Showing 144001 words to 147000 words out of 328222 words
Chapter 49 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
gaisawan da ita lokacin shima ya shigo.
A,a gaku kamar tare kuke tafe mana kun shigo lokaci guda haka mama dubu ke fadan
hakan .
Sai Anty Rukkaiya tace daga can gidansa muke ai tafiyan nasane dama munzone gun
sarakan mu da kayan tausan gabansu.
Kaya kuma kayan tausan gaba kamar wani abin bin bashi tunda anyi angama haka ba
wani shiri har wani kaya kuma za a zo sayan bakinsu dashi ?
Yau aka fara hakan idan mijinki bai maki bake shi yana da ra,ayin yiwa iyalinsa
hakan kuma nice nan nasashi yin hakan gareshi ba wani ba.
Meye amfanin samu dama idan kana da zarfin yin abu kayisa a cikin lokacinsa tunka
lokaci ya kure maka don wata rana sai labari.
Kwarai kuwa anty Rukkaiya ta fada daga ta karbe iya dake magana ai har yanzu mama
dubu ana hakan ai silan zaman lafiya maigida yake nema ga iyalansa ga hakan.
Suna dai ta fadansu dagashi har mama shiru sukayi lokacin kowa da irin abinda
yake tunane a zuciyarshi idan yake auna zancen mama da rashin son hakan da yayi din
karara.
Ita kuma mama sai auna irin yadda dan nata ke kashin kudi akan zancen matansa ko
wani lokaci har yaushe ya gama da zancen wanan auren daya dauko balle ya dauko
wanan din ?
Ina kayan suke yanzu ta fada tana sauke ajiyan zuciya tana kallon yaya Ai don
tasan halin Rukkaiya har take ita ba kamar Ai din ba.
Suna mota ta bata amsa sai lokacin ya dago yana fadin mama aina jima da sayansu
tun lokacin dana hada lefen Rahama suma na hada masu nasu don ban garine ba a kawo
masu ba.
Allah ya kyauta ta fada tana daukan jug din kunnun kamu da aka dama mata tun
safe bata sha ba salima yasawa kira daga falon.
Ta fito tana gaidasu ta juya wajenshi yake cewa Salima kira saratu kuje mota kaya
na nan bayan mota ku kwaso sai kije ki kira min su Asmau suzo nan.
A,a kaiko a can za a kai masu bakaji bahaushe yace tausan kirjiba a yaren
mutanen sokoto wanan ai na ban hakkurine ba zasuce dai bakayi masu ba ai iya ta
tare da fadan hakan.
Kai tsohuwar nan tasan komai wanan gaskiyane mu da mukai masu laifi aimu zamuje
mukai masu har daki ko yaya Ai ke fadin hakan.
Salima dai tana tsaye yace jeki ku dauko salima ku kawowa su mama su gani kafin
a mika masu ya fada yana kallon Salima din.
Ta samu saratun zata shigo don su gaisa da yan uwan nasu take fada mata zancen
yayan nasu ta wani bata rai tana fadin kaya kuma kayansuwa kuma ?
Ni inana sani ta bata amsa a takaice ta wuce ta bata kara furta komai ba zuwa
wajen motan nasa ta bude bayan motar da dama saida ya bude ya fito.
Dankari kayan su waye haka wai ta kara fada tana karasowa wajen motan ita dai
salima takaicine ya kume ta sai gashi ya fito shiya taimaka masu ya fitar suna
shiga dashi.
A tsakiyan falon iya suka tara kayan shiya shigo a karshe da wani daya dauko ya
aje gaban mama yana fadin mama ga naki nan.
Yaya Ai ban fada maku tun can cewa wanan na mama bane wanan kuma nasu iya dasu
salima ikon Allah kai Jafaru kace yan tausan gaban suna da yawa nikan naga abin da
yawa.
Salima jeki wacan na wajen ki dauka ki mikawa matar habu duk suka kalleshi ya
fuske yayi niyar hakan shiyasa ya fada a gaban kowa yaya Ai wanan nasu Asmau ne
idan kun tashi sai su kama ku mika masu.
Ikon Allah lokacin abu ayisa kanina kayi kokari Allah ya saka maka da alheri
anty Rukkaiya ta fada cikin nuna jin dadinta ga abinda dan uwan nasu yayi.
Kai haba ai hakan ya zama riya nime zanyi da wani kayan tausan gaban uwargida
kuma da sauri Rukkaiya tace a,a keko maman Habu.
Wanan ai sai dan da yasan darajan iyayye da yan uwa yake wanan wani ai kome za
aji bai dameshi ba albarka kawai a yanzu zaku saka mashi.
Sai lokacin ta sauke ajiyan zuciya tana fadin Allah yayi albarka an gode anty
Rukkaiya tace Allah kuma ya basu zaman lafiya ya kawo zuria masu albarka a ciki
muzo suna haka kafin shekara.
Ya mike yana fadin zan lekasu tare suka fita da salima daga part din ta dauki
na Yanda ta nufi part dinta dashi cikin farin ciki.
Lokacin anty Rukkaiya ta mike tana fadin bari mu bude muga abin arziki muba ido
abincinsa abu yayi kyau wallahi jafar kayi ko yanzu da mama ta yarda tayi wani
aurene bayan baba ai a kara haifo muna irin jafaru bamu fushi.
Aka kwashe da dariya na mama aka fara budewa sai am barka sukeyiwa kayan turmi
biyarne da lace har da dadduman sallah a ciki yaya Ai tace kin gani maman Habu a
samu na muna addua kenan tana daga dadduman sama.
Turaren ciki suka dan fesa dakin ya dauki kamshi wanan aikin anty salma ke nan
gaba daya an yaba komai a wajen .
Rigiji rakwaf inji hausawa don Asmau dake zaune a falon tare da maigidan don ita
Saiba daki tashige tana jan kamshi.
Shiko tunda ya zauna bai daga daga wajen ba yana zaune tare da Asmau da yaran
suna hira sai gasu suka fara gaisawa yaya Ai ke fadin ina yar uwar takine ?
Tana ciki ta fada tana kallon hanyan dakin Saiban ta yunkura ta mike zuwa kiranta
lokacin ya mike ya shige dakinsa ya rufo.
Saiga su sun fito tare suka samu waje suka zauna ta gaidasu a tsatsaye da ina
wuni suma suka amsa da lafiya.
Yaya Ai ta soma magana take fadin to Asmau Nusaiba gunku muka zo wanan kayan
nakune na fadan kishiya aci da hakkuri don Allah.
Tsuweee Saiba taja wani tsuki da kowa wajen ya kallota yaya Ai cikin rashin
damuwa da hakan take fadin hakkuri dai za ayi tunda shi kowa keyi abinda muka gada
ke nan.
Da fatan zaku zauna lafiya da yar uwar taku itama daga can muke munyi mata fada
daidai gwargwado da azauna lafiya don Allah tunda yanzu an zama daya.
Yaya Ai zaman lafiya kam ai babushi tunda tun farko ba a nemi a zauna lafiya ba
yanzu daidaine J yazo ya auro muna wanan yarinyar a matsayin kishiyar mu ?
Haba dai don Allah ayi muna adalci mana don Allah abinda akai muna anyi daidai ke
nan ga hakan ?
Yaya Ai tace adaiyi hakkuri dama hakan muka gada ai a rayuwan mu tunda mun fito
musulmai Alhamdullahi ai kishiya inga hakkuri abokiyar zamace saidai wanda basu
gane hakan ba .
Yanzu dai ga kayan fadan kishiya nan mun kawo maku don bai zaunu bane ba abayar
a cikin lokaci ba a yi hakkuri don Allah.
Babu komai yaya mungode Allah ya bamu hakkurin zama da juna mun gode ai muna
godiya ta mike zuwa dakinta itama nusaiban ta mike tabar wajen a fusace .
Anty Rukkaiya tace ikon Allah yar nan da karfin hali kike kuwa kema ai wata kika
sama kika shigo kuma tayi hakkuri ba a hakkuri haka aka zauna dake ?
Ashe taji sai ko ta dawo tana fadin in ita taga tana iyawa ta zauna ni banga ina
iyawa ba dama anzo a fada muna maganane a fakaice yadda aka saba ashe ?
A,a Nusaiba kar kice zakiyiwa su yaya rashin kunya a nan gaskiya Salima ta fada
don tunda suka shigo da kayan ba wanda ya fita a cikinsu.
Wanan hayaniyar yaji ya fito yana fadin wai meye meke faruwane wai haka ?
Yana kallon Salima din .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
4️⃣9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Shiru tayi ta juya zuwa dakinta cikin hasala ashe baki ciki yar iska ba daki dawo
ki maimaita abinda kika fada a gaban yan uwana.
Yau in baki mamaki don da kinbar gidan nan na har abada su yaya zaki kawowa
rashin kunyar ki sun wuce hakan a wajena balleke.
Duk iya shegenki da iskanci ya tsaya akaina amma banda yan uwana don kamar
iyayye suke wajena bazan daukar maki wanan iya shegen daki dauko yi a gidan nan ba.
In zaki zauna kiyi hakkuri yadda kowa yayi ki zauna idan baki hakkuri kuma kofa
a bude yake gareki tun yanzun nan kaji min sakarai mara lissafi ba a hakkuri ke
akai hakkuri dake aka zauna koba wata kika shigo kika sama a gidan nan ba.
Akwai yar cin aman data fiki keda kika yaudari kawarki kika hana mu zaman lafiya
don son kai irin naki ?
Yi hakkuri Jafar mu ai mun tashi ke nan muma tunda munyi abinda ya kawo mu.
Mu yanzu idan bata so dai ruwanta Allah ya gani ka fita hakkinta ai ba kowani
namiji ke wanan ba yanzu don ya kara aure.
Yanzu a zamanin nan in bashi ba wani namiji zai kashe maki wanan galarin haka
kuma baki shafa masa lafiya ba gidansa ?
Shi ya daukesu don ya mayar dasu gida a hanya yayi fada sosai yake fada masu
irim damuwan da saiban har asmau suke sakashi ciki.
Sai hakkuri suke basu a nan family house suka sauka tare da nasu abin arzikin har
yan uwan zaman mama dubu alherin ya shafa.
Dama haka yakeshi muddin ya samu kudi sai kowa na tare dashi ya sani don zaibi
yan uwa daga daga ya dinga masu dan alheri daidai gwargwado.
Wanan yas arzikin yake bukansa kamar an bude masa kofofin arzikinsa ga baki daya
shi mutum ne mai yawan alheri.
To wanan alherin daya shigo maine yabi yan uwa ya raba masu abin arziki har
mazan da yan unguwa abokan arziki ya samu abinda ya basu a lokacin.
Kwana shidda ke nan yayi a gidana kuma zai koma washegari don aiki daya taso mai
na bussiness dinsu lokacin sun samu kaya irin wanda suke fita dashi waje din zai
tafi ya gani.
Ance sabo turken wawa a yan kwanakin na saba da yaya Jafar sosai yadda yake jana
a jiki hakan yasa na fara sakewa dashi inda ko fita yayi kafin ya dawo na shiga
damuwa.
Shiko sai shirye shiryen tafiyansa kawai yakeyi daga gidan iya har nan da nike
ni kadai abubuwa kawai yake shigowa dasu yadda ba zamu nemi komai ba ke nan a
bayanshi.
Gwargwado yaya Jafar yana kamanta adalci a dan fahintar danayi mashi yadda yake
a tsakanin iyalinshi din haka kuma ina ganin yadda yake mu,amulansa a baya kafin na
aureshi.
Missalin hudu ya shigo gidan nasu kai tsaye part din iya ya nufa wanan
dabiansane yanzu sai ya fara shiga yaga kwanansu ya wuce zuwa wajen matanshi.
Saidai ga mamakinshi a nan part din ya samu matan da kowa na gidan zaune inka
debe yar uwara da yanzu ke zaman kadaici ita kadai don kamar an hada mata kaine a
gidan gabadaya sai salimane ke kula lamarinta.
Suna ganinshi sukai tsuru tsuru bakin dayansu kallo daya yayi masu ya fahinci
akwai matsala haka ya daure ya gaida mama da iya ya samu waje inda saratu ta daga
ya zauna yana fadin.
Lafiya dai ko ?
Ina fa lafiya Jafaru fitina su wa yan nan ai bata kwana a wajensu ko yaushe
tsaye take suna figanta.
Wai kayan nan daka shigo dasu suke fada a kai yakai harda bugaiya suna nema su
illanta kansu sujawa mutane aiki.
Fada kuma akan me iya to gasu nan dai kaji a bakinsu ance waka abakin mai ita
yafi dadi dama.
Duban inda suke zaune yayi yana fadin ke Asmau ya akayine tace ina daki Nusaiba
ta sameni wai na rage kayan nan dakai muna su yaya suka shigo dashi.
Wai da suka tafi na hurhura kayan cikin na kwashi masu kyau nabar mata marasa
kyau don haka in fito da nawa ta dauki abinta niko bansan wasu kaya dana dauka a
cikin nata ba.
Innalillahi ya ambata a fili ya katse mata zancen da fadin iya kayan nan komai
iri daya aka saka don gudun haka yanzu haka kayan haihuwan ita asmau suna nan aje
don kada tazo ta haihu ban kusa a girsheni don hakane ban kawosu gidan nan ba na
aje.
Amma kuma wai kinji abinda wanan mara hankalin take fada yanzu komai fa kala
dayane a cikin akwatin saidai a banbanta kala kawai .
Samu sukayi aida Allah bai kashe ya basu kai ba daka zama bawan matam da basu
godewa irin hakan ba zai faru ba to sun samu sai suyi iya shege ai mama ta fada
cikin kunan rai.
Mama laifine yau na samu banwa iyalina ba au duniya saita zageni kan hakan to ya
zama laifi kan a wajen matanka yanzu .
Yanzu idan nayiwa Rahama kayan lefe ban masu komai ba ni kaina nasan sai Allah
ya tambayeni akan hakan tunda ina da halin yin hakan garesu duk da nasan karshe
wullakantawa zasuyi tunda basu iya tattali ba a rayuwansu.
Nusaiba baki da tsoron Allah a lamarin ki kayan nan bake kika rokeni ba ganin
daman kainane na hado makushi yan uwana da suka kawo kayan nan ranan saida kika
nemi yi masu rashin kunya.
Don baki da kunya yanzu kece kika dawo kina fadan kayan kuma ke bafa dole bane
zama dake Nusaiba koda duniya muka haifa dake kin sani ?
Kawune ya shigo yasa yayi shiru bai cigaba da fadan da yakeyi ba lokacin
gaidashi yayi ya mike yana fadin mama ni gobe zan koma daga can ina ganin har kasan
waje zan fita don mun samu kaya zan bi jirgi in samesu can.
To wani kasa aiki kuma kuka samu na fita kasan waje yanzu Jafar kawu ke tambaya
yace eh ba wai kasan wajen turawa make nufi ba ai nan ghanane kawai na fadi hakan
don ta gane.
Ghana ba kawai bane ai Jafar ya fada yana dan dariyan yake a fuskansa zuciyarsa
kuma tana mashi tafasa da wanan zancen da yaji don yasan a baya kome jafar din ya
samu zai fada mai.
Yana fita part dinsa ya nufa Nusaiba ce ta fara mara masa baya ta bishi ganin ya
nufi part dinsu yasa ta biyoshi ba tare datayi magana ba .
Dakinsa ya nufa ta bishi a baya ta sameshi duke yana daukan wani takarda a drower
ya dan juyo jin anshigo dakin ya ganta tsaye a kansa.
Yanzu tafiya zakayi baka dawo gidan nan ba kome komu bamu da hakkin ka dawo
wajen mune inka gama kwanakin ka a can din.
Kwanakina ai bangama ba zan tafi tunda saura kwana daya in mata a gidan ta
kinga kuwa ko ita ban karasa mata kwanta ba ke nan ai ?
Cabdi wanan ai zaluncine wallahi mu meka maishemune wai yanzu ?
Abinda kika maida kanki shina mayar dake Nusaiba ke inkina da kunya har zakiyi
wanan maganan a gabana to inama kikaga kunyan balle babu sam baki da kunya don ban
taba zaton haka kike ba ai sai a cikin yan watanin nan nasanki tsab.
Kome zakace zakace ai tunda anke an baka kasha ka lashe baki yanzu mun zama
banza da bamu da amfani mu a wajenka.
Au ba wankewa tayi ta ban ba, kaina kafa nasha na lashe ,ai ban tsaya saita
wanke bama nina kafa kai na lashe komai da kaina.
Lalai akwai kazan uban nan kuwa don gabadaya an sauyaka yanzu har da abinda
baka yi ka fara yinsa gidan nan to mu zuba da ita wallahi.
Ki dai zuba yadda zaki iya kwasa aurene dai nayi baku da kudin wani na kara aure
ba yadda na auroki aka tara shedu haka itama na aurota gidana.
Yazo ya wuceta da takardan a hannunshi zuwa falo nan ya samu Asmau ya zauna
yana duban takardun nasa saiban ta fito ta sameshi tana fadin.
Wallahi duk abinda mutum keyi Allah na ganinsa ka dauko yarinyar nan don ka
bakanta muna rai kan abinda bamuyi ba akace munyi.
Zancen da abakin yan uwanka mukaji suna fadin ga ciwon dake jikinka shine laifin
ka dauka ka dora muna a kai yanzu ?
Na fada maki ai zaki girbi abinki koban fada ba yan uwana da suka fada din banji
a bakinsu ba sai naki.
Badai dadi haka yakai yamma dasu a gidan yabasu kudin cefane dana sauran bukata
yayi masu sallama ya tafi ya barsu nan.
Ranan da ta sauka gida tayi mamakin ganin gidan a share tsab komai an gyara ba
yadda ta saba tafiya ta dawo ta samu gidan kaca kaca ba wanan karon har da abinci
aka aje mata shimkafa da miya da salad .
Tabarma suka baza a tsakar gida tare da yaranta dake jiran ta bude jakkar
tsaraban data dawo dashi ta bude jakka ta mikawa yaro guda kudi tana fadin amso min
coca colan kwalba bata gora ba mai sanyi zakace a baka yaron ya karbi dari biyar
din ya fita sai gashi ya dawo da kwalban cock din dake nason sanyi a hannunshi.
Ya mika mata ta karba tasa baki ta balle murfin