Showing 96001 words to 99000 words out of 328222 words
Chapter 33 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
Ina ni ina ya J me tarin mata har biyu inje ata uku yar uwata tana ta farko a
wajen mijinta ai gara na yarda da Faruq dana buge ga auren ya jafar da wa yan nan
mata nasa kome yake kuwa ina .
Ai in an gani lahira maza suka kaini badani ba da wa yan nan dambun dankaron
matan nasa ai kazanta zai kasheshini don ko ruwan goran part dinsu ba zan iya kaiwa
a bakina ba yadda nake da tsandan tsiya din nan bakin kyan kyami ke gareni ta ya
zan jefa kaina ga halaka ina gani.
Me zan gane da auren ya J a rayuwata banda fiti ki duba yadda kullum ta Allah ta
waye sai sunyi fitina a tsakaninsu anshiga rabon su can dai gasu gada inji
bahaushe.
Wai anty har da tsayawa tana saurareb shirmesa shirme mana ta yaya don tabin
hankali zai tunkareni da zancen soyayya tunda aure ai soyayyan ke kawoshi toni ina
soyayyan da ke tsakanina dashi ?
Banki ba dai mutunci da tausayi saboda halinshi da kowa ke yabo na kirki ga
kyautatawa na tare dashi yasan darajan dan adam fiye da tsammanin mutum.
Baya da wanan ba wani feeling da nake dashi akansa banda zumunci sun rikeni
kanwa na rikesu yayyuna aje a hakan.
Na idar da sallah la,asar ina zaune a wajen nayi tagumi anty salma ta shigo
dakin nawa tunkan ta karaso take fadin ke kuma meye haka ?
Kin wani zauna kin buga uban wanan tagumin duk a kan zuwan wanan yayan naki kike
haka kome ?
Babu komai anty na fada cikin cool voice takai zaune tana girgiza kai gami da
fadin ban yarda ba Ramaah ?
Ta yaya zakice min babu komai bayan nasan abinda kikewa tagumi meye na tagumi a
cikin zancen nan.
Bayan duk wani mahuluki mamallakin hankali ya dubi zancen bawan Allah nan hanyan
daya dauko itace hanya mafita a kan ku baki daya.
Bafa ko wani namijine zai iya daukan wanan matakin da yake shirin dauka a yanzu
ba zargi da tozarci babu kyau Rahama sam bashi da dadi wallahi.
Let him prove himself to them yakai namiji namijin gwadawa gobe su kara irin
wanan katobaran basu bama duk wata macen arziki zata kama kanta da zargin mijinta
ai idan yayi hakan.
Bayan haka duk wanda ya zauna dake kike fada masa irn halaiyan bawan Allah nan
zaiso kasancewa dashi Rahama .
Tun kafin na ganshi irin labarinsa da kike min yasa na fahinci kin kamu da
kaunansa ba tare da kinsan hakan ba saidai kina gani kamar halinsa kawai burgeki
yakeyi hakan ba kauna bace kike masa.
Tun farko Rahama ke kika cusa kanki gareshi ba tare da kinsan maza basu san hakan
ba sai su dauka kaunace ta soyayya kake nuna masu idan kana masu hakan .
Wanda ke kuma a wajenki kin dauki hakan da ramuwar alherince zuwa gareshi don
kyautatawan da yake maki fiye da mijin yar uwarki.
Meye a ciki don kin aurensa banda alheri ke a kaddarama ba aure zakuyi ba aje a
hakan wallahi kin rama abinda sukai maki don dole zukatansu ya kusa bugawa idan
labarin kun sarku dashi ya riskesu.
Kinga ko a nan kin dauki fansan bakin cikin da kika cusa masu idan yaso daga baya
in za a shirya din a shirya idan ba shirin ma a zauna a hakan kin dai rama sun kuma
razana.
Balle d guy is handsome and wealth kinga akwai hutu a tare dashi so banga abin
tsayawa kina wani saka kanki a cikin kunci irin haka ba ?
Ta koma matsowa tana dafani tace ko da baki sonshi a yanzu let play a game to
his wife ki nuna kin amince din da bukatanshi yan iska muga iya gudunsu.
Ba sunce sun iya yiwa mijinsu zargi ba don suna kishin yar uwarki zasu hada dake
to zamuyi wasa da hankalinsu fiye da yadda suke zaton sunyi muna a yanzu.
Kici kudinshi kawai suna kallo saidai yaji daga baya kin tsayar da mijin aure
amma don ramawa sai mun rama wallahi .
Daga goben nan zaki fara fita wani vocational school dake nan cikin gari zaki
koyi gogewa da wayewa ki iya tako da kowa a garin nan.
Wanan hjy Yabi yar kawar mama itace ta bude wajen don tallafawa mata halin
rayuwan nan da ake ciki saboda mace macen aure dayai yawa a yanzu so na kirata tace
ba matsala in turoki kawai goben.
Kinga kafin hutunki ya kare kin dibi na diba a wajen ai so ki maida hankali don
Allah ki koyi abinda ya kaiki duk da nasan ke baki da shiririta irin haka.
Naji naji dadi sosai a raina don ko banza zan rage zaman kawai da nakeyi zan dan
shiga mutane in rage nauyim zuciyata .
Har anty Salma ta fice dakin juya zancenta nake a kasan zuciyana ta yaya zan iya
tsayawa da yaya jafar a matsayin soyayya mutanen da nakewa kallon yayyuna najini.
Nafita na dan cakula abinci badon baki naso ba saidan ciki ya dauki nauyi na dan
zauna da anty muka taba hira ranan hiran mama mukayi don suna germany sunje ganin
likita a can.
Tana ban labarin ga kafa na ciwo kuma mama taki daina cin nama da akace ta rage
munyi dariya da take fada min tace ko taci ko bataci ba ciwo dole tayi.
Ita kan namanta zataci gashi duk ranan da taci naman washegari kafan nata zai
tashi da fitinan ciwo da sai tayi data sanin hakan.
Lokacin sallah ya tayar damu muka shiga daki bayan na idar zama nayi ina lazumi
a wurin har aka kira isha,i na mike nayi sallah don haka ko a gida da bi,an mu yake
saboda kwadayin ladab dake cikin hakan.
Zancen zuci na zauna yi wayana ya dauki kara na mika hannu na dauko a zatona yar
uwata maria ce don a ranan bamu gaisa ba tun safe da ita.
Number ce ba suna hakan yasa nake kwankwanton ko waye ya kirani lokacin na dai
dauka ina fadin hlo muryan yaya J naji yana ajiyan zuciya yana fadin.
Da fatan zakiyi hakkuri don nasan na barki a cikin zullumi da tunanen bukatan
danazo dashi a kanki yau.
Tsananin sonkine Rahama ya hana min sukuni don na tsunci kaina a cikinsa don
haka na kasa sukini da natsuwa a tare dani ke kuma kika zabi guduwa ki barni a
cikin damuwa.
Rahama kiyi hakkuri ba zan iya boye abin da zuciyana ke ji akanki ba yanzu ko a
gaban waye idan hakan dana aikata kuskurene kike gani ki ki daure ki fahince ni don
hakan ba kuskure bane a wajen Allah.
Ina son ki sani duk wani dan adam da yake rayuwa a doron kasan nan to kuwa yana
tare da kalubalin rayuwarsa ni na dauka aure shine matsalana a rayuwata.
Katseshi nayi da fadi a cikin kyarmar murya dana samu ba hada haruffan a bakina
ina fadin don Allah yaya kayi hakkuri ba zan iya hakan ba kai yayana a matsayin
yaya nake kallonka wajena.
Amma sai naji yace nima haka ai Rahama har gobe har gata ke din kanwatace hakan
ba yana nufin zamu daina zumunci mu bane saima mu kara donkonsa a tsakanin mu Allah
kadai yasan mutanen da suyi alfahari da wanan hadin namu nan gaba.
Kit na kashe wayan don na fahinci idan na biye masa da sauraren kalaminsa zan
iya mashi rashin kunya girma ya fadi to kada akai wajen yasa na kashe layin ga baki
daya.
Na wurga wayan saman gado ina jan tsuki don na faginci tabas da ake fadan namiji
baida kunya hakan gaskiyane saidai subar ke mace da jin nauyin idon mutane .
Koda anty ke wani zancen wai na garasa inci abin hannunsa ni ba zan iya
yaudaransa ba free,falo zan fito mashi fili in,nuna bani kaunan manufarshi kawai ya
rabu dani
A ZARIA
Tunda ya habu ya dawo a cikin dare yana part dinshi bai fito ba har karfe goma na
safe ya samu ya daga don tun bayan sallah asuba ya koma ya kwanta barci.
Wanka yayi ya shirya ya fito falo matarshi na zaune tana ba Abbati abinci ya
fito ya samesu a nan din dinning ya nufa don yayi breakfast kafin ya fita.
Wai ina Rahama tun jiya banji motsin ta ba ya fada yana kallon matar nasa shiru
tayi bata bashi amsa don har lokacin a kufule take da zancen.
Bakiji bane nace ina Rahama ?
Bata nan ta bashi amsa a takaice.
Tana ina ?
Tana Abuja tun lastweek .
Abuja kuma meta tafi yi abuja ba a fada min ba bayan a karkashina take zaune
ehh don a karkashinka take ai shiyasa ake muna yadda akaga dama a gidan nan.
Kamar ya ban fahince ki bafa ?
tace zancen ke nan ai tana Abuja tunda an hada kai ayi matasheri da kazafi don a
tozarta mu tsawa ya daka mata ta fada mai meya faru ta tsaya tana wani zancen
banza.
Nan dai ta kwashe komai kamar yadda Nafisa ta bata labari bayan tafiyana don
bataji ainihin yadda zancen yake ba da farko.
Mikewa yayi ya bar abincin dake gababshi dagashi sai jallabiya a jikinshi da
gajeren wando part din iya ya nufa yana tambaya ina Saratu ?
Tana part din ya j salima ta fada yace good ya juya zuwa can din inda ya sameta
rashe rashe saman doguwar kujera kwance.
Basu ankara da shigowansa ba sai ganinsa sukayi gabansu fuska daure yace ke uban
me kike a part din nan ?
Saida ta dan jefo mai kallon rashin kunya take fadan ba komai tare da sauke
kafafuwanta kasa ta tashi zaune hakan ya bashi daman wanka mata mari biyu masu kyau
a fuskanta.
La,illah kaiko Habu me tayi maka harda mari haba dai kai kuwa an hanata shigowa
nan part din ne dama ?
Shoute,up ya fada saida ta dan kadu tana ja da baya ya kallo Saare din yace get
lost kafin na tatakaki a nan sakarai mara hankali kawai da haka zaki samu mijin
aure.
Bayan kina haddasana a tsakanin iyalinmu ko yaushe duk wani makirci da za a hada
gidan nan kina cikinsa why kika bata kanki haka ?
Ki rasa wanda zakiwa sheri sai J dan uwanki riban me zaki samu idan kin batawa
dan uwanki suna ?
Ni yaya yaushe na hada fada a gidan nan wani mari ya kai mata saida hancinta ya
soma zubo da jini ganin hakan baisa ya kyaleta ba .
Wai kasheta zakayi habu don ta fadi gaskiya ai ba itace ta fada ba nice nan don
kowan mu ya gani da idanusa idan ba wani abu take nema gareshi ba zata tsaya tana
magana dashi a gaban mu ?
Au ke uwarsace ke nan bansan abun naki har yakai haka ba ai Nusaiba ashe doka
kika bashi sai wanda kikaso yayi magana dashi a gidan nan zaiyi.
Shiru tayi tana mazurai ya juya kan kanwar tasa yana fadin ki shiga hankalinki
ni ba J bane na sake ganin ki a nan ba tare da yan uwank ba zaki gane baki da
wayau.
Wai kai ka zata wai zaman tsegumi muke yi a nan dama ai ,,,,
Marin daya sauka mata a tsakiyan fuska da yasa ta ga wasu wuta sun gilma a
gabanta yasa ta dafe fuskan ta soma hawaye tana fadin habu nika mara ?
An mareki ko zaki ramane ya fada yana kara nufo inda take da niyar kara kai mata
wani dukan su mama suka shigo falin.
Tun daga kofa mama take fadin habu kai habu fa bada kai nake magana ba ko kayi
haukane wai kul ka sake tabata ranka zai baci .
Wai, Lafiya meye haka meya faru hakane ina daki iya kece min gaka can kana neman
Saare zuciyata ya ban babu lafiya ?
Wai meya kawo hakane don Allah takai kallo ga yarta dake kuka wiwi ta tare
hancinta da hijab din jikinta.
Bata san lokacin data nufeta ba hankali tashe tace munaga rasulu haba Habu
dukane haka ko abu ka kwada mata ?
Wallahi dukane mama a kan matarshi ta fada mai karya da gaskiya yayi muna hakan
wallahi ba zan yarda ba karansa zanyi dan isk,,,
Keko yar nan baki da albarka a gaban mu zaki bude baki ki zagesa ke wace irin
mara tarbiyace wai ?
Barta iya barta ta karasa yau sai an kwasheta a wajen nan duk kika bude baki
kika zageni, zan gwada mata lalai dan iskan nake da gaske kuwa.
Ai bata cika ba tunda ba ita tafito tayi muna haka ba idan ta isa ta fito mana
ai gamu tazo an fada duk abinda ta fada maka an fada din .
Ya kara zabura yayi wajenta mama dake tsaye tace habu kana kara dukan Nusaiba zan
saba maka rai sosai wallahi.
Ji abinda kaiwa yar uwanka ka kyauta ke nan habu ita din mace ce fa, habu, duka
haka kamar ka samu jaka ?
Ke Dubu ki rufe min baki a wajen nan kafin ranki yafi na yarki baci idan har ba
zaki tayashi tsawatawa yar uwasa ba to ki fice daga nan.
Haba Dubu ke wata irin uwace wai abinda yaran nan suka aikata alherine haka da
sukayi dan uwanta fa aka hada baki da ita a bata mashi suna kan zina ?
Na tambayeki nace kazafi da cin amana alherine fadansa koda hakan ya kasance
gaskiya ?
To balle kowan mu nan ya san babu kamshin gaskiya a cikin zancen su dole ran habu
ya baci ya dauki wanan matakin ai.
A hankali mama ta sake hannun saratu data kama tace ai yanzu kin gani idan kince
ba zaki natsu ba sai ya illanta ki a banza ta juya ta fice daga falon.
Kallonsu iya tatyi tace ku saurari sakamakon ku idan kuna jin dadin kunci gari
balufacen mutum baya mata zance har mutuwa.
Gaba kuma kun kulla dashi ke nan daga nan har yumal,imadi indai bafulatanin
asaline zakuce na fada wata rana don sai sun rama shanmatan da kukai masu irin
wanan.
Ai saidai su rame na fada din suyi duk abinda zasu iya shi a dole gashi mai
mata yazo daukan mata fansa zai gane ya mareni wallahi.
Ki dai iya bakinki Habune dai kinsa zai iya fiya da hakan kidai san halinsa
yanzune zai iya dawowa ya jibgeki Asmau data taso take fadan hakan ga Nusaiba.
Malama rufe min bakinki ai tare dake muka hada plan din amma da kikaji yana
jibgan mu lafewa kikayi daki ai gobema kusane zan rama .
Ranan dai mama bata ji dadin iya ba don sai da tayiwa mama din tasa akan irin
yadda take saka ido gida na kokarin lalacewa gasu kuma suna ganin hakan.
Kowa ya shige daki daga mama har saare suka bar iya a falo tana fada saida
Nafisa ta fito ita da salima suka samu ta dakatar da fadan nata.
Ranan dana fara zuwa wajen training nasha dariyan zuci saboda wai wanke wanke
ake tambaya yaya ake wanke kwanoni kafin a saka abincin da za aci ko anyi amfani
dashi.
Wanan yasa na dauki lecture a shirme ashe abin ba haka yake ba akwai yayan hutu
da basu san yadda zasuyi abubuwa da dama daya kamata ace mace ta sani tun tasowanta
ba.
Irin wa yan nan yayan hutun da gata su sam basu san me auren yake nufi ba, sun
dai dauka cewa kawai za,ayi aure aita soyewane da miji shine ma,anan auren.
Cikin dan kwana biyu danake fitan sai gashi nima da nake ganin ai nasan wasu
abin ashe bansan komai dagane da rayuwan mace a gidan miji ba.
Shi aure ba yana nufi ki ba miji abinci bane ko kiyi ta aiki kamar jaka dole
akwai matakan da mace zata bi don rayuwan aurenta yayi lasting a zamanance.
Sosai na mayar da hankalina ina koyon abubuwa da bansan dasu ba ilimi ance
gishirin rayuwa tabbas haka abin yake kuwa.
Don ba karamin kuskure rayuwa matan gidan mu ke aikatawa ba har yar uwana kuwa
dama ance zama da madauki kanwa shike kawo farin kai.
Kar kice yaya ya hakkura ya daina kirana har wa yan nan kwanaki sakonsa kadai
sun cika min wayata irin kin tashi lafiya kinyi sallah kinci abinci ?
Kome kikeyi yanzu har yanzu baki barci ba wasu irin kaya yau kike sha,awan nasa
Rahama ire iren wa yan nan maganan da sannu sabo hakan ya fara shigana ba tare dana
sani ba.
Inda har yakai kwana biyu banji wanan irin tambayan nasa ba da nake dauka daya
mai dani karamar yarinya ashe ko hakan ne don da nuna damuwa da kulawa ake sace
zuciya.
Sai gashi rashin jinsa a yan kwanakin ya fara sakani dan danuwa kadan kadan zan
tuna dashi a inda zuciyana ta fara raya min Allah yasa dai ba matsalan jikinsa bane
kuma dai ?.
To yanzu wa zan tambaya inji duk wanda na tambaya koda yar uwatace zata soma
zargina a kanshi haka na dake dole da dan damuwa yayin da wani sashe na zuciyana
yake ban shawara da in tambayi anty Nafisa ita kadaice ba zata taba fadawa wani
komai game dani ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,
3️⃣4️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA