Showing 306001 words to 309000 words out of 328222 words

Chapter 103 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

daya
shafi J din saboda zuciya.
Tunda ya bar gidan yake zirga zirgan neman kudin tafiya don dan kudin wajensa
daya tsira dasu lokacin ya saka a wani aikin kuma don dai a samu a karu din kada
akai kasa warwas.
Saiga Allah yayi ikonsa kayan sun fito ba abinda ya samesu yayi sadaka ya godewa
Allah yayi hamdallah har yamma basu da labari don ko mama bai fadawa abinda ke nan
ba.
Saida Aminu yaje gidan take samun labari da yake fadin wanan haihuwan maman
zaria ya jawowa uncle alheri ta juyo tana kallon yaron shekeke don jin furucinsa.
Amma kai yarone wani yaro yazo a sa,a yaron da zuwanshi duk ba alheri a cikinsa
sai tsiya Jafaru dake cikin walwala auren yarinyar nan da samun cikinta ya zamowa
mutane tsiya yanzu a gida.
Don baka san yadda muke bane a baya kama sani ai kana zuwa kana gani ko bakazo ba
uwarka daku kuna gani a tallen ku yanzu fa wakeci banda ita, ? itama din yanzu ina
ma ya gansa balle waninta yaci din ?
Amma dai tsohuwar nan uncle da dukiyansa ya fito zaki tsaya kina fadan hakan ya
fito gidan ubanka mama ta jefawa yaron zagi.
Haba mama wanan abinda kike fadi kan jaririn nan wallahi bai dace ba shi yaro ai
Allah kadai yasan arzikinsa sai masu hassashe ke fara fahintar arzikin yaro tun
yana karami.
Amma kina fadan hakan iyayyensa sukaji ba zasuji dadi ba wallahi haba dai don
Allah mama salima ke fadan hakan ga uwar tasu.
Mummy wa zai tsaya saurarenta ma yaron da uncle ya bude baki ya kirashi da
arziki sanadin haihuwanshi dukiyan uncle ya fito jiya kowa na murna da farin ciki
ke kina kirawa yaro mugun abu ?
Wai tsaya Aminu me kake fadine mama fa bata gane ba naji kamar kana son fada
mata wani magana ita kuma bata gane hakan ba sai fada takeyi.
Ai shine mummy jaki brain kega tsohuwar nan no school kayan uncle da suka bace a
can kasan waje sune aka kirashin angani kowa na murna da farin ciki ita tana kirawa
yaro tsiya.
Gashi har anata zuwa mashi murna ana kiran yaro da arziki ke kuma kina nan kina
zuba shirmen tsufa a gida baki gane ba kanin mu arzikine babba sanadinsa yazo muna
da alheri.
Aminun ta kurawa ido tana sauraren bayanin shi don a yanzu ta fahinci me yaron
yake fada mata ga katobaran datayi game da yaron kala kala laifin uwarshi ya shafi
dan jinjirin da baiji bai gani ba a duniya.
Allahu Akbar kai Aminu kace min alherin Allah ya sauka muna a gida lalai wanan
yaron arzikine tunda alheri ya baibayemu a yau.
Salima ke fada cikin jin dadi tana nuna farinciki nisawa mai karfi mama tayi
tana fadin lalai da ya zamo arziki kwana uku da haihuwanshi alheri yazowa
mahaifinshi.
Kai kuma duk kai min karya kam abuda bashi ba saina saba maka a gidan nan ta
yaya abu irin haka zai samu amma mu bamu sani ba saikai zaka jiyo kazo fada muna
shi.
Shi yana fadin a,a ni banzo fada maki ba cewa nayi kanina arzkine don zuwamshi
duniya alherine a garemu tunda ga irin hasken da muka gani a sanadinshi kai, arrrh
mamata ta katseshi da fadan hakan.
Salima kuma tace mama ai dole yace haka tunda yaga baki san alherin da ya samu
ba amma ai tunda,zun yake zaune gidan nan bai fada ba.
Tayi shiru na dan lokaci ta nisa take fadin abinda ban gane ba shine kudine masu
yawa ya samu ko kuma wani aikine ya samu a kasan wajen ?
Ban fada ba don ban sani ba nidai naga mutane suna zuwa kuma naji ana murna a
gidanmu din nasan kuma alherine insha Allah.
Ni baein tafi karki matsa min da tambaya ace kuma nice ba ruwana ban fadi komai
ba tayi mai dakuwa ya fita yana dariya salima tasa mai kira ya dawo take fadin gida
zaije ko wani waje a lokacin.
Yake fada mata ba gida zaije ba tudun wada ya nufa yanzu mama ta aikeshi ya bada
kudin abincin dabbobinta can ya nufa.
Har yakai kofa yaji mama na fadin can kuma ka koma kaima ana kullawa dakai yanzu
na fara tsoronka a rayuwata.
Ya fita yana dariya baice da ita komai ba bai jima da fita ba yaya ya shigo ya
samesu a waje suna magana mama na tambayan su abin arzikin meya samu Nusaiba tace
bata da labari bayan wanan haihuwan wahalan da akai mashi.
Haba dai haihuwar kuma itace wahala Asmau ta fada cikin nuna mamakin jin hakan a
fili Nusaiban tace ban daiyi dake ba don Allah don ai nima bance kinyi dani ba
kalman takice dai ke bukatan gyara gaskiya.
Naga kowa na haihuwansa ai ba wanda aka aibantawa sai ita da babu ko ruwanta da
kowa batama saka kanta a cikin duk abinda akeyi gidan nan ba.
Kai ku rufa min baki don Allah ku wasu irin marasa hankaline wai baku da kishin
juna saina abin banza ana maku kokari mijinku ya dawo hannun ku.
Amma kuda baku raina abin fada nazo ina tambayan akan abinda da naji game da
mijinku kun tsaya kuna min shirme yanzu .
Yanzufa yaron nan Aminu yake fada min ta kwashe abinda sukayi da Aminu din ta
fada masu abinda Aminun ya fada saida ta kai karshe Asmau tace gaskiyane dazun naji
yana waya da yake cin abinci saidai ban kula dameya faru ba.
To kunji abinda ke nan Saiba ta tareta da fadin yanzu shine bai iya fada muna ba
koke mama saidai Aminu yaji a wajen wacan yarinyar yazo nan ya fada.
Ke nan mu dai duk bamu da amfani yanzu idonsa gaba daya ya rufe akan wanan
yarinyar ita kadai yake dauka a matsayin mace ke nan ?
Har yana kiran danshi da arziki ko mu ke nan namu yayan ba arziki suke ba
shiyasa bai damu dasu ba ko sai yanzune aka haifa mai dan gwal.
To ni dai banga wani abu cikin zancen nan ba tunda abin nan in an samu kowa zai
amfana dashi ai Asmau take fada ta juya zuwa kitchen duba girkinta lokacin ya shigo
ya samu mama da saiba din a tsaye.
Kallo daya yai masu ya fahinci wani abu na faruwa ya dai bude baki yana fadin
sannu da gida mama lafiya dai na ganku haka tsaye.
Ai dole ka ganmu nan Malam tunda har alheri na iya samunka ka boye muna saidai
muji a wajen wace ka maryar mata yanzu ?
Menene kuma akayi mama yake tambayanta cikin mamaki tace yanzun har wani abu
zai iya samunka sai dai inji ga ahanun talla Malam ?
Yaron nan Aminu yazo yake fada min wani zance dazun shine abin yake ban mamaki
nake zance da matanka ko sun sani ?
Meya fada maki kuma zancen wai wani aiki ko kaya yake fadi ni bam dai gane
zamcen ba gaskiya don kasan haka yake kamar shu,umi wani lokaci.
A,a mama yake dai gyara maki zance amma ai Aminu bai zo don ya fada maki maganan
ba da kike irin maganganunkine fa yace shi kam kanninsa arziki aka haifan masu yake
kora maki maganan salima ce data fito a cikin shiri ta samu suna zancen take fadin
haka.
Wai zancen kayana eeh anga kayana da akace sun bace wani abokina ya rike a
wajensa dama kada su salwanta shine yanzu da yaji naji sauki ya fito min dasu ya
kirani.
Yanzu na gama shiri gobe nake son zuwa cika wasu bayanai don ina son inbi kayan
idan angama sha,anin sunan nan da za ayi.
Haba malam zancen nan baiyi ba badon yaron nan ba kilama ba zamuji ba ina zai
fada kuwa mama tunda ba dole bane sai mun sani ai ba dai wa yanda yake son su sani
sun sani ba.
Ashe kin gane nufina wanda zasuyi min addua da fatan alheri suna fadawa don
nasan ko banza suna farin ciki da samuna ko rashi.
Zata fara masa haushi ya dakatar da ita da fadin kina sake fadin tak wajen sai
kin bar gida bari na har abada kuwa in kuma kin dauka karya nakeyi ki tanka a yanzu
din ?
Shiru tayi tana mazurai da ido ta kasa magana ya juya ya dubi mama kamar zsiyi
magana sai kuma ya fasa ya shige ciki zuwa dakinsa.
Barshi kada ki tanka mashi don baya cikin hankalinsa yanzu komai yana iya faru
dama haka akeso to ki kyaleshi.
Salima ta kawar da zancen da fadin mama ni zan je kasuwa in dubu wani yadi da
nakeso bata bata amsa ba ta juya ta tafi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/9, 06:52] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

9️⃣5️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Yar uwa saidai ince Alhamdullahi masha Allah don abubuwa sun kankama cikin dan
kankanin lokaci abinda ake fatan samu a rayuwa an sameshi don kuwa tafiyan nan da
yaya ya samu yayi ba karamin alheri ya jawowa rayuwan mu ba sosai mussanman mashi
dani.
Don abinda yasa nace ni anyi sunan moh,d a cikin walwala da dadin rai anci ansha
anyi alheri kuma baby ya samu alheri wanda zance a sanadinsa na samu hakan .
Ubangiji Allah ya tsallakeni daga kaidin mama hassada ko bakin cikine ko kiyayya
da ake min kasancewa da yaya ya zamo min taki a rayuwa lokacin haihuwan dan nan.
Don ba karamin alheri na samu ba ga haihuwan dan da mama da kishiya suka sare
min gwiwa tun a cikinsa ba abinda na samune farin cikina ba sai irin yadda kowa ya
dauki dan zai furta masha Allah wanan photocopy ne kawai na Jafar da mutane ke
furta a bakinsu don dan tun yana karami ubansane sak ya kwaso a kamanninsa.
Ga kyauta ta inda ban zata ba da yake shigo mun in kuma an kawo din uban yace a
ban nice na wahala ai na rike ba kamar yadda muka soma zaman asibiti ba a takure
yana karba din a lokacin.
Ni dai banda tacewa ina zaune mama ke fada min na dauki duk wani abinda zan dauka
don ba a nan za ayi taron suna ba can gida zamu tafi ayi taron don mama tace mu
dawo nan ayi taro a gabanta.
Don haka tun daren suna muka dawo nan gidasu inda matanshi dasu iya da mama suke
zama a gaban mama a part din iya muka zauna.
Na samu salima ta gyara wajen tsab tsohon dakina a nan akai min masauki dani
dasu mama da Biba tun kan muzo saida mama ta gargadeni akam koma meye manufar mama
in daure inyi hakkuri kada in nuna hakan ya bata min rai don Allah.
Nidai kawai murmushi nayi bance komai ba tunda gidan ba bako na bane ai duk wani
abu da nasan cewa zan bukata a lokacin na dauki ba saj na tsaya nema ba a nan din.
Don haka koda ya iso a nan ya samemu don tun yana can ta kirashi ta gaya mashi
umurninta haka yasa daya iso ya nufo nan din ashe saida ya biya can ya aje duk wani
abu da baison ya kawo masa fitina kafin ya iso nan din ya samemu don tunda ya tafi
bai dawi ba sai a daren sunan komai a waya aka shirya yadda za ayisa a taron dashi.
Ina zaune ina bawa yaro nono mama tana zaune kasa tana cin abinci muna hira
mukaji muryanshi suna gaisawa da iya a falo ya gama ya shigo suka fara gaisawa da
mama har yake tambayanta ba dai matsalan komai ko a nan ?
Ai ba a rasaba yanzu dai ai gashi an kwaso mata maijegon an kawo mata bari muga
iya gudunta kuma dubu kam lamarinta sai addu,a gaskiya.
Kibar yarinyar nan ta zauna dakinta ayi suna kin kafe sai ta dawo gudan nan
agabanki nan ayi komai ko anyi nan gabata zata iya hana komaine ni ban sani ba ?
Ba komai iya gara da aka dawo din nan zaifi sakewama don can karshe a bata mata
kayanta da sauran abubuwa ba daida anyi suna gobe saita koma ba ?
Akace maka nifa nasan dubu nasanta sarai yanzu zata iya cewa kuma sai a bari har
wani lokaci sam iya hakan ya zama takurawa ai idan anyi suna su koma can kawai
zaifi nan banda tsegumi me zata zaunayi kuma ?
Daga kofa mama data mike ta fita ta saka masu baki tana fadin tunda anyi suna me
kuma za a tsayayi nan kuma ta koma dakinta kawai mana tunda ba wani wanka irin na
da can yaran yanzu keyi ba ai.
Shina gani mama an daice sai tazo nan anyi suna tunda nan kowa yake anzo gobe
da yamma idan an watse zan mayar dasu gida insha Allahu.
Ya gama dasu ya shigo muka gaisa nan yake tambayan lafiyan mu dana yaro nace
Alhamdullahi ba inda ke maki ciwo kuma yanzu ko ya tambaya nace naji sauki sosai
ai.
An kawo dinkunan naki nace ehh tun jiya anty salma ta ba driver Aminu ya karbo a
gareji good ina hanya na tuna wallahi na sake fadan ankawo ai.
Ya dan tsaya mukai hira kafin yai muna saida safe ya fita don gidan akwai baki
da zasu kwana ga yaya barakha da sukazo daga zamfara ita da kawarta.
Wai dan shigan da yayi ya jima hakan ashe ya zamo laifi kuma wai anshiga hakkin
madam Saiba saida sukai fadan hakan a cikin daren nam dashi yayi mata tas .
Don harda cewa tayi ana tauyesu ana nuna masu banbamci ga komai yazoyi saiya
nuna bambamci a kaina ya fifitani dasu don me zai yanka saniya a hada wajen bukin.
Nan yace koda sunan Buhari ban yanka shanu ba ko wanan ne zakiwa bakinciki kuma
koka yanka ai baikai wanan girma ba yake fadin.
Ooh ashe ke diyar sarkin fawane ban sani ba har kin fita kin duba shanun kinga
wanan yafi girma ko to komai da sa,anshi yake zuwa ina dashine yasa na sayi babba.
Ai Allah yana ganinka duk zaluncin da kakeyi da fifitata akan shi kuma zai saka
muna wallahi tunda haihuwa ai baifi haihuwa ba ?
Wanan yakawo masu fada sosai ya gama ya shige dakinshi don akwai gajiya a jikin
yasa ya rufo dakin da key ya kwanta bayan ya gama komai don ko abinci ita mai fadan
bata aje mashi ba.
Koda ta fahinci ya kargame kofan dakinsa hakan ya kara bankata mata rai kuma
dakyat taga safiya a ranan ba abinda ke damun ta banda irin yadda labari yazo masu
cewa katon shanun da jafaru ya yanka a shagalin.
Akan shagalin sunan da sukaiwa ikirari da farko haihun rashi saiga ubangiji ya
sauya abin a lokaci gashi yaya Auwalne jagoran abin ba wanda ya isa ya kawo mai
raini akan zancen aikin da akeyi din.
Kamar yadda jafar yace ayi da naman hakan akayi kowa don an rabawa yan unguwansu
makwabta na kusa dasu sadaka kana ya aika gida gida dukka tan uwa dake cikin gari
asa albarka.
Kafin abinda ya rage ya aiko da wanda zayi aikin shagalin dashi nan gidan mama
sai abin ya bakantawa mama rai sosai don me Auwal yayi bugun gaba da abin danta
haka bayan gasu ga tan uwasa zai shige masu gaba.
Allah ya taimaka yaya barakha ta iso lokacin ita ke fadin mamanmu yaya Auwal
nefa wallahi kina cewa wani abu yanzun nan duniya zatajiku dashi.
Gara ki kama bakinki tunda shine a matsayin babanmu a yanzu shine babba kowa na
bashi girman shi yau don danki ya yanka shanu yaya Auwal ya raba zakice baki yarda
ba da hukuncinshi.
Aishi jafar yasan me yakeyi da yake sakasu gaba a komai nasa mutanen nan duk da
yan ubanci da adawan da suke nunawa a garemu basu yarda sun nuna cewa muba yan
uwansu bane.
Komai namu ya tashi suna gaba sunayj gwargwado yadda duk wani dan uwa zai tsaya
yayima a cikin gata tanzu akan wanan abin saiki nuna ke baki yarda ba.
Ke kuma Nusaiba zan fada maki wani magana da baki sani ba akan yan uwanmu uban mu
daya dasu dukkan mu kuma a tare kika zo kika samemu muna zumuncin mu.
Har idan ba zakiba mama shawaran alheri akansu ba to don Allah ina tokonki da
kiyi shiru ki daina kawo mata tsegumi tunda kinsan tana daukan zancenki kada ki
hadamu fada da yan uwan mu don Allah ?
Ubanmu ya mutu ya barmu a tare dasu kada kiyi sanafin raba wanan zumuncin namu
don kin zama mai yukan yanke zumunta ke ?
Nina gane a yanzu tunda kika shigo gidan nan lamarin mama ga baki daya ya sauya
wallahi a,a anty barakha kada kiga laifina mana don Allah ?
Kafa biyu da kayan ciki fa aka kawo gidan nan ba dole inyi magana ba ace an
yanke shanu wanan kadai za a kawo muna ayi komai dashi ?
Kuyi amfani da iya abinda kuka gani mana wai tsaya ma in tambayeki kokin manta
da bakece mai haihuwan ba waib?
Don ita data sha wahala ta haifi danta inma korafi itace ya kamata ace ta fito
tayi wanan tsegumin baku dai da yunwan wani nama ko wani dangin abinci a cikin
gidan nan to ki bari


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login