunse nakai mashi ya karba yana godiya na juya na kawo mai ruwan sha
ya soma jan plate din zuwa gabanshi na juya zuwa cikin dakina .
Na dan jima a dakin na fito na samu yaya na fadin to yanzu yaya kake son ayi ke
nan shi ubanka ya koreka gidansa shine ka nufomu nan ?
Bayan haka kai baka da hankaline ko kasheta yayi ina ruwanka da saka masu hannu
a cikon fadan da sukeyi dashi ?
Mahaifinkane fa Aminu baka da hankaline koka fara shaye shayene yaya yi hakkuri
don Allah kasan uwa ba yadda za ayi yana tsaye yana kallon zai kashe masu mahaifiya
ya kyalesu ?
Nice na tsoma masu baki a zancensu bayan na gama sauraren maganganunsu da dansa
din abindana fada yasa ya dan kalloni yana fadin.
Haba Rahama baida hankaline da zai ture ubansa ubansane fa don kawai yaga suna
rigima zai saka baki a cikin zancensu hakan ya nemi albarkansa ke nan ?
Zaune nakai cikin sanyin jiki ina fadin yaya ceton mahaifiyarsa kuma yana iya
saka yayi komai a lokacin rabu da irin gidan nan da ake irin haka a gabab yaya abin
yakan saka yayan shiga cikin zancen wani lokaci.
Don babu mahalunkin da zai zauna ana dukan uwarshi bai dauki mataki akai ba kai
ya girgiza yana fadin Rahama na gane da sauraki kema kina da kuruciya a tare dake .
Har yayi shiru ya dago yana fadin meyasa su yan uwansa mata basu sa hannu a
rikicin ba sai shi zaisa hannu don gashi mai karfi ko zai iya fada da ubansa.
Ba hakana bane yaya yayi kuskure don Allah da gani a jigijce yake a barshi yaje
ya huta bari nasa maigadi ya bude mashi dakin baya guda ya zauna kafin asan abinyi.
Da sauri naji yaya din yace No don me zai zauna muna nan baga can gidan ba ya
zauna mana da iya nace don Allah yaya tunda yazo nan din ka barshi ?
Kayi hakkiri ya zauna nan din bai min magana ba na dade a zaune wajen ina
sauraren amsan shi baice komai ba har lokacin.
Haka yasa na mike ina fadin inka gama taso muje kaga inda zaka sauka din na fice
ba tare da nace komai ba.
Shima kuma baice komai ba sai wayanshi da yake duba ya fita batun mu daga bayan
mu akwai dakuna hudu kamar boys quaters a gidan da suke rufe sai maigadi dake dan
amfani da guda don adana abubuwansa.
Tambayasa nayi ina kayanka ko suna can gidan ka bari yace haka nazo mummy don
bai bari na shiga gidan ba balle in dauki wani abu .
Ok shiga kayi wanka ka huta zuwa anjima kazo ka fita nan titi ka samu kananan
kaya ka saya na juya na bar wajen ina jin yana fadin nagode mummy nagode.
Na koma ciki na samu yaya a zaune zama nayi ina fadin an bude mashi dakin
tsakiya zai zauna a cikinsa shiru yayi ba amsa hakan yasa naja bakina nayi shiru a
cikin tsarguwa da hakan da yayi min din.
Kamar daga sama naji muryanshi yana fadin ke har yanzu baki fahinci mutanen nan
ba naga kina kokarin jawo muna yaron nan a gidan nan banson wani abinda zai kawo
muna fitina ko tsegumi ki barshi can ai kakansa tana nan yaje can wurinta ya zauna
mana don me zai nufo nan