Showing 153001 words to 156000 words out of 328222 words
Chapter 52 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
ga dan cikin ki dubu hau kika gansa dashi ko me da zaki
fadi hakan kan danki dubu akan wanan yarinyar da batayi maki ragowa har kike
kokarin aibanta danki ?
To iya saki fa shi haka yaga mahaifinsa yayi daga zancen fatan baki zai furta wa
yarinyar nan saki dama bai shiryawa fitinan mata ba ya tarasu haka gidansa ?
Ki dai gyara kalamin ki ina horon ki da hakan matsalansuce can kinsan irin cin
mutunci da tayi masa har aka kaiga hakan ?
Saiga Saare ta dawo tana fadin wallahi kuwa wai sakinta yayi ta cikin waya daga
magana kawai ya furta wai ya saketa.
Gata can zata wuce kaduna yanzu dole mama ta mike zuwa part din ta bata hakkuri
akan ta zauna sai kukan da takeyi .
Bayan mama ta fitone yarta ta bugo waya take fadin wai ta dawo gida zaman me
zatayi tunda yace ya saketa din me zata zauna yi kuma ta dawo gida kawai.
Wanan yasa ta fita ba tare da sanin kowa ba tabar gidan zuwa kaduna din itako
mama tana ta neman layinsa bata samu ba saina habu ta samu yake fada mata ya sauke
j din har sun tafi.
Shima gashi ya kusa isowa gida in sha Allahu sai batayi mai magana komai ba ta
bari sai ya iso gida din taji meya faru.
Koda ya iso ko part dinshi bai shiga ba ta tareshi da zancen cikin mamaki yake
fadin saki kuma ita saiba tace sakinta yayi bayan agabana sukai maganan .
Zaginsa takeyi tana ja mashi Allah ya isa shi kuma yace taje gidansu ta huta iya
abinda na sani ke nan ya faru tsakaninsu.
Kunj ko mena fada maku ba yarinyar kirki bace shikan ya juya zuwa part dinsu ya
batsu nan ana zancen saiba din a part dinshine Maria ke fada mai abinda ta fada
game damu din yace hauka takeyi kila ?
Zamfara garin gusau.
Kiri,kiri baraka ta hawa Aliyu kudin nan tace ya bari mahaifinsu ya fara juya
idan sun kara yawa sai a samu abinda aka bashi shima ya soma nasa sana,an.
Tun daga lokacin bai kara magana ba kuma yakawo ido yasa abinda bata sani ba
shine shi Aliyu yasan mai mahaifin nasu ke aikatawa don wata bazarawace a nan
makwabtansu daya taba nema taci mashi kudi ta koma zurmi tayi aure itace ta fito
yanzu kuma bai daddara ba ya koma nemanta gadan gadan .
Shine Aliyun yaso su zauna da uwar nasa ya hanata bashi kudin amma taki
saurarenshi lokacin take ganin kudin yaron ke son ta mika mashi duka.
Shiko Aliyun yadda yaso shine su samu dan fili su saye da rabin kudin rabi kuma
ansan yadda za ayi amma batab basira ya kamata ta dauki kudin duka ta mikawa mijin
nata da sunan zai fara sana,an hatsi dasu yana shiga kauyuka yana soyowa ya kawo
nan cikon zamfara din tayi na,am da hakan.
Balle dataga haikam ya bazama kasuwa sai dadi ya kara kashe mata zuciya gashi in
zai dawo da dan cafanen su na kauye daga ita har yaran sun canza sosai a yanzu
gaskiya.
Zamana da anty Salima da habiba ba laifi gaskiya saidai matsalan daya shine
banda saurin sakewa sosai har yanzu dai halin nan nawa yana nan a yadda takan fada
ita saliman .
Idan naje school na dawo ina daki ina hutawa sai dare zan dan fito mu zauna a ci
abinci a danyi hira kuma in koma dakin karatu.
Wanan yasa take ganin wai banda saki a bakinta nake jin abinda ya faru wai saiba
tana gidansu yaya ya saketa.
Gabana ya fadi sosai da jin wanan labarin don na tabbatar za ace saboda nice
hakan ya faru tsakaninsu niko harga Allah ban sani ba.
Nasan dai kafin yayi tafiyanshi yana lagos lokacin zai kirani mu gaisa wani
lokacin ma shike tashina daga barci da asuba ko kuma ya kira da safe yana tambayan
ko nafita zuwa school ?
Amma tunda yabar kasan sai gaisawa yayi wuya a tsakanin mu dashi matsala dayace
ban yarda na nuna masu hakan ba don salima tana yawan tambayana shi nace yana
lafiya ai.
Ranan wreekend ban fita ba ranan ina daki kwance ina barci anty Nafisa tashigo
muryansune suna hira falo yasa nafito don mu gaisa da ita.
Tunda na fito ta kyala ido ta kalleni take fadin wai wai wai Rahama kece haka
wai lalai aure Rahamane sunan naki yabi zancen kinga yadda kika koma wata buleliya
dake haka ?
Cikon dan kunya nakai zaune ina fadin anty Nafisa sheri zakiyi min kuma bamu haka
dake fa tace wallahi Rahama kin canza min lokaci guda ?
Anty Salima na nuna ina fadin gata nan itace ke ban dadi na koma hakan ai muka
dara gaba dayan mu nakai zaune ina fadin wai anty Nafisa daga barin je in dawo
ranan kikai tafiyan ki ?
To ai gani na dawo Rahama fitan ne yanzu ban faye sonshi ba mutane sun faye
gulma yanzu tin anayi a bayanka har an fara fadama zance kamar mutun shine zai nemo
miji da kansa ?
Allah shiyasa banson fita ko ina aiko gidan iya ni tun bukin ki ban kara taka
gidan nan ba har yau nocking din kofan da akeyi ya katse mata zancen.
Habiba ta mike ta fita don ganin waye sai gata ta juyo tana fadin matar Uncle ce
da wasu kafin ma ta gama zancen sun fado dakin cikin gadara da wani irin kallo.
Duk da gabana ya fadi don ganinsu a lokacin saidai ban nuna hakan a fili ba
naji wata daga cikinsu tana fadin a,a lalai kan Abuja ?
Tunda na mike ban tsaya mu gaisa ba kitchen na nufa na dauko ruwa da abinsha na
kawo masu tare da cups na aje a gabansu naji dayan tace to aimu ba ruwa mukazo sha
ba.
Haba dai kusha ruwa mana na sake fada cikin danjin nauyisu sai naji saiban
tace ainan ba gidan da zamu tsaya bakunta bane balle a kama bamu baki musha ruwa.
Kashedi nazo maki akan mijina Ramaah ina jin hakan nace to nakai zaune gefen
hannun kujeran da anty Nafisa take zaune sama.
Sai naji anty Nafisa tana fadin haba dai anty Saiba hakan aiba girman ki bane
yaya zaki mata gida kice haka kuma ?
Ke Nafisa dakata ban ambaci sunan ki ba dana shigo don haka ki kyaleni inyi da
ita, ita da yanzu take ganin takai tunda tasan yadda suka shiga suka fita suka iya
asirce shi har ya aureta ?
Tunda sun saba da bakar bidan asiri suna mallake mutane har ita ta isa tasa J ya
juya muna baya ya daina shiga duk wani harkan mu wallahi bata isa ba ?
Daga ita har Maria din da kike takama ta samu habu ta mayar dashi saniyan
tatsanku da kowa naku saidai ku tsaya ga habu shida kuka sama amma baku kai can ba
wallahi.
Ashe nakai har na usa kuma ke nan tunda har na iya mashi asiri daya kamashi don
da bakiga hakan ba da baki tako har nan zuwa min kashedin ba ?
Daga daga inda nake zaune nake fadan hakan tare da jin duk wani tsoronta da
shakkunta ya fita a raina lokaci guda.
Wallahi ke Ramaah karamar yar iskace baki isa ba wallahi ina ganin hakan na mike
tsaye na sake fadin ai isan ya kawo haka tunda gashi har kin tako zuwa gidana ko
kunyan hakan bakiji ba ko kin gani gidan ku ?
Ta kwashe da wani irin dariya tana fadin wai gidanki kuji min yarinyar nan fa
kije gidan mana idan kin isa mara kunya kike da gaske kije gidan ?
Gida kan ko yau nake son zuwa zanje don baki da wuta baki da aljanna akaina
Nusaiba kuma gida ba naki bane don haka baki isa ki hani shiga ba.
Bansan ya akayi Salima ta kira mama ba na daiga tana fadin wallahi mama muna
zaune suka shigo ita dasu anty ikilimanta.
Niko ina fadin ai bansan kin dau abinda zafi haka ba dana rigaki yi maki takaka
a gidan inga abinda zaki min din ?
Haka kikace zan dawo ko don ki wallahi nace ki dai dawo don mijinki daya ajeki
amma ba dai niba basan da tsiya kikazo ba dana tareki dashi tun farko ?
Yanzu da kika sani ai sai kiyi wace zakiyi din tunda kin sani ke dai da tsiyan
ta kawoki ai ina sauraren ki ?
Anty salima na fadin wai ba zaku daina ba don Allah ke saiba duk inda akaje baki
da gaskiya tunda ke kikazo har gidanta .
Kaji wata munafuka na amsa da fadin munafuka tafiki Nusaiba ?
Saida ta kalloni cikin mamakin jin abinda na fada nace keda kika yi munafuncin
daya ciki kika fada ciki inkina ganin kin iya sheri an fi wallahi.
Koda yake ba abin mamaki bane ai tunda dama kowa ta dalilin sheri da munafunci
ya sanki a gidan.
Don kawarki kikaiwa kwancen miji gashi har kina nuna kinfi son mijin fiye da ita
a yanzu kin dauka zakiyi min sherine yaje a banza ko gobe kika kara min sheri
zakiga fiyema da hakan wallahi.
Sam ban yarda na raga mata ba kamar yadda anty Salma ta fada min inyi a duk
wace tayi min takaka a cikinsu in debe tsoro da kunya inyiwa maishi tas don gobe
karta dawo min gida .
Hakan ko nayi mata don na debe tsorona a lokacin na shafawa idona tako na mayar
mata da martani don a debe tsoron juna a tsakanin mu dama ina kule da ita a raina
har lokacin.
Jin wayan da Salima keyi da yaya Habu yasa suka bar gidan ajata ajani tana fadin
bata zuwa ko ina sai taga karyan rashin kunyata gidan .
Don naga na samu waje zan kawo mata iskanci zata gwada min ko ita waye ranan don
sai ta murjeni kamar filawa nace mudai murji juna dake Nusaiba bari ganin kinzo da
wa yan nan wallahi, in kuma kina iyawa ki gwada.
Sai kuma ta juya kan Salima da Nafisa tana fadin ku kuma haka zasu kare a gurin
bin kanwar baya bayanku don kwadayi da wullakanci .
Su rasa wace zasu bi har gidanta saini suje suyi aure yafi masu zama gindin
yarinya karama suna zugani ina daukan ni wata tsiyace ?
Fadan ya koma namu duka kowa ya fadawa dan uwa maganan dake bakinsa data sani
batai hakan ba da har gobe tana da matsayi a wajena na wace ta girmeni kuma take
gaba dani a gidan aure.
Saidai kash zuciya yakaita da girmanta ya fadi wajen kowa a wanan lokacin don ita
kanta bata taba zaton zan iya bude baki inyi mata haka ba.
Koda yaya Habu ya iso sun tafi ko yace zai dauki mataki kan hakan agabanmu
yakewa maigadi warning da kada ya kara bari wanan matan su shigo gidan nan.
Anyi haka da kamar sati zancen ya lafane don har kaduna mama taje da kanta suka
dawo da ita bayan an tsawata har lokacin kuma shi bai dawo ba kasan saidai da
alaman yaji duk abinda ya faru don daya kira yake tambayana cewa bata sake zuwa ba
ko ?
Na amsa da bata zo ba don yakan kira a sati saudaya ko sau biyu a cikin sati yaji
lafiyan mu a dan gaigaisa da jama,a kuma.
Hafsatu dake tankade a kofan kitchen taga mijinta ya fito da shirinsa ta bishi
da idanu don yanzu gaskiya karara ya canza mata fuska gashi alkawuran da yayi na
gyaran dakin yaransu bai cika ba.
Wayanshi dayayi kara a cikin aljihu ya tsaya dauka daga kofan dakin nasa ta gane
dawa yake wayan don jin sunan mama dubu daya ambata sun dan jima suna magana kafin
taji ya soma fadin.
Amma ita salima me zatayi da kudi har haka kudin nan fa gaba daya na dauka
nasaka a wanan sana,an takin don yanzu kinsan shike shiga da sauri da daminan nan .
Kallonsa da sauri Hafsatu matarshi tayi ganin hakan yasa ya karasa saka takalman
shi dake kofan daki ya fita ta bishi da kallon tsarguwa.
Wani kudi yake zancen yakai sayen taki dashi dazaice hakan amma ai gamu gani
badai a kan kudin nan ya matse mata ido da wani hurda ya rikesu gaba daya ya sauya
mata.
Dakin dake kusa da hanyar bandakinsune wanda iya take rayuwa da a cikinsa kafin
a sai wancan gidan da suke zaune a cikinsa yanzu.
Shi taga ya gyare fes tayi magana yace bataga ginan ya rankwafo bane kada ya
fadi saita yarda da hakan daya fada lokacin.
Sunyi hakan da yamma yana cin abinci yake fadin ina ganin fa zamu karu a gidan nan
hafsatu amma saidai yadda hali yayi tukun don bamu gama shiryawa ba tukum da
bazawar tawa har yanzu.
Aiko hafsatun tayi cikin shi da masifa ta inda take shiga banab take fita ashe
duk lokacin ankai sati biyu da daura aurensa bata sani ba sai lokacin ya gwada fada
mata aiko baisha da dadi ba a ranan wajenta
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: Seenabu Makawa: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
5️⃣2️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Yaya J saida yayi wata biyu ya dawo lokacin muna gab da fara jerabawa shigowan
yamma yayi garin don na dawo school muna falo da salima da Nafisa da yanzu zamanta
ya dawo gidan tun bayan rikicin mu da saiba data zo har nan gidana taso yi min
yankar kauna.
Sai Allah yaban sa,a na aro rigan rashin mutunci na yaga mata nata haka ta tafi
tana mamakina shi kuma yaya Habu da yaji ya sameta har gidansu yaci mata mutunci
sukayi ba dadi dashi.
Amma kuma da mama dubu taji bata ragawa habu din ba don cewa tayi halin kishine
bai kamata shina miji har ya saka bakinsa ba yana nufin don ina yar uwar matarshi
ya goyi bayana ke nan.
Ita batace abinda saiba tayi tayi daidai ba amma sha,anin kishi ba yadda baya
zuwa don kowa da irin tasa fahintar kada suce zasu nuna wariya a tsakanin mu tun
yanzu.
Baidai ji dadi ba amma kalla baicewa mama din ba lokacin ya mike ya fita bayan
kwana biyu tasa yaya Ibrahim ya kaita kaduna ta samu iyayyen saiba din ta basu
hakkuri kan abubuwan dake faruwa.
Sukuma suka dunguma Saiba din suka mikawa hjy bayan tasha fada kan rashin
hankalin datazo gida tayi min din ita da yan uwanta.
Anty Nafisace ta fara fadin kamar muryan yaya Jafar nake ji a waje donshi na
fada maki a baya haka yake maganansa a cikin dan sauri sauri tare da dan sarke
harshe kamar me i,i,niya wani lokacin.
Don sai ka saurara da kyau zakaji abinda yake fadi wani lokacin saboda saurin
magana da Allah ya bashi.
Shi din ne kuwa ya shigo yana sallama suit ne a jikinsa arsh colour sai farar
riga daga ciki daya dan baiyana fili sakamakon balle anineyan saman rigan da yayi .
Har muna hada baki wajen yi mashi sannu da zuwa ya amsa cikin jin dadi
hankalinsa yana kaina kai namiji baida kunya wani lokaci.
Batare da jin nauyin sisters dinsa ba ya miko min hannu wai inzo inda yake tsaye
na noke kaina da sauri a cikin kunya.
Kaji bakauya don Allah tashi kije miji ya dawo yana kewan ki anty Salima ta fada
tana mikewa tsaye itako Nafisa dariya tayi ta mike itama sai biba tabi bayan su.
Hakan ya ban daman mikewa zuwa gareshi don har lokacin yana tsaye ya ware da
hannayensa alaman yana jira inzo gareshi din.
A cikin wani tako na karasa wajenshi ya mayar da hannun nasa ya rufe na dora
kaina saman kirjinsa ina lumshe idona a hankali tare da ajiyan zuciya.
Kanshi ya dora a nawa yana shakan kamshin ni,intacen mangashi irin na kanuri da
ake hadawa da wasu itattuwa da kayan yaji irin na gargajiya.
Mai,ne na kitso mai inganci da ko ancen kasan nasu ba kasafai ake samunshi ba sai
kinyi bucking dinsa don mamata aika lokacin anjima ba a kawo ba amma dai ana kawosa
naga anty salma ta banye kai tayi kitso dashi.
Nima akai min tun lokacin nake jin dadin amfani dashi ina jin ajikina shima
hakanne don yadda yake shakan kamshin daga kan nawa a lokacin.
Dakinsa muka nufa saman gado muka fada a tare don yaki sakina ya shiga lalubata
ganin abin nasa nason wuce gona da iri yasa nayi dabara na shammaceshi nasamu na
mike da sauri nabar gadon .
A kasalance naga ya koma ya kwanta yayi rigingine yana kallon saman dakin saida
na samu na saita kaina nake fadin .
Ko ruwa baka sha ba yaya ?
Saida ya furzo da iska daga bakinsa yake fadin ruwan da nake son sha an hana min
debe kishina naga ya lumshe idonsa sai danyi kasa da kaina ina fadin.
Ba a nan ya dace ka debe ba ai tunda ba gidan nan zaka sauka ba koka manta a nan
ka tafi da zakai tafiyan ?
Ok kawai yace min a takaice ya kara lumshe idonshi nikan na fice a dakin