Showing 252001 words to 255000 words out of 328222 words

Chapter 85 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

ba ai yadda sukeyi damu a gidan .
Ku kikace Yanda ni baku nane ai don ban iya daukan hakan nagaji wallahi amma
baki mashi adalci ba Rahama udan kinyiwa yaya haka ?
Naji ke kije kiyi mashi adalcin bashike nan ba ta tare da fadin akankifa ya saki
Nusaiba jin hakan data fada yasa na dago na tsareta da idanu ina fadin.
Aikanafa kikace Maria kaina ya rabu da matarshi tace akankine mana nace akanshi
dai idan baki san abinda yasa yakai ga sakinta ba nina sani kuma ban fadawa kowa ba
duk da fadin da akeyi kainane ya saketa din dama yana da niyar hakan.
Ki dai tashi muje kawai kinga har habu yayi fushi dake yau na sake jefa mata
kallo a cikin mamaki tare da mikewa zaune nace habu ubanane ko yayana maria ?
Shigowan ummah dakin ya hanani cigaba da maganan tashigo tana fadin habu ba
ubanki bane amma kamar uba yake gareki ai don shine gatanku acan din.
Kememe na kafe duk abinda suka fada ban yarda na bisu ba mama tashigo muyi
sallama da ita a cikin dabara nan take fada min kin mun daidai Rahama dabaki yarda
kin koma ba a yanzu sai dubu ta kawo kanta gidan nan da kafanta.
Lokacin zata gane kina da ma,ana a wajensu idan ba haka ba bata da niyar barin
wanan halin banzan da dan uwata ke dorata a kai na fahinci gaskiyan tsohuwar nan
dauda ke zuga dubu ga duk abinda tayi mara kyau don ya zama dattijon banza.
Wanan maganan na mama yasa na kara kafewa kyam ban yarda na bisu ba ina jin
suna sallama da su ummah suka tafe .
Ummah harda fushi dani don bayan tafiyansu yinin ranan daure min fuska tayi ko
nayi mata magana a dake take amsa min yasa nima nayi shiru na kyaleta.
Saida safe taga ina shiri take tambaya nace gidan mu zanje can garin mu nan kuma
ta hauni da fada wai na rainata in tafi gidan indai kawune ai nasan abinda zanje in
sama a gidansa .
Ina kuka nake fadin koma meye ummah yafi min tunda gidan mune ko yayi min kansa
yayiwa da in zauna mama tanaci min fuska don kawai danta ya aureni shike nan ta
dauku kiyayyan duniya tasa min.
Ni abinda saratu ke min bai damuna kamar na mama dake fadin zamu mallake mata
diya su koma sai abinda mukace kamar yadda kika maida daddy nan haka mun asirce su
daddy Abuja sai abinda mukace sukeyi akanmu shine itama za a kawo mata ga iyalinta.
Nan ummah din ke fadin matan nan fa na dade da fahintar ta tun zaman mu asibiti
da mukayi da yar uwarki ?
Agabana in kun kawo abinci zata kama fada tana fadin ana barnan abinci ana saki
abin miya haka da yawa don ba asan wahalan nema ba.
Bayan wanan kashin kudin da aka dauko masu a yanzu kuma a koma ana barnan abinci
haka ita ba zata yarda da hakan ba a diga kirga nama kafin a saka a miyan.
Wanan ma kadan ke nan ai na fada na dinga bata labari ta hau tana fadin ita
wallahi ba zata yarda da wanan cin fuskan ba ai muma yayane kamar diyanta bawai
bata son mu bane ai koda sukaga tana nuna hakan kawaicine kawai nasu na fulani take
muna.
Wanan yasa ta dauki zafi akan zancena din take fadin ki zauna sai tazo gidan nan
da kafanta ta sameni na fada mata abindake raina nima kafin ki koma din.
Tun bayan barunsu gidan habu ya fisgi mota yana gudu Iya ta lekoshi daga bayan
mota inda take zaune tana fadin kai hanu kajamu a sannu don Allah ?
Kana zuciya kamar an maka wani abu yarinyar nan tana da gaskiyanta inma laifine
ita dai akaiwa shi ba karya ta fada ba ai.
Tunda yarinyar nan ta kafe haka abin ne ya isheta don Allah nasha fadawa uwarku
ta guji irin wanan ranan kada haka ya faru amma bataji ba.
To wai ni iya ban gane ba me akewa yarinyar nan haka wai naga gidanta daban mana
yazid yake tambayan hakan ?
Kadai fadi duk yadda akeyi Yazid J yayiwa yarinyar nan amma wai shine don jin
dadi zatawa mutane rainin wayau haka din taga yana yinta haka sosai a cikin
matanshi.
Allah sarki dama hakane ai idan namiji ya nuna kai yakeyi sai ace komai yi maka
akeyi ita fa baku fahinceta bane har yanzu nake gani habu ?
Yarinyar nan takafe akan ba zata dawo gidan nan bane kan irin cin fuskan da
uwarku take mata a gaban kowa Dubu take nunawa yarannan hattara da kyamansu tana
sakin maganganu akansu.
Kasani kowa kuma yasani idan matsafane ko mayu aida yanzu sun baiyana daba hakaba
da sauri iya ta dafata tace madallah Amina kin gane matsalan kenan ke ashe ?
Shi wanan bai san komai ba sai zuciya a gaban yaran nan take nuna bata kaunarsu
batayin lamarinsu su din ba kowa bane sun shigo rayuwanku zasu juya mata kanku .
Wani tsuki yayi yana fadin nasan wanan mama aiga maria nan wani irin cin fuskan
mamane bata gani ba a gidan nan kan matan J da bako kyautata mata sukeyi ba kamar
ita kuma tayi hakkuri ta zauna .
Ba zaka hada ba habu don idan anyiwa matarka kana tsayawa tsatin daka ka nuna
bacin ranka kan abin shiko jafar fa bai iya komai saidai ya juya ya wuce kawai har
can gidansu fa take binta itada dauda suyi mata kaca kaca su dawo zakace kadata
nuna itama mutunce don Allah ?
Inda laifi daga Jafaru har dubu da yan banzan yaran nan duk suna da laifi saidai
kawai ace ayi hakkuri kawai shine yanzu amma abinda yaran nan sukeyi banga
sarakuwar gidanmu dakeyin hakan ba gaskiya.
Yarane da suka san mutunci da kimar babba da darajan dan adam mutum indai daga
bangareku ya fito yaran nan zasu darajashi yaya ake son mace tagari ta kasance
wai ?
To mama ai na dauka don kawai wanan abin daya hadata da Saaratu ne take wanan
zuciyar ashe bashi kadai bane tarawa tayi ta amaye muna komai lokaci guda haka ?
Inda zata amaye din ne aida ta amaye muna idan watace ba tas zata fada a gaban
kowa ba cewa ga abinda ke nan amma ita kaga tayi hikima takafe akan bata komawa
kawai ?
Dole aiwa abin tufka gaskiya bansan yaushe mama ta juya ta koma hakaba bayan
tafiyana koda yake ance kawune matsalan komai a yanzu shike hura mata kunne yake
zugata.
Tundana dawo nake son a zauna naji zancen kudin mu dake wajenshi matsalan nan
na j yasa na kyale amma yanzu ai dole mu hadu tunda ina son kudina na fara dan
bussiness dasu .
Habu na fada maka kabar zancen kudin nan don babu su rayukane kawai zasu baci a
karshe don ko mama ta sani babu kudin nan a yanzu.
Babu fa kace bros haba dai wanan wasane kawai kubar zancen agama wanan don
Allah kada ku tayar da wani zance a yanzu muna fama da wanan ?
Shiru sukayi don habu ya fahinci iya saboda mamace dake cikin motan abin daya
shafi iya sune zancen kudin nan bai kamata ace wani na wajen dakinsu yaji zancen
nan ba.
Shiko yazid bai gano hakan ba sai fada yakeyi yana fadin kawu zaisan koshi waye
bai sanshi bane wallahi jin kowa a motan yayi shiru yasa shi fara fahintar akwai
matsala.
Sai mama din ke fadin kai yazid ai kaji iya tace ka bari agama zancen nan toka
bari mana hakan ya isa ba sai ka bata ranka a yanzu ba ai.
Koda suka isa zaria la,asar tayi don haka su basu shiga part din ba saukesu
Habu yayi yace zaikai matarshi gida ya dawo.
Shi kuma Yazid part dinsa ya nufa saisu Iya da mamane suka shiga ake masu sannu
da zuwa don nan suka samu kawu da mama dubu a zaune tare dashi.
Tayi masu sannu da zuwa tana fadin ina yarinyar ko an sauketa gidan can ne don
bata ganni ba iya tace wani gida yarinya kan na hannun iyayyenta sun rike abinsu
kamar kowa .
A,a duk da kunje basu baku itaba ke nan kuma yau ga mutanen banza marasa mutunci
har anbi bayan yar ku kuma ku hanata dawowa akan wani dalili wai kuma ?
Shi nake son ji kawu ya fada a cikin bacin rai iya ta juyo tana fadin akan
dalilinku na cin fuskan da kuke mata ta hakkura tabar maki gidan da danki a zauna
lafiya.
Sallah ya sallame daga inda ya zauna ya juyo yana fadin wai bata dawo bane iya
da gaske ko tana can gidan kun sauketane ?
Bata dawo ba Jafaru ta nuna bata dawowa gidan nan a yanzu ban sanarwa gaba ba
inda rabin dawowanta ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:44] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

7️⃣9️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Wani shewa ta sake wanda yasa hankalin mutanen gidan ya dawo gareta inda take zaune
tana waya bayan kiran da Saare tayi mata din.
Don tana ganin itace tasan da magana hakan yasa ta mike tabar wajen ta koma gefe
daya don taji meta samu ta kirata kuma yau ?
Nan ta fara sheda mata albishirinki Anty Saiba tace goro cikin zakuwa tace yar
iskan nan Rahama tabar gidan nan tun jiya .
Ke ki bari don Allah saiba ta fada tace wallahi yau su ya habu sunje kaduna wai
su dawo da ita tace dasu bata dawowa gidan nan wai ?
Haka suka juyo suka dawo su kaidai taki ta biyosu shine dslilin shewan nata da
har ta dawo da hankalin mutane gareta.
Saida sukaji tana fadin aina fada maki saaratu bashi taci wallahi indai nice
yadda tasa nabar gidanku itama saita barshi wai abin haushima yayanki ai yafi ban
mamaki saaratu.
Wai ace yaki zuwa yaki ya turo tunda nabar gidan nan kamar dama yana jiran haka
ya faru tsakanin mu to shegeb cikin jikintafa yana nan kota zubar ?
A kema kinsan yana nan ai tunda tana son ace ta haihu da yaya ba dole tabar
cikin ba saiban ta amsa da fasin shegiya ai bataga komai ba.
Gara dani ba goyo ba ciki nabar gidan itako yar banzan ko zaman ciki ai ya isheta
yar iska tana wasa dani saina mayar da yar iska ko abin sayen goro.
Waima meya farune tabar gidan take tambaya ?
Wani irin dariyan shakiyanci Saare din ta kwashe dashi tana fadin kin manta dani
ke nan ai dana saka yar iska gaba saida naga bayan shegiya .
Wallahi yarinyar nan baki san irin haushinta da nakeji bane ai hana shegiya
shakar iska nayi ko walwalan kwarai ban bari tayi ba.
Nusaiba tace dakyau nawa ina sonki irin wajen nan wallahi a aina fada maki ki
barni da ita ita a dole tazo cin arziki to taci din mugani yar iska kawai.
Saura wanan shashan matar habu din itama haka zan ta zuga mama akanta sai naga
bayan shegiya su tattara subar muna gidan yan iska muggan iri kawai.
Aini ba barin gidan wanan yarinyar ba Saratu naso har munafukin cikin nata ya
zube banson ma tabar wani alaka a tare dashi wallahi ai in ta haihu dashi taji dadi
kota abinda zata haifa ba a rabuba ke nan dai ?
Barta aiko haka an nunawa yar iska iyakarta don daga kan yarinyar nan yayi yawa
tana daukan kanta ita wata tsiyane kiga tanayi kamar tana jin warin mutane ita gata
maidigiri.
Sun jima suna zagin kansu waini a wajen kafin suyi sallama su kashe wayan uwar
ta kallo Saiba tana fadin wa aka saka tace wai amaryan Jafar ce tabar gidan
subbahanallahi uwar tace.
Nusaiba wanan zaman gidan baisa kinyi sanyi kin koyi darasi ba ashe ? Na dauka
wanan halin da kike a gida zaisa kiyi nadaman abubuwan da kika aikata a baya ai ?
Yanzu akan abokiyar zamanki kikewa wanan mugun fatan haka har kina fatan Allah
ya barar da cikin jikinta don Allah keda kika haifa wani yayi maki bakin ciki da
hakan ?
Sai yaushe zaki hankaline ke Nusaiba irama wace ke turu maki tsegumin tafiki
rashin sanin ciwon kanta ai da zata zauna duk tsegumi da sirin gudansu tana aikawa
waje.
To ki guji naki a wajen ta ranan da zata kwaye maki baya tayi maki tonon sililin
abinda kuke shukawa a tsakanin don tayiwa dan uwanta ciki daya balleke ?
Dama sam rayuwan yarinyar ni baimun ba wallahi don na fahinci itace ta shiga
tsakanin ki da Asmau tun farko ta hanaku zaman lafiya duk amintakan dake tsakanin
ku.
Duniyace ai ita ke koyawa wawa wayau koda baida fahinta wata rana duniya zata
fahintar dashi keda ya kamata ki natsu a yanzu ki komawa Allah inda rabon komawamki
gidan ki komawa uban yarki kin zauna kina wanan hauka haka ?
Katse uwar Nusaiba tayi da fadin mama ke saiki dinga ganin laifinaita da tayi
min fa ta hanani zama dakina ta rabani da mijina ?
Oho ba zakiji ba kenan ko ta ina ta hanaki halinki dai ya hanaki zama a gidanki
Nusaiba waye baisan halinki ba yanzu ?
Duk hakkurin yaron nan da kawar da idonsa jan abinda kuke mai saida kika kaishi
bango ya koma komu yanzu bai ganin darajan mu a idanunsa kuma ?
Ai duk wanan sherin yaeinyar nan ce da baku son a fadi kaifinta har yaushe za a
tsaya goyon bayan wace aka san itace matsalata amma baku son a fadi laifinta sai
saratu dake kaunata ni gabadaya naso subar gidan ba ita kadai ba don ko Asmau
munafukace ta gaske dole sai ta fita tabarni dashi.
Tsuki uwar taja ta juyo tana fadin na yarda abin nan ya tabaki Nusaiba ki matsa
harki samu tabin hankali Asmau dince zaki fitar a gidam jafar ?
Shiko Yazid tun bayan dawowanshi yana part dinshi tare da iyalinshi dan baison
yayi nusa dasu sosai hakan yasa tunda ya shiga bai sake fitowa ba.
Sai washegari daya fito yaje gaida j din suka dan zauna dashi ganin yadda J din
yake kwance yasashi fahintar yana jin jikin nasa ranan.
Muryan J ce ta katseshi da yake fadin yarinyar nan taki dawowa ashe nayi mamakin
hakan ban kuma san abinda taje ta fadawa iyayyen nata ba har suka riketa.
Me zata fada J abinda kuke mata kai da mama da yan uwanka da matanka shine zata
fada mana ai basuce ta fada masu komai ba .
Illa dai tace ba zata dawo bane ita tagaji da abinda ake mata kai baka daukan
mataki koda kana zaune kaga bata da laifi anan .
Don kaika daukota J yakamata ace ka nema mata daraja a idon kowa gidan nan duk
da suna ganin sun girmewa shekarunta amma dai shi zama tare baice hakan ba ai.
Bsice don mutum yana kasa dakai yana auren danka ka dinga muzantashi kana nuna
shiba komai baine haka kuma kowan ku yana kallon yaran nan da matanka sinaciwa yar
mutane mutunci nasan da gidan nan ne ba zamu taba yarda aiwa kannin mu hakan ba a
gidajen auren su.
Shi habu wai yayi fushi don yarinya ta dage akan bata dawowa har saida yakai
sunyi musayan baki dashi don gaskiya inda shine bai yarda aiwa matarshi hakan ai.
Shiru jafar din yayi yana saurarenshi kamar yana tunane kafin ya jefowa dan uwan
tambaya yana fadin atakaice dai yanzu nida mamane masu laifi a wajensu.
Kwarai kuwa bros lafinka anan shine baka tsawatawa lamarin koda kana kusa akayi
mata baka daukan matakin daya dace koda gobe ba za a maimaita irin hakan ba sai
yayi murmushi ga dan uwan nasa dake magana.
Yazid din yace kwarai kuwa bafa wai kai ka nuna mata concern a bangarenka alhalin
tana samun musgunawa a wajen mutanen gida shine kawai abinda zakayi ba .
Yama dole kabata kulawa a ko wani bangare kamar yadda kakeba kowa tunda kaika
daukota cikin gidanka.
Haka kuma ita mama kamar da saninta ake komai ga yarinyar nab banda wanan itama
kanta tana yawan aibantasu a gaban kowa don ko gaida mama sukayi ance bata amsa
masu wani lokaci kaga ba wanda haka zai faru dashi yaji dadi har ya zauna itace
uwar mijinsu fa ni nasan halin mama idan ta tsargi mutum bros ka sani kaima ?
Baiyi magana ba saici gaba da kurawa dan uwan nasa ido yayi kawai a inda yake
zaune yayi shiru ya kafawa kasa ido yana tunane.
Mikewa Yazid din yayi yana fadin yakama a gyara zancen nan abinda na guda kenan
da matana kaga ban yarda ta shiga kwamacalan gidan nan ba don ina da labarin komai
a wajen iya.
Yanzu ya rage naka idan kana son matarka saika gyara ka shirya da abinka idan
kuma ba yadda zakayi don Allah bros kabar yarinyar nan ta tafi taje gaba ta samu
wani mijin .
Sai a lokacin ya dago kai da sauri ya dubi kanin nasa dake magana Yazid din yace
hakane mana ka sallameta ka zauna da wa yan nan mayayen naka lafiya tunda itace
matsalanku.
Ko dai makaho yasan irin hakkuri da sanin ya kamatan yarinyar nan kai kanka kasan
ka tauye mata rayuwa a gidan nan don ba kalan macen da za


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login