Showing 225001 words to 228000 words out of 328222 words

Chapter 76 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

niko sai naga da an dakata da wanan fitan da za
ayi da yaya a yanzu don yana samun sauki sosai kawai dai kamar baison a gane hakan
ne a yanzu.
Nayi tunanen hakan Rahama ina kula da kusan hakan a tsakaninku saboda a yanzu
kin rage yawan tashin hankalin da kika shiga a baya game da rashin lafiyan nan a
yanzu duk babu shi sosai wanan yasa na mayar da hankalina a kanku dole nasan akwai
dai ?
Dan murmushi na sake a gefen fuska ina kawar da kaina gefe take fadin ai bari
almuri zan samu lokaci nayi magana dashi shima sai kuma ta koma tambayan .
Yanzu wani cigaba kike gani ga lamarin nasa wanda ke nuna akwai sauki sosai ga
laluran nasa don hakan ke nuna alaman lafiya idan ya fara wani abu ?
A zuciyana na amsa da abu ko mama tunda ya iya raye dare daga kwance yake iya
biyan bukatanshi nada namiji a hakan amma a fili cewa nayi da ita.
Yanzu mama yana iya daga hannunsa wani lokaci har yana kokarin yunkurawa ya tashi
zaune ko yayi kokarin kiran sunana idan yana son wani abu.
Masha Allah koda ya boye hakan ba laifi bane don zamanin nan da muke ciki wanda
baka zata ba bakayi tsamani ba shine zai ha,ince ka banga laifinsa ba idan har ya
boye hakan gare mu yanzu.
Yanzu matsalan shine ni kinga kamar sun ma fara gajiya da nine nan a yanzu yadda
dubu da sarakuwarta ke nunawa zamana daku a yanzu yakai masu ko ina don na tare
gaba na tare ba a garesu.
Matsalan dai tasan tun Alh yana raye irin dokan daya kafa muna a gidan nan da
kuma irin hadin kan daya sanya na dole tsakanin mu.
Aida dubu nada hankali da bata karbe zancen da duk wani laluran jafar da iyalinsa
a hannuna ba din ko shi dan dakinane kamar yadda kikaga Nafisa yar dakinta a yanzu
tun Alh yana raye irin dokan daya kafa muna ke nan .
Idan ke mace zaki yaye danki zai kira wace zaki ba yayyen dan haka kuma rikonsa
zai koma hannunki ke nan har girmansa.
Sai bayan rasuwan Alh ne kan mu ya dan rabu tun wajen robon gado da kowa ya nuna
nasa halin akan abinda Alh ya barmu dashi.
Yanzu da kokarun mijinki yayi dabaran dawo da hadin kai a tsakanin mu donshi haka
halinsa yake kamar na mahaifinsa .
Shigowan matan su yaya Auwal ya katse muna hiran mu don haka mukan zauna wani
lokacin muna hira tsakanin mu saboda shakuwa da ita da yanzu nayi sosai takan ban
labari irin na kunne ya girmi kaka a yadda na kula zamane akayi a baya irin zaman
mumuke a tsakaninsu.
Irin a fili ana son juna ana nuna babu matsala amma ana kishin mumuke irin zaman
kakanin mu da iyayyen mu da ba a gane kan gida din nan .
Anan falon aka zube da matan su yaya din ana hira lokacin Iya da matar Yazid
suka shigo falon sam bata da marmari don bata sakin jiki da kowa sai iya da mama
kadai take dan zama dasu bayan hakan ko yaushe tana part dinsu bata shiga mutane.
Zakice tana gudu mutane fuskanta kuma sam ba fara,a acikinsa matan gidan suyi
gulma sun gaji sun saka ido don sun fahinci itama ba kanwar lasa bace ashe.
Bayan sun gaisane da iya suke tambayanta ko itace matar Yazid din iya ta amsa
da fadin itace to bai zauna ba balle ya kaita wajen yan uwa a cewan iyan.
A nan muka wuni dasu abinda yasasu tafiya yunwa don an jima ba a gama abinciba
kamar kullum haka kuma da za a kawo aka zubo dan kadan waina mu dukan mu part din
ke nan.
Ina jin lokacin da mama takece masu suje gida su nemi abinda zasuci don wanan ma
komu ba zai isa ba balle su din kullum haka ake abincin kamar na rowa a kawoshi bai
isn mutane saukin abin ma yanzu wani lokaci ita nan takan yo muna dabara daga can
gidan ta idan ta tafi shi muke samu muci.
Da zasu tafi na yafa mayafi na rakasu har bakin get amma saida suka shiga suka
sallami mama dake can part din ance wai tayi bakine bandai san ko suwaye ba.
Sun tafi na koma don in gyara part din na samu Asmau da yara sun shigo muka
gaisa na gaida ita da aiki take fadin tun safe tana tsaye bata huta ba yasa wai
bata leko ba.
Dakin na fito na barta da mijin don in suna ciki nakan dawo falo ko dayan dakin
in dan kwanta wani lokacin kuma inyi barcin gajiya .
Hakan ne ya faru don ban tashi ba sai wajajen karfe biyar saura na tashi nayi
sallah na fito na fara gyaran falon har lokacin suna ciki da mijinsu da yaransu na
dai shiga mun gaisa dasu din na fito naci gaba da aikina.
Nayi mamakin rashin shigowan mama a wunin ranan don tun safe data shigo bata
samu dawowa ba wai tana can tare da baki ake fadi ashe ba wasu baki bane ita da
yarantane a lokacin.
Saida dare iya bata shigo ba naji mama na fadi cikin kashe murya yau akwai
abinda dubu da yaran nan suka samu don tun safe suke hayanita tsakaninsu.
Jin hakan yasa na dago na dubeta take fadin kinsan mu ba a son mu sani don kamar
makiya ake daukan mu duk da iya ta dan kyankyasa min .
Wai yaran nan matan Jafar to har dake dai ke nan ake nufi ko sunce Habu da yazid
din sun dulmuye dukiyan dan uwan nasu suna ci su barku a haka a kula daku dashi.
Ko ita mahaifiyar taku ta kama masune shine habu kin sanshi ya dawo da komai na
jafar da yake juyawa yanzu yace ya daina kula da dukiyan a baya ba an taba wanan
maganan ba yanzu kuma sun tayar da zancen ke ban kuna nake tambayan ta ?
Ke dai bari abune da baka isa yau danice ai wace ta ta fito da zancen nan data
san bata da wayau a gidan nan ?
Ina batun yarona dake kwance ina naga wani batun dukiya can har in bari karamar
yarinya ta dagula min lissafina haka ?
Shiru nayi ina tunane wai wanan matsalan haka daga ina yake fitowane wai na kula
fa ba damuwa sukayi da bawan Allah nan ba sunfi damuwa da dukiya kawai akansa.
Muryan maman tudun ne dake fadin kinsan ita iya ba ruwanta fadin abinta takeyi
kai tsaye tace duk munafuncin daga Nusaibace da saratu ya fito.
Kamar a mafalki mukaji murya kamar nasa da karfi saidai yanayin kiran daya
kwala min din ya sauya da harshensa da muka sani sai gashi a ranan ya ambaci
sunana .
Dagani har mama da sauri muka karasa zuwa dakin yake fadi cikin badaniya kamar me
koyon magana da Allah ya bashi ikon furtawa yace ko akwai kunama a gadon nan ne ?
Da farko bamu gane me take fada ba saboda yanayin dan saurin maganansa haka
kuma yanzu da harshen nasa yake kamar a karye.
Sai can nace ko kunama kake fada ya daga kai da karfi yace a wani irin yanayi
eehh wani abu nake jin kamar yana cizona na yunkura in dagashi na kasa hakan yasa
mama fita daga dakin da sauri .
Ashe taje nemo koda yan uwansa suna gidan sai yazid ta sama ya habu ya fita tun
yamma ya tafi gidansa sai gasu tare da yazid din dasu mama da kowa don mama tudu
tace dasu Jafar yayi magana yau.
Saidai ba a cikin dadin rai ba sabo harshensa da yake kamar a karye wanan yasa
duk gaba dayansu fitowa lokacin .
Koda suka zo Allah ya taimaka na samu na cirashi daga gadon zuwa kasa suka shigo
sai wani irin nishi da yakeyi mai karfi a cikin kugi na wahala.
Mun duba gadon ko ina har jikinsa da komai karkashin gadon duk an duba babu
komai gashi kuma a cikin wani wahala duk ana tsaye a kansa ana binsa da kallon
tausayi.
Hankalin duk wani na tare dashi tsakani da Allah ya tashi a lokacin Asmauce ta
fara kuka ta juya zuwa falo don yazid dake mata tsawan yaya haka kuma kada ta tara
masu jama,a ?
Hakan yasa ta koma falo ganin yadda wahalan yai yawa ga wani irin zufa da yakeyi
yasa na shiga neman magani a cikin wardrobe din da sauri na juya na fita zuwa
kitchen na dora dan ruwan dumi na sauke na fito.
Nan falo wajen Asmau na zauna muka fifitashi tare da ita na koma dakin lokacin
yana wani irin wulle wulle nace wa yazid din ka kamashi a bashi magani ?
Shiya kama min shi ya dago ina kokarin bashi naji muryan saiba na fadin wanan
wani irin maganine kuma a daina bashi abu barkatai don Allah haka ?.
Ki bashi kinji naji muryan yazid yana fada hakan yasa na bashi din naku fara
shafa mai a duk jikinshi yana nishi muna mashi sannu har na shafe mai ko ina ban
damu da wai su mama na wajen ba.
Ga jikinshi har wani rawa yakeyi a lokacin hankalin kowa ya gama tashi da kuma
tsoracewa lokacin ya habu suka shigo da maria.
In fada maki mai karatu maria bata kyauta min ba nake gani a wanan gabar yadda
takan share lamarina a wanan lokacin sai shiru shirun ta ya zamo min illa a
zuciyana.
Son nasan ko batazo don dan uwan mijinta ba ai zatazo don ni akai akai amma saita
dauki sati biyu har ukku ba tare data leko mu ba taga yanayin da muke ciki dashi.
Har na fara saka hakan a raina daga baya don sanin halinta yasa na share zancen
nacigaba da al,amurana.
Wanan yasa koda suka shigo ma a lokacin ban kulata ba ina gurfane a gaban yaya
din mama da iya sai faman fadi sukeyi Allah ya baka lafiya ya tayar da kafadanka
cikin iyalinka jafar.
Ko asibiti zamune yaya habu ya fada a firgice ko anje asibitin me zasuyi da
wanan lamarin saidai idan za a din daga gefe kuma yazid ne ke faman karanto mashi
addu kala kala daga bakinsa.
Sai zufan ya kara tsananta can yayi wani irin ajiyan zuciya ya lumshe idanunsa
idabuwan mu yana kansa har lokacin acikin tashin hankali dayawa duk sun koma falo
anyi zugun an tsurawa sarautn Allah idanu.
Don ba wani mai iyawa ko gwaninta sai Allah gabadaya kowa ya tsunke yayi kamar
yana barci har yazid din yana fadin ya samu barcine fa.
Can baya na koma na zauna nayi tagumi daga inda nake ina iya hangonshi daga inda
nake zaune din suna shawaran fita zuwa asibiti dashi .
Sai lokacin suka tabbatar da ya soma magana da gaskiya don yadda ya bude ido
yana ambatar sunana da karfi hakan yasa har wa yanda ke falon shigowa da sauri.
Jiki a sabule na karasa din wajenshi yana fada min amai yake son yayi in daga
shi mun kasa fahintar me yake fada a lokacin sai can nagane ina fadin amai kafin ma
na rufe baki ya soma zubo amai ba kaikautawa wani irin bakin amai yake zubowa a
bakinsa din.
Ya Allah yasa dafin wahalan kake amayarwa jafar Allah yasa karshen wahalankace
hakan maman tudu ke fadin hakan a gareshi sai yayi kamar ya lafa kuma ya can ya
fara kakarin amai din.
Oho har muna fadi kafara jin sauki sai kuma ga wanan lalura kuma yanzu nan fa
muke zaune da yar nan muna hiran akanshi.
Don yanzu akwai alaman sauki sosai a yanayinshi sai gashi munji daga ciki yana
kakari ashe kuma zancen ya baci .
Allah dai yasa saukin ke nan yazo da hakan mama tudu ta karasa zancen nata dashi
tana kara mayar da hankalinta kanshi.
Muryan yazid dake fadin amarya ki daga daga wajen wata daga cikinsu ta kwashe
aman nan hakana ya fada yana kallon inda Asmau da Saiba suke zaune.
Dan jim sukayi sai Asmau data yunkura tana daga danta daga jikinta yace No ke
ki zauna ki rike danki wanan ta kwashe ita.
Ai zancen ke nan wanan abin kowa ya shafa ba ita kadai ba amma sun mayar da
zancen ya koma wani abu na daban a wajensu yanzu iya ke fadin hakan.
Yace wace bata iyawa ta koma gidansu mana iya mu lafiyan shi mukajawa ba wani
kishi ba can koda sun bar mata din ai wanan zata iya ma tunda gashi tanayi ba tare
data kula da abinda suke nufi ba ai.
Na lura da hakan sosai tunda na dawo garin nan iya dama ina son gaskanta
hakanne da idona gashi ko nagani a yau.
Tun safe daya fara aman nan yarinyan nan itace tsaye a kansa suna binta da kallo
me hakan ke nufi ke nan maganganun da kukeyi a kanshi damu yan uwansa ya zama
gaskiya ke nan jira kuke ya mutu ku wawashe dukiyan nasa yasa har kuke ragen dan
uwansa daya kama komai ya rike a hannunsa yana ci da iyalinsa.
Dagowa tayi tana fadin mu muka fadi hakan mu akace ma mun fadi hakan a ga habu
din wazai fada in baku ba inda kuka fada sako yazo kunnen mu ai ?
Kallon Saare tayi da sauri yace kwarai friend din munafuncin ki kenan ai ita ta
fada inda za aji cewa mun kama komai mun rike dani da habu koda mun rike din
laifine hakan ?
Wanan magana ina kuma ya fito magana haka babu dadin ji mu da ke neman rayuwan
dan mu ina zancen wani dukiyansa kuma ya fito a yanzu haka ?
Ga sakaran nan mara mutuncin yarinya mana mama bada ita suke zama suyi gulman
muba tunda ta zama banza a cikin mu banga laifin maza dake gano halinta su gujeta
ba don munafuncin saratu yayi yawa mama.
Idan anyi magana mama tace an mata kazafi da sheri ba abinda take nufi ke nan ba
yanzu tunda ana zaman jiran gado ai sai kowa ya san zafin gadon da zaici din ke nan
tunda ba wanan ce kadai zataci gadon nasa ba.
Juyawa mama tayi gun saratu din tana fadin amma saratu abin yai maki yawa wai
meyasa kike nuna baki damu da dan uwanki bane ke ?
Kin taba ganin wanda yaki nasa yaso bare dan uwa marfin jallone fa yau jafar da
sauran yannan ki sune zaman mahaifin ku a gareki sabodawa kika san yarinyar nan ma
a gidan nan ?
Wanan da kuka tasa a gaba da tsina tafiku sanin ciwon kanta don da biyu take
kula dashi haka na farko daukan da tayi masa na dan uwa wanda ya kamata ace kune
kuke hakan sai na biyu alakar aurataiya daya shiga tsakaninsu kinga riba biyu zuwa
ulku ta samu a gareshi .
Kun dauka gulmace gulmacen ku da kyashin da kuke nuna mata zai sa ta gaza dashi
hakan bai kara komai ba illa karfi da kuzarin da kuka kara mata ga hakan yanzu.
Kada ku dauka bai san meke gudana bane a hakan wallahi yana fahintar komai dake
faruwa wajen nan ni ba yau ba yaran nan sun jima da zube min a idanuna .
Karku dauka gari ba a san me kukeyi bane ansan komai an kuma sakaku a baki tundau
ke saratu kaf yan uwa sun tsanaki a yanzu.
Ido rufe maman tudu take fada masu magana iya son ranta yazid na kamawa inda
yakewa mama bayanin cewa wai har saratu take fadawa salima cewa sunyi shawara cewa
zasu kai karan habu kan ya danne komai na jafar ya hana masu gaba ya hanasu baya
basu san komai da ake ciki da zancen dukiyan jafar ba ki duba fa mama da saratu za
ayi wanan maganan haka idan ba sun saba hakan ba da ita dama ?
Shine salima ta samu habu da zancen take fada mashi abinda ke nan wallahi sunki
shawaranane da tun jiya ba wace zata zauna a gidan nan gaba dayab su.
A,a yazid ka cireni cikin zancen nan ai gasu nan idan suna abin su ban kulasu
ina can ina aikina komai aka kitsa nikan bada sanina bane wallahi tunda nice ke
girki kullum saboda su mama dukiya yakai min uban diyana da bai da lafiya Asmau
take fadan hakan.
Dama na kula da hakan tun kwanaki cewa yarinyar nan ita kadai ke girkin nan don
ko yaushe ka shiga itace a kitchen tsaye .
Yau nasan ke munafukace Asmau dama kina hakane don munafunci ashe me nakeyi don
munafunci da kikace ba zaki kara girkawa kowa komai ba tunda mama tudu tace ba za a
kwana dashi ba mena fada ki fadi a gaban kowa mana yadda mukayi dake ?
Nan dai tonon asiri ya tashi a tsakaninsu inda har sunan saratu din yafi yawa
komai da ake kitsawa ita da saiba ce ke kitsawa har zuwa wajen malam da sukeyi duk
Asmau ta fallasasu a bainan kowa yanaji harda abinda basu zaci zata iya fada ba
game da suratansu na hassada .
Ranan dai rayuka ba dadi a gidan ga mai ciwo ga kuma tone tonen maganan da
yazid yajawo akayi na fallasa inda mama dubu a karshe tafi kowa bakin cikin hakan
jin saratu abinda take kullawa don kawai ta bata tsakaninta da yayanta din kamar
yadda Asmau ta fada.
Saida yaya jafar yayi kwana biyu a cikin wanan halin aman har yakai dole aka
kara mashi ruwa leda biyu manya ko zaiji karfin jikinsa.
Don gabadaya a wanan gabar duk yan uwa an debe rai ma a garesa gaskiya ga badama
a koma asibiti dashi haka tunda ansan ciwonsa dai sai Allah saukinsa bana asibiti
bane don maganan likitoci gudane su


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login