Showing 90001 words to 93000 words out of 328222 words
Chapter 31 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Nasamu na gama exam dina haka na dukulo na dawo gida da ciwon kai ga yunwa da nake
tunanen shiya haddasa min ciwon kan don ban iya cin komai idan na taka school sai
idan na dawo gida.
A haraban gidan na gansu zaune yadda suka sabayi wani lokaci idan sun bushi
iska hakan zasu fito nan farfajiyan gidan su zauna a dasa daban hira da tsokona.
Irin wanan zaman na fahinci da gaiya sukeyinsa wani lokaci idan suna da kudirin
cin mutunci ga wani a gidan suke wanan zaman.
Shigowana yayi daidai da karan budan get din gidan mota ta shigo hakan baisa na
juya inga mai shigowa gidan ba a lokacin saida akai horn na gane ya J ne ashe ya
fita ya dawo a lokacin.
Daidai inda ya sameni kiris ya rage inkai lungun mu ya dakata da mota ya sauke
glass sunana da naji ya ambata yasa na dakata na juyo ina gaidashi.
Ko ban kalla ba nasan idonsu yana kan mu a lokacin shiko gaisuwan tawama bai
amsa taba sai cewa da yakeyi dani wai Rahama meye matsalan da kike gudana a yanzu.
Murmushi na dan sauke ina fadin yaya gudunka kuma wallahi exam muka fara sai
yau din nan muka karasa wanan yasa ka daina ganina.
Ya maki kyau shiga zanyi maganin ki ai daga ke har Nafisa zan zauna daku ku
fada min idan kuji wani abu daga garemu ne kuke wanan halin sam banji dadim matakin
da kuka dauka ba wallahi.
Nagode yaya na fada ina dan rusunanwa na hau step ina murda kofan mu na shiga ban
san ya akayi ba dai bayan sallah isha,i saiga Nafisa a part din mu tana fada min
wai yaya J yana neman mu wurinshi.
Yadda nake dagani sai wata dogowar riga mai v neck mara hannu sky colour hijjab
dina fari danayi sallah na fito daga part din mu nake ce mata dama dazun yace zai
zauna damu ashe da gaskene.
Ok dama dazun din da gaske ya tsaya dakene rikici sukeyi da matanshi akan hakan
nidai naji yashigo yana fadawa mama a hasale har ya tashi dukan Saare iya ta hana.
Shi yaya har yaji sauki duka haka ke nan iya abinda na iya fada ke nan don ni
zargin nasu ban daukeshi da wata manufa ba tunda a gabansu dai na tsaya dashi din
suna gani.
Kuma meye a ciki don ya tsayar dani na tsaya shine kuma zai zamo abin fitina har
da zancen duka a ciki ?
Kin gane Rahama wallahi yau ina ganin za ayita ta kare a gidan nan kila na bar
gidan nan a yau din nan don ba zan lamuci zancen banza ba bari dai muje din muji
kiran zakisha mamakina wallahi.
Rashin mutunci da iskanci nida na taso gidan yawa kowa da halinsa ana nuna min
iskanci in kyale saidai idan naso hakan shiru shiru aiba tsoro bane dama.
Ke kenan Anty Nafisa nikan ai kila barin gidan zasuce nayi tunda zargi ya fara
shiga haka ko basuce in bar gidan ba aini zan bar masu.
Akan me gidansune bari dai muje muji ai mama da kowa suna can wajen hakan ne kuwa
koda muka shigo da sallaman mu falon duk suna zaune harshi dake waya a lokacin inda
na fahinci zai koma bakin aikinshi a kwanan nan yadda yake fadi a waya lokacin.
A jam,i nayi masu ina wuni muka samu waje muka zauna a gefensu falon yayi shiru
bin ko ina nakeyi da kallo har kasan da nake ganin tun dawowansu bai samu mopping
ba kayane a ko ina yasha a falon wanda nasan aikin yaransune hakan.
Suna da wani hali ko yaro yana barna ba za a tsawata mashi ba haka kuma idan dan
wani yayi barna har inke uwa baki kwashe abin ba a nan zai tabbata wajen.
Ba karamin wahala mukasha wajen gyara falon nasu ba lokacin har ya koma daidai
yadda yake son gani kullum a rayuwansa.
Muryanshi ya dawo dani na dago kai da yake fadin Nafisa kin dai gani ba falon da
kukasha gyara shine ya koma haka saboda na tara jakkai da basu san arziki ba sai
tsiya da bakin kishin banza a rayuwansu.
Haba dai daina fadan hakan jafar ke Rahama dazun kun fitane tare da yayan ku da
yamma ko shi ya daukoki daga bokon da kikaje ?
Kallon ido da ido nayiwa mama din cikin mamaki ina fadin wani yaya ciki mama ni
kadai nake zuwa in dawo yauma aida Aisha muka dawo ita ta bani lift a motan gidansu
da akaje dauko ta.
Ina kikaga yayan ku nace nan gida zan shiga part din mu yadda Saiba ta gyara
zama irin bata yarda din nan ba yasa na yi shiru.
Ya taba daukan ki ko yakai ki wani wajene bayan haka dakata mama ina da number
Aisha din bata gidan Alh wada din nan ba sai ta kira layin Aisha din.
Wai ke dama kina nan yau ai nake ji wajen kanwarku din nan dazun na ganta a
hanya tana jiran mota na rage mata hanya kinsan yarinyar bata da sakin fuska.
Aita fada min dazun din shine na kira inyi maki godiya haba dai akan wanan
wallahi salima baki da kirki ko kadan kizo ga gida ga gida ki kasa shigowa ?
Bari zan kiraki anjima don Allah ta fada tana kashe wayan ta kallo kowa dake
saurarensu tana fadin kun daiji yanzu ai.
Kinji ko mama kinji da kunnen ki wa yan nan jakkan suna son bata wa yarinyan nan
suna a banza to bari kuji wallahi.
Jafar dakata iya ta fada yau koka dauki Rahama a motanka laifine hakan nace
laifine a garinku ?
Wai meyasa samun waje yake son zama iskanci bari kuji in fada maku Jafaru dai
namijine mata hudu Allah ya halasta mashi yi akansa.
Ashe kuwa matukar hakan Allah ya yarde masa ku din nan baku isa kuce sai yadda
kukeso zaiyi ba a rayuwansa .
Ba a kallon mata ke Nusaiba kika kutso cikin rayuwansu da danyen aurensu kika
saka saida ya auroki gidan nan aka kawoki don bakin ciki kada abuyarki taci bakici
ba.
Dariya anty salima keyi nasan hakan ya bata haushi ta soma magana tana fadin ai
gashinan iya ki tambayeshi idan nina kutso kaina bashi yace yana sona ba ?
Ke rufa min baki har yaushe na taba ganinki nace ina sonki Nusaiba bayan wasikun
batanci da kike rubuto min kina bata kawarki wajena ?
Har kikayi nasaran hada baki da abokina kuka,,,,,,
Jin irin tonon asirin da yake mata a gaban kowa yasa tayi saurin katseshi da
fada tana fadin bayan duk bina da kayi a yanzu zakayi min sheri.
Ya isa haka don Allah wanan kanku kuke tonawa asiri bayan abinda ya wuce koma
meye yanzu ai kun zama daya a tsakaninku don haka ki koyi hakkuri da zaman tare.
Kinzo kina zargin mijiki da yarinyar nan yau idan Jafaru yace zai auri yarinyar
nan ke kin isa ki hana hakan tunda ke ba,a hanaki ba ?
Tun zuwan yarinyar nan da yar uwarta gidan nan kuka dauki kiyayya da hassada kuka
dorawa yaran nan don mijinsu yana da dubaiyane aksn dan uwansa da ankai ga yadda
kukeso .
Ki duba yanzu bai ko sanda shigowan yarinyar nan ba amma kince wai tare sukazo
gidan nan da ita ya sauketa a waje.
Ni kuma na fada a cikin mamaki kwarai kuwa abinda suka fada ke nan cewa tare
muka shigo dake na saukeki a waje saidaga baya na shigo gidan hakan bai mun ba kuma
na dakatar dake muna magana.
Tace ko a bayansu ina kwance ina jinya abinda mukeyi ke nan dake dama sai Saiba
tace ai muma ji mukayi cewa komai itace ke maka ita da Nafisa .
Ba ance bane kwarai sukeyi min komai ko yanzu ma a gaban ku su din ne dai zasuyi
min kome nake so wace zata zauna ta zauna wace bata iyawa kuma ga hanya nan sai ta
tafi.
Kaina na sada kasa abinda yar uwata dai take zargi ya tabbata ke nan a kaina
yanzu sai muryan saiban naji tana fadin .
Ko sunyi fa sai me in zaka iya sweety ka aureta kaga wa hakan zai dama ?
A zabure ya harzuko mata yana fadin haka kikace ko tace an fada din inka isa ka
aureta mugani ko ba nufinka ba ke nan ?
Wanda ya fada muna in bai gani ba zaiyi karyane nan suke ma komai ai wa,,,,,
Ke yarinyar nan baki da kunya yanzu ke don Allah bai zuba maki kunya a idonko
ba mijin da kika kyamata a gaban mu zaki dawo yanzu kice kina fada a kansa ?
Nan fa kuka nuna kuna kyamarsa don ciwon da Allah ya jarabeshi dashi don baki da
kunya ko kadan yanzu kin dawo kina fadin wanan zancen banza haka don samun waje.
Mikewa nayi duk suka bini da kallo falon ban tsaya jin nauyi kowa ba na fice
daga dakin kai tsaye zuwa part din mu na samu maria ta idar da sallah take fadin
yanzun nake fadin in biki ai.
Sai gaki tun dazun wayan ki keta ringing ba tare danayi magana ba na shige dakin
na dauki wayan Sa,id ne ke faman kiran layina saurayin daya lake min saidai a
ganina ba a yarda in tsaya dashi ba zasuce yarone don yadda naga sunyiwa anty
Salima shiyasa ban damu da kulashi ba.
Sai kuma ga kiran anty Salma ya shigo wayan na daga ina mata sallama ya kuma
najiki a wani mood ko baki da lafiyane ?
Lafiyata lau anty kawai dai sai nayi shiru meya faru ta sake tambayana sai naji
kawai in fada mata ko zanji sanyi a raina ko kadan ne.
Wallahi anty Salma sha,anin gidan nan ya isheni matan yayan ya habu sun saka min
ido suna kokarin bata min suna ga abinda bashi ba.
Cool down Ramaah kiyi min bayani yadda zan fahinta nan na kwashe komai na fada
mata Maria tana tsaye tana saurarena saida taji anty salma ta soma magana da bataji
ta juya ta fita daga dakin.
Anty salma ke cewa da zaran kun gama exam dinki ki taho nan kiyi hutunki ki
kyalesu can yan iskan mata kawai na bata amsa da mungama yau ai.
Shine suka tareki da bacin rai ga gajiyan exam a tare dake goben nan zan turo a
daukeki har gida ki shiri ba maria waya muyi magana .
Hakan yasa na mike zuwa falo bata nan na duba dakinta nan ma bata nan sai na leka
waje naji hayaniya yana tashi a wajen.
Nacewa Salma ina zuwa na kashe wayan nabi bayan ta daidai da zan shiga naga mama
ta sakota gaba tana fadin tayi hakkuri suma sun fadane don batanci amma ai fadan ya
koma masu ciki yanzu don matakin da jafar din ya dauka.
Ranan kan sunsan sun taba mata yar uwa don tayi masu abinda basu taba zato ba
ta zagesu tas dama ance kunne ya girmi kaka ina jin muryan saiba daga cikin part
dinsu tana fadin idan ta isa tasa a yau din nan a dauki mataki a kansu din idan
habun ya dawo.
Ranan dai da bacin rai kusan kowa a gidan ya kwana da safe nake fada mata Abuja
nayi wurin anty salma inyi hutuna a can din.
Bata koce mijin ta aibai gari ba yadda ta saba tauyeni shi kuma idan ya dawo
yake hanawa sai cewa tayi hakan ma yafi.
Sai can nace kuma kada in tafi na barku daga ke sai Abba ku kadai a cikinsu tace
ki tafi ba abinda zasuyi min ki daga ki basu waje kawai zaifi sauki har a kwana
biyu.
Karfe daya da yan mintuna muna hanya ban tsaya sallama da kowa na gidan ba sai
Nafisa data shigo taga ina shiri nake fadawa Abuja zan tafi ranan.
Sai ga mama ta shigo tana tambaya yanzu maria kan wanan zancen da akayi ya wuce
zaki tura yar nan Abuja tayi murmushi tana fadin badon shi bane mama dama tana da
niyar zuwa tayi masu hutu a can.
Yanzu haka driver da zai dauketa yana hanya tafe takai zaune tana fadin koda
zata tafi ba dai yau ba kan zancen nan dai ya kawo wanan tafiyan shi Habu ya sanda
zancen tafiyan natane yau ?
Zan kirashi a waya mama dama yasan zata tafi ai ummah ma tace ta tafi din tace
to shike nan Allah ya sauwaka ina daki ina jinsu sai mamakin hali irin na mama na
sanyi hali nakeyi.
Barma dawowan su din nan abin nata kamar ya sukurkuce ne gabadaya kardai abinda
suke fada kan suna shige shige gaskiyane hakan ?
Koma dai meye sun samu waje da yawa ni dai har tagama ta fita ban leko ba kuma
ba a jima ba driver da anty salma ta sheda muna ya taso tun bakwai na safe ya iso
daukana din sai da aka gama saka kaya a mota anty maria ta matsa min nashiga na
sallami su mama na fito muka dauki hanya.
Karfe hudu da wani abu muna Abuja don mun tsaya kaduna mun karbi sako na kuma
shiga nayiwa ummah sallama na tafi.
Tunda aka shiga min da kayana nashiga nayi sallah ban fito ba ina daki don har
lokacin ina jin zuciyana a cunkushe abinci ma nan anty salma tasa aka biyoni dashi
ta fita ta barni da yaranta zuwa asibiti duba wata kawarta.
Wa jajen karfe biyar maria ta bugo take tambayana mun sauka lafiya na amsa da
lafiya yaya na barsu kuma tace lafiya kalau ga Abbati yana kewana.
Nace a bashi waya yana jin muryana yasa kuka nake lalashin shi a waya ina mashi
waka nan uwar ta karbi waya tana fadin ai habu ya kira yana fada wai meyasa na tafi
ban bari ya dawo ba.
A raina nace tunda ubana yake ba amma a fili cewa nayi da ita dana bari ya dawo
ba zai yarda in zo ba yanzu ko gani hankalina kwance saidai kewan su don ba karamin
shakuwane tsakanin muba da ita.
Shigowan anty salma dakin yasa mu dakatar da maganan ta karbi wayan suka danyi
sharfi akan zancen na wani dan lokaci.
Bayan sun gama take fadin wallahi sunyi arziki ba a gari daya muke ba da sunga
tsiya don sai nayi karansu wallahi.
A bakin iya yake jin tafiyana Abuja din daya shigo take fadin ina kashiga yau
Jafaru yake fadin ina can kofan gidan mu iya da abokaina .
Nikan nace da kana gida ba zaka bari yarinyar nan ta tafi ba ban zaton zasu
barta ta dawo gidan nan kuma don wanan sherin na matanka Jafaru.
Wace yarinya iya ?
Yarinyar nan me take da suna Nafisa dake zaune take fadin wai Ramaah take nufi fa
sunan ma ta kasa fada kullum sai an tuna mata sunan .
Ina taje Nafisa tace Abuja dazun aka aiko da mota aka dauketa daga can yanzu kan
ai ta tsufa Abuja ita kan saiga salima ta fito daga dakinsu tace .
Nifa banga laifinsu ba gara data gusa ta basu waje wanan zargin ya kare hakana
haba don Allah wanan iskancin har ina don Allah ku dauki kishin yar uwarta ku
yabawa yarinya bataci ba bata sha ba don Allah dai.
Humm, kawai yace ya mike tsaye yana fadin iya zan fita me zan sayo maki yau iya
?
Jafar kaji saukin fitane irin haka naga dare ya soma yi a yanzu kardai don
shedanun matan nan naka zaka tsiri fitan yamma haka ?
Bai bata amsa ba ya fice daga gidan motarshi ya nufa ya shiga ya zauna maigadi ya
bude mashi lokacin ya ciro waya yana neman number waya.
Nidai ina waje tare da anty salma ya kira harya katse ban dauka ba lokacin dana
dawo kuma ban koma takan wayan ba nayi sallolina na kwanta.
Washegari tunda safe ya fito a cikin shirinsa ya nufi wajen su mama ya samu
suna azzakar din safiya ya gaidasu yana fadin zai danje kaduna kila ya isa har
katsina saidai yadda hali yayi sunganshi .
Haka ya bar zaria zuwa Abuja don shi kadai yasan yadda ya kwana cikin bacin rai
ya kulla wanan ya kwance ko iyalinsa sai a bakin kannesa suke jin baya garin.
Sam bai manta da gidan anty salma ba direct ya dira gidan ya dan jima a kofa yana
kiran waya ba a dauka ba yasa ya fito yayi sallama.
Daga cikin masu aikin gidan wani ya shigo yana fadin wai anawa Anty Rahama
sallama daga zaria bakuwar data zo jiya.
ZAINANB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,
3️⃣2️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Kallon juna mukayi da anty din don zaune muke muna karyawa muna dan taba hira da
ita wanda hiran exam dina nake bata tana dariya.
Shine wanan mai aikin ya shigo yana fadin sakon daga zaria je kace waye yake
sallama da ita ?
Ya juya ya tafi ita kuma tace kin fadawa wani