Showing 117001 words to 120000 words out of 328222 words

Chapter 40 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

matsayin mijina da fitinan gidansa
ta ina zam soma wanan badakal auren da ya hau kaina yanzu kuma ?
Har nayi sallah isha,i na koma saman gado na kwanta maganganun inna kemin yawa
a kai na kasa hadasu a waje daya.
Ni Rahama nice zanwa yaya Jafar asiri don ya soni ba yaya Jafar mai mata ba ko
wani irin namiji ba zan iyawa a siri don na mallakeshi ba a ina ma zan samo asirin
da zan masa din ?
Zancen maganin na dashi ya fado min a rai gabana naji ya fadi na furta na shiga
ukku shiyasa taimako yake da wuya a zamanin nan.
Ko dai sun dauka maganin na asirine da zaisa ya soni nayi mashi a lokacin harwa
yasan da zance haka banda nafisa da ya habu sai shi jafar din.
Shigowan anty Salma ya katse min tunanane ta shigo tana fadin ke abinci fa
bakya jin yunwa ne kika kwanta ,?
A hankali na dago idona da sukai ja duk da ba kuka nayi ba a lokacin amma bacin
rai yasa idanuwana sun sauya min lokaci guda ba yadda na dawo daga gidan mama ba.
Meya faru kuma take tambayana muryan can kasan makoshi nake fadin ba komai anty
tace ok ga abinciki nan nace jummai ta sako maki a kawo maki nan baki jin dadi ba
lalai bane ki fito.
Allah sarki anty salma ba abinda ya dameta ita hankalin ta kwance komai nata
cikin gata ba tsamgwaman rayuwa nake fada a kasan zuciyana sai naji tace ke
Ramaah ?
Jafar din nan naki wani irin mutum ne shi gaskiya mutumin arzikine sosai wallahi
a cikin matansa akwai mai cikine ashe ?
Kai na gyada bata jira cewata ba taci gaba da fadin dazun nan ya turo min da kudi
da za aiwa mai jego da jariri sayaya har daku daba haihuwan kukayu ba bayan lefe da
na tausan gaba daya saka aka hada mashi.
In wanine yana zancen aure a gabanshi aiba zai tsaya tuna hakan ba har ya tsaya
hada kayan haihuwa kan wa yan nan yan iskan matan nasa.
Ni wallahi Ramaah tun bangasu ba bakiji yadda na tsani halaiyansu ba haka kawai
su hana bawan Allah shakat a rayuwansa don iskanci da samun waje wai meyasa matan
hausawa akasarinsu suke hakane ?
Naji ance wai ita dayan matar nasa tayi yaji tana gidansu tun ranan da taji
zancen auren shi kuma yace a barta can ba inda zaije tunda bashi ya turata ba.
Kala bance da ita ba akan zancen har jummai tashigo tana jera min abincin ta
gaidani da jiki ta fice a dakin kallona tayi tana fadin ki tashi kici abinci kisha
maganin ki.
Kada mijinki ya dawo ya samu kin fada yace amanan daya ban ke nan na bari kika
koma haka nidai banyi magana ba ta kare ta fita tana jaddada min da inci abinci fa.
Sannu a hankali cikin hiran anty Salma nake ta tsuntar magana wai ashe har kudi
yaya Jafar ya bayar a saya min wasu abubuwan da nake bukata.
Saidai tace kudin suna hannuta don ita dasu mama sun hada min kayan daki komai
daddy yaba da kudi a saya min gwargwadon hali ta kara ta sai min moderate din kayan
kitchen na zamani dasu.
Da anty Salma tasan zancen aurena akan jafar yana daga min hankalu da sam zata
dingayi min zancen ba amma bamu zama bata sako min zancen shi a gabana duk dade
gyarane irin ta yayyu take min a lokacin.
Ina kuma karuwa sosai ga wasu abu da take ban duk da tare muke faman dirka da
ita wani lokaci kuma ni kadai zata ba in shanye tas a gabanta.
Training din rayuwan gidan miji aiko zama tsakanin mama da daddy dole kayi course
sun tsufa amma rayuwansu zakice yarane har yanzu su balle anty salma dake cikin
ganuwan kurciya a lokacin tana shanawa da mijinta.
A cikin hakan muna waya da yar uwata har da mama saidai suyi ta kwantar min da
hankali sam ban tsamaci hakan ga yar uwata ba na dauka zata shiga damuwa fiye dani
sai gashi naga akasin hakan gareta.
Ranan da mama ta kirani tana tambayana jafar ta kashe wayan ta barni da mamakin
ta don dai ban taba tsamanin hakan wajenta ba yadda takeyi min maganan .
Itace fa mai min addua Rahama Allah ya baki miji nagari inda zaki huta kema sai
gashi a yanzu lokaci daya ta sauya min.
Yandace ta kirani take fada min abinda ya faru har mama din tazo ta karbi wayan
wai suna tuhuma Jafar ya daukeni ne mun fita tare dashi shine yasa tazo ta tabbatar
da hakan a kaina.
Bayan ta tambayi Nafisa tace da ita muna waya ina Abuja har yanzu amma hakan
baisa ta yarda ba a yadda nake ji a bakin anty salma zancen tarewana wani satine
insha Allah.
Hakan ya kara saukar min da faduwan gaba ta ina zan fara ina zan kama yaya zanyi
in zauna wanan gida da sunan auren jafar a kaina.
Har wata zuciya tana ban shawara da ingudu in koma garin mu sai na tuna ai can
aka daura min auren alkakan a kaina dole dai na tsurawa sarautan Allah ido.
Sunje Zaria kwana su daya suka dawo saidai kaduna tace min zata ashe zaria sukaje
gyara min daki saida ta dawo tana santin gidan take fada min ai sunje sun yimin
jerene a zaria .
Gaskiya Rahama kinyi sa,a sosai gidan ki ke kadai ba wani hayaniya ko saka idon
da wani zai maki irin ta maria ke kadaice a babban gidan saidai gaskiya gidan nada
girma sosai.
Mun samu ya gyara gidan ya saka komai amma muka saka kayanshi a falonshi Kayanki
da akai maki nan muka gyara maki naki falon hakama daki biyu muka gyara maki sai
muka bar wancan a matsayin turakan maigida.
Ni ba tsayawa saurarenta nakeyi ba ba don duk abinda zata fada ba burgeni yakeyi
ba saukinsa ma yanzu da naji cewa ba a gida daya zan zauna da matansa ba .
Sai abin ya dan min dadi a raina koba komai wanan zullumin da fargaba zai rage
min akan ace muna zaune waje daya dasu.
Nasamu training fiye da zaton ki mai karatu dan zaman da nayi da anty salma ta
bude min ido ta wayar dani banda tsoro ko fargaba a baya har ina jin idan na koma
zaria zamu kwashi yan kallo dasu.
Sai gashi zancen auren nan na yaya Jafar a kaina yanzu ya jawo min cikas ga duk
plan dina nima yanzu dole ta kaina nakeyi yadda zan kasance dasu .
Balle nace zan taya yar uwata danayi niyar tayata zama da fitinansu yanzu kam
nasan a kaina abin zai dawo gaba daya tunda dole in zauna kamar yadda daddy da mama
suka roka a gareni.
Shi kishi ko zaman aure ga ya mace halittane garemu mata wanda bamu san muna da
baiwanshi ba sai in mun gwada.
Haka kawai mace ke tsuntar kanta da iya irin rayuwan data zabawa kanta zatayi dma
gidan miji don haka a bangarena idan na zauna ni kadai abinda nake tunane shine ta
ina zan fara a gidan ?
Da bangaren shi yaya Jafarne ko bangaren matanshi ko kuma bangaren mama da
yaranta duk da nasan banda matsala dasu saida Saare amma yadda anty Nafisa ke fada
min a yanzu mama ta canza sosai game dani.
Nikan an sakani cikin tsaka mai wuya a wanan auren an tauye min rayuwata da yawa
me zangane a wanan gida hakan ya zamo sonkai ga yaya Jafar duk da bansan ainihin
manufanshi na zarga min abinda bai shafeni ba.
KD
Cikinta mahaifiyarta tayi da fada akan ta shirya ta dawo dakinta kafin tayiwa kanta
aikin dana sani haka kawai zaki kwaso kafa kin dawo gida kin zauna don mijinki
kawai ya kara aure ?
Har uwar ta gama batace kalla ba don sai take daukan uwar bata damu da itaba
yasa a kullum take nuna mata ta saita koma haka zikau ba wani magana akan shanmatan
sa Jafar din yai mata.
Saidai Halisa yarta ta shigone suka kebe tana fada mata irin matsin da uwarsu
ke mata akan ta koma zaria din .
Yaya takan fara magananta ke nan fa don me zaki koma zaria Jafar baizo ba ita
bata tsayawa ta kwatowa mutum hakkinsa idan kuma za a kwato mashi ta hana,.
Yanzu dai muje gidan anty Sabi,a muji kota samu aika sakon don nafi bukatan sai
kin rikeshi zaki koma har in zaki koma din ne yar ta fada hakan yasa Nusaiba ta
mike ta shirya suka fita ita da yar uwarta.
Da kafa suka taka zuwa unguwar don ba nisa gidan Sabi,a din da alaman matar
gidan tana da baki don motar da suka gani a kofan gidan.
Sun shiga da sallama suna falo zaune suke amsa masu an fara gaisawa bakuwar
Sabi,a ke fadin waiba Saiba umar bace ?
Nice ta fada tana kallon mai maganan kafin tace sa,ade yakubu ko suka kwashe da
dariya son tun barinsu makaranta rabon da su hadu don haka da murna suka rungume
juna.
Saiba ta kalli Sa,adatu tana fadin wai Sa,ade kece haka kinyi wani fresh dake
kamar wata matar gwauna ?
Murmushi wace aka kira din tayi tana fadin kaji ki dai da wani zance Nusaiba har
yanzu dai halinki yana nan na zolaya ko ?
Wallahi kina inane wai yanzu nusaiba ta kara tambayanta tace ina nan gefe daya
ba kun manta da kowa ba yanzu haba dai ai kema kinsan hakan bai yuyuwa nakan
tambayeki wallahi.
Har yanzu kuna tare da mustapha ko haba dai daram kuwa muna calarba yanzu
kinsan a can yake aikinsa .
Kice min mutumiyar kinyi nisa da garin nan gaskiya na daina jin ki gaba daya
wallahi lalai mustapha ya iya rikon aure kinga yadda kika koma wata babban mace ?
Gaskiya da ganin ki kin samu kan mustaphan nan a hannu Sa,ade murmushin
kasaita tayi tana fadin Saiba ke nan wani samunshi nayi kuma ?
Takai zaune a gefenta tana fadin wallahi sa,ade kin kara hadewa ba irin mu ba
nan ni gani wanan dan iskan zai kasheni wai wata kishiyar kuma ya kara auro muna
yanzu .
Cikin mamaki Sa,ade take kallonta tace saiba kanki daya kuwa da hankalinki kuwa ?
Mijin naki kike zagi da dan iska meye a cikin kara aure don ya kara aure saiba ?
Wai ina labarin Asmy ne har yanzu kuna tare kuwa ta bata rai tana fadin muna nan
tana zaria muna nan muna bugawa da ita.
Murmushi tayi tace kema Nusaiba kinsan ai dole ayi hakan kema kawarki ta kut da
kut fa kika ciwa amana kina tunanen Allah zai barki haka ba jerabawane ?
To amma ai naji ance kuna cikin rufin asirin ku don ina da labarin ku mijin ku
bai rageku da komau ba na rayuwa.
Naga tun haduwan ku kin kwacewa Asmy shi yana kuma yi maki yadda kike so to me
kike bukata kuma ina ruwanki da kara aurensa ?
Wallahi Sa,ade ba zaki gane bane ni yanzu ai nayi nadaman aurenshi uwarshi da yan
uwanshine fa suke juya shi har mu .
Haka basu kaunarmu ko kadan tundai ni basu sona musanman mahaifiyarshi da
kaninshi wai shine yanzu don cin amana kanin nasa yasa ya auri kanwar matarshi fa.
Ni kuma nace bai isa ba wallahi don ubansa sai naga yadda shegiya zata zauna a
gidan nan ?
Umm,umm subbahanallah Nusaiba har yanzu haka kike da wanan halin naki ashe wallahi
gara tun wuri ki bari zaifi.
Ni dai shawarata gaskiya dolene ki sauke wanan girman kan naki da wani jiji da
kai har in kina son gane kan mijiki dole kiyi masa biyayya kamar yadda Allah yace
ki kuma zauna lafiya da abokan zaman ki.
Abincinsa shimfidansa da komai nasa hakama yan uwansa sai kiga kun zauna dashi
lafiya amma idan kikace ba hakaba sai abinda kikaga dama zakiyi kinsan wallahi ko
yar gwal kike ba zaku shirya ba ita Asmau fa da kika sama ?
Na tabbatar ba haka take ba ita saidai yanayin zama dake sauya mutum wani lokaci
don dai zuwa yanzu,,,,
Bari kiji Sa,ade wallahi kinsan tun ba yau ba daga shi har Asmau basu isa su
sake min halina ba don bawani mutuncin da zan tsayayi akan kishiya.
Ke kika dauki wata tsiya wai biyayyan aure irin na matan da da suke wahala akan
aure haka kawai in zauna ana juyani.
Aure kuma nace bai isa ba wallahi kuma wallahi bai isan bane falon yayi tsit
ana sauraronta a lokacin.
Sai Sa,adatun tace waike hanashi auren zakiyi inace sai yaso zai zauna dake dai
tunda ragamar auren yana a hannusa.
Ai sai idan ya raga makine zai barki ki zauna har ki daga mashi hankali dashi da
sauran matan nasa yanzu idan kin tada hankali yace ki bar masa gida fa ?
Gabantane ya fadi sam ta mace zai iya yin hakan ta lamkwashe a waje daya tana
tunane Sa,ade ta kalleta tana murmushi tace wallahi don haka kibi sannu.
Gara kiyiwa kanki fada don namiji zai kara aure zaki tsaya kina wanan daga
hankali haka duk gatan mace yau akace ta koma bazawara an gama dake.
Don haka kibi sannu ku zauna lafiya kibar wanan cika bakin kada zance ya koma a
kunnensa daga gefe halisa yarta tace shi nake fada mata.
Shiyasa na kawota nan wajen anty ta dai dan bata dabarun mu na mata itama tayi
kaddari kada dai ta koma baya a cikin kishiyoyi.
Mafalki ke nan anty Halisa ai in banyi gaba ba babu shegiyar da zata shigo tayi
gaba a wajensa bari dai in koma kawai ki gani.
Haka dai suka zauna suna bata shawara amma a banza don ko daya bata dauka a cikin
shawaran nasu ba lokacin har Saaden tayi masu sallama ta tafi.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

4️⃣1️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Tun bayan wayan ya habu da Jafar inda ya Habu ya fadawa Jafar cewa idan ya gama ya
kamata ya dawo gida don har yakai mama ta tutseye maria ta kira Rahama tana
tambayanta ina kake.
Which means tana zargin cewa kuna tare da Rahama din tunda ana kiran wayanka bai
shiga so kada su takurawa yar mutane da zargi a kanka .
Wai meke damuwan mamane Habu ?
Saida Habu ya dan fura iska a bakon shi yace da dan uwan zargina shine su kawu
da yar iskan yarinyar nan Saratu.
Saratu tana daga cikin wanda suke dagawa mama hankali akan zancen nan son basu
shiri da Rahama tun farko kasani irin halin nan yasa nayi mata duka kwanaki ai.
Ga yar iska taki karatu wai wanan mayaudarin mansur ta kwallafawa rai yanzu ni
kuma nasan mansur bata isheshi kallo ba banda ya yaudareta kawai.
Mansur kuma wani mansur kake nufi yace mansur dai naka mana ai tare suke dashi
haka kawu ni sai yanzu nake tuna abubuwa da dama da mutumin nan yakeyi muna J.
Amma mama bata gane hakan idan anyi magana tace ana son rabata da dan uwanta
tillo sai ta nemi sabawa mutum a kansa.
Ok wanan karon ku barni dashi nida kaina zan dauki mataki a kansa ai ba sai anyi
wani magana dashi ba kawai nasan inda zan kamashi.
Ka kyale kowa banson ka fadi wani zance daya shafi auren nan nawa don Allah Habu
ka barsu duk abinda za a fada suyi ta fada a kaina.
Kudi kuma na shirya tsab ranan da duk na dawo washegari in Allah ya yarda zan
gabatar masu da kudin don haka ka lalabasu har in dawo don Allah.
Ok zaka dawo kwanan ke nan ?
Ehh saboda karatun yarinyar nan Rahama banson karatunta ya tsaya sun kirani
sunzo sun gyara gidan sun saka mata abinda babu .
Maria ta kirani tans fada min mutanen suyi masu kokari sosai sai godiyan Allah
gaskiya mutanen arziki Allah ya hadasu dasu ba kowane zai rike amana haka ba ?
Ya halakansu yake dasune Jafar ya tambayi kanin nasa yake fadi just mahaifinsune
yayi aiki a karkashin Alh har ya rasu shi kuma tun yana raye Alh ya rikesu tankar
yan uwanshi shine har yanzu suke halaka bayan ranshi.
Kai Habu na dauka ai yan uwansu na jinine wallahi a,a fa kawai haduwan jinine duk
da halakan ai ta zama ta jini yanzu ido ya lumshe yana raya abubuwa a zuciyan shi.
Don sam bai taba zaton cewa ba halaka tajini bane tsakanin mu dasu ya dai dauka
akwai zumuncin da muka rike akansu suma suka rikemu din.
Sun dan kara tataunawa kan wani zancen kafin suyi sallama su kashe wayan kowa
da irin abin dake cikin zuciyan shi a lokacin .

ABUJA

Ni mamaki nakeyi yadda anty salma take faman rawan kai a kaina haka sai kudi take
kashi ga gyaran jiki da sauransu duk saboda zancen tarewana wanda nake sa rai bai
wuce karshen satin nan da za a shiga.
Duk da naji tana waya bayan mama tayi min buki a nan Abuja sai a koma can kaduna
kuma ummah ta hada min walima daga can za a kaini gidan miji .
Tankar ban wajen a lokacin saida ta gama wayantane ta kallo tana fadin waike
haka zakita zama da angon nakine ba magana ?
Shirun kifa ya fara ban


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login